Chapter 50 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   50 / 101

147K to 150K   out of 302.2K words

saki fa shi haka yaga mahaifinsa yayi daga zancen fatan baki zai furta wa yarinyar nan saki dama
bai shiryawa fitinan mata ba ya tarasu haka gidansa ?

Ki dai gyara kalamin ki ina horon ki da hakan matsalansuce can kinsan irin cin mutunci da tayi masa har
aka kaiga hakan ?

Saiga Saare ta dawo tana fadin wallahi kuwa wai sakinta yayi ta cikin waya daga magana kawai ya furta
wai ya saketa.

Gata can zata wuce kaduna yanzu dole mama ta mike zuwa part din ta bata hakkuri akan ta zauna sai
kukan da takeyi .

Bayan mama ta fitone yarta ta bugo waya take fadin wai ta dawo gida zaman me zatayi tunda yace ya
saketa din me zata zauna yi kuma ta dawo gida kawai.

Wanan yasa ta fita ba tare da sanin kowa ba tabar gidan zuwa kaduna din itako mama tana ta neman
layinsa bata samu ba saina habu ta samu yake fada mata ya sauke j din har sun tafi.

Shima gashi ya kusa isowa gida in sha Allahu sai batayi mai magana komai ba ta bari sai ya iso gida din
taji meya faru.

Koda ya iso ko part dinshi bai shiga ba ta tareshi da zancen cikin mamaki yake fadin saki kuma ita saiba
tace sakinta yayi bayan agabana sukai maganan .

Zaginsa takeyi tana ja mashi Allah ya isa shi kuma yace taje gidansu ta huta iya abinda na sani ke nan ya
faru tsakaninsu.

Kunj ko mena fada maku ba yarinyar kirki bace shikan ya juya zuwa part dinsu ya batsu nan ana zancen
saiba din a part dinshine Maria ke fada mai abinda ta fada game damu din yace hauka takeyi kila ?

Zamfara garin gusau.

Kiri,kiri baraka ta hawa Aliyu kudin nan tace ya bari mahaifinsu ya fara juya idan sun kara yawa sai a
samu abinda aka bashi shima ya soma nasa sana,an.

Tun daga lokacin bai kara magana ba kuma yakawo ido yasa abinda bata sani ba shine shi Aliyu yasan
mai mahaifin nasu ke aikatawa don wata bazarawace a nan makwabtansu daya taba nema taci mashi
kudi ta koma zurmi tayi aure itace ta fito yanzu kuma bai daddara ba ya koma nemanta gadan gadan .
Shine Aliyun yaso su zauna da uwar nasa ya hanata bashi kudin amma taki saurarenshi lokacin take
ganin kudin yaron ke son ta mika mashi duka.

Shiko Aliyun yadda yaso shine su samu dan fili su saye da rabin kudin rabi kuma ansan yadda za ayi
amma batab basira ya kamata ta dauki kudin duka ta mikawa mijin nata da sunan zai fara sana,an hatsi
dasu yana shiga kauyuka yana soyowa ya kawo nan cikon zamfara din tayi na,am da hakan.

Balle dataga haikam ya bazama kasuwa sai dadi ya kara kashe mata zuciya gashi in zai dawo da dan
cafanen su na kauye daga ita har yaran sun canza sosai a yanzu gaskiya.

Zamana da anty Salima da habiba ba laifi gaskiya saidai matsalan daya shine banda saurin sakewa sosai
har yanzu dai halin nan nawa yana nan a yadda takan fada ita saliman .

Idan naje school na dawo ina daki ina hutawa sai dare zan dan fito mu zauna a ci abinci a danyi hira
kuma in koma dakin karatu.

Wanan yasa take ganin wai banda saki a bakinta nake jin abinda ya faru wai saiba tana gidansu yaya ya
saketa.

Gabana ya fadi sosai da jin wanan labarin don na tabbatar za ace saboda nice hakan ya faru tsakaninsu
niko harga Allah ban sani ba.

