Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
da shirun take fadin ku saya zakace nace idan kuje dashi aka saka a fridge zaiyi
rabin shekara a can bai baci ba wanan karon a cikin hausa tayi maganan tana kara bude manyan koren
dake gabansu.
Sahabi bai yarda da zancen ta ba don abar zancen yake fadin wai ina zamu samu abinci mai kyau a
wajen nan ?
Ta dan juya kafin ta fara masa kwantace ganin baigane ba yasa ta kwalawa wata yarinya kira da Maria
zoki nan saiga wanan yarinyar dake firgitashi tun zuwansu garin itace aka kira da Maria din.
Yarinya ce karama saidai da gani ba sai an tambaya ba don kamarsu da yar uwar nata da aka kira da
yanda sukayi kama sosai ita wanan din dai ta girmewa yarinyar a shekarune kawai zace sai dan haske da
karamar ta dara babban dashi.
A cikin yare take fada mata ta kaisu wajen saida abincin yan maiduguri ta amsa da to tana watso masu
idanuwanta masu kama da madaran tana wani irin juyasu alaman suje din tayi gaba suka bi bayanta .
Zansu tafi babban matar ke fadin ya zancen sayan kayan sahabi yana kokarin fadin su barshi kawai shi
kuma Abubakar din yace dasu a bari su dawo zasu saya hakan yasa yaga fara,a a fuskan yar budurwan
data kashe zuciyarshi da mamakinsu.
Sun kama hanya tana gaba da dan kwarya karami a hannunta bata ko tsaya wani jerawa dasu ba tasha
wani kwana suna biye da ita har zuwa wanan wajen da basu san dashi ba.
Oya mun gode ki tafi kada a nemeki Sahabi ya fada sai ta amsa da to tana kallonsu saidai taki gusawa
daga inda take.
Abubakar daya kula yace da yarinyar yaki zo nan Abubukar ya fada yana kallonta da sauri ta biyoshi a
baya zuwa inda suka nufa.
Tare suka shiga shagon yasa aka hada mata take away guda ukku ana mika mata ta juya a guje cikin
murna bata ko tsaya godiya ba ta nufi sansaninsu kai tsaye da gudunta a cikin murna.
Murmushi yayi ya juya wajen sahabi dake mamakinshi yace mutumina yaya dai nisawa yayi yana zama
ya soma fadin tausayi suka bani wallahi.
Haka duniya take ai dama ba ko yaushe mutum ke samun yadda yake so ba a duniya sahabi ya fada
yana kallon abinci gabansa da aka aje masu.
Abincine lafiyayye mai kyau irin na hausawa ga kamshin man shanu yana tashi acikinsa sukaci sukaiwa
yan uwansu take away.
Duk abinda yake hankalinsa na gun wa yan nan mutanen don hakane ya saci jiki ya koma sansanin nasu
saidai ya samu basa nan don lokacin yamma tayi sai wata mace dake zama a kusa dasu.
Yake tambaya take fada mai ai basu kai dare a wajen sun koma gida saidai gobe tunda safe zai samesu
sun fito insha Allahu.
Washegari kuwa rana ta biyu da taron mutane sun fara tattara kayansu don shirin komawa garuwansu
daga ciki har dasu Abubakar duk daidai su sai an rufe taron suke son su kama hanya komai dare a ranan.
Bai manta da zancen yaran nan ba don da zancensu ya kwana a zuciyarshi yana son ya san wani abu a
game dasu din.
hanya kama ya nufi runfarsu tun daga nisa ya fara hango ita babban wacce yake kyautata zaton
mahaifiyarsuce ga wasu yan Nageria suna sayan kayansu.
Don kayan nasu gaskiya yayi kyau sosai haka ya karasa gaban ya dan tsaya yana dakon su gama
cinikaiya da wa yanda ya sama din a wajen.
Karamar ya fara gani a gabansa tana binsa da kallo kafin ya tsinkayo babban dake tafe da amalanken
shannunsu dake dauke da kore.
