Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
nan baki gajere mai dan fadin kai da
tumbi baida tsawo sosai dai haka dashi kafirine bai sallah bai chochi ?
Still yana shiru yana tunane na dan lokaci don ya kasa gano ko waye wanan mutumin da akai masa
kwatancensa saboda abokan hurdan nasa ai yawanci kafiraine.
Hjy kinyi sakaci sosai akan yayan ki akwai matar data so fada maki gaskiya a baya amma baki mai da
hankali ba kan hakan ?
Itama mama nunawa tayi bata gane matar ba a daidai lokacin da J yace malam kwarai kuwa na tunashi
tabbas anyi hakan bayan shan ruwa na fito na sayo abinda zanyi buda baki bakin wani shago na hadu da
wani daya kira sunana ya nuna min sani ban sanshi ba amma shiya sanni.
Yake min murna da cewa shiya dade da sanina ai muka sha hannu dashi sai malamin yace a lokacin ya
shafama abin don da shirinsa ya fito dama.
Yanzu malam yaya za ayi yace Allah shine maiyi mu saidai mu danyi namu dubarun da Allah ya hore
muna ai.
Yana ta jan tasbahan da yake aikinsa dashi kafin yayi murmushi yana fadin dewa ya,i wanan yarinyar da
karanbani take saidai ba zasu iya komai da ita ba.
Wace yarinya ke nan kawu ya tambayi mutumin yace gata nan dai a cikinku take wata mai dan tsayi da
manyan idanuwa saura kiris ta kai ga nasara a shirinta.
Amma baku bata daman hakan ba da zaku bata dama da anyi nasara koda baku zo nan ba saidai tana
shakkun wani abu a zuciyarta kuma.
Wacece ke nan malam gasu nan dai a tare daku su din alherine a wajenku kasan wani lokaci Allah kan
muna wani baiwa amma bamu fahintar hakan sai muyi sakaci da abin.
Amma shi nan gaba zai fahinci komai kai yake jijigawa yana fadin yarinyar tana da gwargwadon sani
amma a yanzu tana tsoron aiki da hikimarta .
Nafisace ko mama ta fada wata kila itace inji kawu ya fada daga gefenta sai mutumin ya dora da fadin
hjy lalai ki samu wanan matar dake son maki bayani don tasan komai.
Ya dai basu magani bayan surutan da yayi tayi a ciki harda zancen matan yaya din da abin ya kara daure
masu kai suka maishi alheri yace dari biyu kawai zasu bashi sadaka in an samu lafiya su dawo su bashi
abinda Allah ya hore a garesu suka fito suna mamakinshi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️2️⃣
2️⃣
4️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Basu iso zaria ba sai goma na dare nayi barci a lokacin don mun dan samu sabani da anty Saare inda Iya
da anty Nafisa suka shigan min da cewa.
Idan banyiwa yar uwata abinci nakai mata ba wa zai kula min da ita tunda mijinta lalura ya kamashi
yanzu bai cikin hankalinsa akan dan uwansa.
Hakan kuma sai ya zama laifi saratu ba dole bane duk abinda ta dafa ace saita zubo muna tunda
abincin asibiti takeyi abinda mara lafiya ke ra,ayine ai ta dafa mata ni inama ganin kokarin yarinyar nan
wallahi nafisa ke fadan hakan .
Saare ta kallota tana fadin kada tayi kokari mana wa tayiwa ba kanta ba nifa dole in fada yarinyar nan
tunda taje Abujan nan ta dawo ta canza gaba daya a gidan don taje Abuja zatayiwa mutane daukan kai
kamar wace taje london.
Abinki dai hassadane Saare inbashi ba wani daukan kai yarinyar nan takeyi gidan nan yarinyar da bata
ko saka kanta cikin sha,anin kowa ?
Dama ai hassadane hakan kada ki dada ki kara indai anty Saarece yanzu haka acan lungun yaya J akai
haka tazo ita ta ara ta yafa abinda bai shafeta ba.
