Chapter 40 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   40 / 101

117K to 120K   out of 302.2K words

waje
Allah dai ya gyara nace dake iya ta sake fada.

Matar kawu bata sake magana ba tayi shiru don dama itace mai dumi a falon kana jin muryanta yana
tashi tana bada labari.

Anty Asmau kikace yarinyar nan ce ya aura ni sai naga kamar ba ita bace wallahi wanan fa kanwar
matar Habun gidan nan dai yar doguwar nan ?

Ummm,humm bari ke dai safena wallahi itace ya narka kudi ta gyaru mana tunda ba abin kai sake bane
abin daga can sukaji muryan Saiba cikin tashin hankali tana fadin.
Wallahi bai isa ba yaya dama na fada maki akwai yaudara cikin zancen nan wai ki duba imaging gidane
fa ita kadai a ciki ya kama mata sannan ace wai mutum yayi hakkuri ?

Asmau ta dan dubi yar uwarta dake kusa da ita tana dan sakin murmushi don duk da zafin hakan da
takeji tafi jin zafin saiba a zuciyar ta don da alama ta manta duk itace sillan hakan a rayuwansu.

Abinda tayiwa rayuwansu na shigowa rayuwansu ta bata masu zama ita da mijinta da tun suna kanana
suke soyayya sai gata kwatsam ta rusa masu duk wani mafalki nata lokaci guda.

Wanan yasa bata kai Saiban jin zafin zancen auren ba da farko yadda Saiba ke cika baki yasa tana dan
shan jinita ga zancen amma yanzu da tayi arba da yadda yarinyar nan Rahama tashigo a tsatsaye yasa ta
ji wani dadi yana kume mata zuciyanta na muguntan kishi.

Don haka zata koma gefe daya tasha kallo duk da ba zata yarda a mayar da ita tatakan gida ba zata dan
turza itama ganin ba aimai da ita baya ba a gidan.

Wanan abin yaiwa Asmau dadi a zuciyata duk da dai kishin kowa nadashi amma ko hakan da Jafar yayi
ya nuna ita din ba kowa bace a yanzu kamar yadda yayi mata a baya yayi matukar mata dadi a zuciyarta.

Ganin saiba data fito daki fuuu ta nufi hanyar fita tasan part din mama zata nufa aiko basu rufe baki ba
wajen tafawa sukaji hayaniya ya kaure a gidan.

Mikewa tayi da kyat saboda tsohon cikin dake jikinta ta marawa part din iya baya Nusaiba ta samu
zaune gaban mama tana kwasan kuka tana fadin wallahi mama ba zan yarda ba.

Tunda duk kan mu a nan gidan ya ajemu da kowa don me zai dauki yarinyar nan ya kaita wani gida
wallahi Allah mama ban yarda saidai ya sakeni idan baisona ne ?

Shigowan Asmau da yar uwata yasa ta sasauta zancen tana fadin don ya nuna muna iyakar mu muba
kowa bane a yanzu zai muna haka ?

Ikon Allah iya data dauro alwala zatayi sallah take fadin hakan yanzu ke Nusaiba namijine don yayi
abinda yake gani daidai a gareshi zaki tsaya kina wanan bori haka ?

Iya don Allah kiyi sallah abinki an tabasune dole suyi magana iya tace ina tabawa wajen nan ina nan
kuke da safe kuna mashi dariya don uwarsa tace ba zata bashi wajen zama da yarinyar nan ba ?

Jin dirin motansu matar kawu yasa iya tayar da sallah don kada su shigo su bata mata lokaci bayan
wanda ta bata din a baya.

Sai gasu sun shigo da sabon labarin da suke bayarwa wanda ya tayar da hankalin duk wanda ke wajen
don Jafar yai masu bazata yau.

