Chapter 30 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   30 / 101

87K to 90K   out of 302.2K words

jam,i nayi masu ina wuni muka samu waje muka zauna a gefensu falon yayi shiru bin ko ina nakeyi
da kallo har kasan da nake ganin tun dawowansu bai samu mopping ba kayane a ko ina yasha a falon
wanda nasan aikin yaransune hakan.

Suna da wani hali ko yaro yana barna ba za a tsawata mashi ba haka kuma idan dan wani yayi barna har
inke uwa baki kwashe abin ba a nan zai tabbata wajen.

Ba karamin wahala mukasha wajen gyara falon nasu ba lokacin har ya koma daidai yadda yake son gani
kullum a rayuwansa.

Muryanshi ya dawo dani na dago kai da yake fadin Nafisa kin dai gani ba falon da kukasha gyara shine
ya koma haka saboda na tara jakkai da basu san arziki ba sai tsiya da bakin kishin banza a rayuwansu.

Haba dai daina fadan hakan jafar ke Rahama dazun kun fitane tare da yayan ku da yamma ko shi ya
daukoki daga bokon da kikaje ?

Kallon ido da ido nayiwa mama din cikin mamaki ina fadin wani yaya ciki mama ni kadai nake zuwa in
dawo yauma aida Aisha muka dawo ita ta bani lift a motan gidansu da akaje dauko ta.

Ina kikaga yayan ku nace nan gida zan shiga part din mu yadda Saiba ta gyara zama irin bata yarda din
nan ba yasa na yi shiru.

Ya taba daukan ki ko yakai ki wani wajene bayan haka dakata mama ina da number Aisha din bata
gidan Alh wada din nan ba sai ta kira layin Aisha din.

Wai ke dama kina nan yau ai nake ji wajen kanwarku din nan dazun na ganta a hanya tana jiran mota
na rage mata hanya kinsan yarinyar bata da sakin fuska.

Aita fada min dazun din shine na kira inyi maki godiya haba dai akan wanan wallahi salima baki da kirki
ko kadan kizo ga gida ga gida ki kasa shigowa ?

Bari zan kiraki anjima don Allah ta fada tana kashe wayan ta kallo kowa dake saurarensu tana fadin kun
daiji yanzu ai.

Kinji ko mama kinji da kunnen ki wa yan nan jakkan suna son bata wa yarinyan nan suna a banza to bari
kuji wallahi.

Jafar dakata iya ta fada yau koka dauki Rahama a motanka laifine hakan nace laifine a garinku ?

Wai meyasa samun waje yake son zama iskanci bari kuji in fada maku Jafaru dai namijine mata hudu
Allah ya halasta mashi yi akansa.

Ashe kuwa matukar hakan Allah ya yarde masa ku din nan baku isa kuce sai yadda kukeso zaiyi ba a
rayuwansa .

Ba a kallon mata ke Nusaiba kika kutso cikin rayuwansu da danyen aurensu kika saka saida ya auroki
gidan nan aka kawoki don bakin ciki kada abuyarki taci bakici ba.
Dariya anty salima keyi nasan hakan ya bata haushi ta soma magana tana fadin ai gashinan iya ki
tambayeshi idan nina kutso kaina bashi yace yana sona ba ?

Ke rufa min baki har yaushe na taba ganinki nace ina sonki Nusaiba bayan wasikun batanci da kike
rubuto min kina bata kawarki wajena ?

Har kikayi nasaran hada baki da abokina kuka,,,,,,

Jin irin tonon asirin da yake mata a gaban kowa yasa tayi saurin katseshi da fada tana fadin bayan duk
bina da kayi a yanzu zakayi min sheri.

Ya isa haka don Allah wanan kanku kuke tonawa asiri bayan abinda ya wuce koma meye yanzu ai kun
zama daya a tsakaninku don haka ki koyi hakkuri da zaman tare.

Kinzo kina zargin mijiki da yarinyar nan yau idan Jafaru yace zai auri yarinyar nan ke kin isa ki hana
hakan tunda ke ba,a hanaki ba ?

Tun zuwan yarinyar nan da yar uwarta gidan nan kuka dauki kiyayya da hassada kuka dorawa yaran nan
don mijinsu yana da dubaiyane aksn dan uwansa da ankai ga yadda kukeso .

Ki duba yanzu bai ko sanda shigowan yarinyar nan ba amma kince wai tare sukazo gidan nan da ita ya
sauketa a waje.

