Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
kuryan
uwar dakan da akaiwa kwaskwarima yana kasa.
Maman tudu dake rike da ita tun tana fadi a ciki har zancen ya fito fili tana fadin ikon Allah aure shiya
gaji haka yau Saratu Allah ya nufa aure ya kawota nan kasan kuma ina ji sunan garin nan a redio amma
ban taba tunanen zuwanshi ba.
Sai faman gaidasu da zuwa yan gidan keyi har suka kai dakin nata suka zauna kallon juna kawai suke a
tsakaninsu sai yaya barakhace ta iya fadin .
Shiko dai wanan mutumin a gidan yawa haka gidan kowa da kowa zai kawo saratu ina laifin ya kama
mata haya a wajen gidan don Allah dai.
Ke dai bari ai wanan dalilin yasa muka koma muka fadawa Dubu abinda idon mu ya ganan muna ai baki
san abin takaici bama barakha ni hada ban dakin nan shine ya tayar min da hankali fiye da komai.
Ga matansa kauyawa gidadawa dasu ke bari kawai abin bai faduwa dai wallahi daki ai kun samu an
gyara komai dafa ciki gudane iya falon nan.
Gaskiya mutumin nan bai kyauta ba wallahi haba dai a,a barakha idan baku sawa auren nan albarka
kuyi shiru don Allah tana fa son abinta ita don haka ku daina wanan magana.
Idan matansa kauyawane ita yar birni saita koya masu komai a sannu harsu gane ai dama shine amfanin
surka auren da maza keyi yanzu.
Nusaiba ce ta fito daga kuryan da suke tana fadin nikan zafi kamar zan suke wallahi dakin nan idan na
kwana a cikinsa haka ai ina sankarewa kafin safe ?
Meyasa wa yanda ke gidan basu sankare ba sai ke ku dai iya bakin ku a rabu lafiya don Allah irin
maganganun nan babu dadi gaskiya.
Mama tudu ta tarewa Nusaiban numfashi abinda take fada a lokacin yasa taja bakinta tayi shiru ta tafi
tana guna guni nan mata suka fara shigo masu da kulan abinci dama a gajiye suke don nisan tafiyan da
sukayo.
Wasu sallah suka farayi wasu kuma neman abinci irinsu Saiba ke nan tun wajen bude abincin sukai
arba da bakin miyan dake cikin katon kula girke a gabansu miyan dai ga abin miya amma gaskiya yana da
wuya yakai bakin mutum ko don bakinshi.
Inda Allah ya taimakesu kunun daka da aka kawo masu hade da abincin wanda yaji kayan kamshi ga
suga zaikai mudu biyu da robobin sha shi suka dinga afkawa cikinsu don yunwa abinci kan abin miya suka
tsame sukaci.
Akwai gaji don haka suka fara shirin barci tun a can amarya saratu ta fada masu idan anzo za ayi dinner
don haka kawarta da akazo da ita take tambaya zancen dinner din ?
Take fadin itama har yanzu angon bai kirata ba kota kira wayanshi yana kashe bata samunshi har barci
ya dauketa ba zancen dinner din.
Washegari hayaniyar mutanen gidan ya tayar dasu wajen kewayawama fitina ne haka suke bin lafiya
har amaryan suka dai samu sukai alwala sukai sallah.
Su mama suna falo suna dan gaisawa a daidai lokacin sukaji amarya ta fasa kuka daga kuryan daki
hankali tashe suka isa gareta banda mama tana zaune tana azzakar din ta na safe.
Sai dai ta jefa masu baki daga inda suke saida ta idar ta mike ta samesu tana fadin shifa aure
mukaddarine duk inda Allah ya nufa zakayi aure saika taka wajen.
Abu guda ya rage maki a yanzu shine hakkuri wata nacen tana neman hakan bata samu ba ke kuma
gaki kina son butulcewa Allah yanzu da baiwan da yayi maki.
Kinsan alheri dake cikin aurenki da bawan Allah nan da Allah ya hadaku tare shine mijinki aure ba
kyalkyalin duniya akajawa cikinsa ba zama na amana matukar akwai so a tsakanin ka miji.
Ki bar komai ga Allah kisa hakan shine alherinki a yanzu kinsan tanadin da yake maki ai yasan gidan
daya dauko ki da inda ya daukoki don haka halinki yanzu shine jarinki saratu ki natsu kibar wanan
shirmen da kikeyi.
Kowa nan da kalan zabin da Allah yai mashi duk abinda kika gani ya faru da bawa rubuttace tun asali
gareka.
Ni banga wani abin damuwa ko shiga tashin hankali ba saratu kinafa son mijinki so ba inda baikai mace
a duniyan nan .
Da kalaman mama ta samu natsuwa suma din su saiba dake sakin magana duk mama tayiwa kowa
gugan zana a wajen kowa ya kama bakinsa.
