Chapter 2 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   2 / 101

3K to 6K   out of 302.2K words

muna tsaye da kafafun mu.

Irin bangaren dakin mama ke nan dake da yara kana a cikin gida don ita Allah bai bata haihuwa da wuri
ba har mata biyu sukazo a bayan ta sukai ta haifo yayansu sai can kwatsam ubangiji ya azurta da samun
ciki.

Dama kamar camfi haka zancen yake kuma ga duk matar da bata haihuwa zakiga ubangiji ya azurta
hannunta da arziki duk sana,an data dafa zaiyi albarka sosai a rayuwanta.

Saidai da zaran mace ta soma haihuwane zakiga arzika ta ya soma jayewa sannu hankali ya koma ga
yaya kuma wanan abin kamar wani camfi haka yake idan mutum ya duba.

Haka har in Allah bai azurta ta da haihuwan ba zakiga mace komai ta dafa da sunan neman kudi abin
nan zaiyi albarka sosai a rayuwanta.

Anan dai kamar wani baiwane ko hikima na ubangiji daya barwa kansa sani akan hakan saidai kiga
mace ba haihuwa tanata wahala da yan uwa bata gajiya da hakan.

Irin wanan rayuwan mama Dubu tayi da farko a rayuwan zamanta gidan mijin nasu abaya tana da abin
hannunta sosai datake juyawa wanda har yakai ta mallaki wani fili babba a lokacin .

Saidai ta boye hakan ga yan uwan zamanta tabar wanan tsakaninta da dan uwanta da yai mata jagora a
lokacin har ta mallaki wanan filin a wani sabon unguwa da gwaunati ke yankawa mutane filin.

Wanan dan uwan nata shine ya karfafa mata ta soma gina da sunan saita bada haya inda taja daku part
part har hudu a gidan saidai Allah bai nufi ta karasa ba Allah ya karbi ran mijin nasu inda ya barta da yara
kanana tare da ita.

Sai bayan rasuwan mijin nasu da son kai ya shigo cikin rabon gadon sune manya dake da diya masu
girma da kuma yan uwa dake fada aji suka shiga suka fita aka tauyewa marasa galihu hakkinsu.

Dan abinda ta samu ita da yaranta shine suka sayar ta karasa gina wanan gidan nata data soma gina
sai kuma hakan ya dawo ya tsonewa abokan zamanta idanu daga baya.

Wanan ya kara ja mata tsana da tsangwama daga ita har yaranta saidai duk da wanan mama Dubu
bata yarda ta bargidan mijinsu wanda ba a kai ga rabashi ba har lokacin tana zaune ciki har yanzu a part
dinta anan take rayuwanta da yaranta kanana da basuyi aure ba.

Bayan ta dawo daga kai sadakan hayaniyan yan cikin gidan ne ya tareta tunda ta doso gidan hakan
baisa ta tsaya kula mai sukewa hayaniya ba don indai da sabo ta saba da hakan ai.

Wayanta dake makale a caji ne ya ta samu ya kara ta dauka muryan Habu dintane taji yana sheda masu
saukansu lafiya tare da mata bayanin irin nisan tafiyan da sukasha a hanya.

Murmushi tayi tana fadin a godewa Allah daya kaddara saukanku lafiya Habu tunda ankai lafiya ai
Alhamdullahi.
Sukai sallama don sahabi ya shiga nema masu abinda zasu dan samu suci a wajen shi kuma lokacin ya
shiga masallaci ya yayi sallah ya fito shine ya nemi mahaifiyar tasu .

Akwai sabo da shakuwa sosai tsakanin mama Dubu da yaranta ta koyar dasu shakuwa da ita irin ko
wani hali suke din nan ko a inane kuma zasu kira mama su sheda mata halinda suke ciki din.

Suna gama wayan ya sauke ajiyan zuciya tare da shafo fuskansa yana bin garin da kallo wanda yake
kallonsa tankar a Nageria yake bawai kasan waje ba.

