Chapter 9 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   9 / 101

24K to 27K   out of 302.2K words

da gani daban take a cikin fulani don tayi kama da wace ta
zauna a birni ba a cikin daji ba.

Bayan magariba Ramaah tayi sallama part din Iya ta sauke kayan abincin data dauko niki niki tana
gaidasu inda suke zaune.

Abincine Yanda tace na kawo cikin murmushi mama tace a,a abincin hardamu aka sakawa angode aida
tayi iya bakinku sai mijinta.

Sare ce ta mike ta karba suna fadin sun gode har Ramah din ta juya taji muryan mama na fadin.

Nace ba idan kun karasa aikin a can anan wajen Iya zaki dawo da kwana idan kin karasa saiki dawo nan
din ki kwanta kinji.

Ta amsa a ladabce ta fita na part din ya J ta dauka ta mika masu inda ta samesu zaune a falo duk da
hiran nasu ba wani hiran arziki bane mai tsawo.

Amma ya zama dole garesu don dokan da maigida ya kafa a kansu yanzu kuma kowa na tsoron yayi
abinda zai bantale masa auren a lokacin da suke jin dadinsa.

Gaidasu ta fara a falon ta dire abincin acikin wani kula mai kyau tana fadin abincine daga wajen amarya
a gyatsine Saiba ke fadin ta aje a saman table din.

Babu wace tace angode a cikinsu ko a gaidasu da mai girki ba wace ta iya fadan hakan a cikinsu haka
yarinyar ta fita tana mamakin hali irin nasu.

Part din yar uwan ta koma taci abinci saida ta gama ta mike take fada mata abinda mama dubu tace
dan shiru yar uwar tayi indai son samune taso a barta da yar uwanta da take amana a wajenta yanzu ta
zauna a wajenta din.

Saidai ba yadda zatayine don umurnin mama dubu ne hakan tayi mata saida safe ta fita zuwa part din
tsofin don ta fahinci ana son ta bar ango da amaryansane lokacin.

A bangaren yaya Jafar kuma Ramaah ta fita bada dadewa ba saiga maigidan ya shigo suna mai sannu
da zuwa ya amsa tare da bin kulolin da kallo ya kai zaune yana fadin wanan abincin fa ?

Daga bangaren amaryan Habu aka kawosa Saiba ta fada tana mikewa donta dauko mashi abincinshi da
suka girka a part din.

Saidai taja ta tsaya tana bin maigidan da kallo wanda ta sama ya bude abincin yana zubawa tare da
yaba yadda aka tsara komai cikin nuna wayewa da zallah gwaninta tare da iya tsabta da kuma sanin
darajan dan adam.

Bai jira wani cewa ba ya mika hannu ya fara serving din kanshi saiga Saiba ta fito da only warmer din
data zuba mai ja,loop din taliyan da tayi na manja.
Tunkan ta karaso ta soma magana tana fadin wanan abincin yarincan ne fa ga abincin ka nan na
dauko maka ?

Bai kullata ba yacigaba da zuba abincin a cikin plate iya yadda zai iya tare da fara zuba miyar yana jin
wani irin tukuki a da zafin matan nasa na yadda basu iya tsayawa suyi girki haka irin da malam bahaushe
ya sani saidai shiririta irin na shirmey din nan da matan yanzu keyi saboda sakaci.

Mikewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana shirin zamane ta kara fadin J fa bafa nina
girka ba wacan yarinyar ce matar Habu ta aiko muna dashi.

Bissimillah taji yayi yana yankan tuwon ya fara kaiwa a bakinshi tare da lumshe ido don jin yadda
tuwon ya hadu tsab rabo da yaji tuwo haka tun suna gida mahaifinsu yana raye mama na girki ta saka
masu.

Komai yaji acan acan kayan yaji na gargajiya sai dandanon daddawa ga kuma kamshin man shanu dake
tashi gwanin ban sha,awa.

