Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ragewa.
Rayuwan malam bahaushe akwai kalubali da yawa a cikinsa inda wani zubin ake yawan tauyewa mace
incinta da sunan aure.
Akwai part din da babu kowa a cikinsa instead daya ta zauna a cikinsa amma iya tace sam hakan ba zai
yuyu ba wanan din dai shine kasonsa don haka shida ya dauko auren mata biyu lokaci guda dole ya
zauna a cikin nasa hakana.
Sani Allah sani ma,aiki aka samu kawu Dauda ya rokan masa wanan filin daya fadada girman ginansa
har ya bambanta dana yan uwa saboda kara fadin wajesa da akayi.
Saboda raba gado da akayi yasa yaran mama Dubu tun bayan auren yayansu Jafar da hjy Iya ta koma
gidansa da zama suma kusan rayuwansu a can gidan suke da zaran sun dawo hutu zasu tare a wajen
kakansu suna tayata zama wanda shi jafarne ya tilasta masu yin hakan.
Haka kuma idan suna gidan wajensa yana da wuya ka samu gida kaca kaca a cikin kazanta don suna
tsayawa su gyara tsakani da Allah.
Tsab mama Dubu ta gama shiryawa don zuwa ta dubo mahaifiyarta da iyalan danta don tana hasashen
Asmau ta samu karuwa a jikinta yadda hjy Iya ta fada mata .
Idan zata zakice ba a gari daya suke zaune ba don shiri takeyi sosai sayi wanan sayi wancan taje masu
dashi sai kice tazo daga kauyene ganin su.
Saida ta gama shirin da komai ta fito tana fadawa mutanen gidan nasu zataje ta duba su iya ta dan
kwana biyu wanan ba bakon abu bane sunsan data saba yin hakan .
A zaton suma basu dauka zata zauna kamar take zaune din nan ba a cikinsu da Allah ya albarkaci yayan
nata sosai fiye dakowa a gidan kusan ace dai sune sukaci moriyan gadonsu da aka raba na marigayin.
Tunda wasun su har sunka ga saida kadaran da suka gada din sun koma rabe rabe duk da mahaifin
nasu bai wani dade da kwantawa dama ba sosai.
Dama ance mai zari a wajen rabon gado shine nasa bai faye albarka ba kusan haka dinne ya faru don
kuwa su yan dakin hjy babba da aka tsaya masu suka samu kaso mai tsoka sune suka fara wullakanta
dukiyan nasu.
Wanan ya jawo tsaiko da iyayyen mata suka hana yayan nasu raba wanan baban gidan da suke zaune
ciki a yanzu inda sukai rayuwa da mijin nasu.
Tunda gidan mata hudune ras irin ginan malam bahaushe duk da ko wace bangarenta a kewaye yake
sai babban falon marigayin inda turakasa yake a nan yayi rayuwa har Allah ya karbi ransa.
Don haka har gobe idan ka shigo kaga yadda suke rayuwansu zakice ko maigidan nasu yana rayene
amma kuma kowa a yanzu yana cin gashin kansa sai dan abinda ke shigo masu da akan kasa kamar
yadda dai aka sabayi tun baya Allah yasa mu dace ya jikan iyayyen mu da rahama Allahuma Amin.
Daki daki tabi tana masu sallama da sai ta dawo yadda kowansu keyi idan zai dan fita sukai mata Allah
ya kiyayye zakice ba wani abu na rashin jittuwa a yadda sukeyi din.
Saidai hakkurin wani ya dara na wanine a zaman don anyi ba daidai ba an nuna hadama da zalama daga
bayane suka sulhunta kansu kan hakan.
Yan jikokin gidan da almajirai suka dauko mata kaya suka nufi bakin titi inda zata hau keke zuwa
unguwar su iya din.
Fitanta soma zancen ta ukkunsu dake fadin yau kuma ta haka aka fito muna ba Habu yayi tafiya ba
kada ya dawo ya sauke abinda ya dawo dashi mugani a bamu tabon mu .