Komai nasu rayuwan da komai zaka iya kirasu da yan Nageria don hatta shigan suturunsu iri dayane da
mutanen Nageria .

Mazan shaddane ko yadi ajikinsu da kalan dinki kuma iri daya dana yan Nageria saidai ya fahinci suma
suna da yawan kabilu don yanayin shigar tasu daya sha bambam .

Ya fahinci akwai masu siffan larabawa a yanayin shigarsu haka kuma a take wajen ya fahinci
bambamcin dake akwai da wa yanda basa sallah a cikinsu.

Mota ya bude ya zauna yana dakon abokan tafiyanshi da sukayi tattaki don duba abinda zasu dan iyaci
a wajen don suna son su fara haka na,uransu da zai watsowa al,umman duniya shirin kai tsaye.

Ido ya dan lumshe a cikin gajiyan dake dibansa don ba abinda yake nema a yanzu sai inda zai dan saka
hakarkarinsa ya huta duk da yasan hakan yana da wuya.

Inda ka dosa Habu alherin ka yana wajen muryan boyar Allah nance ta safiyan jiya da yabaro kofan
gidansu da kwallan maciji yaji ya ziyarceshi a karo na biyu ke nan tun bayan barinsu gida zuwa nan .

Don ko acikin mota yayi wanan tunanen inda ya zabura ya daga cikin dan firgita dajin muryanta kamar a
gefenshi take zaune.

Me wanan matar take nufi da zancen haka din don sai a lokacin ya tsaya yana nazari a kan wanan
matar mai yawan murmushi da fara,a a fuskanta.

Kana da tarin mahassada da makiya ka kula da addua da sadaka a rayuwanka inda ka dosa alherinka
na wajen zancenta ya dawo mai karara a zuciyarshi.

Raba kanka da irin mutanen nan masu neman abincine kawai ba wani abuba kadama ka bari zancenta
ya zauna a zuciyanka.

Wani sashe na zuciyarshi ya gargadeshi da hakan lokaci guda tsuki yaja yana mayar da kanshi saman
kujera zubur ya mike zaune don karan gugan motar tasu da yaji anayi ya duba .

Wata bakar yarinya daba zata wuce shekara takwas zuwa tara ba haka ya gani tana zoza hannunta jikin
motar alaman dai abin ya bata sha,awa har takai hannunta tana wasa da kuran da motar ta kwaso a
hanya.
Ido ya kurawa yarinyar ya kasa magana data jaye sai binta kawai da yake da kallo gata bakace amma
kuma kyakyawan gaske.

Han din boniyo ke maria ki jaye wajen nan kada ki daukowa mutane magana ke kadaice yarinya a
wajen kowa bai kai hannunsa ba sai ke ?

Addah barin taba na koma naba da labari a ruggan mu naga motan tv har na taba da hannuna da sauri
yar uwar tazo ta jaye yarinyar tana dangwarar mata kai cikin jin haushi da takaicinta.

Yare ta soma cikin fada fada har lokacin tana kai hannu tana dangwaranta kan ta taba mota zata ja
masu matsala suna zaune kalau.

Baisan lokacin daya bude baki yace da ita barta mana ki daina dukkanta hakana jin hausanshi yasa yar
matashiyar budurwan daga kai ta kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta fisgi hannun yarinyar sukai
gaba .

Binsu yayi da kallo kawai daidai lokacin daya daga cikin abokan tafiyansa ya dawo yana fadin oga akwai
matsalan abinci fa a wajen nan.

Son mun duba gaskiya abincin nan sai a hankali wallahi saidai fura kan da nono wanan gaskiya ko
kamfani za a bude a nan albarka.

Baida damuwa ibrahim akwai dan abinda na riko gudun haka ban manta da rafiyan mu zuwa calabar
ba ai.

Ku karya mu soma aiki kada lokaci ya kure yana fadin haka ya mike zuwa bayan dogon motan nasu da
suka loda kaya ya bude ya shiga ciki.

