Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
dauri zan fita ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya ya
mike ya fito falon shima ledan na hango saman center table din falon na nufi wajen ledan har na duka
zan bude kuma na dago zuwa kitchen na dauko plate da su knife da ruwan wanke hannu irin wanan
sallon mazan nasanshi a gidan anty sallama ai.
Na samu ya zauna ya baje saman kujera irin zaman a bude kafa din nan ya dafe goshinshi da hannu
dayan shi yana murzawa.
Na duka na fara kiciniyar budan ledan naga take away irin wanda kake iya hango abinda ke cikin roban
da alama dai kamar ganyece da wasu tarkace haka.
Saidana bude naga rabin kazace da ganye da aka gyara yaji hadin turawa sai dan shinkafa manne a gefe
daya ko wani roba haka yake da abin.
Dayan ledan na jawo dake ta maiko da kamshi kayan cikin ragone a cikinsa mai yawa sai kamshi yakeyi
anyi mai irin gashin zamani din nan dayan kuma shima dai namance ta rago gassassa a cikinsa yaji su
albasa da kabeji da kayan kamshi.
Saidana gama hada komai yadda ya dace na dago kai na kalleshi ina fadin bissimillah yaya sai naga ashe
duk hankalinsa yana kaina shima a lokacin.
Sai naji yace ki zauna tare zamuci ai dake nasan bakici komai ba na noke kai cikin kunya ina fadin idan
ka gama zanje daki inci ai.
No no wai kunyata kike jine yana magana yasa hannusa daya ya jawoni zuwa jikinshi ya zaunar dani
saman cinyarshi.
Noke noke na farayi ina kokarin zullewa don hakan da yayi min din bakon abune tunda ban saba hurda
da namiji ba haka ko yan uwanmu maza ba tare muke rayuwa ba a rugga yunda su suna yawon cinrani.
Kokarin kaimin a bakina yake a dole saina karba na dai karbi na farko amma taunawa na kasa hadewa a
gabanshi ga idon daya tsura min wanda yasa na fara kwarewa lokaci guda.
Ruwa ya miko min na dan kurba bai duk da haka bai yadda ya sakeni ba a rikon da yayi min dole ba
sarki sai Allah na biye mashi ina karba a kunyace ina hadiyewa a cikin kunya.
Saida yaga na koshi ya barni na koma gefe ina kallonshi yadda yake cin abincin ya tabbatar min daba
karamin yunwa yake ji ba lokacin.
Ya gama na kwashe kayan zuwa kitchen na dauraye na fito har lokacin yana zaune yana waya a wajen
dana barshi daki na nufa harya gama wayan nasa ashe barci ya daukeni.
Har ya gama ya shigo dakin ban sani ba a cikin barci naji ana tabani hakan yasa na dan yi niyar dagawa
sai naji ya matseni a jikinsa yana wasu maganganun da na kasa iya tantancesu a lokacin.
Ga kasa daya dora a kafadana ya sakarmin nauyinsa ban gama mamakin hakan ba naji yana sumbatar
wuyana hakan jikinane ya fara rawa lokaci guda.
Abinda ya kara dumatani jin wasan yau bambanta dana dareb jiyan da yake min yafi na daren jiyan don
ya bambanta da wasan da zan tsaya fada da baki a nan.
Sai karfe shida da rabi ya samu sallah safe balleni da saida nayi da gaske na iya lalabawa zuwa bandaki
na tsabtace jikina.
Ga zuciyana da tayi min wani irin nauyi da ba zance ga daliliba don nasan wani abu daga rayuwata ya
tafi ke nan sabon rayuwa yazo min a yanzu duba ga yadda bani samun natsuwan barci a dan tsakanin
nan.
Har na idar da sallah na samu na mike na gyara gadon na sauya shimfida da kyar na koma na kwanta
don zazzabin da nake jin yana son kamani a lokacin.
Hakan yasa ina gamawa na koma na kwanta da niyar gari ya dan kara wayewa in daure in fito kitchen
ashe barci ya daukeni mai nauyi irin barcin wahala din nan bana dadi ba dai kam.
Sau biyu yana shigowa dakin yana samu ina barci gashi ko karyawa banyi ba ga abin kari dsyasa yaya
Habu yazo muna dashi tun safe.
Har yazo suka dan zauna kan zancensu da mama ban samu ganawa dashi ba a lokacin yaso ya ganni mu
gaisa koda yaya ya duba mashini har lokacin ina kwance jikina yai zafi kuma ban falkaba balle insha
magani.
Har yaya Habu din ya tafi shima ya mike zuwa dakinshi yayi wanka ya dawo nawa dakin still ina
kwance a takure ina barcin .
Ya tsaya ya kura min ido na dan lokaci kafin ya kai hannusa a saman jikina yana taba temperature dina
yaji jikin ya gashe sosai a lokacin.
