Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
da gargadinshi akan kada kowa yasan hakan don na kara masa gobe
nasan matsalan dan uwana wajen kwadayi.
Jin dadin hakan yasa yace kai amma Ramatu kin kasheni yau to jo kiji wani magana na matsa ya soma
magana kamar a cikin rada zakice yana tsoron wani yajimu duk da matarshi saida ya turata cikin gida ta
samo leda ya san min dankali.
Wanan daman muka samu ya fada min wasu sirika da zamu fito na dankawa matarshi itama dubu biyo
don nayi mata faein sani dani akai nemanta a lokacin bayab mune akai aurensu.
Na kurune da dani aka hadashi amma uwarshi tace sam bata yarda da hakan ba ita don idon mu ya
bude da yawa zanwa danta wayau na hanashi aje Nagge.
Nikan taimakona tayi a lokacin da irin gulman nasu da camfi na kauye da suka dora muna wanan yasa a
kullum baffa ke fadin mugaye muke masu bakin jini a haka zamu kare a kiwo.
Ni nasan Allah yana sonmu shine ya kawo sanadin da bamu hadu da baffan mu ba lokacin don da yaga
yadda muka koma komai na iya faru a lokacin don baffa mugun bafulatanine sosai shiyasa mutane ke
masa lakani da maita.
Mun dawo lafiya baki alaikum da kamar ba zamu samu taro wajen yan gidan mu ba kome suka gani
oho masu saiga Asmau itace ta fara shigowa yi muna sannu da zuwa.
Daga baya Saiba tashigo a yatsene take muna sannu da dawowa ya hanya muka amsa mata da lafiya
kalau.
Acan gida mun shiryawa ummah sosai gaskiya yaya Habu yayi kokari ba kadan ba tunda ba wani
sana,a yar uwata takeyi ba.
Bayan dawowan mu da sati biyune ummah muta tare a gidan sabon mijinta dake kaduna a unguwar
Dosa mama dubu dasu inna sukai mata rakiya a cewansu sunyi mamaki kwarai ashe mutumin ba
karamin mutum bane .
Ita matarshi data rasu ta barshi da yara biyar tsohuwar lauyace mai zaman kanta haka yayan nasa ma
duk karatu sukeyi basu zama a gida.
Nikan sai najiwa ummah tsoron hakan don yan bin nan ba ai masu shigen kutse haka duba ga yadda
mu nan muke fama da facalan yar uwata a wajen kishi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Mu dai bamuje kaduna ba saisu mama dubune sukai mana kara ita da kishiyanta inna da yanzu itace
kamar uwar dakimu gidan saboda tana nuna muna kulawa sosai kodon muna tare da yartane oho ?
Koma meye damunzone gidan zata karbe Abbati tana angonta tana ba,a kasancewa itace amarya
acikinsu.
Wanan yasa muma muke zama a dakinta har dai shakuwa ya shiga tsakaninmu sosai da ita bamu gane
ko mama dubu tana son hakan da mukeyi ko bata so ?
Har dai yakai ya habu da kansa yakan dauki yaron yakaiwa inna shi don yawan tambayansa da takeyi
lokaci lokaci kota niko gari tazo gida tace tazo duba maigidantane ita da iya.
A kullum kuma inna tana kan muna nasiha game da zama tare zakice ita din yar uwamuce ta jini donshi
shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu da ita harma yayanta.
Don haka ta takawa mama wajen rakiyan ummah gidan sabon mijinta akaduna sai gashi sunje sunga
abinda basu zata ba a can din.
Yanzu tsakanin mu da ummah wayane mu duka kowa na kiranta yaji lafiyanta tana ce muna lafiya
kalau wanan ke kwantar muna da hankali.
Gaskiyane da wasu mata idan mazansu sun mutu sun barsu da yaya koda iyayyensu suna raye suke
fadin gatansu ya fadi gatansu ya tafi wanan zancen ba karya bane don mun gani a kanmu a rayuwan mu.
