Chapter 37 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   37 / 101

108K to 111K   out of 302.2K words

ko matata a
cikin zancen nan sai kin kwana a gadon asibiti ranan .

Idan kuma kin dauka karyane ko wasa ki gwada ko a yanzu kigani abinda zai faru dake a wajen nan .

Yaja wani guntun tsaki tare da jefa mata wani kallo ya juya zuwa ciki baiko tsaya ya fahinci tashin
hankalin data shiga ba a lokacin.

Don da farko ba aure suke zargi ba kamar nemanta sukaji ance yanayi shine ta kasa hakkura don ranta
daya gama baci a lokacin.

Sai gashi zance ya banbanta Habu ya fito yana fadin wani magana na daban da bata taba tunanen
faruwan hakan ba wai jafar ne yayi aure ?

Auren ma auren yarinyar data gama sanin sirinsu gaba da bayansu waiko da gaske habu ke wanan
zance ko kunuwantane basuji meyace kan zancen ba ?
Ta juya a fusace zuwa cikin part dinsu hankali tashe Asmau dake tsaye tana mata magana akan su tsaya
su bincika gyale ta dauko da waya ta nufi hanyar fita daga part din.

Wai ina zaki don Allah nusaiba ki natsu mana abi komai a sannu habu yana iya fada maki hakan don
ranki ya baci kawai tunda ba shiri tsakanin mu dashi.

Ko juyowa ta kalli Asmaun dake magana batayi ba ta fice gidan kai tsaye ta hau abin hawa sai tudun
wanda family house ta samu mama da abin duniya ya isa lokacin.

Da kyat ta daure suka gaisa da wasu daga gidan ta fada dakin mama Saare ce a waje tana wanke
kwanaku tana ganinta ta mike tana fadin daga ina haka saiba ?

Mama na ciki ta iya fada tana nan Saare din ta fada ta fada dakin ba gaisuwa sai kukan data fashewa
mama dashi wanda ya jawo hankalin mutanen gidan.

Suka nufo part din mama din mama dai tana zaune ta zuba mata ido gashi sai tambaya meya faru akeyi
duk sunyi shiru sai Saarece ta iya fadin.

Yaya jafar ne yayi aure ya auri Rahama kanwar matar yaya habu lokaci guda suke fadin Rahama dai
Rahama aure yaushe hakan ya faru ?

Haba yar nan akan wanan kika shigo da kuka haka me yaya zata iya yi akan hakan tunda anriga da an
daura aure yanzu meya rage kuma bayan hakkuri inna ke fadin hakan.

To ba a aure ita tayi ina mijin kawarta ta aura amma ai ita wacan batayi tashin hankalin nan ba da tayi
hakkuri gashi an zauna lafiya .

Duk wanda zaizo sai yayi kwatance a kanta da cewa hakkuri akeyi ai itama ai wata ta sama kuma tayi
hakkuri haka ta mike bata iya fadan komai ba ta fice kuma direct ta nufi wajen shiga motan zuwa
kaduna.

Baifi yan mintuna da hakan ba yaya Habu ya dora yadda akai daurin auren a rugga ya rubuta Jafar and
Rahama Allah ya bada zaman lafiya abin median nan danan aka san da zancen auren aka fara yadawa
masu dorawa suna dorawa a saman wayansu.

Ganin hakan Jafar ya kira habu yake tambaya yake cewa dashi yanzu kan ai kowa ya gama sanin
abinda ke nan ya kwashe komai ya fada mai saidai ya boye mashi zancen da mama tayi game dashi don
gudun bacin ransa.




ZAINAB IDRIS MAKAWAMURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



3️⃣9️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Kwance nake har lokacin cikin gajiyan da ba zance ga dalilinsa ba ina dai dangata hakan da fitan da
mukayi da anty salma yasa jikina weak a lokacin.