Daidai Asmau data gama shirya danta ta fito dashi rugume a hannunta itama tabishi da kallo tare da
mamaki ta zauna a saman kujera.

Wai ikon Allah yanzu girkin nata zakaci J ya dago yana kai loma a bakinsa ya hade yake fadin wai wanan
din sunansa me kin isheni da wanan abin da kike dafa da sunan abinci.

Wanan din shine muka sani da abinci a gidan nan ba wanan shirmen da kukeyi ba ku diba yarinya
karama tasan ta girka wanan abincin hakawa mutane ?

Ku me yaci karfinku da ba zaku iya ba ya dauko gutsuren nama ya kai abakinsa ya lumshe ido kallon
Asmau saiba tayi cikin mamaki itama ta lumshe idanunta.

Tana fadin wai bari dai nima naci naji hannun ta da akewa yabo haka ta fara serving din kanta itama
saida ta loda taja plate din gefenta ta fara ci.

Loma biyu taci ta dago tana fadin kici kiji abincin ya hadu gaskiya ba laifi kici don Allah murmushi tayi
cikin takaici tana kallon kulan dake hannunta ta dangware tana fadin wanan ai baiyi ba.

Ta fara jan plate din ta bude ta zuba kadan don ta gano matsalan abincin ta fada ta soki wanan girkin
da taga suna santinsa.

Saidai ta cinye wanda ta zuba din ba tare da tasan tayi hakan ba shiko maigidan ya tashi da duk
abincin ya koma cin naman da bai jin zai gaji da cin wanan naman da kamshin sanadarin girki ke tashi a
cikinsa.

Da sallama ya shigo tana zaune tana addu,a saman sallaya ta juyo tana amsa mashi sallaman babban
rigan sa daya ishe,shi a jikinsa ya debe ya sagalo a hannunsa ya dora saman kujera yana zama.

Shafa addu,an tayi ta mike tana fadin sannu da dawowa yaya Habu kai ya dago ya kalleta jin yadda ta
kirashi a ranan sabanin yadda ta saba kiransa da dan zaria.
Murmushi yayi yasan wanan sunan a bakin su Sare tajishi kallamane da kannesa ke kiranshi dashi dole
a wajensu taji wanan sunan.

A cikin muryanshi mai natsuwa yake fadin amaryata ya zaman kadaici ina Ramaah ya dan fara dube
dube yana neman yarinyar a zatonshi tana daki zaunene.

Rigan daya aje ta dauka tana fadin tana wajen su mama tun dazun au ke kadai ta bari nan ke nan ya
fada yana kallonta cikin so da kauna tare da godiya ga ubangiji Allah daya nufeshi da samun wanan
tsatsiyar yarinyar a matsayin mata a gareshi.

Wanka zakayi ko sai kaci abinci muryanta ya katse mashi tunanensa ya dago ya sauke mata kallo yana
fadin bari muci abincin sai na shiga gaba daya.

Ta juya ta shige ciki ta aje rigan ta fito ta sameshi ya lumshe ido yana godewa Allah indai Yanda
tacigaba da hakan a rayuwanta zaifi kowa murna da aure a rayuwanshi.

Ga abincin can na jera a dinning ta fada ya kalli daning din ya hango kuloli a jere gwanin ban sha,awa
ya lumshe ido yana mikewa tare da kamo hannunta .

Idonta tayi saurin lumshewa lokaci guda tana maijin wani iri a zuciyarta basu nufi dining din ba sai ji tayi
yakai mata runguma yana sauke ajiyan zuciya da itama shita sauke lokaci guda tana hawaye.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC




MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

11️⃣00️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Rayuwan aure mai tsabta suka shimfida a tsakaninsu a ranan inda yakwana yana lalashin amaryan nasa
wace ya sameta da mutuncinta da kimarta na ya mace.