A yadda hardo ke fada muna a yanzu duk shanayen mune wajen baffa shanayen da idan da zamu
mallakane zasu taimaka muna harmu taimakawa wanin mu a rayuwa.
Sai gashi badon ubangiji ya rufa muna asiri sanadin ya Habu ya auro yar uwata ba da rayuwan mu a
bautan baffa da iyalansa zai kare muna.
Sannu sannu yau nakai UG 3 da dadi da wuya haka karatun ke zuwa min a daidai yayin da Anty Salima
take shirin zuwa bautan kasa a lokacin kuma muka shiga wani tashin hankali sabo dayafi na baya a gidan
rikona inda yar uwata take aure.
Don ko an samu sakon ya Jafar wanan ciwon kan nasa a yanzu ya dawo inda abin har yafi na farko ga
fadan masu fada labari yazowa mama kamar hauka yayi a lokacin.
Innalillahi wa inna alaihin raji,un tashin hakan da muka kwana dashi muka tashi dashi kr nan a gidan
wanda yasa su kawu dasu yaya habu kwasan jiki zuwa garin da yake.
Da alama ba dadi don duk lokacin da wani zai kira a gida aji halinda yake ciki amsa dayane shine jikin
dai da saukin musulunci za ace kawai amma ba sauki sai a wajen Allah.
Rana daya naga damuwa karara ga iyalinsa ranan da ya Habu ya kira yana fadawa mama cewa da
wahalan da Jafar yake ciki mama gara a roka masa Allah kawai saukin mutuwa.
Sai mama ta fashe da kuka kuka mai tsanani dole kowa a gidan kukane na tashin hankali ba maiba
wani hakkuri a gidan lokacin.
Duk muna falon iya gaba dayan mu in banda iyatu dake faman aiyukanta a wajen gidan nan saiba ke
fadin mama ko zamu shirya mujene ?
Ai yanzu ba zancen zuwa bane tunda gida zasu dawo dashi a gwada a gani abin na asibiti yaki suncesu
basu ga ciwon komai a jikinsa ba komai nasa yana lafiya don haka bana asibiti bane abin iya take fadan
hakan ga matar nasa.
Dawowa dashi din garama da suke can labari kawai mukaji bamu gani ba don ganinsa a irin halin da
yake ciki shine babban tashin hankali ga yan uwa da abokan arzikinsu.
Kai innalillahi tashin hankali baida kyau don ciwon maimakon aga sauki sai kara sabon sallo na ciwo da
yakeyi yau ya taba nan gobe ya canza waje duk a jikin nasa.
Idan ya taso yana kugi duk inda mutum yake a gidan yana iya jinsa saboda zafin ciwo a yadda naji har
salinta jikinsa ya farayi yana saba irin na macizai.
Haka na shirya na bar gidan a cikin damuwa ganin mama yadda take kuka a gaban kawu da iya tana
fadin wanan wahalan yai yawa in tafiyane Jafar gara katafi ka huta da wanan wahalan haka.
Duk da nake yarinya banji wanan adduan ta mama yai min dadi ba musulumi sauki aka sanshi dashi da
nema a wajen ubangiji ba zancen baki ba.
Masu fadan hakan bawa yasan abinda zai tar a gurin Allah ne shidai bawa ya nemi sauki koma meye a
wajen ubangiji shine mafita.
Har nakai school da wanan zancen nake a zuciyana a karo na farko da kusan shekara biyu ke nan da
zuwan mu gida ban taba gwada kiran layin Dage ba sai a ranan naji ina son kiran Dage in sanar dashi
halinda dan uwar mijin yayata yake ciki don mutumin arzikine sosai ya J komai mutum zai iya masa don
ya cetoshi daga wanan uku ban da yake ciki na bautan ubangiji .