Asmau da taji zancen yana batun hautsana mata rayuwa tacewa yar uwarta suje don a gabansu komai
ya wakana.
Saiba sai sabon kuka data saka lokaci guda cikin tashin hankali ba wanda ya farga da fitanta don kowa
da abinda zuciyarshi keyi a lokacin .

Matar kawu dai iya ta rufe mata baki haka mama tana ji a ranan in Jafar baiyi hankali ba zata iya mashi
baki don saura kiris akai wajen yadda take jin yaudaran da yayi mata da yayanta yana ci mata zuciya
lokacin.

Wai ace yau Jafar ne yayi mata wanan tozarcin da bata taba tsamanin hakan gareshi ba duk cikinsu
Yazid ne mai rawan kai da kuma tauri amma Jafar shine salihin su.

Don haka wanan karyan da akace ance ya shimfida a gidan wanan yarinyar dole ya sayar da komai nasa
a yanzu yaba yan uwansa hakkinsu.

Kwandala ba zata daga mashi kafa daga ciki ko kudin bai kai miliyan goma ba zai san inda ya nemo aka
basu hakkinsu inyaso shi ya zauna haka din tunda shiya jawa kansa hakan .

Kamar Jafar ace mata ukku ina zai kai mata ukku da shekarun nan nasa sai taji duka matan nasa tana jin
haushin su a lokacin.

Ita saiba da tazo tana wani babatu ba zata yarda ba ta bari ta gani idan yaci dadin amarcib da yarinyar
tunda harsu abin zai shafa yanzu taga karyan iskancin kowa a gidan yanzu.

Itako maria tasan hanyar da zata fito mata ba tace ta iya kisisina ba daga ita har uwarsu suna ganin sun
kitsa yar uwarsu tazo aci arzikin su dasu to za a ci din ta gani .

Tasan dai gudu ya kare mai a yanzu tunda yarinyar nan ta tare gidanshi dole ya dawo garin yanzu taga
ta iyakar gudun da yakeyi din nasu yanzu.

Muryan matar kawuce dake fadin hjy Dubu ni zanje gida nabar kawun yara da tsaron gida tun dazun
yana gidan shi muka bari da zamu fito.

Mama dubun ta dago tana fadin hafsatu zaki komai in kinje kyaba yana labarin abinda ya faru ko sai ki
sanar dashi da safe ya sameni nan ina wajen iya.

Wai ina salima ta dauko maku ajiyan abin shan dana bata dazun ?

Wai Salima ai tunda muka dawo kaduna suna wancan gidan da aka kai amarya gaba dayansu basu
dawo nan ba anty Baraka ta fada .

Kaji wata ja,iran watau tasan komai tun safe kallon mu takeyi shine ta kyale mu ta kara jin abinda ake
fada to za a fasa fadane tunda ya kwamshe kudi shi kadai yana faca ka ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/11, 10:54 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



4️⃣2️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Anan muka kwana dasu salima dake tayi min sheri wai itace ango din zata wakilci yayanta ita da Nafisa
ko a cikin dare muna shirin kwanciya saida aka kara kawo naman gashi mai, mai da tsoka anyi mashi irin
gashin nan mai ruwa ruwa ga yaji da su kabeji da albasa an cakudashi mai yawan gaske da abinsha na
kwalaye.

Daga dakin da muke muna jin su hjy yabi suna guda ganin irin gadan da ake baje masu a cikin bajinta
don duk basu zaci hakan ba.

Daga falo ina jin hjy yabi na kwalawa anty salma kira tana fitowa tace yoo Salma kinga abin arziki haka
yaki karewa a gidan kanwarki ?
Ai nace munga wajen zama mukam kila sai angon ya dawo ya tasamu gaba ya maida mu gida irin
wanan gada haka aiba zamuso komawa gidaba mukan ana kawo muna wanan arziki haka.

Fadawa yarinyar nan ta kara zage damtse taci arziki tabar arziki a inda ta ganshi don wanan wajen
sakata da walawane ba irin na zubarwa ba.