Sai ita amaryansu tace aiko yaya bata da haka kowa ya sani nan gaskiya ko bamu gani ba sai an bamu
in rabon mu ya ratsa.
Ni bance bata bamu ba ai maganace kawai nakeyi ta fada a hasale don ba a kama mata yadda taso aja
zancen da nisa ba ta katseta.
Yaran da suka rakata zuwa titi ta sayawa rake sai dari dari data basu suka dawo gida da murna hakan
yasa data dau kaya zata fita suke taso durrrr subi bayanta da sunan rakiya don dan wanan ihisanin da
take masu.
Itama hakan yana mata dadi tana jin dadin rakiyan yaran wani lokaci takan daukosu suzo su wuni su
koma in Jafar na gari mota tana a wadace .
Daidai kofan shiga gidan mota ya ajeta da kayanta sanin da mai adaidaita din yai mata yasa ya taimaka
har cikin get ya shigar mata da kayan kuma bai tsaya karban kudi ba duk da tsawan da take mashi akan
ya tsaya ya karbi hakkinsa amma yaki saboda mutunci.
Kauyen Zakuwande ya samu halartan baki daga sassa na duniya mu sanman a yan nahiyar africa
manoma da masu kiyo da suka cika wanan gari dam ko ina bakine dake halartan taron mafi girma da
akeyi bayan shekaru.
Engineer Abubakar daya gama hada duk wani na,ura da zai hasko masu tauraron dan adam dinsu ya
sauko daga saman motan yana kara duba saitin dayayi da kyau kafin ya nufi bayan mota ya bude yana
dauko goran ruwa ya balle yana kokarin zuba don dauraye hannunsa.
Hankalinsa sam bai kaiga dandazon mutanen da suka kewayesu suna kallon aikin nasu ba sai lokacin
daya gama wanke hannun ya kwankwade sauran ruwan ya cillan da goran gefe .
A lokaci ya kula da jama,an dake waje ashe akwai inda yafi Nageria kauyanci don goran daya cillan suka
taru suna wasoson dauka .
Har da manya wani dattijo daga cikin masu rige rigen daukan gora da aka tureshi tare da kekensa yasa
Habu din fadin subbahanallahi yaje da sauri ya kama tsohon yana tayar dashi tare da kekensa yana
mashi sannu.
Tare da tambayan baba bakaji ciwo ba ko yace banji ba dana naso dai in samu wanan jallon nasaka
ruwa a ciki yara kuma sun hana.
Ina zuwa yace ya koma ya dago gora biyu cike da ruwa ya kawowa dattijun ya bashi cikin girmamawa
godiya tsohon ya fara mashi sau ba adadi yaja kekensa ya tafi.
Juyawa yayi yaje gun yan uwansa da suka zubo mai idanu saida ya karaso ibrahim ke fadin wanan yasa
danasha ruwa saina jefa gora a bayan mota.
Tausayi tsohon yabani yana bukatan gorance da ganin haka yafada ibrahim yace tun dazun yake tsaye
ai yana kallonka .
Watau wanan gari gashi dai babbane cike da jama,a kuma amma kullum basu wayewa su kasan abinda
ya kawo hakan yace ina zansan hakan ni dana fari shigota yau din .
Yace gargajiya donsu har yanzu gargajiyansu yana nan basu yarda sun dauki akidar nasara sunsawa
kansu ba aikinsu ke nan noma da kiyo komai arzikin mutum ata wanan hanyar zai nuna halinsa.
Gaga kuwa ba zasu taba cigaba ba matukar basu yarda da nasara ba a rayuwansu gargajiyace
tsantsanta a garin nan ka duba ko tsarin shigarsu mafa dabanne kuma kowa da irin al,adansa wajen nan.
Hakan yafi masu sauki kallo daya zakai masu kagane basuyi sakaci da addinin su ba har yanzu yawan
kabilu kuma ai duk zubin fulanine garesu ko larabawa.
Haka sukai ta hira tsakaninsu suna jiran lokacin da zasu fara gabatar da shirin nasu don komai a yanzu
hada lokaci kadai suke jira.