Ramaah tun wancan case din da akayi na kayan sallah da kuka hana a bata ta kama kanta a cikin gidan
nan sai tacewa yar uwar nata salima dake magana.
Wa zata kamawa kai mufa nan gidan mune ba cin rani mukazo ba wanan yasa na fito daga dakin iya
dana idar da sallah magariba nake fadin.
Anty Saare nima gidan mijin yar uwata nazo idan ba haka ba aiba zaku ganin gidanku ba nasan baki
kaunar zaman mu gidan nan kuma Allah yayi mu zauna daku din tunda Habu ya dauko yar uwata dole ki
ganni a gidan in baki son ganina yau kisa Habu ya saki Yanda gobe idan kin ganni ki fadi abinda kikeso a
kaina.
Ke nikike fadawa magana haka Rahama ke yar gidan uban waye nace yar gidan ubana malam Aliyu
bafillace rugga da kika fada.
Shi kenan kun dauka mu fulani dabbobine bamu da wayau ko hankali kowa sai yaso ya raina muna
hankali girmanki nake baki don abubuwa amma tunda baki so muje a hakan ai kowa ya iya rashin
mutunci.
Yanzu kin samu abinda kike so ai tunda kikaiga fada yarinyar nan ta fada girma kuma ya fadi ba salima
ta karbe iya data soma maganan a lokacin.
Bata daiji dadin kowa ba a cikin zancen donshine tunda na shiga daki ban fito ba tunda naji kawu na
fadawa iya ba zasu kwana ba donshine banje part din su Yanda ba.
Sun gaji da zaman jira suka kwanta sai anty Salima dake zaune tana kallon film wayanta itace taji
dawowansu maigadi yana bude masu get.
Ta tayar da iya tana sheda masu sun dawo taji maigadi na budan get din yana gaidasu da dawowa a
lokacin hakan yasa suka bude kofan ni dai ban fito ba don idona biyu ina hadiyan bakin cikin Saare a
zuciyana a lokacin kinsan bafulace da bakar zuciya dama.
Sai washegari dana fito na gaida mama dake zaune falo tanawa iya bayani abinda mai magani ya fada
ta juyo tana amsawa kafin na mike nakoma daki tabini da kallo.
Kodai yar nan malamin nan yake nufi dai don wanan kunun tsamiyan da take damawa shi kadaine
abinda Jafar yake sha ya zauna a cikinsa.
Kai ba ita bace dai nafi sa ran Nafisace dai bata kai karshen zuci ba da takeyi taji iya na fadin jiya Saratu
bata kyautawa yar nan ba.
Akan abinci ta zauna taci mata mutunci a gidan nan wai tayi girki bata zubo masu ba ta zuba min ta
kwashe takai asibiti zokiga yadda tayiwa yar nan falle falle a gidan nan jiya.
Garin yaya haka ya faru kuma me saratu ke nema da yarinyar nan don Allah ai jiya takai ga bata amsa
ta fada mata ba,a daji aka daukosu ba suma suna da uba ai dalili yasa ta ganta nan din tasa habu ya saki
yar uwarta idan ta sake ganin fuskanta a gidan nan.
Ai gaskiya ta fada idan ba dalilin yar uwarta ba ta yaya zamu ganta gidan nan da tana zaune ta mike
kafa habu ya kawo masu yar aiki ko ?
Bafulace zaka rainawa wayau ka zauna lafiya don ma yaran nan nada wayewan kai suna amfani da
iliminsu aida ta dajinne datace data gane bata da wayau gobe ba zata kara raina masu wayau ba.
