Chapter 60 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   60 / 101

177K to 180K   out of 302.2K words

ke nan nace ehh ina mikewa ban faye shiga ba irin yau don lecture gudane gareni
malamin ma kuma ance baya gari yayi tafiya.

Ok ya fada yana miko min hannayesa biyu da alaman wai in dagashi daga kwancen banki ba na mika
mashi hannayena din ya mike zaune bandaki ya shiga na mike na wce wajen iya.

Tana zaune tana dan hira da biba nashigo ina gaida ita da kwana na samu biba tayi wanka tana shafa
mai nace kiyi ki shirya ga uncle nan zai fito muje falo mu karya a can yau.

Bidiri yau da mai gidan za a karya ke nan nayi murmushi nace iya ai hakan sunnane a musulunci zama
tare da iyali a danji korafin kowa hakan yana kuma kawo shakuwa a tsakani akace .

Don sammakon da mukeyine muna fita yasa ba a samun yin hakan wani lokaci don yadda muke
karyawa a gurguje kadin mu fita.

Dolene miji ya kulaka ai yar nan duk sauri da abinda ke gabanki baki gaza bashi kulawanki haka nima
nan da yar nan me zai hana mace ta sace zuciyat mijinta tana hakan.

Abinda suka gaza ganewa ke nan ba asiri bane ke sa miji karkata sai tsaban kulawan mace wata mace
bata dogara ga asiri ko wani siri ba akan miji sai zalla tsaban kyautatawa da take masa yake sa miji ya
ahagala a kanta haka .

Dan zaman na fahinci komai game da zamantakewan ku gidan nan akwai banbanci sosai a gidan nan da
can gidanmu .

Wa zai zauna ya baka kulawansa irin hakan da kikeyi mace tasan muhinmancin da darajan namiji haka
ace miji ba zai bata kulawansa ba wanan ai karyane.

Barsu can su zauna suna kishin hauka da bai fishesu ga abinda ya dace suyi amma haka zasu barshi har
sha daya wani lokacin wai ba a gama abin karyawa ba.

Toke iya waya tambayeki muryan Biba ya katse mata maganan ta mika mata dakuwa da hannu daga
inda take zaune tana fadin ungo naki nan yan nema idan zaki mai da hankali ki koya a wajen yarinyar nan
gara ki koya ki tashi da wanan halin duk da naga kina da kwazon kima kinayin komai yadda ya dace.

Ni dai ina gefe zaune bakin gado ina murmushi nace iya kinsan taji kina zancen iyayyenta shine ranta
ya baci.

Kai anty ni da nake shan harara wajen mummy ko ranan sunna gani zaune tana raba abu data kawo
kaina ta tsalakeni taba ta kusa dani ko ruwa saida dare mummy salima data ban abinci nasha ruwa a
gidan nan ranan.
Kinji ko ai kinji tsiyar basu da hankali ke meye naki a ciki ina mijinsu ya kawoki nan zama ko wajensu
kuma yana iya kaiki ai inga halin arziki ai.

Sun kasa gane hakan da sukeyi suna bata kansune a wajen yan uwa duk da yan uwan suka nuna masu
sunfisu daraja bakomai bane kuma hakan sai kwadayin duniya.

Ai kinga uwarki da yar uwarta da suka kama kansu inba wani dalili mai karfi ba basu zuwa gidan balle
su shiga shirginsu din bakiga suna mutuntasu ba dole tundai Rukkaiya da bata daukan raini.

Shigowansa ya katse masu zancen yashigo yana fadin iya kedawa ke fada haka tunda safe tun ina falo
nake jin muryan ki ?

Nida sarakunan kishin nan mana matanka su nake zankada tunda safe matarka tace damu yau tare
zamu karya dakai shine abin yaban sha,awa nake fada dasu.

Murmushi yayi yana kallona yace haka tace ta hanani barci wai in taso kada mu barki da yunwa kiga
laifinta ?