Kuyi hakkuri mu dauko tushen labari don fahintarku masu karatu nagode.
ZAINAB IDRI MAKAWA
[12/26, 2:55 AM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sallaman mama Dubu yayi daidai da jefo plate din shimkafan da Saiba tayi ya fado saman hijjab din
jikinta kafin ya gangara ya sauka kasa daidai kafanta ya tsaya.
A hankali mama tabi plate din da kallo haka kuma take kallon yadda sauran shimkafan dayake
gangarowa daga saman jikinta zuwa kasa.
Kaita girgiza ta dago ta saukewa Nusaiba kafin ta mayar kan Asmau data dafe baki cikin tsoro da firgici
kai ta sada kasa tana mai tsananin jin kunyar uwar mijin nasu.
Da kyat mama ta iya budan baki tace yaran nan har abin yakai haka a gareku daga haka ta juya don
bari part din taga hjy Iya a tsaye itama cikin takaici take kallonsu.
Gara dai da kuka gwada ga uwarku yau tunda ni kun raina min arzikina mata kamar dabbobi kullum
fada dan abu kadan fada kamar karnuka.
Akanku aka fara zaman kishine wai in ba auro mata ana haihuwan ku kun mayar da gidan yaro gidan
yan tasha gidan dambe .
Badon makwabta na tsoron jidalina ba da yanzu gidan nan ya cika da yan kallo tunda kun zama
mutanen bamza.
Kishi haukane wai mijin ku yana wajen nemawa kansa rufin asiri ku kuna nan kuna tona masa asiri a
cinkin unguwa sai yaushe zaku bar wanan bakin kishin nakune wai ?
A hankali mama da ranta yake bace ta zagaya Iya tani dake masifa ta karasa ficewa daga part din zuwa
nasu wajen kokarin cire hijjab dinta da suka bata takeyi kada ya lalace ban daki ta nufa taja bucket ta
jikashi tare da yayafa omo ta barshi a jiki.
Fita tayi waje don bata zauna ba kayanta dake can ta waje ta shiga kwasowa zuwa cikin falon
mahaifiyar ta din a daidai lokacin Iyan tani ta kara fada ta juyo zuwa wajensu rai bace.
Ta samu mama na kokarin zuge zip din dan jakar kayanta data dauko wanda zatai dan kwana biyu
dashi a nan zani ta dauko daga ciki tana sauyawa.
Wuri ta samu ta zauna iyace ta soma magana tana fadin yau naga yaran banza a gidan nan yara kamar
tashin gareji ace babu wanda zakaiwa fada yaji.
Sallaman Asmauce data shigo tana sune kai hannunta dauke da cooler abinci tazo ta dire a gaban
mama a daidai lokacin kuma itama Nusaiban ta shigo da ruwan data surka da postard cleak ya rine a
cikin jug ta aje gaban mama din cikin girmamawa.
A,a ku dauki abinku ni a koshe nake daga gidan mijina nafito yanzu koda bai raye bayansa basu barmu
a cikin yunwa ba Alhamdullahi nagode.
Zaune Asmau takai tana dan dukar dakai Allah ya gani tasan mama mace ce mai kawaici da kawar da
kai daga abinda sukeyi bata kulawa koda ance ga abinda sukeyi a kullum nasihanta dasu shine su zauna
lafiya suba mijinsu farin ciki ga nemansa.
Fitansu koma bayansane ga harkokinsu tasan zaman kaunace ya hadasu da danta don haka suma dul
biyun tana kaunarsu tunda dantane ya daukosu ya kawo matasu amana a cikinsu.
Yau sai gashi iya shegensu yakai har plate din abincin danta suka watsa mata saman jiki ya watse a
tufafinta ita yanzu me zatace da boyar Allah nan mace mai zurfin tunane da kawar da kai irin mama.
Kaita kara sadawa kasa ta soma magana mama don,,,,,,
Asmau jeki kawai kuci gaba kada ku bari zaman nan dai ina son ku sanin na bautan Allah kuyi akwai
hakki da amana a tsakanin mu daku da mijinku dake can yana neman abin rufin asirin mu.