Gashi ashe sakacin su yasa basu koma can wajen wancan malamin daya taimaka masu ba da farko
tunda sukaga sauki suka fita batun koda kawu ya koma yace ba abinda zai iyayi yanzu da ace tun wancan
lokacin sun dawo sun karbi abinda yace din da sun bashi goron sa da wata kila hakan bai faru ba a yanzu
don an riga da ancin masa ko ciwo yayi nisa wanan zancen tunda kawu ya dawo ya shedawa mama ta
fita hankalinta ga baki daya.
Cikin ikon Allah ina danna kiran layin ya shiga bai dauka ba har kiran ya katse a kasa nake tafe hakan
yasa na kara danna mashi kira a karo na biyu.
Sai gashi naji an daga ana faman fadin Alo alo alo murmushin karfin hali nayi ina fadin who is speaking
au kafirata ka kirana ashe ?
Naji Dage din na fadan hakan na sake sallama don na fahinci zai iya kashe wayan a lokacin ya amsa
sallama yana fadin wake magana ?
Nace budurwankace ta birni da kaba layin wanka koba dage bane yace kwarai kuwa nine Dage nace to
ni aljannace na kirakane muyi soyayya shiru yayi da har yasa na daga wayan na duba koya kashene a
lokacin.
Sai naji yana fadin Aradu Ramatuce oho yar nema ja,ira sai yau kikaga daman kirata watau ?
Ina gwada layinka Dage baya shigane nayi mai karya yace kai kinshan me Ramatu kudin da kika ban
ardu kudin albarkane ai watau da wanda kika bani da wanda kika ba inneje na hada suk na sawo muna
dan karo mace dana miji Ramatu bakiga yadda suka haifa muna diya ba wallahi kowa sai magana yakeyi
nashe wa tsayahu wanan karon zumuncine tsakanina da Ramatu.
Dariya na kwashe dashi na katseshi da tambayan mutanen gida har baffa yace kul ardu kun kuru da
baku samu baffan nan a gida ba lokashin .
Yayi cizon yatsa yashe ai zaku dawo shi za a kawowa shegan taka ita maria harda haihuwa da kado ko ?
Gabana ya fadi nasan za a rina dama indai baffa ne da suke kira da magajin tauri duk wani maison
maganin tauri yazo yaga baffa ya warke.
Dage akwai wani bawan Allah dan uwan mijin maria da akaiwa makaru nan dai na tsaya nayi mai dan
bayanin abinda nasani game da ciwon yaya din.
Kai amma ke Ramatu a kwaiki da shirme wallahi ina wanan garin dana fara baki shi zaki dinga mashi
hayakinsa haka kuma.
Ki samo magarya kunne gomasha bakwai kada ki dada daga hakan a samu dutsen tama kinshanshi ko
nace a,a amma zan nema yace kwara ukku kacal a saka kasan tukuyan a tafasa a tare saiya dahu sosai a
sauke ya huce a diba hannu uku asha sai ayi wanka da sauran .
In Allah ya yarda da zakuga sauki zan binciki baffa nayi mai karyan wani nason taimako a waje na bashi
dan kudi sai ya fada min wanin.
Bari na turo ma kudi a wayan ka ka sayar ka bashi ba sai ka taba naka ba Dage ayi haka kuma Ramatu
haba dai ka barshi kawai nayi niyane ai.
Wurin mai shago na tafi na bashi kudi ya turawa layinsa lokacin haka ake tura sakon kudi sai gashi ya
kirani yana fadin arradu Ramatu kinyi lafiya kun ketare kaidin baffa shima baffa yana fada gaba dayan ku
kunfi karfinsa ai.
Ya gwada sa,ansa akanku ya kasa cin maku tunma ke yace ke iblishiyace da zaki kai wani lokaci a
wajensa da kin kwance masa karfinsa.
Haka dai muka rabu dashi yana ta shirmensa na tare abin hawa zuwa gida saidai kuma me a gidan dai
badadi don wani tashin hankali na dawo na riska inda mama tayiwa matan jafar kaca kaca a ranan .