A dimauce ya fara kiran sunana a hankali hakan yasa na bude idanuwana a cikon nauyin barci na sauke
a kansa yana zaune gab dani ya dan rankwafo jikinsa zuwa nawa yake fadin.
Rahama baki da lafiyane haka har sosai shine baki fada min ba muje asibiti ?
Idona dake lumshe na kara dan budewa ina fadin idan nasha Panadol zan warke basai naje asibiti ba..
No tashi dai muje kiga doctor zaifi ga jikinki yayi zafi haka kice in barki a gida ?
Bari nasha magani idan bai bari ba sai muje asibitin na fada ina kokarin mikewa cikin karfin hali.
Ina zakijene wai na bashi amsa da magani zan dauko a jakkata ina jakar take ya tambaya yana kallona
don duk maganan da mukeyi dashi tun shigowan shi idona a runtse yake na kasa hada ido dashi.
Gaban mirro yaje inda na nuna ya dauko maganin da goran ruwa ya dawo yana mika min dakyat na
dago kai zan karba a cikin kunya.
Yake fadin toki bude ido mana ki karba ya zauna gab dani jikin mu yana gugan na juna dashi na sakeyin
kasa da kaina.
Murmushi naji yayi yana fadin Ok har yanzu kunyane to bari na sake fitar da kunyan taki donki daina jin
nauyina gaba daya don naga kamar da sauran ki har yanzu.
Da sauri na kalloshi wanan karon ina fadin wallahi ba haka bane kawai ba zan iya bane nayi kokarin
komawa saman gado don yanayin jikina.
Yayi murmushi yana dafa goshina ya bare maganin ya bani nasha ya mike yana fadin ina zuwa falo ya
fita ya hado min tea mai kauri ya kawo min saida ya tsureni nasha ya fita da kofin na koma na kwanta.
Barci na koma ban falkaba sai wajajen sha biyu da rabi har lokacin yana gida ranan bai fita ba shima
barci yayi ya rufe gidan don duk wanda yazo ya koma ya umurci maigadin daya rufe gidan kada ya
budewa kowa.
Jin motsin falkawana na shiga bandaki yasashi bude idonshi daga kwancen da yake yana barci a gefena
kafin na fito na samu ya kunna wayanshi daya kashe.
Don tunda zai kwanta ya kashe wayan don kada a dameshi barin maganan da yakeyi da wanda yake
wayan yayi ya dago yana fadin to ya jikin naji zazzabin naki ya sauka tun dazun ?
Da sauki na bashi amsa ina zama bakin mirro na don shafa mai saboda na tsaya nayi wanka a bayin
kafin in fito.
Ya mike zaune da wayan saidaya gama ya tako zuwa inda nake ya karbi man ya fara shafa min a hankali
na lumshe idona a cikin kunyarsa.
Saida yazo daidai kirjina sallpn da yake murza min man yasa na bude idona na kalleshi ta cikin mirro ido
ya kashe min ta cikin mirro yana fadin in daina aikinane fa ?
Dariya ya bani da yasa na danyi murmushi a fili nace nagode yayi hakana ai shafa man ya isa malam.
Aikinane wanan don haka babu godiya abarni nayi da kyau nayi kasa da kaina kawai saida ya gama don
kanshi yakai min kiss a goshi yana fadin bari na dan watsa ruwa nima tunda naga kinji sauki ya fita daga
dakin zuwa nasa.
Saiba dake zaune tana cika tana batsewa don haka ta kwanta takuma tashi a hakan ga kuma wani bakin
cikin daya kara izo mata .
Don tun safe bai shigo gidan ba har wanan lokacin haka yasa ta mike zuwa falo a cikon fushi ta samu
Asmau da yaran suna cin indomie a plate daya.
Ta zauna tana jan tsuki Asmau ta dago kai tana fadin kin tashi ke nan ta wani kallota tana fadin aiba
barci nakeyi ba dama.
Wai kinga dan iskan mutumin nan har yanzu bai leko gidan nan ba tunda ya aje dabbobi a gida yoko
dabbobi ma muke ai ya bamu kulawa gari ya waye haka har daya da wani abu ?
Asmau tace wa,kenan fa ?
Ta yo mata kallo mai kama da harara tana fadin J mana don ranan bai samu sweet J din ba a bakinta sai
J data kirashi dashi cikin hasala.
Keko dai amaryace fa dashi Nusaiba yana can yana soyayyewa tukun ai dolesa dai ya lekomu dama don
ya huta ya ki kawota nan cikin mu ya kebeta daban ai.
Wata amarya har ina amaryan take abu haka kamar kara shi yaga mutum har yaje zubar da mutuncinsa
akan wanan yarinyar.
