Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
tafi maigadi ya tareni yana fadin ashe
abinda ya faru ke nan ?
Yaso ya bisu zuwa asibitin sai yaga ba kowa a gidan Allah ya bashi lafiya ya tada kafada na amsa da
amin nashiga ciki.
Habi bata gida nasan tana gidansu donshi na shiga dakina kai tsaye wanka nayi na fito na gyara jikina a
yanayin da nake ciki banko tuna da abinci ba a ranan .
Tea na hada da niyar insha kada in kwanta da yunwa saidai na kasa shan koda rabin kofi ne a lokacin
don bakina da nake jin ba dadi.
Ina ganin kamar ko wani lokaci zasu iya kirana suce min ya cika a yadda na barshi din ga gidan ba kowa
sai hakan yasa tsoro ya kara shigana duk da maigadin mu yana daga wajen gidan a lokacin falo na dawo
na zauna a cikin zulumi ina jan tsabaha tare da tunanen yanayin da yaya din yake ciki.
Daga karshe dai na mike na rufe kofa na koma cikin daki bayan na kashe wuta ko ina a gidan ina cike da
zullumi a zuciyana.
Alwala na dauro nazo nayi sallah nafila nakai wani lokaci ina nemawa yaya sauki a wajen Allah kafin
dan barci ya saceni zuwa dare kuma na falka ban kara runtsawa ba har safe ina idar da sallah na fito
zuwa kitchen abinci lafiyayye na hada inda shi kuma nayi dabaran dama mashi kunu ko za a samu ya dan
sha.
Karfe bakwai har nayi wanka nashirya na fito na kulle gidan na doshi asibitin gabana sai faduwa yakeyi.
Tunane kan nayisa kala kala a zuciya yau idan na rasa yaya yaya zanyi da rayuwata ina zan shiga a
duniyan nan mutumin da nake mafalkin shimfida rayuwa mai inganci dashi nan gaba gashi kuma Allah ya
jarabeshi yana cikin halin hau,ula,i a rayuwansa yanzu.
Zance nice ta farkon isa kota biyu na samu su yaya na ciki suna tsabtace masa jikin daya bata Allahu
akbar bansan lokacin da kuka yazo min ba.
Sammakona yasa na samu daman shiga gurinsa kai tsaye yana kwance kamar yadda muka barshi dai a
jiyan dan bambanci sun sauya mashi kayan jikinsa zuwa jallabiya tufafin nasa da suka cire mai yaya isah
ya miko min na karba.
Iya tashigo tana fadin ga abin karyawa nan tazo muna dashi shikan ai ba abinda zai iya ci a hakan da
sauri nace na dama koko ko zai dan karba a gwada a gani.
Shawaran hakan suka karba na hada kunun na dan fifitashi saidai mazane sun rasa dabaran da zasuyi su
bashi.
Nice dai cikin karfin hali na gwada karban kofin a hannun yaya na doshi gadon ina sunkuyawa nace
sannu yaya ya karfin jikin kuma Allah ya bako ikon cin jerabawan nan .
Suka amsa da amin amin yaya ka dansha koko gashi na dama maka koda kadan ne don Allah cikin ka
babu komai a cikin sa cikin ikon Allah sai yai kamar ya lumshe idanunsa a lokacin.
Na dibo na fara dan dago kansa a hankali ina dura mashi kokon yana shiga cikinsa har muka samu ya
dansha kamar spoom biyar haka dai suna fadin Alhamdullahi wanan dabaran yayi kuwa na shan koko
din.
Iya ke fadin aiko yunwa ya isheshi mutum kwana nawa cikinsa babu komai a lokacin su mama suka
shigo dukkansu da kishiyoyinta aka fara gaisawa.
Yaya Auwal ke fadin amarya tayi dabaran bashi koko ko zaisha gashi ko mun samu cikin ikon Allah ya
dansha din sai mama tace nima nayi tunanen hakan a raina.
Nan yan uwa suka fara cika dakin da abinci da kayan dubiya ina zaune a gefe takure har kishiyoyina
suka iso saidai su Maria sun rigasu isowa tana fadin mun biya mu daukoki maigadi yace muna kin fito
tunda safe ai.
Kafin na amsa iya ke fadin zuwata ai yayi muna rana tunda an samu ya dansha kokon data damo mashi
ta bashi ya karba sosai yasha.
Irin maganganun nan da ake fada akaina mai kamar da ana yabona shine ke kara hadasa min kiyayyana
a zukatan wasu a wajen irin kishiyoyina da su Saare dake gani iyyye iyye ne kawai irin nawa da son nuna
ni din watace datafi kowa.
Itako iya kamar zuzuta zancen takeyi a lokacin don suji haushi don sai kara cusa magana takeyi tana
fadin ai ko dazun da yarinyar nan ke mashi addua ya karba.
