Chapter 75 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   75 / 101

222K to 225K   out of 302.2K words

kinga jariri Rahama a takaice
na bashi amsa da banje ba yaya kuma ban zuwa.

Ya kalloni da sauri tare da furta subbanallah lafiya meya faru nace dashi ba komai kawai dai banjin
zuwa gidan ne kawai a yanzu.

Nasan dole dai akwai wani abu amma yar uwarki ta haihu zakice ba zaki ba Rahama ko akwai abinda ya
farune ban sani ba yake tambaya ?

Ba komai hakan dai nace ba zani ba na sake fada ina kokarin fita daga dakin bansan ya sukayi da mama
ba sai gashi naji maman tudu tana min maganan tace.

Mijinku ya fada min kina fushi da yar uwarki nima nayi tunanen hakan tun shekaran jiya da naga bakije
gidanta ba har wanan lokacin saida raina ya bani akwai dalilin hakan ?

Kiyi hakkuri da yar uwarki kada ki bari har a gane kuna da matsala da ita a gidan nan ki shirya gobe kije
ki dubata in ma wani abu tayi maki ki boye hakan kada ki yarda a gano hakan ayu maku dariya.

Wanan maganan da mama din tayi min yasa na shirya naje tare dasu da iya ina gidan mahaifiyar mu ta
bugo waya nake ce mata ai gani gidan acikin harshen fulatanci nake fada mata abinda maria din tayi min.

Take fadin wai nasan halin maria ai wanan halin nata ai yasa aka hadota dani zuwa aure katse ummah
nayi da fadin dana san haka zai cika dani ta dalilinta ta kuma gudu ta barni da ban biyo ta zuwa garin nan
ba.
Baki yarda da kaddara ta riga fata ba ke nan ko ina kike tunda Allah yayi jafar mijinki ne sai kun hadu
don haka ki daina cewa itace tayi sanadin haduwan ku Allah ne ya hadaku tun farko.

Wani malolon bakin ciki na hade ina goge fuskana ban tsaya ba duk yadda taso in tsaya muyi shawara
na koma gida tare dasu mama hakan yasa ta fadawa habu mijinta halin da muke ciki da ita din.

Ba kunya sai gashi ya shigo da yamma gidan muna zaune saman baranda muna shan iska don ba wuta
shi yasa muka fito daga wajen ginan mu samu iska.

Bandashi yaya da yake ciki zaune tare da mama suna hira bayan mun gaisa dashine har dan shiga sai
kuma ya dawo yana fadin zo nan Rahama ya shige ciki ya barni ina kallonshi ta baya.

A dakin na samesu su ukku tare da ya J da mama suna zaune na shiga ina kara gaidashi bai karba min
ba ya hau fadin Rahama meya faru tsakaninki da yar uwarki ta kirani tana kuka wai kinki tsayawa kuyi
maganan komai a tsakanin ku.

Saida na lumshe ido ina hadiyan zuciya nace ni din nan kuwa yace look Rahama banson irin haka dole
akwai wani abinda ya faru tunda har tace hakan.

A,a habu ba zaka shiga tsakaninsu kayi saurin yanke hukunci ba yanzu ka nuna kamar laifin na wanan
yarinyarce ita kadai ita matar naka bata fada maka dalilinta nayin hakan ba ?

Tace ita bata san tayi mata komai ba haka kawai ta tsiri fushi da ita yaushe ma maria zata tsaya yin
haka ga wani balle Rahama ?

Kaji ai mama ta fada niko a cikin yaren mu na soma magana ina fadin ai dole kace hakan tunda dukkan
ku baku dauki hakan wani abu ba tunda niba mutum bace.

In zaki fada da hausa ki fada kina muna maganan da bamu ji so kike ki tayar mata da hankali bayan
kinsan halin da take ciki a yanzu.

Ina jin hakan bansan lokacin da hawaye yazo min ba na soma fadin niba mutum bace ai tunda ta kasa
yi min abinda ya dace lokacin da nake neman wani na kusa dani a wajena.

Kamar yaya ya fada ya kura nin ido zuciya yazo min na ci gaba da fadin ashe ba dadi itama ta shareni
kamar bata san inda na fito ba ?

Dama ai ,,,,,, kai habu kada ka matsawa yarinyar nan don Allah kasan dai a yanzu halin da take ciki don
Allah ka daina maganan nan tunda tace ba komai kasan dai ba fada maka abinda ya hadasu zatayi ba .

Nayi mata magana dazun taje ina shike nan koma meye ai ya wuce dai yanzu ko so kke ta tare a gidab
ka baki daya tabar mijinta a nan kwance ?