Don cewa da mama tayi da wani zaman burni ko cikin daula ai gara kauye din inda hankalinka yake
kwance a san kana kauyene ba sunan kana cikin daula ba wanan zance ya tabawa Saiba rai inda tace da
ita mama keyi a zuciyarta.
Kamar ana koransu kafin takwasa na safe duk sun shirya tafiyan komawa zaria a gagauce ga matan
gidan duk da safiyane sai dake dake sukeyi suna wakokinsu a cikin raha na nuna murnan auren daya
daga cikin ahalin gidan ana fadin su jira a gama furan barna sukace akwai nisa tsakanin zaria da nan gara
subi hanya da wuri.
Sai wajen shiga mota suka samu ganin ango yazo sallamansu nan mama tayi mai dan nasiha yana ta
godiya suka tafi suka barta a nan din cikin mutanen da bata taba sanin kalan rayuwansu ba haka ya mace
ta gada dama a kaika inda baka zata ba a rayuwa Allah yasa mu dace amin.
Ranan yan uwan Aminu mata da yaya barakha tazo dasu wajen bukin suka zo gidan mu dama ranan
zai koma can gidanshi ya gama kwanakinsa a nan.
Abinci lafiyayye na shirya masu ba wani daure fuska koma ba sakewa sosai kada raini ya biyo baya na
barsu sunyi yadda suke so tunda gidan kanin uwarsune suma kuma basu wuce gona da iri ba yadda nayi
zato.
A can gida kuma mama hankalinta a tashe yake har saida yan kai amarya suka iso a wahale kowa na
neman abinda zaici a cikinsa maman tudu bata tsaya ba ta wuce gida da ita da yaya Rukaiyya.
Sai mama hafsatu da yaya barakha da Saiba data nufi part dinsu suka rage a gidan yadda suke neman
abinda zasucine ya tayarwa mama da hankalinta sai dai batayi magana koma meye ai zataji su kuma
basu cewa kowa komai ba kar yadda maman tudu ta kwabe bakinsu tun can din.
A nan gida kan wajen mama ba wanda yai magana sun daici abinci sun kuma ce sun barta lafiya tana
can sun barota ita kadai.
kamar yadda ake barin ko wata diya idan an kaita gidan miji nan mama tayi shiru na dan lokaci ai kuwa
can part din yaya jafar kuma gajiya bai hanasu fada ba.
Don saiba na shigowa ta kula da kayan da yaci abincin rana ta soma fadin halan gidan nan sweet J ya
kwana ?
Asmau tace ehh cikin ko in kula daki ta nufa har ta tube tufafin jikinta kamar an tsikarota sai gata ta
fito tana fadin .
Asmau ya kwana a nan kuma kinsan nice da girki kika yarda ya kwana a nan ban gari ke dai yar cin
amanace ta gaske wallahi ?
Cikin mamaki Asmau ta dago tana fadin tau fa kaji manya don baki gari sai kada ya kwana a nan ko ai
bansan haka kika kafa doka a gidan nan ba ?
Aida zaki tafi saiki fada min kada na kuskura in karbeshi idan ya dawo tunda kinsan jiyan zai dawo
gidan nan kuma kikayi tafiya ?
Fada sosai sukayi tsakaninsu wanan kawai ya isa ya tuna maka saratu don da tana gidan da tun a
lokacin ta iso part din ko kuma ta bugawa saiba din waya tun tana can ta fada mata abinda ke faruwa a
gidan.
Har suka gaji suka kyale juna akan a bari maigidan ya dawo tunda shine munafukin da yayi hakan
saiban ta shiga tayi wanka ta fito don tunda sukaje sun kasa yin wanka a bayin gidan.
Abincima da Asmau ta bata kin karba tayi tabar matashi a falo ta fito zuwa part din mama ta duba ko
akwai abinci a can taci .
Ta samu don mama tayi girki don isowansu din ta zauna taci tana cicika a lokacin mama ke fadin
mutumiyar ki dai tana can ta zama mutanen sokoto ?
Mama aida sokoto din take da sauki wani shegen gidan yawa ya kaita fa gina kamar na mutanen dauri
abinda babu dadin fada gaskiya.
Kai Nusaiba bakiji me maman tudu ta fada ba albarkan aure yafi riyan dake cikinsa kayi abu daidai
karfinka ba karya yafi kayi karya girman ka ya zube.
Meye laifin gidan tunda yana da gidansu aurene fa ba inda bakai diya mace ta mike tana fadin yaya ai
gaskiya na fada .
Ita mama da take fadin hakan ai ta fadane kawai tunda bata yarda akai yarta wanan wajen gaskiya kam
abu daine bai faduwa kawai sai ayi shiru hafsatu ta fada daga gefe.