Yana wajen suka sauke kayan tsab suka jera kafin ta dago ta soma gaiyar dashi a cikin dan fara,a kafin
tace dashi na dauka kun muna wayaune ai kun tafi koda yake bakai kama da mayaudariba ba kai kan.
Jiya kuma sai kukayi wahala haka kuka saya muna abinci mai yawa angode Allah kara arziki me za a
baka daga ciki ta fada tana kallonshi tana dago kai ?
Samu tayi ya zuba mata ido baya ko kiftawa sai tayi murmushi ta sake maimaita wane kake so yace
yanzu ni ina na san me zance dake ?.
Tace wanan zaka iya saya kakaiwa iyali mata ko mama da yan uwa zasuji dadin tsaraban shi ansan ka
shigo kasan cameron .
Ko data dago kai still yana kallonta sosai sai taji ta tsargu da hakan ta dan dukar da kanta kasa tana
wasa da zara zaran yatsunta.
Bakayi magana ba ta kara fada kallon yadda ake durawa mutane a jarka yayi yace nawa duka kayan
nan da kika sauke ?
Ido ta zaro waje tace dukka fa kace zasu iya kaiwa dubu hamsin da kudinku na Nageria ga mamakinta
sai taga yana kokarin zaro kudin daga jikinsa.
Kuyi min parking dinshi yadda ba zai samu matsala ba kudin abinda zakiyi amfani dashi ayi parking
yana ciki saidai don Allah ?
Saita dago ta kalloshi yayi mamakin ganin idonta da hawaye jikinshine yai sanyi ya dan matsa kusa yana
fadin.
Lafiya dai tayi kasa da kai tana fadin bansan irin godiya da zan maka ba a yau da an watse taron nan
bamu saida kayan nan ba ba karamin fitina zamu shiga ciki ba don zamuyi hasara sosai zamu kuma shiga
cikin ukuba.
Saboda me ya tambaya yana kasheta da ido donson jin karin bayani shidai yanayin yarinyar yayi mashi
sosai tana da natsuwa sosai dayake hangowa a gareta.
Murmushi tayi tana fadin dogon labarine mundai gode da wanan taimakon da kayi muna Allah ne
kadai zai sakama da alherinsa.
Amma meya dawo daku kasan nan kuda kuka saba da rayuwan Nageria kuka zabi dawowa nan ku
zauna ?
Ya zamuyi bamu da kowa a can yanzu wanda yayi sanadin zuwanmu can Allah ya karbi abinshi dole
muka dawo kasan nan tunda ba yadda zamuyi.
Kina da waya in naje mu dinga gaisawa daku tace da ina dashi wanda nake amfani dashi a school saidai
zuwan mu nan gaskiya mun kadar saboda yanayi saidai ka ban number wata rana zan kira insha Allah.
Ai har karatu kinyi ashe kuma kika kare a nan kina tallan nono tace wanda baida gata ai duk yadda
rayuwa tazo mashi haka zai rungumeta mun rasa gatanmu tunda mahaifinmu ya rasu Allah ya jikansa
yace ta amsa da amin.
Sai wata rana kenan zaki kira ba zaki kira kiji ko mun sauka lafiya ba ko kuma ina da bukatan wanan
abin ki turo muna dashi.
Dariya abin ya bata cikin dan kunya take fadin kayi hakkuri banda wayace kona karba ba zan kira ba din
kaga ai gara dai kar nayima karya.
Kinsan wajen motar mu ko ta amsa da ehh yace a shirya komai kusamemu can ya juya ya tafi ta bishi
da kallo tana yaba irin kirkinsa da halarci.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A tsaye ta sameshi suna hada kayansu sallama tayi daga bayanshi cikin yar siriryar muryanta ganin
kalkon mamakin da Sahabi ke mata a bayanshi yasashi juyawa da sauri yagame sahabi din ke kallo a
wajen ?