Muryan ya habune ke tambayan kawu ya fito akace bai karaso ba tukun yace iya tazo suka fita ashe
zancen zuwa wanan wajen yai mata.
Take fadin ya kamata kan aje din aiko wancan karon banso ya tafi tafiyan nan basu je ba amma da yake
Dauda munafukine sai yakawo uzuri ga tafiyan yace wai yana gudawa lokacin.
Koma dai meye yau din nan iya nake son muje din don nayi mafalki jiyan nan ba dadi wallahi ciwon nan
haka zaita bibiyan mu bawai Jafar kadai ba kowan mu sai hakan ya nadesa idan har ba a dauki mataki ba.
Ga zancen nan ba kowa ya kamata yasan dashi ba tunda ba zancen da za a fito a fada a fili bane har
wani yaji abune daya shafe mu mu kadai wanan.
Amma saidai naga kamar dole a fasa din don yau idan kawu ya kawo min uzuri wallahi za a jimu dashi a
wajen nan wanan yasa na kiraki iya.
Wanan shine daidai na rasa me dauda kewa noke noke ga zuwan nan gashi har ankai ga yadda ba ason
akai din dole kayi masa jam ido ko zuwan zaiyi amfani a dace.
Har ya juya ya dawo yana fadin sai kuma kula dashi ina son aba Rahama daman hakan ta dinga bashi
kulawa idan tana kusa tunda yana jin muryanta yana bada responding kinga hakan ai alaman saukine.
Shina fada jiya da dare ko yau kuma muga alama hakan don tabashi koko yasha da kanta hakan za ayi
yanzu dai idan mun dawo idan babu cigaba nan asibiti sai mu koma gida dashi iya.
Aje ayi na gargajiya a gani don ko lokitan nan dan Zamfara shawaran daya bani ke nan jiya yace abin
nasa kamar akwai sihiri a cikinsa din haka sai mun hada dana gargajiya.
Kawune ya doso wajen da matansa biyu sai dan amaryan nasa dake dauke a hannunsa iya ta kallesu
taja tsuki tana fadin babu komai yanzu a cikinsa banda tabara akan wanan auren da yake ganin yayi.
Suka karaso suna gaisawa tare da tambayan ya mai jiki din yace da sauki zai shige iya race barsu su
shiga kaika tsaya muyi magana dakai ke hansatu idan kin shiga yi min magana da Dubu ina nemanta nan.
Lokacin ne kuma muka fito dakin nida maria muka kebe muna magana dan nisa dasu sosai saidai jin
yadda ya habu ke daga murya yasa hankalin mu ya koma akansu.
Duk da bamu ji sosai amma na fahinci zancen tafiya sukeyi nasan kuma can din inda nakwana da
tunane suke shirin zuwa.
Sai lokacin nakewa maria bayanin komai tayi mamaki kwarai dana san hakan nace shiya fada min komai
wallahi kamar yasan hakan zai faru dashi har dalilin dawowan iya wajena saida na bata labari.
Take fadin kinga bambancinsu da ya Habu ke nan shi bai zama ya fadama damuwarsa ko wani abin
rayuwansa saidai yayi tayin abu noku noku a zuciyarsa.
Ya habu din ne yazo ya wuce mu a fusace ya shiga dakin bai jima da shiga ba likitocinsa sukazo hakan
yasa aka fito daga dakin.
Sun jima a ciki sosai kafin ya habu din ya leko yana kirana hakan yasa na mike zuwa dakin na samesu
tsaye a kanshi na gaidasu.
A cikin harshen turanci likitan ke fadin itace wanan ko ya amsa da eeh ya kalloni yana fadin madam
sannu ko ya kuma mukaji da jimame don Allah wani aiki zaki danyi muna a yanzu.
Muna son kiyi magana da maigida ko zamuga responding din hakan a garesa kinga in akwai
improvement zamu dan gane musan abinda zamuyi mashi.
Kin gane Rahama ana son kije kusa dashi yanzu ki danyi mai wani abinda zaisa ko ya dan motsa koya
bada amsa ya habu ke fadin hakan a cikin damuwa.
A hankali na motsa zuwa bakin gadon gabana sai faduwa yakeyi suko duk sun motso kusa sun zuba min
idanu sai addua nakeyi a zuciyana.
Hannunsa na koma a hankali na hada da nawa nakai zaune bakin gadon ina fadin sannu yaya Allah ya
baka lafiya na shafo fuskansa sai yayi kamar ya lumshe idanunsa yana ajiyan zuciya.
Great naji wani likitan ya fada a gefe ki kara yin wani abin madam wanan bahaushen ya fada gareni na
lumshe ido nace dan gyara zama ina fadin.
