Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
murmushi na karasa shigowa ina gaidasu da gida suka
amsa min take fadin.
Cigiyar ki nazo yi Ramaah yaya yace kun dauke kafan da part dinsa bai san dalilin hakan ba a yadda na
kula kuwa hakan ya dan dameshi.
Ni kuma aiko dazun da zan fita nashiga mana da safe yanzun nan kuma dawowana ke nan ai ban zama
yanzu zamu soma exam yasa hankalina ya dauko.
Kyaleshi kinji kinsan halin yaya J ai da damuwa da wanda ya damu dashi yanzu dan kulashon da
kukeyine yaga kun daina shine yake wanan magana shi haka yake da damuwa da mutane shiyasa ake
saurin kamashi.
Dan kallonta nayi na kau da kaina gefe ina wasa da Abbati daya zo ya fada jikina ban jima ba na mike
da yaron zuwa ciki.
Nasan dai ta fita tunda naga anty Maria ta shigo dakin gab da magariba take tambayana meya hadani
da Saare na dago ina fadin Saare kuma ?
Yaushe ba abinda ya hadani da ita take fadin in daiyi sannu ita ba don mama da ya habu ba ba zata
yarda ina sintiri a part din yaya J ba.
Tunda tasan halin matanshi ba mutuncine dasu ba hakama Saare din na dai share zancen zuwa don ban
bata amsa ba.
Saidai a kasan zuciyana ina tunanen me akace ya hadani da itane wai tunda bakina da nata dai bai hadu
ba duk bare baren da takeyi a kaina din.
Tunda bata nuna dani takeyi ba akan me zan tsaya nuna mata nasani balle yanzu dana kama kaina da
shiga part din da sunan jinya.
Shima kuma addua muke mashi Allah ya bashi lafiya ya mike don ba mai fatan ya tabbata a hakan da
yake din.
Na share hakan kwana biyu kuma ranan weekend na gama wanki nayi wanka sai gata again wai yaya J
yana kirana.
Saida na shirya naje suna falo zaune na shigo nake gaidasu da kwana suka amsa min yake fadin
Rahama lafiya kwana biyu na daina ganin ki ?
Ita Nafisa ance tayi tafiya amma ta dawo jiya sai a lokacin ma nake jin cewa su Nafisa din sun dawo
daga tafiyan.
Nake fadin ba komai yaya exam zamu soma yasa ban zama yanzu exam zai hanaki shigowa ki duba
yayan ki Rahama ?
Sai nayi kasa da kaina bance komai ba don mama data kura muna ido tana sauraren mu itace ta kawar
da zancen tana fadin yace kiyi mai irin ferfesun da kikayi ranan ya tsaya kuma tareki da tambaya.
Wayyo Allah da mama ta sani ko shi yaya din da basu sakani wanan aikin Allah bai hada jinina da kifi
ba duk bafulatanin asali haka yake inba mu fulanin zamani ba .
Sam bafulatani bai cin kifi ace zaki dauki spoon ki motsa miyar kifi ki kuma dauka ki motsa miyar
naman dashi ko one spoon kikai a bakinki a ranan idan kin soma amai kamar zaki amaye duk hanjin
cikiki.
Amma don kawaici da alkunya haka na mike zuwa kitchen din nasu na soma aikin hada ferfesu din ina
gamawa na bude fridge an kawo kifi mai yawa da gani sabon zubawa ne ballo na wanke na hada.
Ban fito ba saida na kammala komai na zuba na nufo falon dashi na samu mama bata nan ta fita saishi
da wani abokinshi a falon suna hira.
Sallama nayi na aje tare da gaida abokin nasa ruwa naje dauko mashi naji bakon na fadin kai mutumina
wai dama kayi sabon aurene ban sani ba ?
No wander naga alots of changes a tare dakai da kuma yanayi yaushe ka auri wanan african queen din
banda labari ?
Yanzu daka sani ai bai baci ba gashi kun gaisa amma gaskiya ba ganin fuska ba wanan karo kan ka
tsaya ka zabo abinda ya dace dakai.
Allah ko ya fada hangoni dayayi tafe ruwa na dauko masu da drinks na aje gaban bakon daketa faman
sabarin baki ga abokin nasa.
Godiyana ga Allah banyi kwaron hannu na dafa kadan ba tunda nasan mama da yaranta na wajen sai
kuma Allah ya turo wanan bakon nasa yazo.
Furcina yasa bakon dan kallon mu da nake fadin nagama yaya shike nan ko akwai wani abin naji yace
jeki Rahama zan nemeki idan mun gama.
Zo amarya mana kada ki tafi ban sayi baki ba bayan abincin da kika karrama ni dashi haka tun ban ciba
kamshi ya danne hancina kudi ya dibo daga aljihunshi ya miko min na dan dubi yaya din yai min alaman
dana karba.