Wai suna gudunshi suna kyamarshi don haka mama tace sai subar gidan ita zatayi jinyar danta in da
rabo in yaji sauki su dawo mashi amma yanzu kan sai sun bar mata gidanta.
Tunda babu wace keda hankalin da zata kula dashi iyakarsu su dan shigo suyi shaaaa su fice babu mai
zama ta kula dashi a cikinsu.
Hakan ya farune da Asmau ta shigo dakin da yarta yana dan cikin hankalinsa ya mikawa yar hannu da
tazo wajensa sai uwar taki bari yar taje.
Shi jafar din ya dubi matar nasa yana fadin inku kuna kyamana a haka har da yayana zaku hana su
rabeni Asmau ?
Kawu da mama na zaune lokacin da hakan ya faru mama tace sun ma isa sunce suna kyamar ka jafar ?
Yace aigata nan idan akwai wace ke yarda ko gadon nan ta taba haka nake fama idan baku kusa kona
kirasu basu zuwa su taimaka min komai zasuyi min a wullakace suke min shi suna gudun su dauki cuta a
jikina.
Wanan ya harzuka mama ta soma bala,i da tashin hankali har haka ya faru ita saiba sai ta fake da tayi
yaji ta kwasa ta nufi kaduna wai mama na yawan takura mata .
Ita Asmau bata tafi ba shine mama tace har ita din ta tafi duk mai zaginta ya zageta amma basu zama a
gidan.
Nima na kula da hakan a lokacin saidai sanin halinsu yasa ban dauki hakan wani abuba tunda haka
yake zaune da abinsa.
Na rasa yadda zanyi in aiwatar da maganin nan ga yaya j ina zance dasu na samu wanan abin ina part
din mu mama ta kira waya da inzo mu kula mata da Jafar zasu tafi wani waje ita da kawu.
Don a lokacin ita Saare tana school ita kuma Salima ta wuce bautan kasa saini da Nafisa ne a gidan
muka shiga part din nasa tsit don matan gidan da basa nan kwana biyu.
An dawo da Asmau mama tace taje ta huta kawai haka ba yana nufin zata raba mata aure da mijinta
bane bata dai son ganin su gidan a yanzune.
Lalai ankai hali dubu makura mace mai hakkuri ta iya yanke wanan hukunci don haka kawu yace suje
din kamar yadda tace har ta huce.
Anty Nafisa tashi mu shiga dakin yaya ayi komai a gabanki don Allah akwai taimakon da nake son yi ban
samu daman hakan ba a gidan nan .
Kallona tayi a tsorace tana fadin me zakiyi Ramaah nace zo muje anty Allah ya gani taimako zamuyi da
zuciya daya.
Dakin muka shiga da sallama ya kwance gwanin ban tausayi muka gaidashi ya amsa muna da kai dakin
ya danyi shiru gabana sai faduwa yake ina kuma kare mai kallo nace yaya don Allah ka fahinceni.
Akwai wani magani da aka bamu a gida nake son in jaraba mu gani amma ina tsoron hakan bansan me
zan fada ba yasa yanzu na sameka ga anty Nafisa don Allah yaya ka daure ka dinga sha koda ban kusa
anty Nafisa zata baka zamu fadawa iya kuma.
Maimakon ya amsa min sai hawayene ke zuba a idonshi na fito da kullin maganin muka zuba mai a
kunnu bai ki ba yasha muka kara kwantar dashi.
Mun jima a wajen zaune sai sha biyu su mama suka dawo gidan kawu ya sauketa ta samemu a dakin
wajensa zaune bamuyi barci ba.
Mu muka taimaka mata tayi mashi komai a ranan daman dana samu kuma weekend ne don haka
yasha maganin kusan na kwana uku ina bashi a boye.
Mu gyara dakin mama tayi mai wanka kafin ta fito na kwashe zanin gadon na shimfida wani na feshe
dakin da kamshi.
