Chapter 41 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   41 / 101

120K to 123K   out of 302.2K words

a cikin zance.

Nima ai hakan yasa naji dadi da kika fada a cikin gida cewa yaya yace gidan anty Ai za ai komai har baki
su wuce.

Wai baki ji sakaran nan Saiba ba da nake fadawa iya tana tsaye sai cewa tayi wai dama ita ya dace aje
can tunda taronna yan kauyene ai.

Kuci abincin mana na fada ganin sun bar abincin a bude yana sanyi a lokacin saidai hakan bai hannusu
hiran ba sukaci gaba da hiran yadda Saiba tayi ta iya shege tana cika baki.

Salima ta kare da fadin saiga shegiya tayi lakwas dataga karyan bariki baki ya mutu ance bayan zuwan
mu nan ai bala,i tasa don wallahi yaya yayiwa kowa bazata ga auren nan.

Gaba daya ya nunke kowa a baibai don bai bari kowa ya fahinci komai ba su matar kawu ba a samu
kafan iya shege ba wanan karon da bukin maria yaya habu matar nan tayi iskanci sosai wallahi.

Ta hana komai karshe ta kwashe takai gidanta sukai ta amfani dashi muguwa kawai ni wallahi nasan
itace ke kara yiwa mama fanfo akan komai.

Itama mama ni har mamakin yadda ta sauya nakeyi ni yanzu har tsoro nake ji idan mun koma gida
nasan ana jirace damu mu koma a zazagemu.

Ina gefe daya na takure a waje daya ina sauraren hiransu wanda nake ta auna abin a zuciya da nice
mama bataso komai me nayi mata haka ta tsaneni lokaci guda ?

Sallah magaribane ya tayar damu a wajen nashige daki suna falo nan sukai sallah ina zaune na kunnu
wayata naji karan budan get din gidan muryan maigadin gidan yana tashi.

Wai ashe maigidan ne ya dawo a lokacin yake mashi sannu da zuwa salimace ta leko tana fadin ke ga
yaya nan wallahi dama ya habu yace kila yau din nan ya iso ai.

Mukan zamu tafi gida ke ban yau ashe sai lokacin na dago ina fadin haba anty salima ku tafi gida kamar
ya ?

In kun wuce dawa zan zauna kuma a wanan gidan kaji munafuka angonki ya dawo kice wai dawa zaki
zauna inba kina son sai dare yaya ya gargadamu mubi hanyan tudun wada da kafa ba.

Don wanan kwaliyan haka muddin yaya ya gansa yau wallahi idonsa rufewa zaiyi yace me kuma ya
tsayar damu ?
Na girgiza kai ina fadin anty Salima bamu haka dake fa keda kuma nake samun sauki a wajen ki kin
maye min gurbin mariata yau.

Tayi waje tana dariya na soma jin muryansu suna mashi sannu da zuwa yana amsawa a cikin muryan
nan nasa da dan maganan shi da sauri da sauri yana fadin a,a Nafisa kuna nan ashe sannuku da kokari fa
salima ya akayi kunsha hidima fa.

Can dai na daina jinshi a falon suma hakan saidai baifi ko minti biyar ba kuma naji yana fadin ya haka
kuma ina kuma zaku da daren nan .

Muryan Nafisa naji tana fadin gida yaya wai kada dare yayi muna a nan mu rasa abin hawa yace gida yin
me kuma don Allah ku mayar da kayan nan ba inda zaku yanzu kamar wa yanda ake kora kuma ina ita
Rahama din ?.

Muna ga rasulu na fada karda kirana zaiyi haka gabansu shifa haka yake ashe da kowa tsatsaye ba
ruwansa.

Ina zaune a inda nake na maida hankalina a wayata naji an ruro kofan da sallama ta dan dago mukai
arba dashi naji gabana ya soma faduwa .

Shima hakan yaji gabansa ya fadi a yadda ya hangoni din zaune saman kujeran dakin na dan dogara
jikina ga hannun kujera din da wayata a hannuna.