Naji bakon na fadin kai akwai irin matan nan har yanzu ashe gaskiya J ka dace kwarai wallahi kudin ma
sai ta tambayi izzinin ka zata karba ?
Gaskiya kayi dace Allah yasa abin yacigaba a haka ni abokinsane sosai tare muka taso dashi saidai bani
zama a nan yanzu shine ya rabamu har baki sanni ba na mika hannu kawai ina fadin wawa sai zuba yake
haka na tsani namiji irin haka wallahi.
Na fito na hango Saare tsaye kofansu tana waya ban sake kallonta ba na shige part din mu da kusan a
jere suke a barin dama dana yaya J din sai dai akwai dan tazara sosai a tsakanin su.
Inda part din su mama ke barin hagu yana kallon nasu yaya din da wanan dayan part din da ake cewa
part din yaya yazid ne shi ko yaushe yana rufe saidai da yarsu tazo daga zamfara kwanaki aka bude mata
ta sauka ciki da yaranta.
Sai tsakiya dake da fili tsakanin gidajen duk girman wanan filin da haka nake tashi in shareshi tas amma
yanzu na ba kaina lafiya ko ita wace akace yar aikin bata iya sharan wajen yanzu sai almajiraine ke zuwa
kwana bibiyu suna sharan wajen.
A basu abinci da kudi garama namu part din muna sharansa har wajen gidan mu zaki gashi tsab dashi
saidai a tsarin ginan yanzu na ya J yafi sauran girma don filin dake bayanshi an hade dashi anyi gina da
aka karawa wajenshi girma sosai donshine nasa part din ya fita daban dana sauran.
Ina zama saare na fadowa part din saida gabana ya fadi dana ganta na dauka wata tsiyar tazo yi min sai
naji tana fadin .
Ai bansan kina part din nan ba Ramaah dana shiga me kika bar su yaya sunayi da zaki fito nace kila
abinci zasuci na dai dafa mashi taliya fara da ferfesun kifi yace ayi mashi.
Wai kinsan wanan yaya mansur din abokin yaya saurayinane kuwa ya tambayeki ni ko ince kinji suna
magana a kaina don Allah ?
Wallahi banji ba ni ina kitchen na gama na aje masu na barsu suna hira a wajen na fito sai naji tace
barin koma na gani ko sin gama ?
Har ta gama surutunta ta fita maria bata daga kai ta kalleta ba sai bayan ta fita taja muna kofa maria
din tayi tsuki tana fadin wahalalla kawai.
A haka zata kare ance ko saurayin arziki bata dashi ina ganin shine na Abujan data lekewa tana so din
nan yazo ?
Itama ke sonshi mama bashi ke sonta ba aiko akwai aiki wallahi gara kaso wanda ke son ka ba wanda
kake so ba anyi ma kina so yana so yaya aka kare balle wanda kake cusa kanka wajensa.
Kudin daya ban na aje ina fadawa yar uwata din abinda yace nace shifa ya dauka aure yaya yayi sai
zuba yakeyi harda miko min yana fadin gashi na sayen bakine tunda bai san lokacin da akai buki ba.
Maria tace don bai sanki bane yasan duk kannensu ai ba zai dauka kema a gidan nan kike zaune ba aje
kudin nan ki nunawa mama tunda ta dalilinsu ya baki shi.
Mama kuma na fada ina kallonta tace to Ramaah ina gudun abin maganane wallahi kada yaya ya fada
masu abindake nan suce kuma wani abin.
A,a wallahi saidai inba yaya din inji me zaice ai dukkansu kyaleni sukayi a kitchen suka fita da bakon
yazo don me zan basu nikan ba zan bata ba don tsab zata karbesu wallahi.
Nafisa fa tace in anyi muna abin arziki mu daina nuna mata tunda karba takeyi bata bamu sai naji tace
ke Nafisace Ramaah ?
Waima ko sai yaushe zasu dawone mutumiyata naji kewanta sosai wallahi na zata kwana biyu zasuyi
kawai a can ai sai gashi suna batum share kwana goma.
Sun dawo jiya naji mama tana fadin ance sun dawo tana garin nan yana da wuya dama ta dawo gidan
nan gaskiya don anty saare din dake gida yanzu nasu baizo daya ba.
Don cewan da takeyi wai don kwadayi an mamaye komai anayi ta ina za a bari matan yaya su dawo a
yanzu shine sukai fada har tayi fushi lokacin ta kwashi kaya zata koma gida saida akaiwa Saare din fada.
Kingani ko dama saida nayi wanan tunanen a raina don wanan abinda kukeyi za a dauka da wata
manufa ake hakan kinsan mutane yanzu da sheri.