Nasan dai kafin yayi tafiyanshi yana lagos lokacin zai kirani mu gaisa wani lokacin ma shike tashina daga
barci da asuba ko kuma ya kira da safe yana tambayan ko nafita zuwa school ?

Amma tunda yabar kasan sai gaisawa yayi wuya a tsakanin mu dashi matsala dayace ban yarda na
nuna masu hakan ba don salima tana yawan tambayana shi nace yana lafiya ai.

Ranan wreekend ban fita ba ranan ina daki kwance ina barci anty Nafisa tashigo muryansune suna hira
falo yasa nafito don mu gaisa da ita.

Tunda na fito ta kyala ido ta kalleni take fadin wai wai wai Rahama kece haka wai lalai aure Rahamane
sunan naki yabi zancen kinga yadda kika koma wata buleliya dake haka ?

Cikon dan kunya nakai zaune ina fadin anty Nafisa sheri zakiyi min kuma bamu haka dake fa tace
wallahi Rahama kin canza min lokaci guda ?

Anty Salima na nuna ina fadin gata nan itace ke ban dadi na koma hakan ai muka dara gaba dayan mu
nakai zaune ina fadin wai anty Nafisa daga barin je in dawo ranan kikai tafiyan ki ?

To ai gani na dawo Rahama fitan ne yanzu ban faye sonshi ba mutane sun faye gulma yanzu tin anayi a
bayanka har an fara fadama zance kamar mutun shine zai nemo miji da kansa ?

Allah shiyasa banson fita ko ina aiko gidan iya ni tun bukin ki ban kara taka gidan nan ba har yau
nocking din kofan da akeyi ya katse mata zancen.
Habiba ta mike ta fita don ganin waye sai gata ta juyo tana fadin matar Uncle ce da wasu kafin ma ta
gama zancen sun fado dakin cikin gadara da wani irin kallo.

Duk da gabana ya fadi don ganinsu a lokacin saidai ban nuna hakan a fili ba naji wata daga cikinsu
tana fadin a,a lalai kan Abuja ?

Tunda na mike ban tsaya mu gaisa ba kitchen na nufa na dauko ruwa da abinsha na kawo masu tare
da cups na aje a gabansu naji dayan tace to aimu ba ruwa mukazo sha ba.

Haba dai kusha ruwa mana na sake fada cikin danjin nauyisu sai naji saiban tace ainan ba gidan da
zamu tsaya bakunta bane balle a kama bamu baki musha ruwa.

Kashedi nazo maki akan mijina Ramaah ina jin hakan nace to nakai zaune gefen hannun kujeran da
anty Nafisa take zaune sama.

Sai naji anty Nafisa tana fadin haba dai anty Saiba hakan aiba girman ki bane yaya zaki mata gida kice
haka kuma ?

Ke Nafisa dakata ban ambaci sunan ki ba dana shigo don haka ki kyaleni inyi da ita, ita da yanzu take
ganin takai tunda tasan yadda suka shiga suka fita suka iya asirce shi har ya aureta ?

Tunda sun saba da bakar bidan asiri suna mallake mutane har ita ta isa tasa J ya juya muna baya ya
daina shiga duk wani harkan mu wallahi bata isa ba ?

Daga ita har Maria din da kike takama ta samu habu ta mayar dashi saniyan tatsanku da kowa naku
saidai ku tsaya ga habu shida kuka sama amma baku kai can ba wallahi.

Ashe nakai har na usa kuma ke nan tunda har na iya mashi asiri daya kamashi don da bakiga hakan ba
da baki tako har nan zuwa min kashedin ba ?

Daga daga inda nake zaune nake fadan hakan tare da jin duk wani tsoronta da shakkunta ya fita a raina
lokaci guda.