Idan kun zauna lafiya kuji dadin hakan idan kuma kunki kome ya biyo bayan hakan kuka da kanku kada
ku kuka da wanin mu nan Allah ya gani munyi iyakar yinmu akan ku kun kasa kwantar da hankalinku ku
daina wanan shashancin kishin a tsakanin ku.
Sauran mata da suke zaune da kishiyoyi ake ganin kamar zaman lafiyane a tsakaninsu kokari suke suna
danne kishinsu a idon jama,a kowa da kuke ganin yana zaune lafiya danne abin yake kasan ransa shin ku
ba zaku iya hakan ba don Allah.
Mama wanan yarinyar yar rainin wayauce waini Asmau zata zubawa abinci a plate a kawo min don ta
raina min wayau kome Saiba ke fadan hakan ga mama.
Hannu mama din ta kara daga mata tana fadin ban tambayi ba,asiba don Allah komai mutum yayi kansa
yaiwa ina dai son ku sani ba a wullakanta abinci a zauna lafiya.
Wanan shine maganata dukkan ku nan ba zance bakusan abinda nake nufi ba tunda kowacen ku
uwarta tana da kishiya a gida.
Mama bani wullakanta abinci wullakancintane kawai ya mota innice nace ta ban abinci cewa take naje
cikin tukunya in daba shin laifine ni har na zuba mata a plate mama ?
Amma dai kinsan niba wullakantata bace da zaki ban abinci a cikin plate kamar nazo bara a wajen ki
kema kinsan nafi karfin hakan wallahi.
Yanzu dai sai kuyi ai garara ku nunawa uwar naku halinda kuke kwana kuke tashi dashi a cikin gidan
nan ta gani ksllon Iya din mama Dubu tayi tana fadin mama kin hada kayan na soma wankewa ?
Don dama duk aka kwana biyu mama tana zuwa gidan ta gyarawa mahaifiyarta waje tayi mata wanki
da sauran gyaran waje sai idan yan matanta sun dawo hutu suna gari suke dauke mata hakan.
A cikin matan Jafar din babu wace zatace bari ta dan gyarowa Iya part din ta matukar basu din bane
sukazo sukayi wurin zai koma fes.
Ganin mama din ta fita batunsu yasa Saiba fita cikin hasala tabar Asmau nan saida zata mike take kara
fadin mama kiyi hakkuri don Allah.
Jeki Asmau a kula don Allah kece dai babba a gidan nan kanninku da abinda kukeyi sukr koyi don Allah
Asmau arika tausan zuciya idan rai ya baci.
Fita tayi tana tunanen irin halin mama dubu na sanyi hali macece datake rike girmanta da kawar da
ido akan duk abinda ke faruwa danta dasu iyakarta nasihan da zaiwa mutum amfani gaba idan yabi.
Saidai ko tayi kokarin bin nasihan da ake mata hakan bai samuwa don Nusaiba taza fito da sabon
fitinan da sai tabiye mata sunyi fitina.
Ita wanan tana da dama sosai fiye da wacan fitsarariyar da tafita duk wani fitina daga wanan nusaiban
yake fitowa a gidan nan Iyace ke wanan maganan bayan fitansu.
Taron yarane kurciya shike rudinsu a wanan lokacin wanda sukeyi a kansa yana can baima san suna
yiba zasu zauna su halaka kansu haka a banza kan namiji.
Wata rana ko ance suyi hakan ba zasuyi ba ai don girma yazo a lokacin saidai su koma kishin mumuke
wanda yafi wanan da sukeyi zafi.
Mamace take fadan hakan ta mike ta dauko tsintsiya don ta fara gyaran dakin Iya din da yayi kaca kace
ga kura ko ina a falon har makewayin data shiga yana bukatan gyara idan zai samu.
Komai a wajen taron nan yana gudana daidai sun fara hasko wa duniya abindake wakana wanda
hakan yasa hankalinsu daukuwa da aikin don abune da yake son natsuwa don kada a samu kuskure.