Ga wani irin ni,inttacen kamshi mai kashe jiki dake masa barazana da zuciyarsa ya tako har zuwa
gabana na dago cikin sanyin murya ina mashi sannu da dawowa .

Ya lumshe ido yana amsawa da yauwa amarya kinsha kamshi ya kika zauna ke kadai a nan gasu can a
falo su ko duk bakuntace har yanzu ?

Kamar yadda ya dake ya nuna ba komai nima hakan na dake na fara bashi mamaki nace a,a sallah
nashigo inyi sai ban fita ba.

Taso kije wai gida zasu yanzu amma nace a,a saboda me zasu gida yanzu daga dawowata muje falon
mu samesu .

Jin hakan yasa na mike tare da daukan dan yalolon gyalena dake gefe daya daga dagashi sai wani
kamshi ke fita na daban a dakin hakan yasa ya lumshe idonshi.

Ina mikewa naji ya cabki hannuna lokaci guda gaba dayan mu saida kowa jikinmu ya amsa yayi wani
yarrr tundai ni da tunda nake babu namijin daya tana ko gwada rike min hannu a rayuwata.

Inda shi kuma tsaban taushin da yaji a hannun nawane ya dimautar dashi haka muka fito falon suna
zaune tsit a falon sun kurawa tv ido sukaji muryanshi yana fadin.

Ga dai matar gidan na kawo muku tunda kuna son yi mata tawaye ku gudu zuwa gida Nafisa tace Allah
yaya daka barmu mun tafi tunda ka dawo me zamu zauna yi kuma a nan ?
To ke Rahama kinji sai ki basu hakkuri ni dai ban korar maki suba kada kice don ni suka tafi na dan
kallesu nayi murmushin da nasan zai dagulashi aiko saida tsikar jikinsa ya tashi nace aiba zasu tafi ba su
barni ni kadai.

Bari na kawo maka ruwa yaya nan na zare hannuna daga rikon da yayi min a cikin dabara na nufi
kitchen a cikin wani tako da ban ma san ina yinsa ba lokacin.

Inda ya shagala da kallon bayana ga rigar ta daneni ta baya mazauna da nakan juyawa anty maria don
taji haushi suna boucing a ciki.

Ya zauna yana lumshe ido a cikin gajiya ga wani bakon kasala da yaji lokaci guda yana sauka mashi
tunda yai arba dani ya koma daya sani hakan zai samu taro da yabar yaran nan sunyi tafiyansu amma
yanzu ya riga daya kwafsawa kansa kuma ai.

Ruwa na dauko a cikin tumbula da zaki iya ganin ruwan karara kwance a cikin madaukin sai cup din
glass irinsa dana hado dashi na kawo gabansa na dan rage tsawo ina tsiyayya masa lokacin ya sauke
hannunsa dake saman goshi ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya da shi kadai yasan dalilinsa.

Ya miko hannu ya karbi ruwan tare da fadin thanks ya kai bakinsa saida ya shanye ruwan tas ya aje
kofin yana fadin Salima yasu iya dai ?

Au bakaje can ba ke nan yace direct nan na nufo ai nagaji sosai yau salima da safen nan fa na dawo
Nageria na kuma hau jirgi zuwa Abuja daga lagos yanzu kuma gani gida aikinga akwai gajiya.

Kayan na kwashe zuwa kitchen na barshi dasu nan suna dan hiran zumuci can na gama yan dabaruna
sai gashi na kata fitowa da da try din dana hada na sake direwa a gabanshi.

Kazace data sha gyara wace taji albasa da kabeji su tattasai da kayan kamshi nayi warming dinta a
ovorn ga kuma lemun kwakwa da madara na kwali na aje na kallosa.

Naga duk hankalinsa yana kaina nace bissimillah yaya dare yayi kada ka kwana da yunwa suma nayi
masu tayi.