Ni wallahi ba zan dauki hakan ba shima ya sani akan wanan yarinyar ya dinga nuna mu bakomai bane
itace mutum mu tashi tun safe yaki ko bugo waya ya tambayi lafiyan mu dana yaran nan ?
Ruwa Asmau ta dauka tana bawa yar wajen Nusaiban ba tare data kula da abinda saiba ke fadi ba sai
abincinsu sukeci da yaran.
Taja tsuki ta rarumi wayarta dake gefe tana fadin wai don iskanci harda kashe wayoyinsa tun safe nake
gwada kiransa ana cewa wayan yana kashe.
To aina fada maki baki yardaba ke nan da zancena amarcifa yake sha ai dole ya kashe wayansa bakiji
ance amarya kona kara bace amaryace balle wanan yar filoce fa.
Koba hura sai asha nono don dara dara surbajo ce yana can ana gigitashi da abin na amare.
Kiran ya shiga yayinda take watsawa asmau wani harara da take dauka sakarai bata san ciwon kanta ba
ita kan taji ya dauki wayan ba bata lokaci tace dashi.
Malam dabbobin daka aje a gida ba kulawa suna bukatan ka anan kan wanan sakaran yarinyar har zaka
nemi ka wullakantamu kaki shigowa tun safe wajen mu ?
Ohh Saiba Allah ko gari ya waye ashe shaf na shagala an rudani bansan har gari ya waye hakaba ai
wallahi ashe kuna son ganina ?
Na dauka baku da bukatana ai yasa na shagala a inda akasan muhinmancina namji mutumin dake
gudun ka yake kyamarka kada ka shafa mai ciwo ya naka a yanzu ya samu wanda bai kyamarshi me kike
gani ke nan zaiyi a yanzu ?
Yar iska sallon yaudaran datazo ma dashi ke nan dama yasa akai munafuci aka koramu gida don a
samu shige maka wallahi mu zubo dani da itace a gidan nan.
Zakizo nan ke nan inda muke Ok fine sai kinzo din ai gara kizo kiga inda aka san zafina da darajana zaifi
ta kashe wayan a cikin takaici da kunnan rai.
Kinji ko meyana fada maki a yanzu yana cikin gigin amarci komai yana iya fadawa mutum idan yai
magana dama kyaleshi kikayi .
Tunda duk tsiyarsa dai baikai dare bai lekomu ba nan don haka meye zai damu mutum akansu yanzu.
Taja tsuki ta mike tsaya zuwa dakinta har ta zauna kuma ta fito saigani Asmau tayi ta fita ta girgiza kai
tana murmushi tana fadi a fili wahalala kawai ba dadi ashe ?
Tasan dai ba fita zatayi ba a yadda ta fita don ko mayafi bata dauka ba don haka kila cikin gida zata tace
ai cin tuwon kishiya rankone.
Nusaiba kuma part din iya ta shiga ta samesu zaune dasu anty baraka suna hira iya ina mama take
keya baraka ta bata amsa taja ta tsaya saiga habu ya shigo yana fadin.
Ina mama karfe hudu mutanen nan zasu shigo a zauna na kira J yace dani zai shigo kafin lokacin yau
hutu yakeyi yasa bai shigo ba.
Ai dole ya huta yau angone fa balle jafaru da bai samun hutu kullum a uzurce yake da tsabga baida
lokacin kansa balle na wani.
Yanzu ko dole yabawa amarya hakkinta ai ya zauna tare da ita na dan lokaci su huta tare itama akwai
gajiyan buki a tare da ita iya ke fadan hakan cikin rashin damuwa da saiba na wajen lokacin.
Balle yau Rahaman bata jin dadi tun safe ya kirani na kawo masu abin kari daga nan nakai masu har na
fito bata san nashiga ba tana kwance.
Kai masha Allah kace abu yayi kyau haka yar albarka kenan haka muke son ji ko yaushe Allah ya shirya
muna yayan mu a tafarkin addinin musulunci ga baki daya abu yayi kyau wallahi sosai.
Ba a kawo amarya washe gari ka ganta kwashi kwashi da idanu ba kunya ba tsoron Allah tana rawan kai
da guloto sakarai bata san mutane na mata kallon banza bane sun dauka hakan wayewane yanzu banda
sakarci.
Dariya habu yayi ya juya zai fita mama ta fito tana fadin Habu naji muryanka ina bandaki ya juyo yana
fadin ehh mama dama zancen malaman nan da zasuzone nazo fada maku da karfe hudu sukace zasuzo
yau.
Don tsabga garesu saida J ya kirasu dazun da naje wajensa shine sukace zasu shigo da karfe hudu din in
sha Allah.
Yanzu fa nake tunanesa na dauka yayi tafiyane ai banga ya shigo gidan nan ba yau yana nan mama yana
hutawane kawai zai shigo anjima.