Ta fita zancen wayan nan matasa nata ta kama mijinta duk macen da take gidanta ita kadai sai taso
saka kishi a kanta kan kishiya tasaka batama da wata kishiya a duniyan nan.

Yo mai zai dameki yar nan tunda ba unguwa daya kuke dasu ba iyaka kiyi hakkuri tare da matanshi kika
sameshi don haka kada ki yarda kiyi dakon kishinsu a zuciyarki ki wahala .

Idan yazo miji ya tafi sai an dawo sai kiga an zauna lafiya duk abinda zai masu ko zaiyi da wata a cikinsu
kada ki yarda wai ranki ya baci .

Don haka wasu mata suke wanan yasa ake wahalan aure a yanzu ka samu mutum da iyalinsa kace saika
rabasu da karfi da yaji.

Wanan yasa matan yanzu da yawa basu son kishiya don basu san ko da wace ka shigo masu ba munji
ta soma hauka kada ki yarda saboda da kishiya Allah ya konaki gobe kiyama ki barta ita tayi tayi duk
abinda zatayi ke dai rike Allah da Annabinsa makami a gareki.

Komai tsiya dai bata tasowa tazo nan sai ranan da kuka hadu in har wani abu ya haduku nuna mata
kawai ke baki da lokacin shirmensu.

Shiko miji da ance yau yana gidan ki ko baya gidan ki kyautatawa a tsakanun ku kada ki yarda kiyi
sanya wajen ganin farin cikin maigidan ki.

Sunyi maganganu masu inganci da in mutum nada hankali zai dauka don babu shege a cikin zancensu
da farko inda daga baya kuma suka koma barkwanci anty salma na zolayansu da ko a koro masu naman
ne ?

Washegari tunda naga suna shiri na shiga damuwa don sammako zasuyi har matan kaduna su hudu da
ummah ta hadomu dasu lokaci daya suka juya tare da tukwaicinsu na kawo amarya da anty su babba ta
mika masu daga ango.



SOUTH AFRICA



Shi kanshi ya kadu iya kaduwa da ganin irin riban daya samu a wanan harkan ta ma,adanai daya soma
tare da Maibei .

Da farko yaki shawaran nata kamar dole tayi mai kan wanan halakan bayan dogon bayanin yadda abin
zai kasace a tsakaninsu.
Maibei tasoshi da arziki a rayuwansu ta kawo mai boyayyen sana,a damu yan arewa bamu faye
daukanshi da muhinmanci ba a nan.

Sai gashi shiga farko da kayansu yayi yaga ya samu abinda lissafin kan mutum ba zai iya kwatantawa ba
wai duk a sunan riba.

Ranan daya kira Meirbe yana sanar da ita irin yadda kayan suka samu karbuwa cewa tayi dashi ai dama
na fada ma saidai ka zama boss ba zaka kara zama a karkashin wani ba idan har ka gane wanan sana,an.

Ta fita da ma,adaine akwai wuya akwai hadari a ciki saidai amfaninsa yafi ga mutum yayi mata godiya
suka kashe waya.

Bayan satine ya kirata kuma again bayan sun gaisa yake fada mata ya gama komai yana son ya dan
dawo Nageria saboda family dinshi.

Take fadin haba dai family ai donsu ake neman kudin nan sunsan kana wajen neman kudi me zaisa ka
damu ?

Kinsan ina da mama kuma ina da yan uwa meaibe haka kuma matana a ysnzu ukku nayi sabon aure
ina gab da tafiyan nan yanzu haka amaryan nawa ta tare a gidana ban gari.

What kai at your age kamarka ke da mata ukku gentle man haba haba ina zaka kai mata ukku a
rayuwan ka me kake so ga mata hakane ?

Dariya ya kwashe dashi tace wait woo are you kidding me in wasa kakeyi ka bari please ina aure dai
mutum ya samu mace daya is ok for him sai su haihu tare su dubi yaransu ?