Ni kuma na fada a cikin mamaki kwarai kuwa abinda suka fada ke nan cewa tare muka shigo dake na
saukeki a waje saidaga baya na shigo gidan hakan bai mun ba kuma na dakatar dake muna magana.

Tace ko a bayansu ina kwance ina jinya abinda mukeyi ke nan dake dama sai Saiba tace ai muma ji
mukayi cewa komai itace ke maka ita da Nafisa .

Ba ance bane kwarai sukeyi min komai ko yanzu ma a gaban ku su din ne dai zasuyi min kome nake so
wace zata zauna ta zauna wace bata iyawa kuma ga hanya nan sai ta tafi.

Kaina na sada kasa abinda yar uwata dai take zargi ya tabbata ke nan a kaina yanzu sai muryan saiban
naji tana fadin .

Ko sunyi fa sai me in zaka iya sweety ka aureta kaga wa hakan zai dama ?

A zabure ya harzuko mata yana fadin haka kikace ko tace an fada din inka isa ka aureta mugani ko ba
nufinka ba ke nan ?

Wanda ya fada muna in bai gani ba zaiyi karyane nan suke ma komai ai wa,,,,,

Ke yarinyar nan baki da kunya yanzu ke don Allah bai zuba maki kunya a idonko ba mijin da kika
kyamata a gaban mu zaki dawo yanzu kice kina fada a kansa ?

Nan fa kuka nuna kuna kyamarsa don ciwon da Allah ya jarabeshi dashi don baki da kunya ko kadan
yanzu kin dawo kina fadin wanan zancen banza haka don samun waje.
Mikewa nayi duk suka bini da kallo falon ban tsaya jin nauyi kowa ba na fice daga dakin kai tsaye zuwa
part din mu na samu maria ta idar da sallah take fadin yanzun nake fadin in biki ai.

Sai gaki tun dazun wayan ki keta ringing ba tare danayi magana ba na shige dakin na dauki wayan Sa,id
ne ke faman kiran layina saurayin daya lake min saidai a ganina ba a yarda in tsaya dashi ba zasuce
yarone don yadda naga sunyiwa anty Salima shiyasa ban damu da kulashi ba.

Sai kuma ga kiran anty Salma ya shigo wayan na daga ina mata sallama ya kuma najiki a wani mood ko
baki da lafiyane ?

Lafiyata lau anty kawai dai sai nayi shiru meya faru ta sake tambayana sai naji kawai in fada mata ko
zanji sanyi a raina ko kadan ne.

Wallahi anty Salma sha,anin gidan nan ya isheni matan yayan ya habu sun saka min ido suna kokarin
bata min suna ga abinda bashi ba.

Cool down Ramaah kiyi min bayani yadda zan fahinta nan na kwashe komai na fada mata Maria tana
tsaye tana saurarena saida taji anty salma ta soma magana da bataji ta juya ta fita daga dakin.

Anty salma ke cewa da zaran kun gama exam dinki ki taho nan kiyi hutunki ki kyalesu can yan iskan
mata kawai na bata amsa da mungama yau ai.

Shine suka tareki da bacin rai ga gajiyan exam a tare dake goben nan zan turo a daukeki har gida ki
shiri ba maria waya muyi magana .

Hakan yasa na mike zuwa falo bata nan na duba dakinta nan ma bata nan sai na leka waje naji hayaniya
yana tashi a wajen.

Nacewa Salma ina zuwa na kashe wayan nabi bayan ta daidai da zan shiga naga mama ta sakota gaba
tana fadin tayi hakkuri suma sun fadane don batanci amma ai fadan ya koma masu ciki yanzu don
matakin da jafar din ya dauka.

Ranan kan sunsan sun taba mata yar uwa don tayi masu abinda basu taba zato ba ta zagesu tas dama
ance kunne ya girmi kaka ina jin muryan saiba daga cikin part dinsu tana fadin idan ta isa tasa a yau din
nan a dauki mataki a kansu din idan habun ya dawo.

Ranan dai da bacin rai kusan kowa a gidan ya kwana da safe nake fada mata Abuja nayi wurin anty
salma inyi hutuna a can din.

Bata koce mijin ta aibai gari ba yadda ta saba tauyeni shi kuma idan ya dawo yake hanawa sai cewa
tayi hakan ma yafi.

Sai can nace kuma kada in tafi na barku daga ke sai Abba ku kadai a cikinsu tace ki tafi ba abinda zasuyi
min ki daga ki basu waje kawai zaifi sauki har a kwana biyu.

