Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
dauko mai sabon jallabiyansa dake wardrobe wanda bai taba amfani
dashi ba ciwo ya kasheshi don a baya yana sayo kayan shan iska ya aje a gida.
Wani baki mai addon zaiba maikyaun desine na dauko mashi ya saka muka fito falo na gabatar mashi
da abinci .
Yadda yake nuna farin cikinshi a fuska yasa nasan yana cikin nishadi a lokacin har ya gama ina gefe ina
taimaka mashi a wajen ci bayan mun idarne na mike na kwashe kayan zuwa kitchen nasa biba ta wanke.
Falon na dawo na kamashi muka koma saman dogon kujera mai cin mutum ukku muka zauna wayansa
ya shiga kara ya dauka hakan ya ban daman mikewa daga wajen na shiga shawagi a cikin falon zuwa
kitchen din mu.
Duk wayan da yakeyi idonsa yana kaina har ya gama lokacin ina tsaye a kitchen din Biba tana min hiran
wasu makwabtansu da sukai fada ina dariya.
Jin shirunsa yasa na fito falon na sameshi na zauna a kusa dashi ina fadin naji kana fada yace bari
Rahama bansan me mutane suka dauki hakki ba a yanzu Rahama ?
Mutane basu tsoron Allah ko kadan kowa dai kokari yake ya gina kansa koda haramun ne a duniyan nan
yanzu wai suna fada min kayan dana tura kafin ciwin nan ya kaini kwamce an sace rabi.
Ba dole a sace ba kayan da in nakai abina bai wuce inyi wata biyu zuwa ukku sun samu shiga ba amma
tunda vani wajen kowa yayi abinda yaga dama dasu.
Shi Habu na rasa irin zuciyarsa ya hau ya zauna yana fushi wai don mama da Nusaiba sun jefa masa
zargi a dukiyana yau idan habu ko yazid basu tsaya min ba Rahama wa zai tsaya min a garin nan ?
Na dauka koda ace ban raye su masu tsayawand suga sun kare min hakkin iyslina da nasu gaba daya
amma sai abubuwa akeyi barkatai wanda hanlali bai tunanensa.
Na kansa a raina wanan ciwon wani jerabawan rayuwace Allah ya aiko min dashi da zan fahinci yadda
lamarin duniya ya koma a yanzu.
Don mutane ko da ranka ashe sai kana da amfani ake rayuwan komai dakai sai kana cikakken mutum
duniya har dan uwanka zasu dama dakai Rahama ?
Sosai nagodewa Allah da dabaran da Allah ya ban nayiwa kaina haka kema haduwata dake Allah kadai
na barwa sanin dalilin hakan a tsakanin mu dake.
Don ta dalilin aurenki Rahama har Allah ya ban dabaran boye kudina a gidan nan ba tare da nakai banki
ba har ke dake zsune gidan ma bakin san da hakan ba don da suna account dina yau Rahama da kudin
nan dana aje anan suma an batar dasu kamar yadda wa yan nan suka salwanta min mun koma banda
komai.
A lokacin kallon mamaki nake mashi yayi murmushi ya gyara zama yana fadin wallahi haka kawai nasa
aka kawo min kudin nan nan gida kamar wani abu da niyar idan na dawo daga tafiyan da nayi basai na
tsaya shiga bank ba wajen miliyan ,,,,,,
Sallaman Yazid daya shigo lokacin ya katseshi duk muka bishi da kallo lokaci guda don yaja ya tsaya
daga kofan shigowa falon yana tafa hannayensa.
Kafin ya soma fadin wai don Allah yayane nan nake gani haka ko dai wani yaya J din kika sauya munane
yau din ?
Tsuki Jafar yaja yana kawar da kai ya karaso yana fadin to ina mamanka dake can tana fada a kanka ko
ita taga wanan sauyi yau haka sai tayi mamaki zata daina fadan da takeyi dakai tun jiya.
Na fada mata dama kai keda jikinka da iyalinka ta barka kayi abinda ranka yake so amma tace ba haka
ba tunda bakaji sauki ba don me zaka dawo nan ka tare kuma ?
Bayan kasan har yanzu magani kake sha ni itace ma da fitinan ta ta tayar dani tunda safe yau wai na
kawo maka maganin nan kasha ya miko mai wani leda dake hannusa fari.
Yace ba Rahama ita mama fadan me takeyi a kaina ko na zama yarone yau kuma da za ace sai yadda
akayi danine wai magani ko a nan nake ba zan sha maganin bane ?