You know iam muslim my religion accept this for me our prophet comand us to marry four wives if
posible for a man and there is special reward for doing that in islam .

If you can feed them give them a shelter and cloth them and all there needs katseshi tayi da fadin is
that all you can give a woman my friend stop telling me this ?

Wai har kana fadin kayi sabon aure for where my friend wace mace zata yarda ka aureta kana wani
duniyan ka barta a gida ?

Iam telling you wallahi ni angone nayi aure kafin na bar Nageria kalman wallahin da taji ya ambata da
suka san musulmin kwarai bai wasa dashi yasata fadin .

Eeee way are you serious my friend ya kara furta wallahi i marry a young fulani girl but she is schooling
now in A B U zaria ,,,,,,

Ta sake katseshi da fadin so you are serious friend who is dis lucky girl that charm you heart ?

Tayi sa,a data sameka a matsayin miji a rayuwanta duk da ka bata mata tsari don nasan ba zataso ta
zauna a cikin mata haka da yawa ba tana educated ?
Dariya yayi yana fadin mu a wajen mu musulmai wanan ba matsala bane don haka muka taso muka
gani ga iyayyen mu.

Sun dan jima suna hira kafin suyi sallama da juna akan zai kara kiranta idan tafiyan nasa zai yuyu a
lokacin kamar yadda yake so.

Bayan sun gama waya ya zauna yana tunanen zantutukan da sukayi da ita din haka dinne gaskiya akwai
tauyewa a cikin lamarin wani lokaci amma zai iya kokarinsa wajen ganin bai tauyewa kowa hakkinsa ba.

Yau da ace baida zarahin hakan ya kumayi hakan yasan akwai tauyewa sosai a cikin lamarin yadda zai
daukota ya jefa cikin matansa da kansu har yanzu basu bari ba balle a dauko wata a hadusu zama a waje
daya.

Matan dakowa nasa baida mutunci a idonsu kowa suna masa kallon bai isa ba har dai Saiba daya dauko
wace bai gama sanin halinta ba ta yaudareshi ta hanyar abokinsa.

Wai kuma yanzu itace mama take nunawa goyon baya don saboda Saratu kome shiya rasa abinda ya
rufewa mama ido har take masa wanan mumunan fahintar ayanzu.

A iya saninsa ya taso cikin yiwa mahaifansa biyayya tun mahaifinsu yana raye har zuwa kawu da suka
dauka mutum na uku mafi daraja a idanusu.

Amma yau sai gashi an wayi gari duk hakan na kokarin ya tafi a banza wajen mama tunda har take iya
zarginsa akan kudin da bai taka kara ya karye ba.

Ya dan murmusa ya gyara zama don tuno ko dai saboda Rahamane har kiyayyanta da mama ya
shafeshi haka amma a iya saninsa ai mama bata taba nuna bata kaunar yarinyar nan ba a gabansa.

Don ko dan zaman jinyasa da sukayi ya fahinci kamar akwai kyakyawan halaka sosai tsakanin yarinyar
da mama don yadda take yabonta a gabanshi yana daya daga cikin abinda ya kwadaita mashi yarinyar ta
kasance daya daga cikin iyalinsa don ita mama din data nuna hakan .

Sai gashi kuma abinda bai taba zato bane ko tsamani yake fitowa daga mama din yasan sun taso
mahaifiyarsu na matukar sonsu a rayuwansu.

Mama irin mahaifan nan ne da keda rayuwan da ran yaronsu ya baci gara nasu ya baci sau dubu a wuni.

Haka kuma akan danta zata iya yin komai yasan da wanan don haka dole akwai wani abinda ya faru da
baisan dashi ba game da mama din.

Koma meye tunda har ba laifi yayi ba kawai don ya auri Rahama zaisa mama ta nemi tozartashi haka a
idon duniya ?

