Chapter 73 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   73 / 101

216K to 219K   out of 302.2K words

haka ba zaisa ta shareni da
yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya saboda laluran cikin jikinta da take fama
dashi.

Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba zan iya ba hakkurina
yana gab da karewa a gidan nan yanzu.

Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun sake wani rigimane
kuma yau din dasu ?

Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina tunda bata kaunan
mu to wai meya hadakune haka Ramaah ?

Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya tashi dan jin mena fada a
lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na rikice kuma.

Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida don na kirata hankali
tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen ummah kaduna.

Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a zauna lafiya baga Yazid
a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu.

Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka rabu ya kashe wayan
yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na ukku ya daga suka gaisa.

Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba ko dazun munyi
waya da kai ai ?

Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali tashe tana kuka yace
gaskiya ban sani ba dan uwa .

Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don dai ta kira a cikin
kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa.

Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su irin na mata amma
bari na shiga inji dai ?
Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J din ne so me zasu tsaya
sunyiwa rigima kuma ?

Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har su sakata kuka akan
hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ?

Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace miji da matane fa
meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana fadin no banyi mamaki ba ai
amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka
dirkawa diyar mutane ciki ka barta a cikin tashin hankali da surutun mutane.

Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura jallabiyarsa a jikinsa zuwa
cikin gida.

Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda ke faruwa ke nan da
gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake
kai tsaye.

Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi nazarinsa baiga wani abin
daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai fito mai da zancen ba.

Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito bane kina daki tun dazun
kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ?

Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na samu yaya J din
shidaya a dakin yana kwance.

Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya ban kaunar ganinsa a
rayuwata

Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a rayuwa kusan nace
saboda shine nake ganin hakan a yanzu.

Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi haka kuma a
yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje nace shine dashi.

Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga nan din shine kawai
mafita a gareni da zaisa in samu sallama.

Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na kalleshi ba lokacin na
dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga.

Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da in gama wankan naji
zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a cikin zancen nan ?
Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da muhinmanci a
zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama wani abu yake so na shareshi baki
kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin hakan da nayi ba ?

Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina da mijina inyi hakkuri
dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san tsakanin mu.

Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun samu sabani a tsakanin mu
nasan ranta ba zai taba dadi dani ba.

Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri na isa gurinshi
nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo.

Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga kinyi kuka binshi
nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba.

Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko kofan dakin kamar a
cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ?

Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk abinda mutum keyi a boye
Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane.

Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana maishi ta nufi
wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa.

Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko gaisawan dole da mukeyi da
aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin.

Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka tufafi a jikina nakai kofa
take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a gidan nan.

Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya wuce hakan data fada
yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din.

Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama suna jirace sai
gasu sun fado dakin ita da iya.

Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan na cacan baki na
kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu.

Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina da bakin magana banda
abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ?

Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana mashi don an kiraki
da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ?

Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da muke zuwa,,,,,,,,
Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan mama da
tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi abina.

Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji abinda ya fada dai
yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman ehh kamar wani tsohon kadangare
dashi lokacin.

Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana kallonsa yace saiba kiyi
hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan sakeki ya fada kamar maganar tana kwato
mashi a bakinsa.

Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin zancen nan wallahi ranki
zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke
meye naki a cikin zancen wai ?

Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya isa yace kar yazo yau
ninaji karfin halin maye da hauka.

Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda aurene kawai ya
hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi.

Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu yarinyar nan sheganta
masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da fadin.

Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu ta nuna kinfi kowa a
wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ?

Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi tunda ba a bace jinin
gidan nan suke ba.

Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga baya naba kaina
shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo gidan.

Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da ranan nan ya wuce
ya shiga wajen dan uwansa.

Ya jima a ciki ya fito yana fadin amma mama abinda yarinyar nan takeyi a gidan nan yai yawa Yazid
shima ya shigo ya sameshi suka hade nan wajen iya da mama din suna fada muna daki da Yanda alokacin
tana faman ban hakkuri.

Habu sai fadi yake ban taba gani kojin irin wanan abin ba su lokaci da sukai cikin su wayayi kokarin
sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa yi kaduna lokacin.

Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za a biye mata a
zama daya ba .
To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita zancen ta tun muna sheda
juna tsakanina dasu a gidan nan .

Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe su ake cuta da aka
hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai
tsaye yace.

Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a ranan hakan da
tajine yasa ta fice daga part din.

Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake matatace nayi abinda
nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda zakiyi.

Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama tayi auren saiba
zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen.

Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta dole da yamman nan ta
nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata a lokacin.

Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin watan haihuwantane
ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana zuwa.

Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe zasu zo su tafi
damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu ai.

Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna bada hakkuri ana
cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma.

Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba daya iya tace yau
dubu kinkai ga yadda kike so ke nan

Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda uwar mazanmu ta
nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a kaunarsu ba.

Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna halin kyara da hattara a
garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga hakan.

Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu don haka ba zasu
saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi.

Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su daddy din da suka
hakikance lalai tafiya zasuyi damu.

Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika dake saidai ki sani
yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki rasa dan ki guda tunda baki yarda
da kaddara ba a zuciyar ki.
Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai kare a kanki ranan
da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi dasu.

Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran nan suka fada
akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki goyi bayansu.

Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a wajen yaro
yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake maki gudu ke nan a kullum
dubu ?

Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya gane kuskurenshi
cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya gada wani lokaci.

Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har aka nunawa yarsa
haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi dasu.

Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya cikin jikinta ai gara
kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa.

Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada hakkurine cikin nan
kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga hakan.

Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya ishi bawa ya kara yarda
da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su
zaifi.

Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai akai rashin sa,a ya
fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa hankalin kowa a falon ya koma kansu
kuma .

Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi a lokacin mahaifin
Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki yau ?

Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu wani dadi kikaji ga hakan
don Allah ?

Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke a cikin gidan da
muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana ki natsu ki kwantar mashi da
hankalin gidansa.

Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai wanan kyautatawan
tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda kowansu yanayiwa ai ?

Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin haushin abinda taji din
a lokacin don ranta ya baci matuka.
Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da right din da zatayi
maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a bangaren yata kinga ashe yarsu itace da
riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi shima yaci arzikin nasa ..

Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi hakkuri yanzu dai ai
taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya
sauka wajen sheganta masa cikin sa din.

Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar nan ta kwana da sanin
zamata a gidan nan yazo karshe.

Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk ranan da wani dan
uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce zata rabshi da maishi a rayuwansa




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/25, 10:51 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣4️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Nayi kuka har nagodewa Allah a wanan ranan daya zamo min kamar na tonon asiri a wajena ranan da
nake jin kamar kasa ya bude inshiga saboda kunya daya lulubeni a lokacin don hakan ya zamo kamar
wani bakon lamari a society ake gani.

Yayin da miji yake kwance a lokacin ni kuma Allah ya nufeni da samun karuwa dashi karuwan da nake
jin tankar i hadiye raina a lokacin .

Wanda bake jin tsanar mijin fiye da kowa don ina ganin shine ya kaini ga wanan abin kunyan a yanzu
wanda a sanadin haka har ya

73 / 101