Zamanta a daji ko rayuwan birni baisa ta zubar da kimarta na ya mace ba a waje daga shi har ita sun
shiga wani hali bayan zazzabin daya rufeta zuwa safe hakan yasa ya fara tsaguwan kansa tare da
tuhuman kansa dabai rangwanta mata ba.

Wanan yasa daga masallaci part din iya ya nufo ya samesu a falo suka gaisa nan yake fada mata cewa
Maria ce ba lafiya.

Wallahi tun asuba jikinta yai mugun zafi tana kuma rufe da bargo tana rawan sanyi ko asibiti zasu tafine
da ita ?

Haba dai kaje iya na tafe mama ta bashi amsa lokacin na fito da tsinya a hannu na tsuguna ina gaidasu
da kwana na wucesu ban tsaya ba.

Tsakar gidan kamar yadda muka saba share gidansu hjy a abuja hakan na duka na fara shara.

Don gidan yana bukatan gyara saboda gidan tunda akai buki ba a samu wanda ya tsaya ya gyara wajen
ba ganin hakan yasa na kwana da niyar gyara wajen na fito tunda safe .

Daga bangaren Anty yanda na fara na gangaro dayan part din da babu kowa a cikinsa har zuwa part
din wa yan nan matan dana shiga jiya nakai masu abinci.

Duke nake na shagala naji mutum a kaina yana gaidani na amsa kafin na duka ina gaidashi farine dogo
yana saye da jallabiya a jikinshi suna da kama sosai da yaya Abubakar.
Saidai yaya Abubakar bai kai wanan fari da tsayi ba shi wanan jin dadi ya huda jikinshi kallo daya zakiyi
mai ki gane yana jin lokacinsa.

Duk a kallo daya da nayi mai na zayyano wanan kamanin nasa dana hango lokaci guda tas nayiwa gidan
kafin na samu komawa part din iya inda na fara gyara tare da tsabtaceshi na fito falon daga kitchen dinsu
dan soma sharo falon na iya a lokacin ya kara sallama ya shigo wanan karon ya sauya tufafin jikinshi
zuwa wasu kananan kaya zakice shidin ba dan hauwa bane .

Kayan sun matukar karban jikinshi sun fitar mai da kurciyansa a fili saiki rantse bai taba auren farko ba
suna fadin Abubakar yayi rigima wanan mai mata biyu din ashe shine mai rigima din.

Mama dake zaune tana jan tasbaha a hannunta ya kalla yace wai ina kuka samo wanan yar mama tun
dazun naga tana aikace akaice gidan nan ?

Kai dai bari yar albarka yar uwar amaryan Habuce da suka bar mata ita a nan shine ta tashi da wanan
aikin ina su Sare ya tambayi kannensa mata .

Wa yan nan mashiriritane ai suna daki kwance ko gyaran kwanciya basuyi ba balle susa niyar tashi iya
fa ya tambaya ?

Ta shiga gun Habu ta duba amaryansa ina ganin yarinyar yar albarkace yazo wai zai kaita asibiti nace
iya ta fara duba mashi ita a gani.

Fuska ya daure a cikin wani yanayi ya kai zaune yana fadin da anbari sun tafi asibitin kada wani matsala
ya biyu baya kuma.

Inba zamani ba ba komaine ake zuwa asibiti ba rashin sabone ga dai iya din can taje ta dubata ai tun
dazun wayansa aka kira ya dauka ya cigaba da wayan karshe ya mike ya fita.

Saida nagama aiyukan gyaran ko ina na nufi part din antyna inda nayi mamakin ganin tsohuwar a
wajen ban tsaya ba na gaidasu na shiga dakin da kayana suke ciki wanka nayi na gyara jikina fes kafin na
fito na samu tsohuwar ta fita daga wajen.

A hankali nakai zaune ina duban kofan antyna din duk da ake cewa mu fulani bamu da hankali
kankantana a lokacin baisa na fada dakin nata ba kai tsaye don muna da tarbiya zaman muna birni bai
barmu da duhun kai ba.