Wani jakka da kula ya jawo ya bude bread ne da cake a cikin jakkan sai wani leda dake cike da kayan
cima na gwangwani ya debo ya fito daga cikin motar ya nufi dayan motan da yan uwan nasa ke ciki suna
hira mikawa kowa yayi suka dauki murna da mashi godiya sai sahabine ke fadin.

Kai Habu habu yaushe kayi wanan dabaran haka bamu sani ba murmushi yayi kawai ya nemi waje ya
zauna ya bude kifin gwangwanin ya soma ci da bread .

Daga kan da zaiyi wanan yarinyar dai ta dazun ya hango daga nesa ta zuba masu ido tana kallonsu
cikin shagala tana magana da wata ta kusa da ita.

A zatonshi abinda yake ci take kallo sai yaga ba haka ba motar dai tasu take kallo cikin mamaki don
yadda take gwada tukin mota da hannunta cikin yanayin wasa da tukin mota.

Dago kai yayi suka hada ido yayi mata alaman tazo ta karba ba bata lokaci tazo da saurinta ya mika
mata bread din da kifin daya soma ci ta juya da sauri ba alaman tsayawa godiya a gareta ta nufi hanyar
da sukabi dazun da yar uwarta.

Goran ruwa ya jawo ya soma dauraye hannayesa yana dan yarfarwa kafin ya bude mota yana fito da
na,uran daukan rohoto ya soma saitawa yadda zasu samu service a wajen taron
ZAINAB IDRIS MAKAWA

[12/26, 2:54 AM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f




MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Baiwa da albarka yana ga yayan baiwa da Allah yasawashi yai masu arzikin duniya da lahira saidai yana
da wuya mu yan adam mu gane hakan da sauri .

Ko wani mahaluki yana da kalan tasa baiwan arziki da Allah yai mai sai mai natsuwa da kula zai gane
hakan mama Duba ta yarda da hakan akan diyanta sun taso da baiwansu saidai rashin hayaniyansu ya
boye wanan baiwan da Allah yai masu.

Yana da kyau uwa tasaka hope akan yayanta ta zamo mai kawar da ido da son nuna kaunar yayaa fili
irin yadda wasu uwayen na yanzu keyi.

Yana da kyau nuna kaunar amma idan kun kebe da yaran don nunawan a fili yana kai idon mahassada
su illanta maki yara ko da bada mugun nufi ba kuwa don wani nasa baiwa a hassada yafi aiki wani ko
daya furta ba daidai ba ga mutum sai hakan ya tabbata akansa din.

Ansan ko wace uwa tana kaunan danta manya sunce badon kaza bata son danta bane take takashi sai
don ya kula da duniya.

Wanan akidar ta mama Dubu shine ta shammaci mutane ta kawar da kanta gun yayanta tun suna
kanana take turasu koyon sana,a basu zama gida ana nuna masu kauna ko so da gata da akewa yaran
yanzu ana kashe masu zuciya daga boko sai boko ko islamiya sai anyi wa yaro jan ido zai tafi islamiya din.

A bangaren mama Dubu wanan tsare yake yaro zai tafi boko daya dawo yaci abinci zai sauya tufafi
zuwa kayan aiki ya fita wurin sana,anshi hudu nayi dole ka dawo daukan karatun Allah wanan kai,dace a
wajenta don dokan data sakawa yaran nata ke nan a gidan.

Yana da wuya ka kyala ido da rana kaga dan mama dubu a gida yana shawagi haka kwana bibiyu dan
uwanta zai ziyarci wurin aikin yaran yagano mata halinda yayan nata suke ciki.

Yayin da ita kuma takan ware lokaci da yayan nata da dare suna hira tana jin shakuwar kowansu na
gyara ta gyara masu maikyau kuma ta kara dorasu a hanya madaidaiciya akai goma zasu watsa zuwa
neman wajen kwanciya zata kashe kallo cikon hikima da nisa tana fada masu akwai boko da safe ga zuwa
wajen aiki gara ka kwanta da wuri ka samu natsuwa yafi zaman wanan kallon .