Wallahi ke Ramaah karamar yar iskace baki isa ba wallahi ina ganin hakan na mike tsaye na sake fadin
ai isan ya kawo haka tunda gashi har kin tako zuwa gidana ko kunyan hakan bakiji ba ko kin gani gidan ku
?

Ta kwashe da wani irin dariya tana fadin wai gidanki kuji min yarinyar nan fa kije gidan mana idan kin
isa mara kunya kike da gaske kije gidan ?

Gida kan ko yau nake son zuwa zanje don baki da wuta baki da aljanna akaina Nusaiba kuma gida ba
naki bane don haka baki isa ki hani shiga ba.

Bansan ya akayi Salima ta kira mama ba na daiga tana fadin wallahi mama muna zaune suka shigo ita
dasu anty ikilimanta.
Niko ina fadin ai bansan kin dau abinda zafi haka ba dana rigaki yi maki takaka a gidan inga abinda zaki
min din ?

Haka kikace zan dawo ko don ki wallahi nace ki dai dawo don mijinki daya ajeki amma ba dai niba
basan da tsiya kikazo ba dana tareki dashi tun farko ?

Yanzu da kika sani ai sai kiyi wace zakiyi din tunda kin sani ke dai da tsiyan ta kawoki ai ina sauraren ki ?

Anty salima na fadin wai ba zaku daina ba don Allah ke saiba duk inda akaje baki da gaskiya tunda ke
kikazo har gidanta .

Kaji wata munafuka na amsa da fadin munafuka tafiki Nusaiba ?

Saida ta kalloni cikin mamakin jin abinda na fada nace keda kika yi munafuncin daya ciki kika fada ciki
inkina ganin kin iya sheri an fi wallahi.

Koda yake ba abin mamaki bane ai tunda dama kowa ta dalilin sheri da munafunci ya sanki a gidan.

Don kawarki kikaiwa kwancen miji gashi har kina nuna kinfi son mijin fiye da ita a yanzu kin dauka
zakiyi min sherine yaje a banza ko gobe kika kara min sheri zakiga fiyema da hakan wallahi.

Sam ban yarda na raga mata ba kamar yadda anty Salma ta fada min inyi a duk wace tayi min takaka a
cikinsu in debe tsoro da kunya inyiwa maishi tas don gobe karta dawo min gida .

Hakan ko nayi mata don na debe tsorona a lokacin na shafawa idona tako na mayar mata da martani
don a debe tsoron juna a tsakanin mu dama ina kule da ita a raina har lokacin.

Jin wayan da Salima keyi da yaya Habu yasa suka bar gidan ajata ajani tana fadin bata zuwa ko ina sai
taga karyan rashin kunyata gidan .

Don naga na samu waje zan kawo mata iskanci zata gwada min ko ita waye ranan don sai ta murjeni
kamar filawa nace mudai murji juna dake Nusaiba bari ganin kinzo da wa yan nan wallahi, in kuma kina
iyawa ki gwada.

Sai kuma ta juya kan Salima da Nafisa tana fadin ku kuma haka zasu kare a gurin bin kanwar baya
bayanku don kwadayi da wullakanci .

Su rasa wace zasu bi har gidanta saini suje suyi aure yafi masu zama gindin yarinya karama suna zugani
ina daukan ni wata tsiyace ?

Fadan ya koma namu duka kowa ya fadawa dan uwa maganan dake bakinsa data sani batai hakan ba
da har gobe tana da matsayi a wajena na wace ta girmeni kuma take gaba dani a gidan aure.

Saidai kash zuciya yakaita da girmanta ya fadi wajen kowa a wanan lokacin don ita kanta bata taba
zaton zan iya bude baki inyi mata haka ba.
Koda yaya Habu ya iso sun tafi ko yace zai dauki mataki kan hakan agabanmu yakewa maigadi warning
da kada ya kara bari wanan matan su shigo gidan nan.