Ina laifi yar nan kin maisheni kamar basaraka ko sarakuwar uwarku ban samu rabin gatan nan a
wajenta ba gashi na samu ga jikokina.

Iya ai dole muyi maki kece fa gatan mu ga baki daya in ba ai maki abinda zakiji dadi ba aiwa,washi iya
na fada na mike ina jin tana fadin cikin raha ashe gaskiyane akwai mata masu tsoron kishiya gashi ko
nagani a yau.

Falon muka fito gaba dayan mu nan aka zauna saman babban shimfidan da nayi maimakon danning
din saboda tsohuwar na fara zuba abincin sai kamshi ke tashi .

Yayin da iya ke faman zuba cikin washe baki da jin dadi muna tsaka da cin abincin sai sallaman mama
mukaji da kawu sun shigo.

Kawu yana fadin a,a lalai iya kan ba zata koma gida ba ana haka duk wanan didiman haka iya ?

Kayi bakin ciki da hakan ne tunda ka kasa danka ya dauka yanayi ko iyan ta fada na yunkura na mike
ina mai barin abincin tare dayi masu sannu da zuwa.

Na gaidasu suka amsa kawu yana fadin nina isa in bakin ciki iya tunda jafaru ya kama muna ni dama
nace da wuya iya kiyi zancen gida a yanzu tunda mukajiki shiru haka ashe dadi jafaru ke narka maki a
nan haka ?

Ta sake fadan kayi bakin ciki ke nan nace aka kwashe da dariya mama idonta yana kan plate din abincin
kowa take fadin.

Ai dole ta koma gida tunda a can take gamu sai zaraya ta barmu munayi zuwa nan dubanta sai iyan
tace na hutar daku ku zauna gidan ku nan kan banda ranam bari inma daukana kukazo yi to ba zani ba.
Kitchen na nufa na barsu suna drama da tsohuwar tasu har na dawo na aje plate din a gabansu ina
kokarin zuba masu abincinne mamatace nikan a koshe nake ban fito da yunwa ba.

Ai badon yunwa zata zuba maki ba dubu tunda tasan mijinta bai kaza dake ba kamar yadda ya bayar
nan ya baku a can ai.

Amma karrama bako yana cikin koyi da sunnan ma,aikin Allah ai ko kin isa kija da hakan kuma yanzu
baki zuwa gidan nan kice wai a koshe kike baki fito gidanki da yunwa ba ke ?

Iya idan ban koshi ba ai zanci koda yaya yazo daukata ya samu ina cin abinci gashi nan ki tambayeshi ?

Amma ba irin wanan bako nidai na zuba nakai plate din a gabansu ina daukan nawa na mike inacewa
biba ta taso muje daki muci.

Shidai yana zaune yana jinsu sai abincinshi yakeci kawu ya fara jawo nasa plate din ya kawo gabanshi
ya soma ci ya fara fadin dubu kici abincin nan kada mu kwareki don Allah.

Ina iya zata yarda ta koma can tana hada wanan a rana haka kafin yakai karshe tsohuwar tace ance kaci
mai dadi idan ka samu daman hakan.

Can babu mai dadin ne iya wanan ai sai a dauka can bamu da irin cimar nan a can din sai dai ace kawai
gyaran ba daya bane kawai.

Ina gyara zaizo daya dubu tunda ilimin abin ba daya ba kefa dubu duk abinda zaki fada iya ba jinki
zatayi ba a yanzu don haka kiyi shiru kawai da zancen nan .

Iya munzo akan maganan yaron nan Yazid ne da Jafar ya sanar damu dawowanshi wai kuma har da
iyalinsa yanzu iya ga Jafar fisabilillah abinda yaron nan ya aikata muna yayi daidai ke nan ?

Ace wai yazid daga zuwa karatu yaje kasan mutane yayi aure a can bada sanin kowa ba a cikin mu ina
shi ina zuwa auren wani kasa iya don Allah ?