Bayan hakan kuma gwargwado muma fulani muna da namu addinin munsa abinda yake daidai da
wanda bai dace muyi ba balle bamu taso cikin duhun kai ba ai.

God so kind na iya kunna gas tun a abuja wanan yasa jin yayata shiru na fada kitchen tare damu
mahaifiyar da yayata sukewa hjy Yaghana girki da mijinta .

Haka diyansu su anty salma idan suna kasan nan mune suke sakawa muyi masu duk wani girki da zasuci
har su bar kasan nan.
Zaman na shekara biyu da rabi ko ukku a wajen baffa baisa komai ya fita kanmu ba tunda a cikin hakan
muka tashi.

Haka yasa na dora ruwan zafi na debo dankali na fara ferewa ruwa yayi zafi na juye a flask na dora
suyan dankali duk a zatona suna dakinsu kwancene basu tashi ba kafin wani lokaci nagama hada
breakfast na zuba a kula na fito daidai lokacin ya Habu ya shigo gidan da ledan magani a hannunsa.

Zaka gane anyi girki don kamshin da gidan nasu keyi gaidashi nayi da dawowa na juya zan fita ya tsaya
yana fadin kinyi breakfast ne Ramaah ?

Ehh na hada yaya gashi can a dining na fada a dan ladabce yadda mukewa su anty salma a Abuja sai
naga ya dan kalleni na second sai kuma ya juya zuwa ciki .

Komawa nayi kitchen ban fita ba na wanke kayan da nayi aiki dasu na tsabtace kitchen din yadda
ummah na koya muna tun muna kananun mu.

Dama kuma idan kinsan bafulatana badai kazanta ba don tsabta kan akwaishi wajen fulani ko cup aka
fara darazanshi wajen wankewa sai yayi fari sol za a barshi haka kore da sauran kayan aikin mata.

Muryansu naji yasa na fito daga kitchen din dauke da kayan abincin part din tsofin dana wa yancan
mutanen kamar yadda naga anty Yanda ta zuba masu a jiyan.

Nasu na fara kaiwa suna falo dukkansu biyun nayi sallama na shigo bread ne ko ina baja baja a falin
yaransu suna wasa dashi .

Kyan kyami naji haka na ratsa ina gaidasu na aje masu abincin na juya da zumar fita daga wajen naji
muryan wata na fadin.

Ke meye wanan din kika kawo muna jin hakan yasa na juyo ina fadin abin karyawane sai akace daku
bamuyi ba anan sai an kawo muna ?

Ita kuma Asmau cewa tayi kice a daina kawowa hakana mun gode basai ta wahal da kanta ba kinji zoki
dauka ki tafi dashi ta kara fadan hakan.

Kallonsu na danyi kafin na yunkura zan dauki kulan abuncin naji muryanshi yana fitowa wani daki yana
fadin ke ajeshi nan kice an gode ni aka kawowa baku ba da zaku yanke hukunci kuba da dokan kada a
kara sako min abinci.

Lah illah amma wanan kan gaskiya baiyi ba dan abin karyawan ma sai ankawo muna saboda me za ace
a zubo muna.

Nikan tunda yace in tafi na fito part din da saurina na barsu sunayi bansan ya suka karasa ba a wajen.

Na koma na dauki na tsohuwar na kai mata suna daki suna hira na shigo ina gaidasu suka amsa na aje
abin karyawan nasu a gefe daya.
Wuri na samu na zauna gefe daya tunda ba sabawa nayi dasu ba lokacin sai ga mama dubu ta fito daga
daki alaman wanka tayi tana fadin .

Badai wanan yar girki tayi ba yanzu nake cewa idan na fito akai mata abin karyawa can wajen ku ai sai
ga kuma wanan abin ta nuna kulan dana shigo dashi da hannu.