Anyi haka da kamar sati zancen ya lafane don har kaduna mama taje da kanta suka dawo da ita bayan
an tsawata har lokacin kuma shi bai dawo ba kasan saidai da alaman yaji duk abinda ya faru don daya
kira yake tambayana cewa bata sake zuwa ba ko ?

Na amsa da bata zo ba don yakan kira a sati saudaya ko sau biyu a cikin sati yaji lafiyan mu a dan
gaigaisa da jama,a kuma.

Hafsatu dake tankade a kofan kitchen taga mijinta ya fito da shirinsa ta bishi da idanu don yanzu
gaskiya karara ya canza mata fuska gashi alkawuran da yayi na gyaran dakin yaransu bai cika ba.

Wayanshi dayayi kara a cikin aljihu ya tsaya dauka daga kofan dakin nasa ta gane dawa yake wayan don
jin sunan mama dubu daya ambata sun dan jima suna magana kafin taji ya soma fadin.

Amma ita salima me zatayi da kudi har haka kudin nan fa gaba daya na dauka nasaka a wanan sana,an
takin don yanzu kinsan shike shiga da sauri da daminan nan .

Kallonsa da sauri Hafsatu matarshi tayi ganin hakan yasa ya karasa saka takalman shi dake kofan daki
ya fita ta bishi da kallon tsarguwa.

Wani kudi yake zancen yakai sayen taki dashi dazaice hakan amma ai gamu gani badai a kan kudin nan
ya matse mata ido da wani hurda ya rikesu gaba daya ya sauya mata.

Dakin dake kusa da hanyar bandakinsune wanda iya take rayuwa da a cikinsa kafin a sai wancan gidan
da suke zaune a cikinsa yanzu.

Shi taga ya gyare fes tayi magana yace bataga ginan ya rankwafo bane kada ya fadi saita yarda da
hakan daya fada lokacin.

Sunyi hakan da yamma yana cin abinci yake fadin ina ganin fa zamu karu a gidan nan hafsatu amma
saidai yadda hali yayi tukun don bamu gama shiryawa ba tukum da bazawar tawa har yanzu.

Aiko hafsatun tayi cikin shi da masifa ta inda take shiga banab take fita ashe duk lokacin ankai sati biyu
da daura aurensa bata sani ba sai lokacin ya gwada fada mata aiko baisha da dadi ba a ranan wajenta



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/24, 10:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: Seenabu Makawa: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



5️⃣2️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Yaya J saida yayi wata biyu ya dawo lokacin muna gab da fara jerabawa shigowan yamma yayi garin don
na dawo school muna falo da salima da Nafisa da yanzu zamanta ya dawo gidan tun bayan rikicin mu da
saiba data zo har nan gidana taso yi min yankar kauna.

Sai Allah yaban sa,a na aro rigan rashin mutunci na yaga mata nata haka ta tafi tana mamakina shi
kuma yaya Habu da yaji ya sameta har gidansu yaci mata mutunci sukayi ba dadi dashi.

Amma kuma da mama dubu taji bata ragawa habu din ba don cewa tayi halin kishine bai kamata shina
miji har ya saka bakinsa ba yana nufin don ina yar uwar matarshi ya goyi bayana ke nan.

Ita batace abinda saiba tayi tayi daidai ba amma sha,anin kishi ba yadda baya zuwa don kowa da irin
tasa fahintar kada suce zasu nuna wariya a tsakanin mu tun yanzu.

Baidai ji dadi ba amma kalla baicewa mama din ba lokacin ya mike ya fita bayan kwana biyu tasa yaya
Ibrahim ya kaita kaduna ta samu iyayyen saiba din ta basu hakkuri kan abubuwan dake faruwa.

Sukuma suka dunguma Saiba din suka mikawa hjy bayan tasha fada kan rashin hankalin datazo gida
tayi min din ita da yan uwanta.
Anty Nafisace ta fara fadin kamar muryan yaya Jafar nake ji a waje donshi na fada maki a baya haka
yake maganansa a cikin dan sauri sauri tare da dan sarke harshe kamar me i,i,niya wani lokacin.