Nayi mamaki yadda wanan ya narka kudi aka hada mashi wanan lefen a cikin kwana biyu rak kayane
dai aka zuba wanda zaki dauka cewa macen ba zata taba neman wani abu mai suna sutura ba ko kayan
kwaliya.

Gaskiya maishi ba karamin kokari yayi ba hakan ko banjitane ko kuma so an dai narka nairori a wajen
nan gaskiya irin tunanen da nakeyi ke nan a zuciyana naji an turo kofan dakina.

Muryan anty salma danafi zaton itace don ba kasafai yan aikinta ke shiga dakunan kwanan mu ba saida
wani dalili mai karfi.

Wai kwance kike har yanzu na yunkura ina mika nake fadin haka kawai naji duk jikina ya mutu nasan
gajiyace na mike ina gaida ita.
Mama ta bugo waya muje yanzun nan tana neman mu dani dake jin abinda ta fada yasa na kallota da
sauri ina fasin mama kuma ?

Lafiya dai ko anty Salma tace ai kinsan halin mama kilama ba wani zance bane tana dai son ta gamune
kawai tace mu taso.

Murmushi nayi don ko yana yuyuwa haka din ne sai muje tace ayya yaran nan ban ganku ba kwana
biyu kuna cikin gaein nan kun shareni ko ku nemeni ?

Hakan yasa na tashi na shirya da sauri don na fahinci a shirye anty Salman ita take a lokacin ba wani
dogon shiri nayi ba wasu dogon riga da ya tsaya iya gwiwa tare da wandonshi sai gyalen dana rufa iya
wuyana tunda daga mota sai mu shige cikin gidan mama din don haka ba saina tsaya wani bata lokaci ba.

Karshema zata iya sakani wani aiki a hakan yasa ban tsaya wani dogon gyara ba kodana fito anty na
zaune tana waya tana ganina ta mike tana fadin muje ko tana mike yaranta.

Na dan marairai ina fafin kin rufo dakinkine anty wayata naso dauka a nan na barta tun jiya sai naji tace
gashi na saka maki a jakata muje saina baki a can din.

Ba wani dogon tafiya bane don basu da nisa sosai da juna sai gamu gidan daddy din tun a waje na
fahinci daddy yana gidan a lokacin.

Yan aiki keta kara kaina a tsakar gudan duk da yanzu gidan ba yawa sosai ko masu aikin su ukune
yanzu ba kamar lokacin da mukai tamu rayuwan dasu ba da muka cika masu gida.

Mama fa ta tambaya tsohuwar tace tana gun Alh suna nan falonsa zaune hakan yasa muka nufi can
naso togewa iya ita ta shiga sai ta juyo tana fadin muje mana kin tsaya kuma kai wanan bakar
bafulatanan dai ?

Murmushi nayi don sanin sun rike wanan wasan ta fulani da barebari a tsakanin mu ko yaushe kuma
har daddy suna tsokalan mu dashi.

Daga mama har daddy din suna waya a lokacin muka shigo abinda kunnena yaji mama na fadi shine ai
gasu mun kirasu daddy zaiyi magana dasu daga baya sai inkirani kiji meke nan.

Ta kashe wayan ta dago kai muka fara gaisawa ranan fuskansu ba wasa a cikinsa don ko dan zolayan
nan babu sai daddy daya mikawa dan salma hannu da yazo yaron ya leke a jikina.

Mama ke fadin karka kama gaye ka sake reshe kwana biyu ba zaka ganta gidan kuba dan nema kawai
salma ta shafo kan yaron tana fadin ai tare zasu tafi zaria da anty salma ko ?

Akayi dariya muka zauna dai a cikin harshensu suke magana wanda duk zaman mu banda gaisuwa da
dan wasu abu da muka rike har yanzu bamu jin yaren nasu sosai amma muna fahintar me suke fada da
kanuri din.

Don naji mama na fadin ban sani ba tace a,a har yanzu dai bansan komai ba amma sai ban kawo a
kaina suke magana ba.
Daddy ne ya ambaci sunana da Rahama hutu ya kare ko sai shirin komawa makaranta na dan dukar da
kai ina murmushi yace to Allah ya taimaka na amsa da amin kawai .