Ai kema ko dazun da mukaci bakici komai bs ki zauna kici Nafisa ta fada nace aiko naci mana anty Nafisa
mamaki kamar zai kasheshi a lokacin haka ya daure ya jawo zuwa gabanshi yana cire foilpepper din dana
rufa ya kai idonsa sama.

Ya kara lumshe idanunsa tare da hamdallah ga ubangiji yake fadin duk tare za aci ai ki zauna muci ya
fada yana masu bissimillah.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/13, 7:35 AM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



4️⃣3️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Wani yanayi na wasan yar tsamane ke gudana a tsakanina dashi agaban yan uwansa a lokacin don saiki
rantse da Allah dama akwai shakuwa ko soyayya sosai tsakanina dashi lokacin a haka muka nunke
zuciyarsu da kasa fahintar mu.

Suma din sai faman mamaki hakan kowansu keyi a zuciyanshi don yadda komai nakeyinsa a natse cikin
wayewan kai nafisace ta fara mikewa wanan lokacin.

Don barin falon wanan dakin da sukaiwa kansu masauki a cikinsa ta shiga da sunan kewayawa bandaki
daga nan bata fito ba kuma.

Kafin Salima itama tabi bayanta zuwa dakin suka barshi shi kadai a falon zaune yana waya.

Don lokacin na mike ina kwashe komai da akai amfani dashi zuwa kitchen na dawo na gyara wajen nan
na samu su dukkansu sun bar wajen a lokacin.
Zuwa lokacin barcine duk a idona don nima hidimar bukin da jewadi ya kashe min jiki don sai a lokacin
nake jin tsamin jikina na gama na nufi dakina na barshi nan a zaune falon kofan na rufo na fara zuge zip
din rigan jikina na fada bandaki.

Ina shiga na fara cude jikina da wani ruwan turarensu na madara irin tasu ta mutanem maiduguri
wanda mama tabani tace dinga hakan dashi da dare kafin na kwanta.

Bayan na gama na fito na dauki Rigan barcina dana dauko na dauka saman gado ina zurawa a jikina ji
don barcine sosai ne a idanuwana nake jiba a lokacin .

Ina kokarin zura rigarne naji anrugumeni ta baya ana sakar min nauyi da sauri na iya furta
subbahanallahi na ambata a fili duk jikina yana rawa lokaci guda don tsoron hakan da naji .

Danshina nayi kokarin juyowa cikin faduwan gaba don ganin ko waye haka ya razanani lokaci guda duk
da ban faye tsoro ba amma hakan dai ya firgitani.

Saidai haka din bai samu ba a gareni don irin rikon da akai min sam na kasa jiyowa din inga waye a
lokacin.

Amma saboda sautin numfashinsa dake shiga kunnena a lokacin naji a cikin wani yanayi wanan yasa
lokaci guda jikina ya dauki rawa tsoro yana dada shigata.

Wani abu naji yana min yawo tundaga tsakar kaina har zuwa yatsun kafana jikina sai kyarma yakeyi don
ban tsamaci hakan a lokacin ba.

Nauyin Kanshi da naji ya kwantar a kafadana yana fadin relex baby Rahama ba komai zan maki ba just
live me to hug you.

Na samu natsuwa kawai nake son samu a wanan lokacin yanzu gareki ya fada kamar mai yin rada a
lokacin cikin kunnuwata.

Kalman na natsuwa na sake maimaitawa a ciyana kamar wanda ya karanto zuciyana din naji yace
please Rahama don't judge me accondin to my sin ina kaunarki har cikin raina ke din kamar zabinace
Allah ya kawo min a sauwake har gida don Allah kada kice zaki hukuntani bisa kuskuren fahinta .

Hawayen da nake kokarin tarewa kada su zubo daga idona sune suka dinga diga saman hannunshi
haka ya sanar dashi kukan da nakeyi a lokacin mara sauti.

Subbahanallahi are you crying Rahama sabodani No no no no don Allah ki daina nasan ni mai laifine a
wajen na shiga maki rayuwa bada sanarwan ki ba.