Karfe daya da yan mintuna muna hanya ban tsaya sallama da kowa na gidan ba sai Nafisa data shigo
taga ina shiri nake fadawa Abuja zan tafi ranan.
Sai ga mama ta shigo tana tambaya yanzu maria kan wanan zancen da akayi ya wuce zaki tura yar nan
Abuja tayi murmushi tana fadin badon shi bane mama dama tana da niyar zuwa tayi masu hutu a can.

Yanzu haka driver da zai dauketa yana hanya tafe takai zaune tana fadin koda zata tafi ba dai yau ba
kan zancen nan dai ya kawo wanan tafiyan shi Habu ya sanda zancen tafiyan natane yau ?

Zan kirashi a waya mama dama yasan zata tafi ai ummah ma tace ta tafi din tace to shike nan Allah ya
sauwaka ina daki ina jinsu sai mamakin hali irin na mama na sanyi hali nakeyi.

Barma dawowan su din nan abin nata kamar ya sukurkuce ne gabadaya kardai abinda suke fada kan
suna shige shige gaskiyane hakan ?

Koma dai meye sun samu waje da yawa ni dai har tagama ta fita ban leko ba kuma ba a jima ba driver
da anty salma ta sheda muna ya taso tun bakwai na safe ya iso daukana din sai da aka gama saka kaya a
mota anty maria ta matsa min nashiga na sallami su mama na fito muka dauki hanya.

Karfe hudu da wani abu muna Abuja don mun tsaya kaduna mun karbi sako na kuma shiga nayiwa
ummah sallama na tafi.

Tunda aka shiga min da kayana nashiga nayi sallah ban fito ba ina daki don har lokacin ina jin zuciyana
a cunkushe abinci ma nan anty salma tasa aka biyoni dashi ta fita ta barni da yaranta zuwa asibiti duba
wata kawarta.

Wa jajen karfe biyar maria ta bugo take tambayana mun sauka lafiya na amsa da lafiya yaya na barsu
kuma tace lafiya kalau ga Abbati yana kewana.

Nace a bashi waya yana jin muryana yasa kuka nake lalashin shi a waya ina mashi waka nan uwar ta
karbi waya tana fadin ai habu ya kira yana fada wai meyasa na tafi ban bari ya dawo ba.

A raina nace tunda ubana yake ba amma a fili cewa nayi da ita dana bari ya dawo ba zai yarda in zo ba
yanzu ko gani hankalina kwance saidai kewan su don ba karamin shakuwane tsakanin muba da ita.

Shigowan anty salma dakin yasa mu dakatar da maganan ta karbi wayan suka danyi sharfi akan zancen
na wani dan lokaci.

Bayan sun gama take fadin wallahi sunyi arziki ba a gari daya muke ba da sunga tsiya don sai nayi
karansu wallahi.

A bakin iya yake jin tafiyana Abuja din daya shigo take fadin ina kashiga yau Jafaru yake fadin ina can
kofan gidan mu iya da abokaina .

Nikan nace da kana gida ba zaka bari yarinyar nan ta tafi ba ban zaton zasu barta ta dawo gidan nan
kuma don wanan sherin na matanka Jafaru.

Wace yarinya iya ?
Yarinyar nan me take da suna Nafisa dake zaune take fadin wai Ramaah take nufi fa sunan ma ta kasa
fada kullum sai an tuna mata sunan .

Ina taje Nafisa tace Abuja dazun aka aiko da mota aka dauketa daga can yanzu kan ai ta tsufa Abuja ita
kan saiga salima ta fito daga dakinsu tace .

Nifa banga laifinsu ba gara data gusa ta basu waje wanan zargin ya kare hakana haba don Allah wanan
iskancin har ina don Allah ku dauki kishin yar uwarta ku yabawa yarinya bataci ba bata sha ba don Allah
dai.

Humm, kawai yace ya mike tsaye yana fadin iya zan fita me zan sayo maki yau iya ?

Jafar kaji saukin fitane irin haka naga dare ya soma yi a yanzu kardai don shedanun matan nan naka
zaka tsiri fitan yamma haka ?

Bai bata amsa ba ya fice daga gidan motarshi ya nufa ya shiga ya zauna maigadi ya bude mashi lokacin
ya ciro waya yana neman number waya.

Nidai ina waje tare da anty salma ya kira harya katse ban dauka ba lokacin dana dawo kuma ban koma
takan wayan ba nayi sallolina na kwanta.