A cikin irin hakan tasan weak point din dukkan diyanta kuma tana tsaye a kansu idan suna dakin nan
zaki dauka yaya da kannentane suke hira a tsakaninsu.

Yar uwa mai karatu idan Allah ya halicceki gidan gadu ma,ana gidan dake da iyali fiye da daya mata
biyu zuwa ukku ko hudu zaki fahinci abinda nake son maki bayani a nan.

Zama a irin gidajen nan zamane mai kama da zaman haya idon kowa na akan danuwa wani bai kaunan
wani da karuwa ko cigaba.

Amma a zahiri zamane zakiga anayi a fili kamar ana kaunan mutum da ciganbanshi sai a badili abin ba
haka yake ba yadda ake nunawa a zahirance.
Mama Dubu ta fahinci haka ta dalilin tsaikon haihuwan da tayi ta fahinci yadda abubuwan suke tafiya a
tsakanin abokan zaman nata ta fahinci wanan akidar sosai ga yayansu.

Za anunawa dakin ana kaunarsa a gabanki amma a bayan ki kamar Allah Allah akeyi yayi wanin abin
magana da kowa zai tofa albarkacin bakinsa a kai gidan yawa kenan .

Irin wanda iyayyen mu ke tara mata fiye da daya zuwa hudu ko wace mace da kalan tarbiyan da zataba
yayanta ko wani daki zakiga shige dabiansu gudane dama hausawa sunce Nono alkalin da.

Don kowani da irin tarbiyan da uwarsa ta bashi zai taso a cikinsa kusan haka wanan abin yake idan ka
bibiya mafi yawa suna tasowane bisa ga irin jajircewan uwa a garesu wanan ke nan.

Mama Dubu yau ta tashi da zuman zuwa gidansu idan nace gidansu ba wai ina nufin gidan iyayyenta
bane a,a gidan da suka gadane ita da yayanta data haifa .

Gidan da suka saida gadonsu suka hada da na wajenta data soma gidana suka mallaki wanan din da
yanzu yaya Jafar yake rayuwa a cikinsa shida mahaifiyar mama Dubu da suke kira da Iya mai mai.

Iya ita ta haifi mama dubu da kawu dauda sai mama dije dake aure a kaduna unguwar sarki sune Allah
ya bar mata a raye amma a baya iya ta haihu basu tsayawa sai ukun nan suka tsaya raye.

Itama iya suna da dan nasu rufin asiri daidai gwargwado saidai ba can can ba auren yaya jafar da zai
tare a gidansa saboda girman gidan sukai shawara da iya ta dawo nan da zama tunda akwai wadattacen
waje a gidan wanan dalilin yasa ta dawo gidan don ta zauna dashi.

Ance a wajen aurensu babban kawarta da tayiwa amaryanshi kawance tunda ta kyala ido taga yaya
Jafar ta daga hankalinta da ita taga miji .

Don bai dace ace wanan hadaden guyen dan bokon irin da take mafalkin aure shine mijin kawarta da
take kamar bagidajiya da ita dai ya dace kuma shi take so .

Ita din yar kadunace don a kuduna iyayyenta suke da zama yayin da ita kuma uwar gidannasa Asmau
mutumiyar Gwambe ce amma mazauna garin zaria aikine ya kawo mahaifinta zaria har yai ginan kansa
zama ya kamasu a garin zaria.

Da farko ance shi yaya Jafar din baya son Nusaiba don yarinyar da ba tsarinsa ba saidai kamar abin
sihiri kuma ya dan soma kulata har abu yai karfi a tsakanisu ta shawo kansa sai zancen aure.

Wata shidene tsakanin aurensa da Asmau dashi da kuma ita a lokacin zancen aurensa da Saiba kamar
yadda nickname dinta yake a wajen kawayenta shi kansa mijin haka yake kiranta da wanan sunan sai ba.

Lokacin farkon komawansa Lagos da harkan business dinsa ne don ya fahinci can akwai harkokin da zai
iya wanda zai hada da nan arewa.