Murya tasa tana kirana daga falon na fito take fadin Rahama daga yau nayi maki iyaka da sa,insa a
gidan nan kinji nasan an bata maki rai amma kiyi hakkuri itama zan fada mata wanan halin banzan nan
data koyo ba alheri bane ga mace tagani ta gaza shiru komai kace sai kayi magana akansa kana tare da
wahala bance kuma inkiyiwa yar uwarki abu sai kin dibawa kowa ba tunda suna da hannayesu kiyi
hakkuri kinji Rahama.
To fadane dai gashi nan irin ta uwa mai son yayanta bata goyi bayana ba bata kuma nuna nayi laifi ba
wanan shi ake fadin wanka da jurwaye ke nan.
Na daiji amma nace nagode mama tace ba komai kinji gaba zai maki amfani yar nan hakkuri baya baci
gabawa.
Allah yaba yar uwanki da Jafar tare da sauran al,umman musulmi lafiya na amsa da amin nashige daki
ashe ta samu Saare a can tayi mata ba dadi a gaban kowa.
Saiba ke fafin amma mama kada kuba wanan yarinyar garati da yawa ta dauka daya take da mutane a
gidan nan ko banza ai duk sun girme mata don me zataki masu girki.
Ya J dake kwance sama dogon kujera mai ci mutum uku ya dago yana fadin wanan wani irin maganan
banza kikewa mutane ?
Kinfi nama sanin abinda ya dace tayine akan mu ko kinfi yarinyar wani darajane a wajenta ?
Koko an fada maki boya aka kawo masu ina da niyar wanan maganan mama ta rigani don aikin da
yarinyar nan keyi a gidan nan babu wace cikin ku dake yinsa tafiku wawiya kawai ko ta zauna tayi girki
aci hankali kwance wanan ba daraja bane banda cin mutunci me kika koya ke ?
Zancen nan dai ba naka bane jafar ka barta aina san abinda nakeyi ba zan zuba ido su saka yarinyar
mutane a gaba ba ina kallo aiki ya wuce nawa da iya kona yar uwarta ba zata kara kauda kara a gidan
nan ba.
Wanan ma da iya ta dauko kwanan ta uku batazo ba son bata iya kallon ga mata zube amma basu iya
komai wa zai zauna yana wanan wahalan haka ?
Suna cikin wanan zancen muka shigo da Iya a cikin jam,i na gaidasu kafin nace yaya ina kwana ya karfin
jiki ya amsa da Alhamdullahi .
Yadda naga fuskokinsu yasa na fahinci akwai abinda ya faru don haka ban zauna ba na mike don barin
falon don kusan ni dayace bare a cikinsu.
Kin hada abincin asibitin ne Rahama mamace take tambayana na juyo ina fadin na rana zanyi masu yau
sunce abar na safe zasusha shayi.
Ai shike nan sun hutar dake aiki naso naje na dubasu saidai abinda hali yayi zuwa anjima tunda jikin
jafar din da sauki sosai yau insha Allahu.
Ya dace aje a dubasu kada suga rashin hankalimu iya ta fada mama din ta sake fadan insha Allahu zan
kekasu yau ina ganin can Habu ya nufa tunda safe.
Ban tsaya ba na fita naje aikin gabana sun dan jima zaune kafin ya mike zuwa daki yana fadin zai
kewaya.
Sumama suma suka bar falon don gaskiya maganin da alaman ya karbeshi sosai ba bugun kai da yakeyi
a lokacin nafisa ta rigasu barin falon ta koma part dinsu.
Salima na zaune tana dakilan wayanta suka fara magana Saiba tace dole tayi hakan don ta danje Abuja
tayo clean baki ganin daga kan data fara yiwa mutane tunda sun iya asiri .
Babu asiri sai iskanci a ina wanan zata samu asirin balle tayi Asmau take fadan hakan haka kike gani da
asirinsu ake haihuwansu.
Yar kauyece fa kibar yan kauyen nan inda kike ganinsu sis haka suke kiran junan su tun farko yanzu in
ana dadin rai hakan ake furtawa juna sunan na sis idan fada yazo kuma za a kira mutun da sunansa na
yanka.