Amma mama ai gaku tare dashi kinsan mama ta hana kowa irin zuwan nan da akeyiwa mace idan an
haihu sai daga can gidane suke zuwa nan tace tunda salima taje taga baby bata koma kuma ace itama
din bata zuwa ai hakan baiyi ba mama.
Amma habu ban zace zaka shiga tsakanin yaran nan ba harka nuna kana goyon bayan matarka haka kiri
kiri inma laifine matarkace ta fara mata ai kasan su fulani da riko nasan shine take nufin zata rama itama
ga nata wautan ?

Sai lokacin yayi magana tunda dan uwan nasa ya soma magana yana zaune ya kura mashi ido yace
dashi habu bakaji me mama tace dakai bane wai ?

To ka barsu kawai banson irin hakan Rahama dai dole taje wajen yar uwarta baka san sanda suka sami
matsala ba haka ba zaka san shirinsu ba kuma .

Yanzu kazone ka daga mata hankali kuma kome tunda dai an tillasata mata zuwa kuma ta tafi ka fitar da
bakinka a cikin matsalansu don Allah.

Su kuma yaran nan da basuje ba don kansu ai sun kumayiwa kansune ba wani ba suma matane ai
kamarsu ko ?

Shina so in fada ka rigani abinda basu kulaba shine maganar da ya J din yayi a lokacin mai tsayi wanda
tunda ya kwanta ciwo zance karona farko ke nan da naji yayi magana mai tsayi irin haka ?

Haka kuma kariyar harshen nan nasa a ysnzu ya rage harafin bakinsa yana dan fita daidai a cikin yan
kwanakin nan tunda ya soma zama da mikewa din nan .

Sai dai kuma na lura da wani yanayi idan ya mike ko yai magana zaita yin zufa yana dan haki na dan
lokaci kafin ya koma daidai.

Wanan karon ma hakan ne ya faru dashi idon dana kura mai shiyasa mama fadin daidai habu din yana
mikewa tsaye tace.

Kazo har ka saka dan uwanka magana yau yaran nan da abin dariya kuke wallahi kowan ku a nan ya
shigarwa matarshi ke nan ko ?

Muryan iyace ya katseta tashigo tana fadin yanzu saratu kece muna gaka nan ka shigo nasan fita
zakayi abin ka kuma yasa na taso.

Iya fushi fa nakeyi da kowa gidan nan yanzu fisabillahi iya ace har dake matana ta haihu bakije kin
zauna da ita ba kina gida abinki zaune iya ?

Yi min adalci mana dan nan iya din ta fada a marairaice tana wani irin lagabe kai tace yaron nan yana
haka ai in nabar gidan nan sai a zageni ?

Hakane yanzuma aida nashigo anan din na sameki bakomai ai iya don kawai na dauke iyalina mun bar
gidan nan shine kowa ke fushi dani ko ?

A,a habu idan kowa yayi fushi daku kasan bandani a cikin shirmen nan wanan abin dana fada shine
kawai dalilina amma kai min aikin gafara gobe zan je insha Allahu in rai yakai.
Sun dan jima suna zance dashi ya fita bai kara bi ta kaina ba nima ina zaune ban daga daga inda nake
zaune ba tare da iya ya fita mama kuma ta mike zuwa bandaki .

Hannu ya miko min alaman inzo inda yaken zaune banki ba na mike zuwa gareshi na zauna a gefenshi
ya soma fadin kina son raina ya bacine Rahama.

Fushin nan da kikeyi da kowa ya isa hakana nine mai laifi ba wani ba kuma nabada hakkurin ai niba
fushi nakeyi ba na bashi amsa ina kokarin mikewa sai kuma na koma na zauna ina fadin.

Na kula kamar maganan ka yana son dawowa daidai amma kuma kana wahala ga hakan don zufan da
naga kanayi da yawa yace haka nima nagani .

Saidai gaskiya ina jin saukin jikin nawa sosai a yan kwanakin nan karfin jikin daine sai a hankali amma
Alhamdullahi gaskiya.

Na lumshe idona ina tayashi yin tasbihi ga ubangiji subbahanahu wata,ala daya nufemu da ganin hakan
.

Wa zaisa bawan Allah nan zai mike haka yau shine Allah ya tayar a cikin ikonsa haka har yake iya wasu
abubuwan daya shafi rayuwan sa dana iyalinshi haka.

Muryan mamace data leko tana fadin to kina ciki bari na leka wajen dubu ance tana fama da kai yau
tun safe data shigo bata dawo nan din ba .

Hakan ya kawar da shirun namu da yake fadin agaida mama din ni dai bance komai ba don nashiga na
samesy zaune da saratu suna magana da ita da saratu nagaida ita naga ta amsa min a dakile.