Zaije gidan zai yi kokarin ganin ba a kai ga samun matsala ba tsakanin shi da mama din ko yan uwan
nasa in sha Allahu yasan wajen matsala gudane sai yayi da gaske akan matanshi don ko bai samu
matsala da Asmau ba dolene zai samu da Nusaiba.
Sau daya ya daga wayanta kafin ya baro Nageria irin ashar din data dinga mai tace zatayi a gabanshi
yasan ba zai lamunci hakan ba gaskiya.

Koma meye yana rokon Allah ubangiji ya kawo mai sauki akan komai ko wani bangare magana dayace
a yanzu itace dole ya jajirce ya kara zama namijin gaske ako wani fanni.

Yajima zaune yana zancen zuci har tsawon wani lokaci kafin ya mike zuwa ciki don ya watsa ruwa a
jikinshi yana son fita da yamman zuwa wani waje.

ZARIA

Tun bayan tafiyan su anty salma gidan yai shiru duk da Nafisa da Salma suna gidan amma suna daki suna
barci kasa kwanciya nayi na fito na gyara ko ina na gidan sai kusan azahar suka tashi banga laifinsu ba
tunda akwai gajiya a lokacin koni ban samun sukuni idan ba naga waje da tsabta ba haka yasa na kasa
kwanciya na gyaro ko ina .

Wanka nayi tare da sallah na saka wani atamfa saiki rantse abayane rede made dinkin ya hadu sosai
gashi kayan sun matukar karban jikina.

Kalansu yayi min kyau sosai dama tasan hakan yasa komai ta zabo min abinda nafiso don sai incema
na zabo a cikin rashin sanin cewa nice mai kayan a lokacin.

Ban fito daga daki ba duk da ina jin muryoyinsu a falon sun kuna tv kuma suna hira saida nayi sallah
la,asar Nafisace ta lekoni taga ina sallah take fadin har la,asar yayi ashe muna nan zaune.

Bayan mun fitone na gabatar masu da dan dabaran da nayi muna don kada mu zauna da yunwa duk da
ban tsamanin hakan akwai abubuwan da zamu iya ci a lokacin.

Tunda ns fito naji salima tana fadin wai kan uban nan wai Ramaah ko dama course aka kaiki yine
Abuja ?

Nifa gaba daya wallahi kin sauya min sai nake kallonki kamar bake ba Allah tun jiya duk kin sauya min
ga sanin da nayi maki ga baki daya kin juye kin zamo min wata ta daban.

Dan murmushi nayi ina fadin kai anty salima wani irin sauyawa kuma don Allah ni din daice Rahaman
da kika sani a idonki.

Gaskiya akwai drama wallahi na yarda da ake fasin akwai wani rahama a cikin aure da sai wanda yayi
yake fahintar hakan.

Na duka na bude abincin dana aje a gabansu suka dago suna fadin meye wanan abincine na basu amsa.

Salima dake kishingide ta kalleni tana fadin yaushe kikai wanan aikin Ramaah nace kuna barci tace wai
yadda na gajin nan nima nasan nayi barci sosai wallahi.

Tun shekaran jiya da ya Habu ya kiramu wallahi bamu huta ba muna tsaye ai dole mutum ya gaji don
ma gidan anty Ai muke akwai yan mata a gidan da suka tayamu aikin .
Wallahi naji dadin kai aikin nan da akayi gidan anty Ai ai kinga yadda take farin ciki kuwa sai kiran
abokan arzikinta takeyi tana sheda masu abin arziki ya sameta.

Da kikace ta bar komai daya rage a wajenta idonta kamar zatayi kuka a lokacin tama rasa me zatace a
lokacin don mamaki Nafisa ke fadan hakan.

Nafisa anty Ai mutum ce fa tafi mun su anty yar malam sau dubu wallahi baki taba jin zance ya tashi
ace da anty Ai

40 / 101