Kasa tayi da kai tana kokarin gaidashi da aiki ta hada da fadin ga kayan ka an hada komai yadda ya dace
daga nan ko lagos zaka ba zaiyi komai ba insha Allahu.
Ba lagos zani dasu ba zariya zan kaiwa mahaifiyata ya bata amsa tace Allah sarki aiko yayi daidai da
bakin tsofi don komai baida tsami da zai hanata bukatansu.
Mungode kwarai wallahi yadda ka taimaki rayuwan mu Allah ya taimaki naka kaima ta fada cikin yar
siririyar muryanta.
Wai tsaya Habu wanan duk kayankane wanan haka kome nifa ban gane ba wuceshi yayi yana fadin ba
zaka gane ba kuwa kai matso ku saka min a bayan mota kunji ?
Lokacin ibrahim ya karaso yana fadin oga kace da shirinka dama muma bari mu debo namu ashe dama
ina son saya ina jin tsoro.
Kaje gunta kayansu yana da kyau sosai tace dariya sosai Sahabi ya kwashe dashi yana fadin ashe mun
saura dawowa garin da alama zamu dawo wani karon kenan kuma ?
Yar filo akwai saura a wajen ku tace eh za a samu bari na duba idan akwai a wajen maman mu ta juya
ta soma tafiya .
Kai dan iskane yacewa Sahabi dake ta kwasan dariyan shakiyanci sahabi din yace dariya nake don
yadda na hasko kayi tsaye ana shadinka kasan wanan aiba karamin shadi zakasha akanta ba wallahi.
Shima zancen sahabin saida ya sakashi dariya in akwai abinda ya tsana a taba lafiyan jikinshi balle shadi
ta ina zai tsaya kan mace ai mai shadi ko gudane balle ba adadi.
Zama yayi saman motan yana sauraren Sahabi dake bayani akan shadi da yadda akewa wanda ya gaza
motsin wayarshi ce da tayi dan tsuwa daga Aljihunshi hakan yasa yaciro ya duba alert ne na lokaci har
yayi niyar mayar da wayar sai kuma ya fasa hakan sim din ya debe daga cikin wayar ya mike tsaye.
Wani wuri dayaga ana sayar da waya ya dosa layin waya ya saya duk da tsadansa bai tsaya neman ragi
ba ya biya ya juya ya koma inda ya fito.
Ya gama turo komai a dayan wayan nasa kafin ya goge na wanan wayan yana gamawa tana karasowa
wajen da kayan ibrahim.
Kudi ibrahim ya ciro ya bata yana fadin Allah yasa dai yadda kika yaba haka yake don kada muje gida
mu samu ba gaskiya bane yana da matsala ?
Irin duban mamaki din nan ta danyi masa kafin ta rausaya kai tana fadin Allah ya tsareni da cutar daku
idan na cuceku ina zan ganku ku yafe min ?
Daga haka tasa kai ta juya ta zoma tafiya inda kayansu yake daga bayanta muryan Abubakar ne yake
tsayar da ita a bayanta ta juyo ta dakata har ya tako zuwa inda take.
Baiyi wani magana ba wayan hannunshi kawai ya mika mata bata karba ba kallonshi tayi cikin mamaki
ki karba mu rika gaisawa idan nakoma gida.
Kaita fara girgiza mashi tana fadin ka barshi bayan wanan alherin dakai muna mai yawa zaka kuma
mika min waya ?
Ko haka mun gode kasan girman taimakon da kaimuna a yanzu har in mutu ba zan manta da hakan ba
a rayuwata zan kuma cigaba dayima addua a kullum kan wanan alherin.
Haba dai ya fada yana dan dariya kafin ya saita kansa yana fadin wai zaman me kike a wanan kasan
yanzu ko wasan nan ya kawo kuma nan ?
Yanayin fuskanta ta sauya lokaci guda tana fadin na fadama kaddaran zaman mu nan sanadin
mahaifinmu daya rasu shine zaman mu ya dawo nan kasan don bamu da kowa can Abuja da muke
zaune.