Yar uwarsu ke nan Nafisa sun fadi hakan a kanta ina gake da ba yar uwarsu ba ai sai sufi camfaki ga
zancen don Allah kadai yasan irin abinda take fadawa matanshi yanzu tunda suna tare.
Banjin tsoron duk abinda ta fada saboda nasan ban aikata hakan don kudi ko don wani abuba saidai
ban jimirin daukan wullakaci a kan hakan yasa na kama kaina tun bata kawo kaina ba.
Ita din yar uwar ya Habu banson nayi rikici dasu don yana mijinki idan nayi hakan bartabanki ne zai
tabu a wajensu.
Shiru tayi min cikin damuwa ta kasa ban amsa ga zancen ganin haka kawai na mike nabar falon da
kudin a jikina don ba zankaiwa mama din ba kome za ayi kuwa tunda nice akaba.
Ranan ya Habu ya dawo daga tafiya ya dawo da abin arzikinshi kamar yadda yake akida wajensu duk
garin da sukaje zasu sayo abinda ake amfani dashi garin.
Za ,a sayo azo dashi gida ayi amfani dashi saidai gajiya ya hana a raba ba sai washegari ya fito dashi
daga motansa .
Nice ya kira na dauka zuwa part dinshi danasu mama duk da ina kyautata zaton mama tana part dinsu
ya J a lokacin.
Iya na sama zaune na gaida ita da kwana ta amsa tana fadin yar nan za,ace baki gidan nan wai meke
faru hakane kun dauke kafanku gaba daya da wajen nan.
Babu komai iya ina nan saidai a yanzu ban faye zama ba ina zuwa makarantane kin sani ai.
Kayya yar nan akwai dai abin da akai maki kika dauke kafanki haka ni zuwanki yafi min zuwan wa yan
nan marasa lissafin ai ki fada min idan an maki wani abin ne na dauki mataki kan maishi .
Nace iya ba komai karatune yasha min kai duk kwanakin nan sai naga ta yafutoni da hannu alaman in
matso kusa da ita na je din kuma ta tausa murya tana nuna min dakin su salima tace.
Ita wanan sakariya tun jiyan ta shige daki bata fito ba wai abokin yayanta take so kiji min ja,iba baki
bari a nemiki ba sai kece mai neman miji don sakarci irin na saratu.
Iya tana sonshine tace jam,jam ai mace takan jira furtawan namijine ba ita ta nuna hakan ba shine
yayanku Jafaru yayi mata tas jiya da dare ta shige daki tana fushin banza.
Ni dai na fita ina dariyanta don yadda tai maganan sai kayi dariya tana kallon labulen dakin zakice
saarece a wajen tsaye lokacin.
Nasan takaicin hakan tsohuwar taji yasa take neman abokin hira ta amaye abinda ke cinta a zuciya don
basu shiri da Saratu sam suna konewa junan su mai ko yaushe.
Ban,san ya akayi ba na dawo daga school na samu Asmau uwargidan ya J ta dawo gidan inda na gane
hakan yarta dana gani tare da Abbati a part din mu nake tambayan ita dawa tazo maria tace min ita da
uwarta sun dawo dazun ita ta kaduna iyayyenta sunce sai karshen sati zata dawo.
Nasan suna kara shiri irin nasune don ance ba karamin shige shige suka iya ba ko wanan dawowan
nasu yabawa kowa mamaki don haka kawai akaji mama tace su dawo dakunan su.
Ance ya j din ya nuna bai son dawowan su amma mama tace aiba tafiyanshi sukayi ba natane don haka
dole su dawo dakunan su.
Sun dai muzanta na fada ina nufar dakin mu naji tace dani ga wanda yasan hakan ba ai tun karfe biyu
tana gidan nan wajen salima nake jin tace Saiba basu gama shige shigensu bane a can.
Amma wai mijin yace idan ta wuce gobe ba dai gidansa ba nasan zata dawo ga goben itama ke nan
gamu dai gani ai duk fa sun lalace ba kamar yadda suka tafi ba daga ita har yar nata .
Ban fito ba ban kcuma da niyar zuwa yi mata sannu da dawowa ina daki ko falon yar uwata kika shigo
ba zaki ganin ba don ban zama a falonta sai daki saboda ya habu dake garin.
Kamar yadda yaba da umurni sai gata tashigo garin wajajen karfe biyar na yamma bata dade da isowa
ba ni dawo daga school motan gidansu dana hangone yasa na gane cewa Saibace ta dawo.
Haka kuma na samu anty Nafisa itama ta dawo gidan nayi mamaki kwarai data dawo gidan a lokacin a
zatona ba zata sake dawowa da sunan zama ba.