Zakija da ikon Allah ke nan ko duk abinda bawa yayi mukkadarine garesa dama dalilin hakan yaje kasan
da sunan karatu don ya hadu da matar nasa hausawa sunce matar mutum kabarinsa ai .

Koda rarafe sai yaje tunda Allah yayi a can matar nasa take kuma dan uwansa ya fada maki dalilin
hakan to meye na damuwan zuciyarki ke a yanzu ?

Iya ba hakana bane naga kayi aure a gida ka auri matar da akasan dabi,u sunzo daidai yaya aka kare
balle ka dauko a wani kasa kazo da ita nan ?

Idan yazo kuma yace saman kanki ko a karkashin wani zai zauna da iyalin nashine wai meyasa kukewa
aure shigan kutsu dubu aurensane bancin ranki a yanzu ko dawowansa kusa daku ?

Iya abinda nake son ki fahinci dubu a nan shine da yaron nan ya dawo gida yayi aurensa a cikin gata
kamar yadda kowa keyi zaifi mutunci kinsan halin mutanen yanzu da maganan da bai shafesu ba iya.
Sai abarsu suyi tayi yanzu ai tunda aikin gama ya gama ko aure harda haihuwa biyu yanzu meya rage
don Allah ?

Ni kawu banga abin tayar da hankali ba a nan tunda shi zai zauna da matarshi na fadawa mama addua
kawai zata bisu dashi yanzu don Allah.

Yaron nan da karatunsa inma yace bai sana,an nan sai aikin gwaunatine yana dai da ilimin sa ko da zai
iya rike iyalinsa tunda acan aiba mu ke rike mashi dasu ba.

Yarinyace karama kwarai matar nasa yar wani malaminsune yaga kirkinsa ya aura mashi yarsa ba ba
tare daya san kowa nasaba fa mama .

Yanzu kuma munan sai muce hakan bai muna ba mu nuna bamu ksunat yarsa mu don kawai bata fito
cikin nahiyar mu ba amma dai ai musulmace ko ?

Nasan dama bakin ku daya dashi tunda kai ya iya fadawa zancen ai dole ka fito da wanan zancen yanzu
baka son a fada tunda kuma kun auro matanda suke son sunfi karfin mu.

Zancen duk a kunnena yake muke nan mama ke nufin muna son fin karfinsu da mukai mata me na
rashin mutunci don kawai mun fito yayan fulani ba zage zagi ba kome ?

Saidai kafin nakai karshen maganan zucina naji iya na fadin shi auren kabila ai ba bakon abu bane don
kowa yayi a cikin mu dagani har ke kuwa dubu ?

Mahaifinki ai asalinsa banufene suka dawo nan da zama aka saje kuma na aurensa tun asalin yarensu
bai bace ba haka kema kuma kika auri mahaifin yaran nan kowa garin nan yasan zuwa Alh yayi garin nan
nema daga Adamawa koba haka bane meye bambancin zance a nan ?

Sai mama din tasa kuka don me iyan ta fadi hakan Biba najin kukan mama ta mike tsaye kamar zata fita
a dakin na zabga mata harara ina fadin karki soma haka ace dake munafuka.

Yaya irin abinda nake gudu ke nan tunda Habu yazo da zancen aurensa naso hanawa amma ka daure
masa gindi akan babu komai gashi.

Jin dadin auren har kanwarta ta cinnawa shi Jafar a yanzu gaba daya kowa yasan yaran ran sun juye min
kan yara don ba haka na tarbiyarta da yarana ba duk kun sani a nan ?

Dubu ki shiga hankalinki wallahi kafin na saba maki a wajen nan meye hadin auren Yazidu dana jafaru
kona habu yanzu ?

Kin fa kusa kai yaran nan makura akan zancen nan idan yaran ku sun sauya ku kuka sauyasu ai ba wasu
ba ?