Boni ya tabbata ga mai zunde yanzu me yarinyar nan tayi maku da zaku sakata a gaba da zaki harda
wanan irin zargin inma asiri tayi ai baku tayiwa ba dai ko ?
Salima inma tana asiri tasan wanda zatayiwa nikan nafi karfinta har kowa nata kuwa haka dai kikace
idan baka damu da mutum ba ai baka zaman kushesa haka ?
Ke Saare bar part din nan kafin ranki ya baci yayan nasu ya fada yana nuna mata hanya don ransa ya
gama baci da wanan halin nasu.
Ke kuma Nusaiba abinda yarinyar ta tsare maki saiki kokarta ki koreta a gidan ki samu sanyin a ran ki
tunda zamanta ya tare maki wani abu.
Salima ce ke ban labari daga baya zamuce Alhamdullahi don gaskiya jikin nasa yayi sauki sosai sati daya
ya iya yi a gida ya soma harkokinsa na yau da kullum.
Haka salima da Saare sun koma wajen karatunsu ya rage gidan dagani sai Nafisa da zance zamanta ya
dawo nan dai ke nan don tafi ganewa zama a nan din donko da mama zata koma gida bata bita sun tafi
ba tace sai mama ta dawo ita tana nan ba yawan hayaniyan nan na gidansu.
Shakuwa sosai na tsakani da Allah ne a tsakanina da Nafisa don tankar yar uwa ta daukeni inda har
dan fi min salimama zance dadin zama don bata da son kanta tare muke komai da ita.
Ba irin rayuwansu bane ita ba sai ta jira kayi mata abuba ita zata tashi tayi da kanta dama aikin dai iya
girkine kawai inyi na safe tayi muna na dare wani lokacin idan tana gida tare zamuyi aikin da ita.
Watan haihuwan yar uwata ya kama kowa hannunsa a gaba duk da likitoci sunce babu matsala ga
hakan saidai komai a hannun Allah yake ai ba a wajensu ba.
Allah cikin yardansa ta haifi danta lafiya lau ba tare da aiki ba ranan munyi murna sosai da haihuwan .
Ya habu bakinsa yaki rufuwa duk daurin fuskan nan nasa a ranan babu wanan halin a wajensa sai washe
baki yake kallo daya zakiyi mai ki gane yana cikin farin ciki.
Matan yaya Jafar kusan sune sukazo a karshe daga gidan duban maijego da jariri sun samemu a dakin
zaune tare da ita muna hira su mama suna waje da ummah mu zaune don an dauke wuta.
Sun shigo sunyi barka basu zauna ba duk da dagawan da mukayi muka basu wajen zama sukace sauri
suke zasu koma gida iyace da mai aiki suka bari a gidan.
Bayan fitansu mama ta aiko Nafisa tazo sai gata ta dawo tana fadin zata bisu su sauketa gida ta karbo
sako a wajen innansu.
Don haka suka tafi tare dasu a hanya suka fara zagin yar uwata harni basu barni ba da uwarmu duk sun
hada sun zagemu tas a lokacin kishin (saure) ke nan wasu suce dashi (Facal) matar wa da kani ko dan
uba.
Yafi zafin kishi wani lokacin ga mata har gara kishiyar da kuke mijin ku daya da matar dan uwan miji
koda ko ba a gida daya kuke rayuwa da juna ba ana samun wanan matsalan sosai a ko wani kabila a
duniyan nan.
Mukan bamu san sunayi ba abinda dai na sani shine basu kaunan mu wanan yasa gaba daya bani shiga
tsabgansu yanzu ko part dinsu tunda mijinsu ya samu lafiya rabona da wajensu ke nan sai inyi kwana
gamu gida daya amma bamu hadu ba.
Ina dakin nasan dai ya dawo garin tunda naga motar dayake amfani dashi haka kuma anshigo da
tsaraba akace shine ya dawo.