Wai ku tsaya me ake kokarin boye min ne mama din ta fada tana duban saiba din ta mike tana fadin
mama ni me zance yanzu ace kuma ina kushe aure sunana yakai tasa kai ta fita.
Munafuka dadai ki fada din mana tunda gulma na ciki ai gara dashi yana da gidan ke ko gida iyayyenki
nada shine balle nina dawo rakiyan yarinyar nan na kula ba mutumiyar arziki bace ita .
Barakha meye laita yanzu har kina kokarin zaginta ai gara da ita ta fada min halinda yata take ciki kuda
kuka boye min fa don yaya tace kada a fada ?
Laifine mama don mama tace kada muyi surutu mu tayata da addu,a sai hakan yazama laifi ni naga ai
abinda yakamata muyi ke nan mama ta fada.
Lalai Barakha dole kishiya ta dinga cin galabanki indai wanan halin naki na saurin yarda da mutanen
yanzu kikeyi a can ?
Yayace zatace kada ku fada min abu ke har ki yarda kiki fada min don kina bi can sun san halinki ke
sokuwace da sauri ta dubi uwar tana fadin ni mama me kuma nayi na sokonci a nan don na fadi gaskiya ?
Damu fada maki abinda zai tayar maki da hankali a banza ita saratu na can zaune dakinta ai gara muja
bakin mu muyi shiru tunda nan Allah ya nufeta da aure.
Wani malolon bakin ciki ya tokare mata makoshi ta kasa ba yar nata amsa don bakin ciki ta mike zuwa
dakinta barakha ta dubi mama hafsatu tace wallahi mama kada ki yarda kice komai kada tashiga wani
hali su jafar su sakaki gaba a gidan nan.
Jin hakan yaba hafsatun tsoro tace ni kingama bari bazo nabar gidan nan yanzu da nace sai yamma zan
karasa gida amma yanzu zan wuce.
Dubu na shiga daki waya ta jawo ta dannawa saratu kira gidan cike yake don a ranan suke wunin buki
tunda amarya ba a gari take ba.
Hayaniyane dakin nata sai cewa take bata jin abinda mama din take fada don idon mutane dake kanta
a lokacin dakin tap yake da yan uwa da abokan arzikin gidan yan zuwa gani amarya.
Gashi duk sun isheta amma ba daman magana yarasu sai hawa saman kujera sukeyi suna takawa
iyayyeb da diyan anci shimkafa an wawatsar mata a dakin nata.
Dole ta koma kuryan dakinta ta kwanta tana kukan zuci Allah ya gani tana son habibinta don irin mazan
nan ne da mata basu dauke ido akansu don kyau.
Wanan yasa duk inda yaje ya taya mace yake samu da sauri gashi iri mutanen nan ne manema mata
ko yaushe tsab yake komai nashi neat tun daga kanshi har takalma zaki gashi neat dashi clean .
Saidai shi dan karyane na gaake kuma manemin mata dama idan kaga na mijin kauye ya faye wayewa
hakane dabiansa neman mata.
Ko ita saratun da karya yaje mata saita lake mai har abin ya zama masu aure bai boye mata ba da abin
yayi nisa ya fada mata shifa dan kauyen sokoto ne haka kuma bawai wani mai kudi bane shi.
Ta dauka yana zolayantane kawai don ya barta sai gashi tace zata daiyi din ko yaya yake don ita a
zatonta kawai yana fadane don ya gwadata ashe haka abin yake.
Allah ya dora mata son habibi a zuciyarta don haka ko yanzu da tan uwa suka watse suka barta bataga
laifisa ba tunda ya fa mata din abu dayane har lokaci bata tantance ba cewa da akayi itace ta hudu a
gidansa.
Bata gaskanta ba saida yan uwan mijin suka hadusu waje daya ana tsawata masu kan zamantakewa
nan tasha mamaki ganin su hudune dai matanshi kamar yadda mama hafsatu ta fada data koma daga
jere.
Wanan yasa hankalinta tashi sosai har saida ta kasa daure ta kira mama da kuka tana fada mata itama
uwar kasa daurewa tayi nan ta nemo kan iya tana labarta mata a zatontama Jafar bai gidan saboda
rudewa ranan bata tsaya yin lissafin kwanan mu ba don ga yarta cikin bala,i.
Ke dubu ki natsu dob Allah zama da kishiyoyi haka kan saratu ne farau din haka keda kika zauna a cikin
kishiyoyi meya sameki nace ?
Iya ba daya bsne da nawa don ni a cikin gari nake kuna jin duriyana kuma ina ganin na gida wanan
kuma wani uwar duniya fa take bako kusa da yar uwarta hannatu ba can fa kauye ya ajeta.
Sai akace kauyen ba a zama ko aure inane bai kai mace wai don Allah ana ce baki ga zuma kina ina
badaci yarinyar nan dai tana son mijinta ko batace dake bata iya ba dubu ?