Ko har kin manta da cin mutuncin da kukai mai keda diyan ki da dan uwanki gashi ?

Nace kin mantane in tuna maki yanzu yadda suka zugaki idonki ya rufe akan danki dake tausayin ki kan
dukiyan da yake kula maku dashi yanzu ina dukiya nan ku yake ina tambayanki dubu ?
Iya meya kawo wanan zancen ai taimakonshi akayi don an karbi dukiya a hannunsa haka kuma shi bai
nuna komai don an karba ai kawu dauda yake fadan hakan ga iyan.

Haka zakace tunda ka damka kana bushashanka dasu ai dole kace bai nuna bacin ransa ba ko tunda shi
ba mutum bane ko ?

To in baku sani ba ku sani duk da kuna ganin bai sauya ba dole abinda akai mashi ya bata mashi rai don
haka kuyi kuka da kanku kada ku dora laifin ga yayan mutane da basuji ba basu gani ba .

Aure kuma mukaddarine ko a ina matanka take sai kaje ka aurota don haka ina son ku fitar da idon ku
akan yaran nan daga yau jafar dai yana zaune da matanshi lafiya inma wani abune kece dai dashi dauda
gashi kune matsalan yaranku nan ba wasu ba.

Kuka mama din ta kara dorawa sosai tana fadin meye zaisa aga laifinta shi kuma kawu yana yan kame
kame nan dai basuji din zuwan ba don tsohuwar bata yarda da zancen da suka zo dashi ba din.

Tace kowa ya fitar da idonsa kan yaran nan da matansu inba rashin hankali ba yaran nan meye
matsalansu da auren yayan ku da kuke son sakasu gaba hakane ?

Ke in kina da hankali yadda yaran nan keda tarbiya ai abin farinciki ne ya sameki ba wanan hakan da
kikeyi a yanzu ba haka akan matan yayan ki.

Sai yanzu na kara tabbatar da kinfi bukatan ganinsu cikin tashin hankali da matayen nasu sama da
zaman lafiyan da sukeyi ashe ?

Ga dan uwankinan inba ya zama munafuki ba da bai iya fada maki gaskiya sai akasin hakan ko yaushe
shi yanzu daya samu wata da take dadada masa ai gashi da tsufansa yana sabari a kanta da yayan
angolan datazo mashi dasu gidansa.

Kiyiwa kanki karatun ta natsu tun kafin yaran na su gane nufinki a kansu dubu su fara mayar maki da
martani don dai yayanki ba rabuwa zasuyi dasu ba kin sani.

Ba kansu ai aka fara irin wanan hadin ba tunda Allah bai hana ba har uba yakan auri kanwa da ya auri
ya duk bai zama illa ba sai a gidan ki dubu kina kokari kija da ayar Allah da Annabinsa a nan kinki kwantar
da hankalinki kiki bari na yaro ya kwanta kuma ?

Yazidu kuma kinsanshi kinsan halinsa to ki matsa dubu kikai ga abinda ba aso akai din har yan uwanki
su samu shiga kina kallo ke kikajawa kanki hakan kuma ba wani ba ?

Nina rasa gane matsalan ki idan na tariyo sai inga duk laifin na daudane don ke kamar kanki a burge
yake yanzu tun mutuwan mijiku kuwa nake hango hakan dama shine katangan daya tare duk wasu
matsalolin da za a fahinci hakan a gareki.

Yanzu dai shawaran da zan bayar a nan shine ita mama tayi hakkuri har yazid din yazo da matar nasa
aga mata wace irin rayuwa ke gareta don Allah a fanci juna shine zaifi tunda ya riga yayi wanan kuskuren
ko ?
Banso dubu ta matsa akan zancen nan ba amma tace sai mu taso a san yadda za ayi ya baro matarsa
ya dawo nan shi kadai kawu ke fadan hakan .