Sai sana,anshi ya karbu sosai dan kudi sun fara shigo masa sosai a lokacin don haka bai samu matsalan
komai ba don bai bukatan taimako a wajen wani.
Haka akasha wanan bukin amare biyu a kusan lokaci guda duk ko da tashin hankalin da uwargida
Asmau tayi kan ba zata zauna da kawar nata ba.

Amma abu da manya kuma tsakanin miji da mata ance sai Allah haka ya shawo kan abinsa manya suka
inmata ta zauna.

Don hakane babu shiri ko zaman lafiya a tsakaninsu ko kadan ita uwargida tana ganin anci amananta
dashi da kawarta.

Yayin da amarya take ganin abinda yai mata kome mutane zasu fada su fada mana ita dai bata damu ba
tunda ta kama mijinta irin yadda take so.

Nusaiba Best friend din Asmau ce sosai saidai wanan kaddaran da Allah ya kawo tsakaninsu ya hanasu
kwantar da hankali su fahinci kaddaran rayuwansu ce hakan.

Na hada miji daya da sunan aure a tsakaninsu zauna suba kansu lafiya a tafi tare zama yayi dadi.

Tun daga wanan lokacin kawance ya watse aka koma zaman kishi kinshin ma irin na hauka din nan
sukeyi a tsakaninsu.

Ga miji ba mai zama baneshi iyaka yazo yayi yan kwanaki ya koma ya barsu nan da iya da itace zasu
zauna har zuwa lokacin daya dawo kuma.

Wani irin zama mai wuyan fasara a tsakanin su suke gudanarwa agidan zama duk da part daya suke
zaune wanda ya kara fadada girmansa lokacin auren Saiba ya mayar masu dashi two two bedroom
babban falo a tsakiya.

Wanda haukan kishi ya saka babu mai tsayawa daga cikinsu ya gyara part din zakice wa yanda basuyi
boko bane a cikin gidan.

Sai in sun fito waje zaki gansu fes dasu kamar ki wanke hannu ki taba sai kinje gidansu ki raina masu ni
dai zee nace har da hali a irin hakan .

Don wani baiyi ba aiba zance ba zanyi ba ko don lafiyata sai idan miji yazone dole mai girki zata tsaya ta
tsabtace mashi falon koshi bawai can ba don kowa na bakin ciki da dan uwansa kada ya gyara dan uwa
ya huta.

Haka kuma bangaren abinci akwai matsala a nan ma din don kuwa idan ba miji ke gari ba haka zasuyi
ta horar da junansu da takaici har sai lokacin daya dawo.

Farkon zuwan saiba taso ace miji ya tafi da ita lagos don ta fadawa yan uwa da abokai ita ba zata yarda
ya barta zaria ba don ba sakarai take irin Asmau ba miji yana lagos ita ta zauna a gida.

Sai bayan ta shigone taso nuna hakan amma uwar miji tace bata kai can ba yadda ta sama sun tsara
abinsu haka zata bi dole shine wanan rawan kan nata ya dan fara lafawa tun lokacin.
Saboda ta fahinci ashe a karkashin iyayyensa yake wanan yasa Asmau dake gabata bata motsa ba take
biye dasu a zauna lafiya.

A cewan mama ba zata bari ya dauki iyali yaje zaman lagos ba don kada ya shagala da dukiyan marayu
dake hannunsa .

Haka zalika zaman shi a can din zai iya dauke masa hankali da gida dudu nawa Jafar din yake inbada
rigima yaushe ma ya isa iya aje mace daya balle yace biyu.

Allah ya taimaka jafar da yan uwansa mutanene dake matukar girmama iyayyensu a yadda suka taso
da tsoron mama da iya kakarsu har girmansu haka suke masu biyayya sau da kafa.

Zaman iya a wani bangare na gidan yayi tasiri sosai a rayuwansu dontane suke rage wani iya shege idan
su fara yanzune iya zata tsaya tayiwa wace bata da gaskiya fes hakan yasa suke dan

2 / 101