Na rasa meyasa take haka wai akaina wallahi to dai kan ka shirya don wallahi fada ta kwanayi ba don
iya ba jiya data biyoka da daren nan iyace ta hanata zuwa sai abin ya ba jafar din dariya haka yasa ya dan
sake murmushi a fuskanshi kadan.
Don sheri sai ya juyo gareni yana fasin wai don Allah amarya nima ba zaki samo min wata yar filo ba
kuwa in kara don dai wanan abin akwai ban mamaki gaskiya ?
Ki duba mutumin ki don Allah yau shine a haka yayi clean wallahi yayi kyau kamar bashi ba jiya jiya nan
da daren nan fa yazo gidan nan amma dubashi don Allah ?
Idan ka gama ka kira min emanual zanyi magana dashi a gabanka yace abinne Allah da ban mamaki
kwarai da gaske ya J baka yadda kayi wani fresh ba ?
Kaji mena fada ai yake fadawa kanin nasa shima yazid din ya dubi wayanshi yana fadin shi nake kokarin
kira ai yanzu hakan .
Mutumin ya dauka suka fara gaisawa da yazid yake fada mai mr Jafar yake son magana dashi yana
fadan haka ya mikowa yayan nasa wayan ya soma magana na mike ina fadin ya yazid a kawo breakfast
ne ?
Wallahi madam dina ta cika min ciki kafin in fito amma zan dan taba kadan saboda kwadayi ya fada
yana dariya nidai na shige na kwaso mai kayan abincin da dan uwan nasa ya karya dasu din na aje mashi
a gabanshi.
Duk da ina aiki ban tsaya ba lokacin amma ina cankar maganan da Jafar din keyi da mutumin akan
kudine yake tambayanshi ba,asin su.
Zance na dashi tun dawowana jiya nake nazari a raina wanda na gama kai karshen tunanena wanda
abinda zuciyana ya ban shine dukiyan sun samu matsala saboda dalilin kwanciya rashin lafiyan nan nasa.
Indai za a rasa dukiya Allah ya bar muna shi Alhamdullahi rayuwa ya nema dama sai anema din daga
baya in Allah ya nufa da sauran rabon hakan.
Kirana da yaya din keyi yasa na fito daga daki tare da amsawa cikin dan muryana din nazo gareshi yake
fadin don Allah dauko min wani file na nan a dakina a drower kasa ki kawo min .
Na nufi dakin na duba nagashi na kawo mai ya karba yana budewa na juya da niyar barin wajen naji
sallama ko ban juyo ba nasan muryan yaya habune a lokacin ya shigo gidan shima.
Hakan yasa na dakata don mu gaisa na gaidashi daga inda nake ya amsa min kan kadaram kadaham
nima na juya zuwa daki ba tare dana tambayeshi iyalinsa ba.
Ina shiga dakin naji ya sun soma magana tun baniin me suke fada har na gane musayan magana
sukewa junan su karshe dai na barjin muryan yan uwan saina jafar din dake magana a cikin fada da bacin
rai yana nuna sakacin da sukayi aiba shi kadai hakan ya shafa ba dukkansune.
Ni dai naji yana fadi a karshe cewa yasan matakin da zai dauka idan ma na waje sun cuceshi har dasu
baiyi tsamanin hakan ba ai.
Nan na soma jin muryan ya habu yana fasin J ya kake son nayi kana sin kaga laifinane a banza cikin
zancen nan.
Kafi kowa sanin bakin jinin da nayi a zancen nan gida ba a barni ba J kasani balle waje mutane yanzu
basuwa Allah .
Ni dai tun ina saurarensu har barci ya daukeni bansan fitansu daga gidan ba barci na samu sosai nayi a
lokacin yana zaune falo bai tayar dani ba don yasan harda laluran cikin dake jikina a cikin barcin.
Ban falka ba sai wajajen karfe daya na falka nayi mamaki yadda na samu barci mai dadi haka a lokacin
na fito falon na sameshi a inda na barshi yana duban takardun dana dauko masa dazun din.
Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana fadin kin tashi na amsa da eeh ina zama nake fadin sun tafi
ashe yace tun dazun suka tafi me zasu fada min tunda suyi shirme .
Zaune nakai a hankali ina fadin na zata ai azahar tayi yace da sauran time kin fara zuwa awo ne ya jefo
min tambaya ?
Hakan yasa nima nake mai kallon mamaki yaushe zan fara zuwa awo bai sani ba duk da dai bangarin ai
a lokacin don haka nayi shiru ban bashi amsa ba.
Saida aka dan dauki dan lokaci ya dago yana fadin bakiji mena fada ba na dan rausaya ina kawar da
fuska nace ni banjin komai ai yanzu.