Iya tace kaji shirme ko na fada maku dubu ta canza a yanzu ina kuka kwana da zancen da nayi maku
zuwa biyan bashin dake kankune dauda ?

Wanan ya kamata ace kunyi ba wanan shirme ba dakukeyi a yanzu auren da aka samu zuria a tsakani
ina ke ina shiga tsakaninsa kuma yanzu ?

Zamuje iya wajen ne yake da wahalan zuwa amma za aje din tace sai yaushe zaku tafi ko sai kunga sun
fara zaran yaran daya bayan daya zaku maida hankali ga tafiyan ?

Goben nan ko jibi nake son duk abinda kukeyi ku maida hankali a tafi wajen nan don naji jafaru yana
zancen komawa wajen sana,anshi cikin kwanakin nan.

Zubur kawu yayi yana fadin gobe iya iya tace kwarai kai harni zamu tafi ba wai ku kadai ba idan baku
shirya ba kuyi kwatance mu tafi nida yaran nan .

Ku diba yaron nan ko bai fada ba ansan da abinda ke damunsa don yana namijin tsayene baku gane
hakan sai ya fadi kasa kuji dadin hakan ?



sorry for missing me wlh iam surfering for tooth pain all dis days yasa kukajini shiru.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/15, 10:44 PM] Zainab Idris Makawa Writer: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa

MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



6️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Motsin kwarai na kasayi a lokacin gashi dai naji fitansu amma jikina ya mutu jikina ya mutu na kasa
motsin kwarai sai dubawa nakeyi ina aunawa me nayiwa mama dani da yar uwata a zaman mu da ita ?

Saidai na kasa hango inda laifin namu yake gareta matsala dai daya shine zance ko yar uwata data dade
a tare dasu bata taba kai korafin mijinta gun mama ba yadda sauran surukanta keyi .

Haka kuma bata taba fadawa mama wani matsala daya shafi aurensu har asani manya su zauna dasu
ayi sulhun hakan .

To balleni da ko shekara banyi a cikin su ba ince mata me akan zama da danta me zan fada ya hadani
dashi ko abokan zama da ba waje daya muke rayuwa ba balle kuma ai bai mun wani abinda zankai
karanshi wajenta ba yadda take so.

Ni dai a ganina wanan ne kawai matsalan amma bansan abinda ke boye ba a zuciyarta amma tsanan
yayi yawa a zuciyar mama kan mu.

Ban san hawaye na zuba min ba a idanu ina dai kwancene kawai naji muryanshi a kaina yana fadin
kuka kuma Rahama meya sameki kike kuka haka kuma ?

Dan yunkurawa nayi ina kokarn mikewa zaune saidai kukan yaki tsaya min naga yakai zaune gefena ya
sake fadi cikin kallona meya sameki Rahama ?

Cikin muryan kuka na daure na iya furta ba komai ina sheshekan kuka tare da kokarin kauda kaina a
gefen da yake zaunen.

Umm,humm Rahama idan kince kuka zaki dingayi kan mama zaki sha wahala sosai a rayuwan ki don
inkin duba bake taiwa hakan ba ni tayiwa don nine zaune dake.
Duk abinda takeyi bake takewa ba don nine take hakan kuma zata bari in sha Allahu ki dai kara hakkuri
nasan kinayi baga mama ba harda kannena musanman Saratu nasan duk abinda ke gudana a tsakanin
ku.

Yanzu haka ina shirin zancen auren sune da zaran Allah ya dawo dani lafiya shine abinda nake son
aiwatarwa ke nan a kansu.

Ki tashi ki shirya zamu fitane yanzu dani dake jin hakan yasa na dan kalleshi ya gyada kai yace ehh akwai
inda nake son mujena kafin na tafi tare dake.

Naji hannusa cikin nawa yana dan murzawa alaman bani hakkuri yakeyi a zuciyarshi hakan da yai min
sai nake jin sanyi a raina har ya

60 / 101