Nan kuma mun dawone a cikin yan uwa saidai duk da mun dawo cikinsu da zama har yanzu suna,,,,,,
Yanda warre ?
Wata bakar mace ta sa mata kira daga wajen saida kayansu hakan yasa ta juya da sauri da zumar ta
wuce saka mata wayan yayi a cikin kwaryan dake rike a hannunta ya juya ya koma inda ya fito ta dan
tsaya ta kalleshi kafin ta nufi wajen nasu saidai kafin takai tacire wayan cikin dabara ta kada a kasan
lalitan dake rataye a wuyanta.
Basu dauki lokaci a wajen ba taba da umurnin su shirya su soma hanya don ganin yadda mutane keta
haramar bin hanya tunda wuri kada suyi dare.
Lagos Nageria.
Tafe yake cikin motarsa kiran kiran benz wace bai dade da mallakanta ba a yanzu sai kira,a dake tashi a
cikin sautin malam Ahmed sulaiman kano.
Yake dan bin kira,an shima kafin wayanshi ya dauki kara hamnu yakai yana rage sautin dake tashi na
muryan malamin addini a Nageria don ya dauki kiran Saiba amaryansa daya gani din saman layi.
Ya akayi Saiba i will call you bank idan na isa yanzu ina hanya ina tukine don Allah ?
Sweet J kada ka kashe don Allah ka saurareni don bansan idan ka kashe wani ya rigani kiraka a fadama
abinda bashi ba.
Meya faru kuma ya fada cikin kaguwa da yaji kome ke bakinta a lokacin dama akan wanan Asmaun ne
wallahi idan Asmau bata kama kanta dani ba sai na illanta mata rayuwa.
Tseweeee ya tsoki yana fadin akan sakarcinku kika kirani ina saman hanya haka bashi bafa Sweet J
mama mukayiwa laifi muka kifa mata abinci saman jikinta.
Yana kokarin kashe waya yaji karshen furicinta a dan razane yace wata maman dai kodai Iya kike son
kira kikace mama ?
Mama dai ta tudun wanda ita nake nufi ta fada a sanyayye innalillahi taji yana ta maimamitawa son bai
taba zaton iskancin matan nasa har zai iya kai haka ba ai ?
Wallahi Sweet J ba,,,,,,,,,
You are very stupid idiot of you don kina yar iska kuyiwa mahaifiyana haka ki kirani kina fada min sai ya
kashe wayar gabaki,daya yana jin wani tukuki a zuciyarshi.
Fuskanshi ya shafo da hannunsa yana gyara zama a cikin motan don yadda yake jin zuciyarsa ya kasa
samun natsuwa da zancen data fada din .
Duk yadda akayi wani abu mara kyau ya faru da mama din akansu shikan wai wani aurene yayi a
rayuwanshi da kullum baida natsuwa a tare dashi kan matan nasa daya tara agida ?
Yanzu wazai kira yaji meke faruwane wai don baima son ji daga bakin ko dayansu a yanzu wanan karon
sam ba zai kyalesu ba iskancin nasu yayi yawa har abin yakai ga mahaifiyarsa haka ?
Wa,iyazu billah a ina sukaga mama din har take fadin sun mata wani abu mara dadi hakane tunawa yayi
tsakiyan watane ake a lokacin don haka mama tazo gidan ke nan gyarawa iya daki .
Dama daga tsakiyan wata zuwa karshen wata take zuwa wajen mahaifiyar nata taimata kwalema don
samun ladan mahaifiya a gareta.
Har in mama zata iya tsayawa akan nata mahaifiyar haka su da karfin su mai zai hanasu tsayawa akanta
har inda karfinsu ya kare akantasu mahaifiyar.
Oh shet yanzu wa zai kira yaji abindake faruwa har ya shiga haraban nasu da mota sai a lokacin
Abubakar ya fado mashi a rai .
Da sauri ya lalubi waya yana neman layin Abubakar din sai gashi ya samesa ya dauka yana fadin na
dauka ka manta da dan kanin nakane ai gamu nan yanzun muke shigowa Nageria ai.