Nice nayi mama anty Yanda tana daki kwance ina gani na fada yar albarka irin yaran nan ai bakuntanku
baida wahala a waje.

Meyene kuka dafane Sare data mike zuwa bude kulan abincin take fada tana bude kulan don taga
abinda ke ciki Arish ne sai kwai da suyanshi yayi kyau sosai bai kuma yamutse ba zakice wata mace ce
tayi aikin.

Ke baki da kunya ku diba kuna daki yarinyar nan duk fadin gidan nan itace ta shareshi tas ta gyara nan
ta gyara wajen yar uwata yanzu kuma ta hada masu abin karyawa.

Kai amma kuwa dai tayi kokari Sare din ta fada nikan hankalina yana ga tv dake aiki ina tuna wani
rayuwa a baya idan an saka waka muka kama rawa muna nishadi a falon yara gidan daddy na Abuja.

Anty Salma yar daddy din itace ke koya muna rawa da waka sai mu dinga rawa ina yawan cin gasa idan
ana competition a tsakanin mu yara.

Sweet zata sayo da cake da yought a dinga rabawa a wanda ya iya rawa wai tana da saurayi mai rawa
da waka shine take koyon waka itama.

Yadda ta fado muna dakin zaisa kaji tsoro tana haki yasa gaba daya muka mayarda hankalin mu a
kanta muna kallonta.

Mijin ne yashigo a hasale ya nufota ta boye bayan mama Jafar meya hau kanka hakane kanka daya
kuwa duk iskaci ai ba zata zo gurina kace zaka biyota ba ?

Nikan tsorone ya kamani sosai da har yasa na mike tsaye juyawa yayi ya fita sai bayan fitanshi ta soma
magana tana fadin.

Kawai don nace ba zaici abincin wacan yarinyar ba shine wai zai dakeni mama din tace wace yarinya ke
nan matar Habu dake sako muna girki idan tayi .

Shine yake ci tun jiya yau nace ba zaici ba na zubar shine ya biyoni zai dukeni kafin takai aya mama tace
kika zubar da abinci Nusaiba har kike fadi kin zubda ?

Mama akan me zai zauna yana yaba girkin yarinyan nan daga zuwanta yana fadin haka aka san mace
da iya,,,,,,,,

Shiru tayi don ganin Habu dake tsaye kofa ya harde hannayesa a waje daya yana saurarensu don
tunda suke rikicin har fitowanta yana tsaye kofan part dinshi.
Ganin mijinta ya fita hasale ya shigo ya gaida mama ya samu tana kokarin aibanta matarshi da
kwananta biyu kawai a gidan .

Zama yayi su Sare suka fara gaidashi ya amsa a dakile yace mama kiyi masu kashedi akan maria idan
suna rikicinsu da mijin su ya tsaya iyasu amma kada su kara hadawa da matana balle mace tace zata
aibanta min mata.

Sam ba zan dauki wanan ba ban shiga zancen yarinya ba mama kada wata mace ta kawo min zancen
banza za a jini da mace a cikin gidan nan.

Nasan za a rina da wanan yau alheri da kyautatawa abokin zama kuma laifine Nusaiba ?

Shi dan arziki a duk inda yake yakan nuna halinsane da irin tarbiyan da akai masa ai alheri kuma a
cikin jinin bawa yake.

Nayi mamakin yadda yaran nan har zasi iya saka muna abinci bama mu kadai ba harku a gidan amma
ku din nan kuna bakin ciki ace yau abinku ya shigo a hannun ko tsohuwar nan balle ni ?

Har yaushe yarinyar nan tashigo gidan nan da wani zance can zai biyu baya binsu mukayi da kallo mijin
da dayan matanne suka shigo part din zama sukayi nan mijin nasu shima ya dora da fadin yazo dasu
gaban tsofin ne ya kafa hujja akan abinda yake son fada game da matan nasa.

Ga kaninsa

9 / 101