Ko baki jin komai baki zuwa asibiti a duba lafiyan ki dana baby din a gani dole ki fara zuwa awo zanwa
yaya Ai magana tazo kuje tare ko kuma maman tudu .
Ni banje na gaidasu ba sai a kirasu suzo kaini asibiti kamar banda lafiya nidai ka barsu karka kira kowa
don Allah na fada a karshe.
To me kike nufi ba zaki ba ke nan ko dole kije asibiti don lafiyan ku idan can gida zaki biya ki dauku
mama din fine amma asatin nan ki je a dubaki please.
Shiru nayi na kasa cewa kkmai saidai nasan tunda ya fada sai anyi haka din don idan ban manta ba sun
taba fadan zuwa awo da Asmau a gabana kafin na aureshi da shigan cikin dan nan nata data yaye din
wanda aka haifa bayan an aureni .
Yana tafe a gajiye ya fito filin kwalo rigansa na kwalo yana rataye a kafadansa saidai yana sharo
kwanan gidansu ya hango dandazon yaran unguwa a kofan gidansu.
Sauri ya kara ya iso kofan gidan fada ya fara da yaran yana korasu duk daya fahinci fadan da akeyi a
cikin gidan nasu da yanzu ya zama kamar gidan haya suka zo kallo.
Gidan ya shiga kanninsa mata ya fara hangowa a rakube cikin damuwa wucewa yayi zuwa bakin
randan ruwan mahaifiyarsu yana diban ruwa a cikin takaici a fili kuma halin ko in kula yaron ya nuna ga
abindake faruwa gidan tsakanin iyayyen nasa .
A yadda ya fahinta da kishiyar maman tasu da mahaifinsune suka tararwa uwar nasu ake wanan
masifan da zage zage a yanzu inda sabo ya saba da ganin hakan dashi da yan uwansa din don zaman
lafiya ya kaurace a gidan nasu tun shigowan wanan matar gidansu.
Karan dukan da yaji mahaifinsu nakaiwa mahaifiyarsu tana kakarin neman taimako ga yan uwansa na
ihun ceto yasa ya yarda mudan ruwan kasa ya nufi wajensu da sauri yana fadin .
Baba a,a baba ya haka kuma ka barsu suyi fadansu mana tunda bada kai akeyi ba zaka kamata da duka
kuma haka a gaban mu.
Uban ya nuna baima san yanayi ba shima haka baisan lokacin daya kai hannu yana banbare hannun
mahaifin nasu ba a jikin mahaifiyarsu.
Aminu zaka shigarwa uwarkane kome amayar baban nasu ta fada bai kulata ba sai kokarin kwatar
mahaifiyar da yakeyi rai bace ganin mahaifin nasu kasheta yake son yi yasa ya nuna mashi karfi ya kwaci
uwar yana dagota daga kasa inda uban ya shake ta.
Baiyi aune ba yaji an kwala mashi abu a kai hakan baisa ya sake mahaifiyar ba sai juyawa da yayi ya
rike tabaryan dake hannun amaryan mahaifin nasu da hannunsa daya yana fadin kika dukeni ?
Dan iska zaka ramane kai ga mai karfi kazo ka tureni ka ceci uwarka ko ta kasheka ta kashe banza da
iska mai halin uwarsa kawai.
Bai kulasu ba yaja uwarsa dake rusa kukan takaici zuwa dakinta rai bace yana fitowa don bai tsaya a
dakin ba suka hade da uban nasa ya soma fadin.
Kai san iska yau din nan saika barmin gidana ni zaka nunawa ka kawo karfi a yanzy har zaka tureni don
kana dan iska ka zabi uwarka dani ko ?
To ka fito dakai da uwar naka kubar min gidana bai kula uban ba ya nufi wajen ruwan da yake diba din
ransa a bace nan ma uban bai kyaleshi ba yabishi yana fadin .
Nafika iskanci dan banza kawai kai har kana ganin kai wata tsiyace ko a yanzu ni zaka daga kan uwarka
dan banza kawai.
Shi dai yaron bai kula uban ba ganin hakan ran iliyan ya baci ya nufi inda suke aje icce ya rarumo ya
nufoshi nan yan uwansa mata suka hau ihu suna fadin ya gudu ga baba nan da icce tafe hankali tashe .
Bai gudu din ba ya nufi bayi ai kuwa yakai mai duka da iccen zafin hakan yasa dan dakatawa yana
kallon uban dake fadin.
Nace ka fice min daga gida mara mutunci wallahi baka zama gidan nan damu dan iska daga kai har
uwarku ku barmin gidana gayan tsiya kawai.