Yaya zaka kara shan koko ko abinci zakaci suna tsaye kamar sojoji sun kurawa ko wani part din jikinsa
ido wanan karon da hannunsa yayi min alaman don hannun ya dan motsa yasa na kalli wajen hannun
nasa da sauri danaji ya motsa din don hannaye mu suna harde lokacin.
Sosai suke fadin akwai cigaba insha Allahu in bashi kunu din su gani hakan yasa na hada dan kunun
koko din na fara bashi saidai wanan karon baisha sosai ba kamar farko.
Suka daiyi dan bayanan su kafinsu fita zuwa inda suka fito aka barni da yaya Habu sakin dake cewa
dani kada ki yarda kina matsawa kusa dashi Rahama ko yaushe ya kasance kina gurinsa .
Ni zamu tafi wani waje dasu mama kila zamu kai dare bamu dawo ba don Allah ki kula kada ki yarda da
zancen cewa ki matsa a nan din.
Kin dai gane me nake nufi duk wanda ya kawo abinci ko wani abu kada ku bashi idan bakece kika hado
mashi ba a daidai lokacin Saiba ta banko kofa tana fadin.
Ai batafimu ba da za,ce sai ita kadai zata dinga shiga don ana son a nuna mu bakowa bane za ai muna
haka tayi shiru don kallon da yaya Habu din ya banka mata yana fadin.
Ke kin gane ba ko wani lokacine zaku dinga shigowa daki nan ba haka kuma ba ason hayaniya a
wajensa donshine Rahama kawai sai yaya isah da yaya auwal aka amimce yanzu su dinga shigowa.
Rahama din tafimune kome ta fada cikin kafeshi da idanu idan ma tafikune ke zakibawa kanki amsa mu
yanzu lafiyansa muka jawa kawai ba wani abin kishin ki ba can don haka ki kiyayye a zauna lafiya yadda
likitoci suka fada din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[4/2, 10:07 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to
join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kuka kan kallo daya zakiyi min kisan nasha kuka a wanan wunin don yadda idanuwana sukai hulu hulu
saboda kukan da nake kebewa inyi,
Tare da tunanen duniya kala kala dake sauka min a zuciyana game da halin da yaya Jafar din yake ciki.
Ina zaune nayi shiru a gefe tabarman dasu mama ke zaune sama bayan mun idar da sallah la,asar
nagama maman tudun wada ta miko min kofi cike da fura har da kankara a sama .
Kaina girgiza alaman a,a don banson komai a lokacin take fadin maza karbi kisha ina kule dake tun
karyawan safe baki kara saka komai a cikinki ba yar nan.
Masu fadin suke dashi don suke da diya dashi aun zage nan suna ciye ciyensu a gaba kowa balle ke din
da sukewa arashun baki aje ko kwai a tare dashi ba balle ki fisu nuna damuwa sun zage suna kai abu ga
bakin salatinsu.
Maza ki karba kisha ki danji nauyi a cikinki kinji Allah ya kareki da takaban kuriciya da suke maku fata
hakan don yafi komai daci da muni ga ya,mace .
Hawayene suka sulalo a idona take fadin ki daure ki daina wanan kukan haka Allah ya tada kafadan
mijinku yasa hakan zakan jikine a garesa.
Karbi maza ki shanye ba a jinya da yunwa don saika fadi mai ciwo yazo ya mike Allah ya tsare dole na
karba nasha din datace min saidai ban iya shanyewa ba na rike sauran a hannuna take fadin maza na
shanye na miko mata kofin .
Dole na kara kurbe sauran ban kaiga idawa ba Asmau ta kwala min kira da nazo daga kofan dakin
hakan yasa na aje kofin da sauri na mike tsaye na nufi dakin .
Don na fito saboda karmu saida hali a waje don yadda take nunawa lokacin dana shiga dakin ko abu
zanyiwa yaya din zata taso da sauri tace dani na bari kawai ai zasuyi mai ko idan na dauki abu zatace na
miko mata abin.
Ganin hakan yasa na fito daga dakin don zuciya bata da kashi zan iya kasa hakkuri na biye mata muyi
abinda ba daidai ba har mutane suji a tafi damu a baki.
Koda na shiga dakin na zata wani abune sai take cemin wai na duba ko ya sake bata jikinshi wani kallo
nayi mata mai nuna baki isa ba.
Kin fimu karfin hali yasa muka kiraki Asmau ke fadin hakan gareni nace na zata ba saini ba zaku iya
hakan ga mijin ku ai.
Ke don mun kiraki kada ki fadawa mutane maganan banza don Allah idan ba zaki iya ba kice ba zakiyi
ba kada ki kawowa mutane wani zancen banza a nan ?
Banda lokacin ki don haka kiyi haushin ki ke kadai dama kin saba ciwon nasa aida alaman ba
damuwanki yayi ba don da baki zauna kina damunsa da waya haka ba akai.