Amma ina son ki dauki hakan a matsayin kaddaran mu gabaki dayan mu Allah yayi sai munyi rayuwa
irin hakan a tare dake koda iya hakane kuwa a rayuwan mu.

So ki bari na gama dan abindake gabana kafin mukai ga matsaya a tsakanin mu ba zan maki dole a
kaina ba Rahama ko haka Allah ya barmu nasan kinyiwa iyayye biyayya dani.
Naji dadin natsuwan da kika nuna a gaban sisters dina ko iya wanan kika barni dashi nagode Rahama
don kinyi min abinda ban taba zato ba a wajen ki.

Na dauka sam ba zan samu kallon arziki ba ko tarbo sannu da zuwa sai gashi kin fitar dani kunya a
lokaci guda wanda ni ban taba kawo hakan agareki ba.

Yana maganan yana kokarin dago habana dake dage yayin dana gane nufisa na cije cikina a waje daya
naki yarda hakan ya faru.

Sai naji yayi murmushi ya dan rage rikon da yai min din da farko wanan karon hannuna ya kama zuwa
bakin gado ya zaunar dani shima ya samu waje ya zauna a kusa dani.

Dan shiru ya biyo baya a dakin kafin yace wallahi Rahama banyi haka don in tauye maki rayuwa ba nayi
don ni a wajena komai naki wallahi yai min ina sonki sosai Rahama saboda halaiyan ki don haka ki ban
hadin kai mu zauna lafiya.

A raina nace bakai bane yanzu fa ya gama cewa jn bashi time in rufa mai asiri ya fara fuskantar
abindake gabanshi yanzu.

Yanzu kuma ya dawo yana rokona da mu zauna lafiya bisa amana kada dai ya zamo munafukin namiji
mai baki biyu ?

Wa yan can suma Allah kadai yasan irin dadin bakin da yaje yayi masu a kaina duk da ban tabbatar ba
amma akasarin maza haka suke da baki biyu ga matansu.

Me aka fada maki Rahama akan zargi wata zuciya ta tuna min da hakan daga bangaren zuciya tiryan
tiryan nake tuno zancen su hjy yabi da sukai min a karshe don haka dole inyi taka tsantsan da rudin
zuciya mai kai mutum ga halaka .

Wanan aure dai matukar bashi yace ya fasa ba dole in hakkura da komai in zauna da yaya saboda
biyayya kamar yadda su daddy suka rokeni dayi don haka alkawari na dauka in sha Allahu zanyi biyayya
ga zaman aurena a gidan ya Jafar har inda rabon zaman a tare dasu.

A zatona zai koma dayan dakin daba kowane kamar yadda anty salma take sheda min wancan dakin
yurakanshine nan kuma nawa sauran dakunan biyu kuma na aje don baki daya kuma na dinga amfani
dashi ni kaina daki biyu ke nan suka ware min ni daya ko ina zan kaishi oho ?

Hannuna ya sake rikowa yana dan murza yatsuna a hankali kamar dai wanda ke wasa da hannun yaro
yayin da wani boyayyen sakon da ban,saba dashi ba ke bin ilahirin jikina yana sakar min da kasala.

Kan na tantance sai ji nayi ya sumbaci gefen wuyana nan da nan jikina ya fara rawa tsoron hakan karara
ya baiyana a gareni lokaci guda.

No kwanta ki huta akwai gajiya a tare dake ya fada yana kokarin kwantar dani saman gadon kamar
karamar yarinya banki ba nayi yadda yacen na dunkule a waje daya ina mai kame jikina.
Wani ajiyan zuciya ya sauke yana kaiwa kwance daga gefena nima din na sakankace da zancenshi
hakan yasa na lumshe idona ina sauke ajiyan zuciya.