Sallah ya tayar dashi da yunwan da yakeji ya fito daga cikin motar tasu mai na,ura zuwa lokacin wajen
taron ya cika makil da jama,a tare da Sahabi suka nufi masalacin sukai ibada ya jima kafin suka fito tare
da dan zaga wajen suna kallon irin baiwan ni,iman da Allah ya shimfidawa yan Africa.
Malam Habu zokaga kayan nono a wajen nan Sahabi ya fada ya doshi wani hanya dashi yana biye dashi
a bayansa koreni gasu nan birjit iya ganin mutum da matan fulani dake ta kaida komo a wajen.
Sahabi din ya tsaya yana taya wani kwaryan nono hakan yasa Abubakar ya fara raraban ido yana bin ko
ina na wajen da kallo direct ya nufi wajen wasu da suka tsabtace nasu da komai a cikin tsabta gwanin
ban shawa .
Malam zoka saya baida tsami ko karni lafiyanyyen nonoce tatsin yau din nan muryan wata bafulatana
ke fadan hakan ya karasa gabansu cikin mamakin jin yadda take hausanta na yan Nageria sak a bakinta.
Sahabine ya karaso yana fadin aina fadama sai inda kallonka ya kare a wajen nan yaji matar fulani din
na fadin wanan na shanune wanan kuma na rakumi ga wananshi da akecewa wara da wani hausan
nonoce sahihi ake dafawa ya hade haka.
Sai wanan kuma cikwai ce mai dadi baida mixed a cikinsa zakaso ka kara idan kayi amfani da kayan don
babu algus a cikinsa ko wani mixed .
Kai amma ke yar Nageria ce ko sahabi ya tambaya tace meka gani tana murmushi a fuskanta.
Kafin tace dashi daga dai can muke ta fada tana juyawa da alaman neman wani takeyi alokacin a cikin
harshen fulatanci take kwalawa wata kira da YANDA yanda yanda tana mata hannu tazo.
Sai ga wata doguwar yar matashiyar budurwa ta juyo wace aka kira da Yanda din takaraso zuwa wajen
matar tana mata fulatanci.
Ido ya kafe ta dashi yana kallon yadsa ta karaso tanawa matar magana acikin yanayinta.
Yayi da Abubakar yake tsaye yana kallonta cikin mamaki yana fahintar me take kokarin fadawa yarinyar.
Daidai lokacin kuma Sahibi ya juya harshe a cikin turanci yake fadin ko ya saye yana da wuya yakai gida
bai lalace ba iyakarsa idan a nan zaiyi amfani dashi kawai.
Sai sukaji muryan matashiyar na basu amsa da fadin ku saya daga nan har sati biyu baya komai koda ba
a saka a cikin fridge ba.
Kayan mu suna dakyau da inganci bawai ina yabo bane don kusaya ko don na cuce ku saboda nasan
zakuso shi ko nan gaba.
Ta kara fada a cikin turanci da alaman gajiya karara a fuskanta lokacin tana dan kakabe kuran dake taba
koren nasu da wani dan gashin dake hannunta na dabba da akaiwa ado da duwatsu .
Tsaye sukayi galala suna binta da kallo tare da tambayan wai dama kuna jin turanci haka ashe da
zaginku mukayi shike nan kunjimu.
Ta dan kai zaune tare dan murmusa tana fadin kadan kadan ba balle nasan ba kuyi kama da wayanda
zasu zagemu ba ai.
Dagajin hausan mamanku na gane ku mazauna Nageriane don hausanta daban da wanda kukeyi a
kasan nan.
Eh daga can muke koma ince a can aka haifemu rayuwace ta dawo damu gida bayan rasuwan
mahaifiyar mu rikon mu ya dawo nan.
Sosai ta bashi tausayi tsab ya gama kallonta yana karance yanayinta turancine neat a bakinta amma
kuma gata ta saje da dabi,un mutanen wajen ba zaka taba cewa ita din tasan ko zo inkasheka ba da
hausa balle turanci.
Yanda din ta kawar