Uwar ta leko ta hau bakin ta har yaron ya shiga bayi sai kuma ya fito ya nufi hanyar waje ya fice daga
gidan cikin bacin rai.
Hausawa sunce kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/23, 10:34 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nasa a raina ranan zai koma wancan gidan donshi ma banyi motsin girkin dare ba don nasan a ka,ida dai
kwana bibiyu mukeyi ga girki tun muna mu ukku.
Balle yanzu da mu biyune tare dashi muna falo zaune tun bayan fitansu yaya Ai da sukazo min sannu
da dawowa a cewarsu.
Muna zaune maigadi yayi sallama ya tsaya daga kofa yana gaidamu bayan ya amsa yake fadin akwai
wani yaro a waje tace daga zamfara yake a fadama sunansa Aminu ?
Kallon sa nayi naga ya daure fuska yana fadin to me yazo yi nan da baije can gida ba wajen su mama
zaizo nan kallonsa nayi nace ko dan yaya Barakhane ?
Yace shine mana don me zai biyuni nan kuma yaushema yazo garin na dubi maigadi dake tsaye nace
dashi ce ya shigo malam don malam nake kiran maigadin dashi.
Ya juya da sauri ya fice fada yaya keyi yana fadin don me zaizo nan barshi yazo najima meya kawoshi
ni ban daukan wanan iskancin a yanzu gaskiya.
Haba dai ba girmaka bane yaya yaron nan ai ya gansu ya nufo nan inda kake don Allah dai kayi hakkuri
kaji abinda yazo yi din.
Yaron ya shigo tun a kofa ya zube yana fadin kawu ina wuni ya amsa mashi fuska daure yaron cikin
in,inniya yasoma fadin dama naje can gidane na samu baka nan su mama ma sun fita akace sai mama
salima ita kuma tana barci.
To sai akace me ita Asmau bata nan ne ya tambayeshi naga yayi kasa da kai ganin na mike tsaye
yasashi fadin mummy ina wuni na amsa da Aminu anzo lafiya yaya su anty ?
Suna lafiya kalau ya fada kafin mu gama gaisawa ya sake jefo mashi tambaya da mekazo yi zaria ko
baka fara school din bane har yanzu.
Nayi jam kawu basu fara dauka bane ya fada na katsesu da fadin kaci abinci kuwa Aminu yace yanzu na
iso mummy naje can ban samesu ba nazo nan.
To shigo mana kaja ka tsaya can a kofa kamar wani bako bari na kawo ma abinci kaci ka huta sai ku
tatauna ko na nufi kitchen din mu abinci na hado mashi mai lafiya yaji ganye a sama da kayan hadi.
Inda yake zaunse nakai mashi ya karba yana godiya na juya na kawo mai ruwan sha ya soma jan plate
din zuwa gabanshi na juya zuwa cikin dakina .
Na dan jima a dakin na fito na samu yaya na fadin to yanzu yaya kake son ayi ke nan shi ubanka ya
koreka gidansa shine ka nufomu nan ?
Bayan haka kai baka da hankaline ko kasheta yayi ina ruwanka da saka masu hannu a cikon fadan da
sukeyi dashi ?
Mahaifinkane fa Aminu baka da hankaline koka fara shaye shayene yaya yi hakkuri don Allah kasan uwa
ba yadda za ayi yana tsaye yana kallon zai kashe masu mahaifiya ya kyalesu ?
Nice na tsoma masu baki a zancensu bayan na gama sauraren maganganunsu da dansa din abindana
fada yasa ya dan kalloni yana fadin.
Haba Rahama baida hankaline da zai ture ubansa ubansane fa don kawai yaga suna rigima zai saka baki
a cikin zancensu hakan ya nemi albarkansa ke nan ?
Zaune nakai cikin sanyin jiki ina fadin yaya ceton mahaifiyarsa kuma yana iya saka yayi komai a lokacin
rabu da irin gidan nan da ake irin haka a gabab yaya abin yakan saka yayan shiga cikin zancen wani
lokaci.
Don babu mahalunkin da zai zauna ana dukan uwarshi bai dauki mataki akai ba kai ya girgiza yana fadin
Rahama na gane da sauraki kema kina da kuruciya a tare dake .
Har yayi shiru ya dago yana fadin meyasa su yan uwansa mata basu sa hannu a rikicin ba sai shi zaisa
hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa.
Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje ya huta bari nasa
maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi.
Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya zauna mana da iya
nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ?
Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina sauraren amsan shi baice
komai ba har lokacin.
Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice ba tare da nace
komai ba.
Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan mu akwai dakuna
hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan amfani da guda don adana
abubuwansa.