Yana dai jinya zakace anty baraka ta fada tana dariya mama dubu tace jinya kuma jinyarwa shidai habu
ya fita yana dariya sai anty baraka ke fadin amaryansa mana.
Itace wai yau ba lafiya saida shi habu yakai masu abinci dazun toooow Allah ya sauwaka tun yanzu an
fara ciwo kuma haka ?
Kaiya banda abinki dubu kaji ance amarya ba lafiya a daren farko ai kasan meya gudana kuma haba dai
kina magana haka ba lissafi kuma dai ?
To iya me kuma nace Allah ya sauwaka yakai yan baya ga danshinta mama dubu ta fada tana zama
saiba ta juya kawai ta fita daga part din ba tare dayi maganan daya kawota ba.
Munafuncin banza da wofi Allah iya nan idan batayi hankali dani ba wata rana saina faceta a gidan
nan .
Iya din Asmau dake kishingide ta dago tana fadi tace kada ki soma gangancin hakan ga iya don wallahi
ba zakiji dadinsu ba kaf dinsu idan kika taba iya ko mama gidan nan.
Kansu fa a hade yake jallone da mufinsa idan kin kula da tafiyan mutanen gidan nan daya bayayi saida
dan uwansa .
Kaf dinsu yaya J shike juyasu gidan nan kin taba iya donshi zasu kyaleki kike zato ki dai tsaya akansa
shidaya munanana maki a yanzu.
Tsuki taja ta mike zuwa daki a cikin wani irin jin haushin kowa a gidan don ba wanda ya damu da halin
da J din keson nunawa akansu yanzu itako ba zata yarda da hakan ba.
Don wanan yar fillon me zubin mayu daya dauko zai nuna su ba matane ko me gaskiya hakan ma ba zai
sabu ba wallahi.
Sai karfe biyu da rabi ya shigo gidan duk da sunga anshigo da wasu kaya sun san shine ya shigo gidan
amma bai zo part din ba tukun.
Asmau dake falo kwance tana wayane ita kuma saiba na kitchen tana hada abinda zasuci maigadi ya
shigo da kayan ko kallon kayan batayi ba inda ya aje ya fita a kofan kitchen din.
Saida Asmau ta shiga kitchen din take fadin au baki dauke kayan nan ba ina ganin yaya yazo dasu fa
kayan miyane nasan aka sayo ta duka tana bude buhun kayan.
Su kayan gwarine da nama mai yawa sai mai gallon biyu a gefe aje da kwalin taliya dana indomie
zasukai shida duk a kofan kitchen maigadin ya zubesu wajen.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/16, 10:18 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Saida ya gaisa dasu iya tagama sakamai albarka ya juya wajen mama yana tambaya suna dai lafiya ko ?
Ido ta zuba mai tana hango annuri da annashuwa a tare da dan nata da hakan ke nuna yana cikin
walwala sosai a lokacin saidai har yanzu tana jin zafinsa a ranta wanda ba zatace ga dalili ba.
Ita dai abinda tafi dauka shine yayi aure bada izininta ba ya nuna bata da tacewa gareshi ya isa yanzu
bai bukatan shawaranta a yanzu.
Inkin debe wanan ba zatace ga abinda da dan nata yayi mata ba da zata fada don Jafar shine na daya a
kaf iyalinta dake mata biyayya.
Zata iya fassara wanan abin da jin zafin abinda yaiwa matanshi na cin fuska don zata kira wanan auren
da sunan cin fuska a wajensu yayi aure ba tare da sanin kowa a cikinsu ba inbada kawu da yaiwa dole ya
daukeshi zuwa neman aure kamar yadda kawu ya fada mata.
Jin tambayan da yake mata yasa ta nisa daga dogon tunanen da takeyi nasa a lokacin tace lafiya lau
muke Jafar ya wajen ita Rahama din naji Habu na fadin bata jin dadi kuma ?
Da sauki tasha magani kafin in fito ta samu sauki don taki yarda muje asibiti ai dama Rahama bata son
ko magani balle zancen asibiti Salima ke fada.
Ai naga alama ta daiji sauki da ranan nan don saida naga taci abinci nafito na barta zaune a falo tana
gaishekuma.
Iyace ta kara fadin amaryace mai batun hankali injin dai kazo min da tawa sauran kazan amarcin naku
ya mike tsaye yana dariya yake fadin iya ke aiba saura za a baki ba taki dakwalwan za a kawo maki dai
kema.
Daga part din iya nasa part din ya nufa inda ya samesu a kitchen tsaye suna sa,insa a tsakaninsu kan
kayan da aka shigo dashi din.
Daga kofa ya tsaya rike da hannun yar wajen saiba yana fadin wai ya hakane kuma ku dai baku zama
bakuyi fitina a tsakanin ku ba ?
Wai cewa nayi a dauko wanan naman daya saura sai a soya kada a hada da wanan shine