Na saba da hakan da mama ke min tun abun yana damuna har yanzu na share na fitar da komai a raina
abu dayane kawai ina kare abinda zaisa ta taba min mutuncina.

Iyakarmu gaisuwa inma tazo waje ina kokari na kaucewa wajen don gudun samun matsala a tsakanin
mu a bakin maman tudu na kara fahintar wasu halaiyan mama din daya kara sa nake taka tsantsan da
ita.

Mun jima a tare dashi dakin zaune kafin Anty Asmau ta shigo da yara suka zauna suna hira hakan ya
bani dama samu na mike nabarshi dasu na fara gyaran part din dana gama kuma wanka naje nayi na fito.

Saida darene mama ta samu daman yi min fada sosai kan nayi hakkuri da yar uwata kada na yarda aji
kan mu har a gane muna da matsala tundai saratu taji zancen zai juya wani abu na daban a bakinta .

Na fahinci ba saratu ba har salima mama tudu ta tsana acewarta mahaifiyarsu ta sagartasu sunki aure
suna abinda suka ga dama a cikin gida zaune.

Dole washe gari na shirya na tafi saidai ban barta ba don yadda nayi kuka itama saida na sakata yi don
na fada mata abinda ke zuciyana.
Inda ta nuna ba hakana bane wai mijinta ya hanata fita saboda matsalanta yasa ta kiyayye dole dai na
zage nayi abinda ya dace ace nayi a wajen duk da karfin hali nakeyi a lokacin.

Saidai nasha zunde da sheri a wajen yan uwansu a ranan kowa da kalan sherin da yake min akan cikin
dana samu a yayin jiyar miji ni dai nawa kawai murmushi.

Ban dawo gida ba kamar yadda kowa ya zata daga gidan ya habu gidana na nufa a ranan a can na
kwana don ina son gyaran gida nida Anty Nafisa da wata yar yaya Auwal mukazo gidan muka kwana.

Koda mama ta kirani a waya nace dasu gani nan gidana mama ina son inyi gyaran gidan ne duk yayi
kura yana bukatan gyara take fadin ga mijin ki nan yana fada dake hakan baisa na dawo ba a ranan saidai
nayi mata bayani maganinsa daya dace a bashi na shafawa kuma su san yadda zasuyi.

Ba komai yasa na koma gida ba sai gulman da akai min kan wai ina ha,intar kishiyoyina na fake ga sunan
jinya na karbe masu miji dama mu fulani haka muke da kwatar maza .

In badon cikin daya baiyana min a jikina ba da ba,a gane muna cutasu gashi najawa Saiba saki saida ya
fara samun lafiya nasa an sake ta saura Asmau itama in batayi hankali ba korata zanyi in zauna ni kadai
kamar yar uwata.

Naji dacin wanan maganan sosai da naji hakan yasa na yanke shawaran komawa gidana tundai da naji
ance Asmau dince take fadin wai sun zama yan kallo yanzu basu gane komai a gun yaya din dul na tare
komai banson kowa yazo kusa dashi saini kadai ashe mun san abinda mukeyi ni dashi ?

Nasha alwashin duk abinda za ace saidai ace don ba zan koma gidan ba kuma zan dai dinga zuwa in
dubashi a can din iya abinda nasa a raina ke nan.

Washegari na tashi da aikin sosai su anty nafisa suka tayani a yadda na fahinta kamar ta samu manemi
a yanzu din don bini bini sai ya kirata a waya sun dade suna hira dashi.

Misali karfe biyu na rana mama ta kira waya tana fadin har yanzu bamu gama bane karya nayi mata
nace mama gaba daya gidan yayi kura saida muka fitar da koma ana kakabewa .

Da dare kuma ta kira tana tambaya nace mama ina ganin sai gobe don da sauran aiki ban koma ba dai
har kwana uku gana hudu nayi abinci da safe na shirya zuwa gidan.

Acikin kwaliyata na shiga da basket din abincina tiwon semo da miyar egushi nayi dayaji nama na aje
basket din a wajen su mama da iya.

Muka gaisa tana min sheri tace kice kin koma gidane da wayau yar nan daga zuwa suna saimu nemeki
mu rasa ?

To meya rage yaya tunda sun gama aika aikansu dashi kuma ai saita koma gida tayi jinyar cikin yanzu
kuma ?

Tana jinyar ciki ita daya ga miji a nan na mike ina murmushi zuwa ciki na samu yayi fushi sosai dani
hakan bai dameni ba na gaidashi da kyar ya amsa min .
Duk daya ban tausayi nasan banyi daidai ba don ko kallon dakin kawai da nayi dakin ma kansa yayi
missing dina don sai ince bai samu gyara ba daya kai sau biyu.