Wai ashe shi yaya Jafar da yaya Habune da sukaje gidan suka dawo da ita nayi mamakin jin ya Jafar din
ya fita a ranan zuwa cikin gari dashi da dan uwansa lalai sauki ya samu sosai gareshi tunda har ya iya fita
zuwa cikin gari.
Ina sallah magariba naji shigowan su anty Salima da Nafisa part din mu suna dariya ban fito ba saida
na idar duk da naji suna tambayan ina nake ?
Suna dariya wai iya tana can tana sakin magana hakan yasa suka gudu zuwa part din mu kafin ta hada
dasu ta zage.
Daga kofa na tsaya ina fadin anty Nafisa munyi fushi ta juyo tana fadin kada ki fushi Ramaah kina raina
wallahi wayarkice ko yaushe mutum ya kira zaijita a kashe.
Haka dai yaya yace dazun salima ta fada dazun ya kira layin ki wayar bata shiga ai yace bai ganki ba duk
kwanakin nan nace kina nan sammako kiyi kina fita zuwa school.
Yadda maria ta kalloni yasa na kawar da kaina gefe daya nima dai naji zancen wani iri balle yanzu da
matanshi suka dawo gidan hakan zai iya kawo zargi a zukatansu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nasamu na gama exam dina haka na dukulo na dawo gida da ciwon kai ga yunwa da nake tunanen shiya
haddasa min ciwon kan don ban iya cin komai idan na taka school sai idan na dawo gida.
A haraban gidan na gansu zaune yadda suka sabayi wani lokaci idan sun bushi iska hakan zasu fito nan
farfajiyan gidan su zauna a dasa daban hira da tsokona.
Irin wanan zaman na fahinci da gaiya sukeyinsa wani lokaci idan suna da kudirin cin mutunci ga wani a
gidan suke wanan zaman.
Shigowana yayi daidai da karan budan get din gidan mota ta shigo hakan baisa na juya inga mai
shigowa gidan ba a lokacin saida akai horn na gane ya J ne ashe ya fita ya dawo a lokacin.
Daidai inda ya sameni kiris ya rage inkai lungun mu ya dakata da mota ya sauke glass sunana da naji ya
ambata yasa na dakata na juyo ina gaidashi.
Ko ban kalla ba nasan idonsu yana kan mu a lokacin shiko gaisuwan tawama bai amsa taba sai cewa da
yakeyi dani wai Rahama meye matsalan da kike gudana a yanzu.
Murmushi na dan sauke ina fadin yaya gudunka kuma wallahi exam muka fara sai yau din nan muka
karasa wanan yasa ka daina ganina.
Ya maki kyau shiga zanyi maganin ki ai daga ke har Nafisa zan zauna daku ku fada min idan kuji wani
abu daga garemu ne kuke wanan halin sam banji dadim matakin da kuka dauka ba wallahi.
Nagode yaya na fada ina dan rusunanwa na hau step ina murda kofan mu na shiga ban san ya akayi ba
dai bayan sallah isha,i saiga Nafisa a part din mu tana fada min wai yaya J yana neman mu wurinshi.
Yadda nake dagani sai wata dogowar riga mai v neck mara hannu sky colour hijjab dina fari danayi
sallah na fito daga part din mu nake ce mata dama dazun yace zai zauna damu ashe da gaskene.
Ok dama dazun din da gaske ya tsaya dakene rikici sukeyi da matanshi akan hakan nidai naji yashigo
yana fadawa mama a hasale har ya tashi dukan Saare iya ta hana.
Shi yaya har yaji sauki duka haka ke nan iya abinda na iya fada ke nan don ni zargin nasu ban daukeshi
da wata manufa ba tunda a gabansu dai na tsaya dashi din suna gani.
Kuma meye a ciki don ya tsayar dani na tsaya shine kuma zai zamo abin fitina har da zancen duka a
ciki ?
Kin gane Rahama wallahi yau ina ganin za ayita ta kare a gidan nan kila na bar gidan nan a yau din nan
don ba zan lamuci zancen banza ba bari dai muje din muji kiran zakisha mamakina wallahi.
Rashin mutunci da iskanci nida na taso gidan yawa kowa da halinsa ana nuna min iskanci in kyale saidai
idan naso hakan shiru shiru aiba tsoro bane dama.
Ke kenan Anty Nafisa nikan ai kila barin gidan zasuce nayi tunda zargi ya fara shiga haka ko basuce in
bar gidan ba aini zan bar masu.
Akan me gidansune bari dai muje muji ai mama da kowa suna can wajen hakan ne kuwa koda muka
shigo da sallaman mu falon duk suna zaune harshi dake waya a lokacin inda na fahinci zai koma bakin
aikinshi a kwanan nan yadda yake fadi a waya lokacin.
A