To Rahama nace yar uwarki tazo dakene nan don muyi maki magana irin ta iyayye yau a duniya dai kin
sani ko Abdullahi mahaifinku yana raye ni Adamu ina iya yanke hukunci a kan ku ?

Zama na gyara don nasan maganar kila a kainane zancen komawata gidan su Yanda da anty salma tace
ba zan koma ba ke nan ta kawo gaban daddu din hakan yasa na amsa da baki da kai da alaman hakane.

Yace madallah ina son kiyi amfani da tarbiyanki da natsuwanki da iliminki haka kuma ki zamo musulma
mai ruguman kaddaran da duk ta samu bawa ta rayuwa walau mai kyau ko akasin hakan ?

Na sake jin kaina ya kulle min lokaci guda har na fara tunanen ko nayi rashin wanine a lokacin falon yai
shiru babu mai magana na dan lokaci.

Mama ta zuba min idanu daga inda take zaune hakama anty salma ke kallona cikin wani yanayi na
tausayi sai duk na kara tsunkewa lokaci guda.

Yayin da suka fahinci tun bansan meke faruwa ba yanayina ya sauya tun soma maganan daddy a kaina.

Yadda duk na fara fita hayyacina tunma basu fada min kome yake faruwa ba kaina dago cikin yanayi na
damuwa da alaman tambayan ku fada min kome yake faruwa mana.

Sai naji daddy yace kiyi hakkuri Rahama a matsayinki na musulma ya kamata ace kin yarda da kaddara
mai kyau ko akasinta.

Don haka ki kaddara hakan da zan fada maki kaddaran kine haka muma iyayyenki bamu isa mu sauya
maki kaddaran kiba Rahama ?

Kai na gyada a hankali haka kuma indai har kin yarda da mu iyayyenkine kinsan ba zamu cuta maki ba
to ina son ki kara daukan hakan da gatan iyayye akai maki aka daura maki aure ba tare da sanin ki ba.

Zubur nayi na mike dakyau zaune ina binsu da kallo ga anty salma kallona ya tsaya sai naga tana min
murmushi da a lokacin na fassarashi dana kiyayya a gareni.

Mama ta karba da fadin kakanku hardo ya daura maki aure kwana ukku da suka wuce da dan uwan
mijin Maria yar uwarki.

Ina fatan zaki dauki hakan a kaddaranki kin dai san ba za a hada kai damu a cuta maki ba Rahama ?

Don haka kamar yadda daddynku ya bukata ki zamo mai biyaya ga mijinki haka kawai da zakiyi shine
zaki nuna matsayin mu na iyayye a wajen ki yanzu.

Haka muma zamu san Abdullahi ya bar muna marayun Allah mun kuma runguma a bayansa .

A iya binken daddynku wanan yaron baida matsala asalima taimaka muna yayi a namu ganin da wani
yazo wanda ba a sanshi ba ba asan halinsa ba ya aureki daga baya azo ana samun matsala kuma?
Hakan yafi muna kwanciyar hankali dake har mu don ansanshi ansan koshi waye haka kuma ki zauna
gashin kanki yafi zamanki a haka hankalin mu kullum a tashe kanki.

Shi aure rahamane ga bawa alherisa yawa garesa don ba akanka kadai kaida kayi auren abin ke tsayawa
ba yakan shafi har wanda baka taba sani ba.

Allah ya taimaka hawaye sun zubo min don sune saukina a lokacin da ace ban samu sunzo min ba a
lokacin komai yana iya faruwa dani wajen.

Kinsan mu fulani da busashen zuciya toni a wajena wanan hawayen da suka zubo min sune saukina a
lokacin saidai duk da hakan saida faduwan gabana yakaini ga sulalewa kasa cikin kaduwa.