Don sai ka saurara da kyau zakaji abinda yake fadi wani lokacin saboda saurin magana da Allah ya
bashi.

Shi din ne kuwa ya shigo yana sallama suit ne a jikinsa arsh colour sai farar riga daga ciki daya dan
baiyana fili sakamakon balle anineyan saman rigan da yayi .

Har muna hada baki wajen yi mashi sannu da zuwa ya amsa cikin jin dadi hankalinsa yana kaina kai
namiji baida kunya wani lokaci.

Batare da jin nauyin sisters dinsa ba ya miko min hannu wai inzo inda yake tsaye na noke kaina da sauri
a cikin kunya.

Kaji bakauya don Allah tashi kije miji ya dawo yana kewan ki anty Salima ta fada tana mikewa tsaye
itako Nafisa dariya tayi ta mike itama sai biba tabi bayan su.

Hakan ya ban daman mikewa zuwa gareshi don har lokacin yana tsaye ya ware da hannayensa alaman
yana jira inzo gareshi din.

A cikin wani tako na karasa wajenshi ya mayar da hannun nasa ya rufe na dora kaina saman kirjinsa ina
lumshe idona a hankali tare da ajiyan zuciya.

Kanshi ya dora a nawa yana shakan kamshin ni,intacen mangashi irin na kanuri da ake hadawa da
wasu itattuwa da kayan yaji irin na gargajiya.

Mai,ne na kitso mai inganci da ko ancen kasan nasu ba kasafai ake samunshi ba sai kinyi bucking dinsa
don mamata aika lokacin anjima ba a kawo ba amma dai ana kawosa naga anty salma ta banye kai tayi
kitso dashi.

Nima akai min tun lokacin nake jin dadin amfani dashi ina jin ajikina shima hakanne don yadda yake
shakan kamshin daga kan nawa a lokacin.

Dakinsa muka nufa saman gado muka fada a tare don yaki sakina ya shiga lalubata ganin abin nasa
nason wuce gona da iri yasa nayi dabara na shammaceshi nasamu na mike da sauri nabar gadon .

A kasalance naga ya koma ya kwanta yayi rigingine yana kallon saman dakin saida na samu na saita
kaina nake fadin .

Ko ruwa baka sha ba yaya ?

Saida ya furzo da iska daga bakinsa yake fadin ruwan da nake son sha an hana min debe kishina naga
ya lumshe idonsa sai danyi kasa da kaina ina fadin.

Ba a nan ya dace ka debe ba ai tunda ba gidan nan zaka sauka ba koka manta a nan ka tafi da zakai
tafiyan ?
Ok kawai yace min a takaice ya kara lumshe idonshi nikan na fice a dakin kada shedan ya ribance mu a
lokacin.

Anty Salma ta fada min duk abinda zanyi ko ma meye kada in yarda in shaga hakkin abokan zamana
don alhaki yana waiwayan mutum watarana don haka nake kiyayye wanan huduban nata.

Ruwa da cup na shirya a ture nakai mashi dakin inda na samu har lokacin yana kwance a yadda na
barshi bai min magana ba kuma har na zuba na fita daga dakin.

Duk da banji dadin hakan ba amma ya zama dole in kiyayye hakan kada mu fada ga halaka dama ta
fada min su maza babu ruwansu da hakan wani lokaci matukar zasu samu biyan bukatansu.

Dakina na koma inda a nan na zauna don kunyan su Nafisa da nake ji lokacin ban fito ba har akai sallah
magariba ina dakin isha,i tayi nagabatar still bai shigo dakin nawa ba har lokacin.

Wanka nashiga har na fito na shirya cikin wani dogon riga ina sai lokacinne ya shigo yana fadin ba zan
samu abinci ba ke nan ma

50 / 101