Har wani dan bashi dakin keyi a lokacin zaune nakai ina gaidashi bai amsa ba ya kyaleni nima nayi
shiru muryan mamace ke kirana tana fadin kizo ki dibarwa mijinki abincin nan nasan zaici sosai tin
shekaran jiya yake maganan tuwo gidan nan an kasa yi mashi.

Na mike naji yace No ki barshi ba zanci ba nayi murmushi ina fadin yaya fushi kakeyi dani ke nan bai
daiyi magana ba harna fita.

Na debo abincin a plate zuwa gabanshi na aje yadda yake kallon abincin yasa na mike na koma na debo
ruwa a gabanshi na zauna na fara dibowa ina bashi da kyar na samu ya karba bayan ya gama fadanshi
cikin zafin rai yana fadin nasan inba niba wazai samu yana taimaka mashi yadda nake mashi ?

A tausashe na soma magana ina fadin yaya ka tuna bafa ni kadai bane matan nan suna da hakki a
kanka tunda yanzu ka dan samu lafiya har kana dan iya mikewa ya kamata suma a basu hakkinsu ladan
nan kowa fa yana son samunsa don Allah kayi hakkuri in zauna gida itama ta dan taba ta samu ladan
hakan .

Na jima da loman abincin a hannuna saida na gaji nakai bakina na sake debowa na mika mashi ya
karba ya kumaci sosai ya gama na kwashe kayan.

A wurin mama nake jin cewa ashe zuwan da Yazid yayi shiya turashi ya daukoni sai yaje ya samu muna
gyaran gidan da gaskiya ranan tace dani.

Ranan munga tashi hankali ai na zata ai inkin dawo zaiyi fada sai kuma naji shiru koda yake dubu ta taka
mashi burki ai tayi mai tas tace ya barki mana idan zaki koma can ne ki koma da yake fadan mu nan ba
mutane bane a tare dashi ?

Ko ita Asmau bata iya mashi komai da kike mashine ta dai kwana nan din sau biyu jiya banga tazo
kwanan ba wai danta baida lafiya tace .

Oho dai na fada a raina ba dai zan zauna ba kuma a nan na wuni na gyara masu ko ina tas na shiga
wajen kowa da yamma kuma nace ni zan tafi kada yamma yayi min.

Kallona yayi Asmau tana zaune ba daman yayi wani abu yace saida safe kawai saiga iya take fadin yanzu
dai kinyi hijara ke nan kardai kin gudu ke nan fa ?

Iya gara ingudu inbarwa anty mijinta tunda ya samu sauki a yanzu itama ta samu nata rabon na tare
waje da sunan jinya na hanasu ganawa da mijinsu yadda suke so .

Kamar yaya kin hanasu ganawa da mijinsu yanzu ko da aka ga idanunsa sun bude aka san wanan da
kikai wahalan ki a lokacin wayace zai kama maki hakan ?
Gulman nan yazo kunneki ke nan don wanan dama kika koma can ke dai ai gulman nan ya jima da fita
gidan nan yanzu da kika tafi din waya iya abinda kikeyi masa din ina zaune yake cikin takaici da kazanta
kawai ya isheshi gidan nan .

Zai dai tattaro ya cin maki can mamaku ma tace gida tayi tunda Allah ya kawo sauki na hanata tafiyane
don in kun tafi gaba dayan ku abin bai dadi gara dai ta sauna har akwana biyu.

Banda gulman me suka iya sunan son miji ne kawai abaki amma babu hus a garesu mutum bai kula da
kansa ba balle wani saida yazid yayi cin mutunci yadda suka bar gaban gidansu da kazanta dazun .

Murmushi nayi na saba gyalena ina fadin ni zan tafi shiru yayi kamar bai jini ba a raina nace kaji dashi
ba dai zan zauna ba din a kara zagina duk a yanzu dai zagin bai kankaruwa a gareni ba riga dana shafawa
kaina wanan kuma ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/29, 10:17 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣6️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Haka abin ya kasance duk da ya nuna baison hakan dana yankewa kaina amma saina dake da safe zan
shigo inyi mai duk abinda na sabayi idan yamma yayi kafin magariba saimu koma gida da Biba ko anty
Nafisa.

Tun yana daure fuska idan nazo har yakai ya dan sake ya fara daina hakan da yake min ina daga ciki
tare da mama nake jin hiran mutanen gidan dake zaune falon da ake jinyasa din salima ke fadin.

Kefa Asmau na kula kwanan nan sai wani sheki kikeyi kina wani budawa meye sirin hakan kuma ?

Koda yake duniya taki yanzu an watse an bar maki miji

75 / 101