Salma da mama sukayo kaina da sauri suna kiran sunana da Rahama Rahama haba dai wanan abin ai
bakai har na daga hankali haka ba ke nan baki yarda da hukuncin mu da kakanki hardo akanki ba ke nan
Rahama ?

Mamace ke fadin hakan cikin kaduwa da halin data gani a ciki shiko daddy namijine yana zaune ya
harde kafa yana zuba murmushi kawai daga inda yake zaune yana magana a cikin yaren kanuri yake
fadin.

Su kamani zuwa daki ba komai bane kaduwane zan sake idan zuciyana ya samu nasuwa amma a kira
doctor zainab ta dubata.

Haka suka kamani zuwa dakin mama saman katafaren gadon mama din suka kwantar dani tare da
kunna min AC dakin daya kara sakarwa jikina yanayin zazzabi sai gashi na fara rawan dari a hakan doctor
din tashigo ta sameni kwance.

Allurai tayi min dama shine nasu tare da maganin da zansha indan watsake tace a barni in samu barci
idan na tashi komai zai tafi in sha Allahu.



ZARIA

Suna zaune gaba dayansu falon iya ga abin karyawa a aje amma sun kasa karyawa sai Salimace data
fito ta zauna ta dauki kofi tana tsiyaya ruwan zafi a ciki.

Iya ta nisa tana fadin tsiyaya min ruwan zafin nan yar nan kada hanjina ya nade ga banza banga abin
tsayawa tashin hankali wajen nan ba.

Don yarinyar na tafi gidansu kan mijinta ya kara aure za a zauna a daga hankali haka ?

Ita da aka aurota ba hakkuri taga yar uwarta tayi ba wani irin iya shegene basuyi ba a gidan nan da aka
kawota saida aka koma ba yan uwan uwargida hakkuri.

Ke dubu lamarinki yana daure min kai wallahi ni banga abin daga hankali ba wajen nan
Yaron nan aure ya kara ba wani mugun abu ya aikata a rayuwansa ba amma kin daga hankalinki haka
ba tunane ?

Iya ba haka bane ban damu da aurensa ba don shi yaga yana iyawa ni damuwata shine ya bada dukiyan
yan uwasa dake hannusa .

Ba zan zuba ido ina kallo yana facaka da dukiyan yan uwasa a saka mai ido

Iya yaran nan sun san da dukiyan su yana hannun Jafar yau ace kuma Jafar baida aiki sai aure aure yana
facali da dukiyan yan uwansa na kallo ?

Haba mama haba yaya jafar ba zaiyi hakan da kike tunane ba wallahi in ma wani ya zugaki wallahi ya
dauki alhakin shi don,,,,

Ke kinci gidan ku zan saba maki rai yanzun nan kul kika kara tareni idan ina maganan nan me kika sani
ke da shirmen banza ?

Salima ta hada shayinta ta fita daga falon zuwa waje bayan ta mikawa iya nata part din ya Habu ta nufa
ta samu ya fita tunda safe sai Maria data samu zaune ga Abba yana wasa a gefe ita kuma tayi tagumi
idonta yayi ja jajir alaman taci kuka har ya isheta a lokacin.

Haba dai Madam ba dai kuka kikayi haka akan wanan zance ba kada ki zama wata mara godiyan Allah
mana naga hakan farin cikinkine gaki ga yar uwarki a gida daya.

Yau dai kinsan ko waye yaya Jafar kinsan kuma tunda ya zabi hakan ya shiryawa duk wani barazanan da
za a tunkareshi dashi gidan nan.

Takai zaune da kofin shayinta a hannu tana fadin ni ina mamaki da kuka kasa gane waye yaya J ?

Ai ki zuba ido kawai kiyi kallo ina fada maki duk abinda sukayi a baya suna ganin sun gama dashi a
yanzu zasu girbi abinsu bawan Allah nan ya dade da bakin cikin wa,yan nan matan nashi a zuciyar shi
amma an kasa gane hakan.