Ido a rufe zuciya tab da fargaba da zullumin hakan dana tsunci kaina a cikinsa lokaci daya naji saukan
hannunsa saman jikina a daidai wajen da nayi shekara da shekaru ina boyon abina da hijjabi ko gyale yau
sai gashi a saukake hannun wani ya kai ga wanan abin.

Bai dai min komai ba a ranan kamar yadda yace saidai nasha luguda kamar mangoron da akeson ya
nuna a lokaci daya.

Da misalin karfe hudun asuba naji tashinsa already na falka a lokacin don sabo da hakan danayi a
rayuwata ban daki ya shiga ya dan jima kafin ya fito yana dan kiran sunna da intashi kada in nakara ganin
na falka ya bude dakin ya fita hakan ya ban daman samu na mike na shiga bandakin.

Wanka nayi ina hawaye har nagama na fito na dauko kayan sallah acikin wardrobe dina na tayar da
sallah ina idarwa na koma barcin don idona cike yake da barci a lokacin.

Alhamdullahi don ko na samu barcin nayi ban falka ba sai wajajen takwas na safe na tashi dakin na
fara gyarawa duk da a gyarensa yake amma haka bai hana na kara tsayawa na gyara ba na sauya zanin
gadon na sharo na kawo kamshi na feshe dakin dashi na shiga wanka.

Bayan na fito na saka kaya wasu light green lace mara nauyi da akai masu dinkin riga da skirt na saka
sunji duwatsu anyi kwaliya a gaban rigan da bakin lace din saina zauna gyaran fuskana a gaban mirro.

Lokacin ya shigo dakin a cikin shirinsa na wasu fararen shadda da akaiwa dinkin gajeren hunnu sai
bakaken takalma a kafasa kansa babu hula.

Da sallama na amsa ina dukar da kaina kasa ya karaso yazo daidai bayana ya tsaya muna kallon juna a
morron nayi kasa da kaina na zame kasan kujeran na duka ina gaidashi da kwana.

Wani irin mamakine da yarinyar nan take kasheshi dashi yaushe rabon daya tunama ana gaida miji da
kwana a addinance ko al,ada ?

Wani irin son ta yaji yana kara shiga zuciyarshi don tunda yake koda tuntuben harshe matansa basu
gaidashi da kwana wani lokacin ma da fada suke tashi tsakaninsu tun asuba.

Hannuna ya kamo muka koma bakin gado muka zauna naji ya ambaci sunana yana fadin Rahama jiya
kin shayar dani farin ciki a rayuwata kin tabbatar min ke din yar mutuncine data gaji hakan.

Kin tsare mutuncinki dana iyayyenki ko a hakan da kikai min nagode sosai Allah yayi maki albarka nayi
kasa da kaina a cikin nauyi da kunyarshi.

Wallahi Rahama komai naki kara burgeni yakeyi ina son ki sosai wallahi don Allah ki ban hadin kai mu
zauna lafiya Rahama".

Abune a baiyane da kika sani tun bayan wata ukku da aurena da Asmau farin ciki ya gushe min ba
zance banjin dadin zama dasu ba don su din matanane amanatace kuma su din.
Amma sun kasa ban irin farin cikin dana taso ina mafalkin kansancewa a cikinsa sun hana min
kwanciyan hankali sun kasa gyara kansu wanan duk ba bakon abu bane a wajen ki don kinsan komai.

Wayanshi dake ringing bai kula dashi ba nakai ido na kalla sunan ya Habu na gani a wayan ganin ina
kallon waya yasa ya dauka yana fadin.

Hello Habu ganina shirya yanzu zan karya in fito kana gida ko ban daiji amsan da habu din ya bashi na
daiji yace hakan yayi daidai zanzo da salima din.

Mike tsaye yana fadin tashi muje ki karya yaran nan sun hada muna abin kari yana falo ina son in
mugama zan shiga gida mu gaisa dasu don ban samu zuwa jiya ba na gaji da yawa.

A raina nace ka daizo hanawa rayuwata shakat malam banki ba din na mike

41 / 101