Sai asibiti muka hadu daya shigo ganin jaririnsu jikinshi a lokacin ya dan dawo sosai zakice bashine yayi
wanan ciwon bala,in ba a watannin da suka shige.
Gashi a yanzu yadda nake ji a wajensu arzikinsa sai habbaka yakeyi don har su mama da iya na kiran
dan yar uwata da arzuka wai yaya J yace ana sanar mashi da zancen haihuwan kuma aka kirasa
kudadenshi sun fito masu yawa daya saka hannun jari a wani harkan mai a can kudu.
Don haka komai baja baja akeyinsa a gidan alherinsa ga mutane kuma bai daina ba kamar ma kada yai
ciwom nan abin ya nunku masa.
Ya shigo da mutane a bayansa yuuuu da suka taka masa naji Nafisa tana gaidasu nidai sau daya na
gaidasu na mike tsaye na koma can wajen gado na tsaya.
A cikin yare anty Yanda take min magana da na dauku dan nabasu don haka nake fadin nikan ina nasan
haka akeyi.
Yar fillo anyi da sintirin zuwa asibiti ya kare sai karatu yanzu ko abinda yaya j ya fada min ke nan a
lokacin na danyi murmushi ina mika mashi dan cikin ladabi.
Amsan shi yayi yana kallo ya jima dashi a hannu sai daga baya na fahinci addua yakewa yaron ashe
naga yana mashi ikima da bin sassan jikinsa yana tofewa har dai ga al,auran yaron ya mikawa na kusa
dashi yana fadin Allah ya raya muna Alh mu bisa kan sunna sunan baba na saka mashi dama alwashina
ke nan idan na samu da in saka mai sunan baba sai ga habu ya rigani hakan.
Ai duk nakane wani mai banbadanci ya fada basu jima ba suka mike don tafiya akwaisu da son
kanninsu don haka ya yafito Nafisa da hannu ta biyoshi kome ya tuna naji yana fadin yar fillo zo muje
mana.
Dole na biyo bayanshi sam ba zan iya yadda suke da yan uwansa ba sosai suke sakewa dashi fiye da
Habu donshi Habu ko yaushe fuskansa babu fara a cikinsa.
Shiko yana da dama sosai yakan zauna dasu yayi hira su fada mashi korafinsu kuma yayi masu maganin
hakan a take matane kawai za ace bai dace dasu ba.
Amma yana iya kokarinsa ba zaki gansu da tufafi da bai dace ba saidai yanayin gyaran ne da basu
tsayawa suyi kawai gara Saiba yar kadunace iya kwaliya a wajensu yake sai dai ita kamar bata amsa
sunan yar kadunan ba.
Mun fito yake fadin to yaya Nafisat party zamuyi ko walima ta kwashe da dariya tana fadin party kuma
yaya kamar wata yarinya karama au to ke in bakiyi yar fillo zatayi ai ?
Ko sai ki hada muna taron fulanin ku ayi sharo ayi rawan sanda nayi murmushi ina fadin yaya ai sai za
aje neman aure ake sharo ba a haihuwa ba.
Au ashe akwai kallo kuwa ranan da zaki kawo muna miji don sai munyi masa shadin nan dubu kafin mu
bashi mata.
Abokansa suka kwashe da dariya wani ke fadin ka ganta kuwa sai jarumi zai iya zuwa don wanan za a
kashe nagge a kanta kana ganinta nan.
Au Allah dai kace mu shirya kwasan nagge ke nan nidai sai murmushi kawai nakeyi don ban iya cewa
komai idan yana min irin ba an nan.
Yanzu ke Nafisa sai mun hadu a gida ke nan ko yar fillo dai wasan Nagge zatayi muna da kiwo ke kuma
kince bakyayin party sai walima ?
Tana dariya take fadin sai mun dawo yaya Allah yasa kana gari ba tafiyan zakayi ba