Mezaisa kike fahintar yau da sune ya habu yaga yan uwansu yace yana so da gudu zasu bashi ya aura
don kiyayyan da suke maki suna bakin cikin kasan ,cewarki matar yaya Habu.

Nasani amma nidai a wajena hakan ba daidai bane Salima don ko rantsuwa nayi ban kaffara nice za ace
na hada wanan abin.

Ai ashe kinsan da hakan to me zaisa ki damu da abinda zasu fada a kanki damuwa ba naki bane don
inkin nuna hakan za a samu sa,an gaya maki maganan banza.

Amma idan anga kin dake ko za a fada ba yadda za a sake a fada maki cikin takaici ba don haka gara tun
wuri ki marawa yar uwarki baya Maria.
Sun dauki lokaci suna magana a tsakaninsu kafin ta mike zuwa part dinsu ta samu kawu ya shigo yana
fadin abinda yafi dai yanzu ya fito da dukiyan a kasa abawa kowa nasa kaso ai yanzu kowa acikinsu yanaa
iya rike nasa.

Kaiyya yaya nifa ban tunanen akwai wanan dukiyan a yanzu illa kawai ya kawo abinda ya saura a
hannusa a kiyasta a bawa kowa hakama wanan gidan.

Kaga idan anyi haka zanga inda zai saka yarinyar nan in tunanesa wanan part na yazid to tun yanzu ya
canza dabara nayi waya da Baraka ta taso tazo asan abinda za ayi dama mijinta ya matsa ta karbo dansu
ya fara juyawa tunda ya gama karatu ba aikin yi.

Hakan yana da kyau kwarai saidai nasan koshi nasa tunanen ke nan a yanzu wanan wajen na dan
uwansa zai saka yarinyar tunda ba wani ginan yayi da zai sakata ba can na daban.

Allah sarki idan kin hanashi saka mata a wajen dan uwansa haya kikeso ya fita ya kamawa matan nasa
Dubu ?

Duk yadda zaiyi shiya sani mama ai yasan baida matsuguni ya daukowa kanshi zancen aure kina gani iya
ko wanan filin daya kara yayi ginan wanan daya dauko kaduna ai cikin filin gidan ya diba ya kara yayi.

Iya sai a kyashi ya mamaye duk kason yan uwansa shi daya nan gaba su koma suna zargina nice na mara
masa baya da yayi masu hakan ?

Yanzu dai maganan gaskiya ke iya a bari ya kawo dukiyan a raba abawa kowa nasa idan yaso in zai
dauki hanyan wajen shi yazid kafin ya dawo sai ya dauka a dinga ba uwarsa kudin ina ganin haka zaifi
sauki tunda abin magadane .

Anya Dauda kuyi tunane kafin ku yanke wanan shawaran yaron nan shine tsaye da gidan nan da yan
uwansa yau don abin duniya zaku rufe ido kuyi mashi hakan ?

Iya ai ba tozarci bane nauyine za a sauke mashi kada daga baya abin yazo yafi haka rayuka su baci
tsakanin gara tun wuri ayi maganin abin zaifi.

Kit Salima da tayi recording din muryoyinsu ta mike zuwa daki bayan ta kashe wayan bata jira komai ba
ta bude ta turawa yayanta komai.

Sun kai wani lokaci a falon suna tatauna zancen kafin suyi sallama da juna ranan mama bata nemi yar
uwata ba saboda har ita wanan lamarin ya shafa.

Sai take ganin laifin duk natane da badon ita ba babu inda Jafar zai ganni ai zancen kawune da yace da
ita mudin fulani abin tsorone.

Zamu mallake mata yaya ta koma bata gane komai ba har gara wa yan nan matan na J ai damu bata
ganin habu komai da yake ciki ba a taba sani saboda boyon kurwa da yakewa mutune.

Wanan zance mama ta haushi ta zauna sosai donshi ta kara hawa zancen cewa a raba gado a

37 / 101