Sam ya manta da cewa Abubakar din baya gida ya kirashi ya sheda mai zasu shiga kasan Cameroon
wani shutting don haka bai gida ke nan a lokacin.
Saiya waye da fadin masha Allah Allah ya kawoku gida lafiya sai zuwa gobe dai ke nan zaku iso yace
insha Allahu nagode yaya J .
Suka kashe wayan yace common wazan kira ke nan kafin yakai karshen tunane aka buga glass din
motan nasa meiyabi ce don yana kallonta ta bangarenshi.
Kallon tsab yai mata kafin ya sauke glasa din yana kako murmushin dole a fuskanshi yace hey how are
you tayi murmushi tana fadin .
Mr handsome ka boye da yawa kwanan nan duk bani ganin ka na dauka kayi tafiyane ai da ban ganka
ba kana jin dadin kafa garin nan ?
Dan murmushin yake yayi mata kafin yace in baki ganni ba aini ina ganinki sometimes tare da wanan
dogo saurayin naki.
Dariya ta kwashe dashi kafin tace waiko ka fara kishi akainane haka da har zaka ganni kaki min magana
wani kallo ya watsa mata na takaici ya karasa fitowa cikin motan yana facing dinta.
Gata bakace bata shafa mai da matan yanzu suke yawan shafawa jikinsu su canza kala ba ita tabar
bakinta na natural maikyau saidai gaskiya idan ace ta girmeshi da kusan shekara bakwai zuwa takwas ko
goma ba zai musa hakan ba amma kuma wai sonshi takeyi a hakan ita.
Yana dai son su rabu lafiya hakan yasa yake dan tsayawa ya biyewa shirmenta wani lokacin idan
mutanen arzkin na kansa ayi hai hai a watse lafiya.
Handsome dama ina son ganin ka muyi wani magana naga kai mutumne mai harkan bussiness so
akwai wani brother nawa dake wanan harkan acan porthercout nake son in hadaka dashi amma kaje
kayi tunane idan zaka iya don harkane dake son natsuwa sosai a cikinsa.
Na yaba da hankalinka da irin natsuwan ka yasa nayima sha,awan wanan harkan ya dade yana neman
dan arewa dayake da amana wanda zasuyi wanan harkan dashi sai nayima sha,awan hakan.
Kallon ta yayi a tsanake yana karontota a zuciyarshi ba wasa a cikin lamarinta don haka shima ya natsu
ya maida hankali kanta budan bakinshi tambayanta yayi da why me ?
Sai yaga tayi murmushi ta dan kara matsowa kusa dashi tana fadin you deserve ita handsome kana da
natsuwa sosai wallahi beside kuma ni din ina kaunarka har cikin raina don haka tunda you are pure baka
harkan banza kai nake son friendship din mu ya zamo zumunci a yanzu dakai.
Ina mai baka shawara akwai alheri sosai da zaka samu a cikin harkan nan har idan ka rike gaskiya a
yadda kake din nan baka sauya zuciyar ka daga baya ba.
Don mutane da yawa a yanzu kudi na canza masu akida saidai idan kayi tunane tunda kana da contact
dina zaka iya kirana naji shawaran daka yanke akai .
Takai hannu ta kamo nasa hannun tana fadin kada ka damu Allah ne ya hadani dakai abar zancen so
yanzu a tsakanin ka daukeni yar uwa a wajen ka.
Zanso ace kaima ka shigo cikin system duniya tanayi dakai kamar kowa amma ta hanya mai kyau bata
banza ba.
Hannun nasu data rike ya kalla tayi saurin saki tana fadin sorry na manta dakai malam ne ai addinin ku
bai yarda da hakan bako iam sorry for this.
Ta sake ta gyara tsayuwa tana fadin ni zan tafi saina jiki nasan ba zakace a,a by god gra grace don
abune maikyau da zai tamakawa rayuwanka.
Nagode yace da ita zanyi tunane akai idan babu matsala