Suna zancen jafar da habu suka shigo part din suna gaidasu nan iya ke fadin to kuyiwa uwarku magana
tun bata jawo maku abin kunya ta kashe auren saratu ba ?
Kashewa kuma akan me mama jafar ya fada yana kallon uwar iya ni baki fahinceni bane abinda nake
nufi don me yayi muna karyan mata daya gareshi ?
Haba mama ai hakane daidai da saratu gidan mata da yawa inda zata ji dadin yin gulman ta da makirci
ba ta iya tsegumi ba tun nan tana shiga matan yan uwa tana hada fada yau gata Allah ya kaita inda zatayi
nata.
Habu nagane saboda matarka ka tsani yar uwarka to koma meya samu saratu yar uwarkace dai mama
ta katse ya Habu daya soma magana.
A,a mama ba wai zancen tsana bace kece kika damu akan wanan abin yarinyar nan itafa ta gabatar da
mutumin nan tana son sa banga abinda zaisa ki damu kanki ba yanzu don Allah ?
Habu yana nufin cewa zata iya zama a duk inda ta tsunci kanta tunda ta koya a gun matan mu da suke
rayuwa tare a gidan nan shi kuma sai bai fada ba kai tsaye.
Iya sai murmushi takeyi tace banda abin dubu saratu mace ce fa yau ko sha biyar aka wanketa a
zamanin nan a kai cikin mata ukku ai tsab zata zauna dasu balle mace kamar saratu.
Ai maganan habu gaskiyane zata zauna tunda ita ta saka kanta auren nan idan kika sa damuwa har ta
fahinci hakan ta kaso aure tazo ta zauna maki gida shike nan.
Addu,a yakamata kiyi mata mama yadda ko wata uwa kewa yarta in yaso sai a saurara aji ko zatayi
korafi aka zaman nata kinga sai a san matakin dauka a lokacin.
Wanan magana ta jafar ya kwantar mata da hankali suna cikin zancen saiga Saiba ta fado masu tana
huci take fadin mama naje can ban sameki ba ?
Ashe kina nan dama karan su na kawo maki kowa yasan dai nice zan karbi girki a jiya amma sai J yasan
ban gari ya dawo yaba Asmau girkina.
Wooo,hwahoo ni jikan mutum biyu yar nan kina data ido kuwa Iya ta katseta sa fadin hakan wani kallo
tayiwa iyan kafin tace da hankalina wajen mama nazo.
To meye a cikin hakan kuma Nusaiba akwai mana mama tunda ban karawa Rahama kwanan ba na
dawo nan bata samu yadda take so ta bata min suna da yar mutane ba.
Na dawo na kwana da Asmau ko kike nufi idan na tsaya can kuma ki dorani a ture ki yawata kina fadin
na saci kwanan ki ?
To na kwana din kiyi abinda zakiyi marata ido kawai bansan baki da mutunci ba ai da bandawo na
samu kinwa Asmau duka ba yau.
Tsuki habu yaja ya mike yana fadin ni zan tafi iya yaya karfin jikin naki dama nazo na dubakine zan tafi
ya mike yana fito da kudi cikin aljihunshi ya mika mata.
Da sauri ta mika hannu ta karba tana godiya hakan yabasu dariya aka wasance J ya mike suka fita da
habun sun jima a wajen motar suna magana kafin ya bar gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/5, 9:25 AM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ina jin irin cakwalin da akeyi cikin dangi game da zancen aure Saratu ban taba furta komai ba game da
zancen shi zance a yanzu tafiya yakeyi.
Bayan haka alhaki kwikwiyone don bin mutum yakeyi koshi yaya shiyasa na katseshi da irin nuna
haushin ta da yakeji yana mata gwai da hakan data fada ciki.
Na nuna mai tankar uba yake a gareta duk abinda ya cika da ita a yanzu ya sameshi don shine matsayin
babba a bangaren mama yanzu.
Ya kance dani haka kike gani Rahama amma su a bangaresu ai yanzu tunda banda komai ai basu ganin
hakan kowansu kar nake kallonshi a yanzu.
Habu ma yafi kowa ban mamaki yasani sarai nina sakashi a wanan harkan asalima sana,atace ta baya
na bar masa amma wai habu nan nace ya cika min kudi nayi wani bussiness ko Allah zai taimaka un daga
yaki ban .
Nayi mamakin wanan zancen da naji duba ga yadda nasan ya taimaka masu sosai a baya koda yake ba
abin mamaki bane idan ance yaya habu yayi irin hakan donshi mutum ne da bai kwantuwa ko kadan.
Ko iyalinsa gaskiya din tana da hakkurine ba a jin kansu da ita don da watace yadda yake tauyeta din
nan da anjisu tuni