Ashe kinji zafin wayan da nakeyi din inkin isa kizo ki karbe wayan insan kincika yar jin haushi kaji min
yarinya da zancen banza har wakike inbashi dayaga abin banza ya nace akanki ba ?
Subbahanallahi dama nayi tunanen hakan ai yasa na biyo ku, yanzu yarinyar nan har bawan Allah nan
yana kwance haka cikin wanan halin ?
Amma baki saduda da wanan halin naki ba sai kin dagawa mutane harshe a nan kuma ?
Muryan mamace data biyoni bayan shigowana take fadan hakan tana tafa hannu don bata jini ba saiba
din ta sama tana fada min maganganu a bakinta lokacin.
Wani daga harshe nayi yanzu kuma mama ita har waye da zata tsaya tana fada min magana akan
abinda zanyi yaushe ta samu wanan power din take ganin takai ?
Amma kin kai sakarai ashe ? har yaushe wanan taga lokacin fadan wani magana gareki a nan yarinyar
dake ta faman darzan kuka tun dazun a waje .
Gadon da yake kwancene ya fara jijiga gaba dayan mu hankalin mu ya koma kanshi hakoransane ya
datse a waje daya yayin da idanuwansa suka firfito waje ma,ana dai ya kara shiga wani sabon hali lokaci
guda kuma.
Ko salatin mama ya isa ya rudamu a lokacin inda Asmau ta fita waje da gudu tana neman taimako ga
mutanen dake zaune waje cikin rudewa da tashin hankali.
Ba maza a kusa iya mu matane da muka cika asibitin a lokacin sai salima data hari dakin likitocin hankali
tashe don kiransu.
Rasa me zanyi nayi saina tuna da dan anty salma ya samu attack irin hakan yadda mukai masa a abuja
da sauri na juya na dauko spoon na nufeshi ina kokarin bude bakinsa na tura spoon din ya datse tsakanin
harshensa da hakoransa.
Kanshi yana saman jikina muryata a cikin tashin hankali na soma fadin don Allah ku rike min kafansa
daga mama din har ita saiban sun kasa hakan shigowan Maria da Anty Barakha ya taimaka min suka rike
kafafuwan nasa dake halbawa.
Innalillahi nake maimaitawa saiga likitocin sun shigo a rude nurse suna fadin a rage daga dakin a fita
don koke koke da yai yawa a lokacin dakin duk kowa na tsaye cirko cirko a cikin tashin hankali.
Ruwan sanyi ko kankara nake fada ina nuna hanyar waje likitan ya kamo hannayesa yana dubawa har
lokacin yana kwance shambal a jikina.
Ruwan da nake fada din suka miko min a daidai kanshi na manna ruwan sanyin lokaci guda ya sauke
wani irin ajiyan zuciya mai karfi ya daina wanan gurnanin da yakeyi da farko.
Dukkan mu matansa mu ukku muna tsaye a dakin a cikin tashin hankali har likitocin sukai mashi abinda
zasuyi din ganin ya lafa suka soma magana a cikin fada.
Ba mun fada maku a daina shigowa ba haka da yawa dakin muna son ganin farfadowansane a ko wani
lokaci zai iya yuyuwa yana jin komai saidai nisan fita hayacinsa da yayine ba zai bari a fahinci hakan ba
zai iya jin wani magana da zai iya daga mashi hankali kuma har hakan ya faru kunga ciwon yana son
canza sabon sallo kuma ke nan.
Na yarda da maganan ka likita don matar nan tasace ke sa insa a dakin lokacin da abin ya faru kaga ke
nan zancen ka gaskiyane ke nan a nan mace ke fadan hakan.
Kuka saiba ta saka mai karfi tana fadin don kawai ba a kaunata za ace nice nayi sanadin hakan ya faru
ya zata fada min magana inki ramawa don ina tsoronta ko me ?
A nan kowa ya raina mata wayau don fahintar itace silan faruwan hakan ashe a lokacin da mama ta
fada.
Anty barakha ke fadin indai hakane aisai duk su fita wallahi tunda ba zaman Allah da annabi sukeyi a
nan ba zasu kashe muna dan uwa da bakin kishinsu kawai ?
Ya zama dole duk su fita likitan ya kalleta yace ita wanan na zaune bida gadon data bashi taimakon
gagawa ina matarshi ce ?
Yana da kyau a barta a kusa dashi na fadawa brother nasa dazun don tana taimakawa sosai wajen
abubuwa da dama ko yanzu badon tana wajen ba da zaiji ciwo sosai wallahi.
Don zai iya fadowa daga gadon haka kuma harshensa zai datse din ya ja masa wani matsala babba
kuma sabo amma taimakon data bashi din ya taimaka muna sosai a yanzu wajen magance matsalan don
haka abarta a tare dashi please .
Amma kowa ya fita