Zakiga ya sauke ajiyan zuciya idan ya zauna na hada mai kunu ina bashi mama tashigo tana saka min
albarka tare da fatan alheri a gareni.
Take fadin Rahama indai ba karya nakeyi ba kamar jikin jafar yana saba (salinta ) alaman hakan kuma
meye ?
Mama duk ta rude daka ganta bata cikin hankalinta nace mama kila hakan wani sallon ciwon ya canza
kuma ?
Naji sauki sosai ya bamu amsa da fadan hakan yana gyara kwanciyarsa ya habu ya shigo dakin nayi
saurin gaidashi yana tambaya ina Nafisa mama ke fadin yanzu take nan tace iya tace tayi mata shayi .
Ya karasa bakin gadon yana fadib J ya karfin jikin naka ya bude ido ya dubi dan uwan yayi dan
murmushi kadan hakan yasa ya Habu din yakai zaune.
Mama bari naje na gaidasu iya na fada ina fita tace kima huta tunda ga Habu ai kafin kawun ku yazo ya
kama min nima na dan jena huta.
Bayan fitana yake fadin yarinyar nan habu yace wa Ramaah ya gyada kai alaman eeh saiya lumshe ido
yace me tayi yaya yace kirki don bai dogon magana.
Sai Habu din ya danyi murmushi mama daga gefe tace meyace wai Rahama yake fadin tana da kirki
aini har tausayi ta koma bani yarinyar arzikice sosai wallahi.
Barci nayi sosai don kwana mukeyi gadinsa a gidan daya motsa dayan mu dake falke zai tambayeshi
me yake so ?
Hakan yasa har zuwa school na dan dauke don maganin da muke gwadawa wanda dagani sai anty
Nafisa dashi muka sani haka kuma yana sha sosai idan mun bashi din kuma yana shan wanda su mama
keyi mashi.
Hadari aka hada sosai a garin hakan yasa mama cikin damuwa ga yaya Habu ya tafi kaduna tare da
kawu gashi ance kada a dage rana ga karbo maganin fita nayi kamar zan shiga cikin gida na fice bakin get
ban samu abin hawa ba haka nayi ta sauri saida na kusa isa na samu mai keke ya karasa dani gidan
mutumin.
Na karbo haka na biyo ruwa da iska na iso tsamo tsamo da maganin gidan nakaiwa mama mamaki tayi
sosai ta shiga yi min fada yadda na iya fita a cikin hadarin nan.
Nace mama gani nayi lokaci zai wuce bai sha ba kuma ga ruwan nan ba a san lokacin da zai tsagaita ba.
Maza kije ki kwabe tufafin nan kada sanyi ya kara kamaki mura ya sauka maki kin daiyi kasada wallahi
bin hanya haka a cikin ruwan nan .
Dakin ta shiga tana fada yake tambayan meye mama din tace yar nan Rahama ashe ta fita a cikin ruwan
nan ta tafi karbo maganin nan dana damu akansa.
Baiyi magana ba sai zuwa can yace mama yaran nan suna matukar kokari sosai wallahi a raye suke
kwana gidan nan.
Aini ban iya cewa komai a yanzu saboda ko yaran nan su saratu ba zasuyi min wanan dawainiya haka
ba wallahi.
Bayan kamar kwana biyu jikin nasa yayi sauki sosai a lokacin ya dan harda tafiya ba tare da an rikeshi
haka kuma kumburin kafanshi ya fara sucewa kafan yana fadawa don yayi kamar turmi a lokacin ba
dadin gani sai walkiya da yakeyi kamar zai fashe.
A takaice bawan Allah nan yasha wuya fiye da tsamani sai zantuka akeyi marasa dadi game da ciwon
nashi kowa da abinda yake fada.
Shi kanshi mijin yar uwata duk ya fita cikin hayacinsa saboda jinyar