Washegari tunda safe ya fito a cikin shirinsa ya nufi wajen su mama ya samu suna azzakar din safiya ya
gaidasu yana fadin zai danje kaduna kila ya isa har katsina saidai yadda hali yayi sunganshi .

Haka ya bar zaria zuwa Abuja don shi kadai yasan yadda ya kwana cikin bacin rai ya kulla wanan ya
kwance ko iyalinsa sai a bakin kannesa suke jin baya garin.

Sam bai manta da gidan anty salma ba direct ya dira gidan ya dan jima a kofa yana kiran waya ba a
dauka ba yasa ya fito yayi sallama.

Daga cikin masu aikin gidan wani ya shigo yana fadin wai anawa Anty Rahama sallama daga zaria
bakuwar data zo jiya.




ZAINANB IDRIS MAKAWA[2/1, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,



3️⃣2️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Kallon juna mukayi da anty din don zaune muke muna karyawa muna dan taba hira da ita wanda hiran
exam dina nake bata tana dariya.

Shine wanan mai aikin ya shigo yana fadin sakon daga zaria je kace waye yake sallama da ita ?

Ya juya ya tafi ita kuma tace kin fadawa wani zakizo nan ne na girgiza kai ina fadin banda yan gidan mu
ban fadawa kowa ba.

Suma kuma sai yau din nan suka san da zancen tafiyana ai da zan wuto kila dai ba daga can bane kodai
kuma mijin anty Maria ne amma shi yana bauchi akace.

Saiga dan sakon ya shigo yana fadin yace nace dake yayankine Jafar na gidan ku can zaria din wanan
yasa na mike ina fadin ya J kuma meya kawoshi kuma ?

Wanan me mata din na anty salma ta tambaya kai na iya gyada mata don bansan me zance ba ta dan
tsuke fuska tana fadin je kace ance ya shigo.

Yana zaune yana waya Isah ya sameshi a mota yake fada mashi ance ya shigo daga ciki jin hakan hakan
yasa ya dan kalli Isah din dake fada mai sakon ciki mamaki yana fadin maigidan yana nan ne ?
Baya kasan hjy ce da kadai sai yan aiki a ciki dan jim yayi kamar yana tunane kafin ya bude motan ya
fito da kafansa daya ya tsaya gyara yanayinsa.

Ya fito wanan isah din yayi mashi iso har zuwa falon na anty lokacin mun bar falon don tace dani tashi
kije ki kimtsa yasan akwai banci da nan da can da basu daukeki da daraja ba.

Idan basu kaunan ku mu muna kaunan ku tunda munsan darajan ku munsan kuma muhinmancin ku a
rayuwan mu.

Hakan yasa na mike zuwa daki na dan sauya kayan jikina din kamar yadda tace na fito fes dani sai
kamshi nakeyi da daukan ido bakina na asalin fulanin mu na Cameroon ya kara baiyana sai golden eyes
dina da samansu yake kamar ansaka min eyelashes garza garza dasu suka kara min ma,ana tsayina yasa
ban saka takalma mai tsini a kafana sai yan ma daidaita haka.

Yana tsaye cikin falon ba tare daya zauna ba ya juya baya yana kallon kofan shigowa daga falon kamar
me tunane yana shakan kamshin da falon keyi a lokacin ga komai na falon white tsab dashi kamar ba
mahalukin dake rayuwa a cikinsa saboda tsabtan wajen.

Haka na fito na sameshi a tsaye na danja na tsaya ina kare mashi kallo duk daya ban baya amma ba
zakice shine a yan kwanakin da suka shude yake cikin bautan Allah haka ba.

Yar siririyar sallama nayi ina karasowa ciki hakan yasa ya juyo gareni ya zuba min idanuwanshi da har
sukasa tafiyana ya fara hardewa lokaci guda saboda tsarguwa da irin kallon da yake min din.

A hankali nace ka zauna mana yaya ai anty tana daga ciki ya dan kalli inda kujerun suke ya nufa ya
zauna a daya yana fadin nagode fuskanshi har lokacin dauke da damuwa a cikinsa.

Tiren dake hannuna na dire tare da jawo dan side table din zuwa gabanshi na durkusa a gabanshi na
balle murfin goran na fara tsiyaya mashi ruwa a cikin tumbulan glass mai kyau da tsada.

Ya miko hannu ya amsa tare da fadin thanks lokacin na mike can nesa dashi na zauna a darare ya zuke
ruwan yana aje glass cup din ya sauke ajiyan zuciya.

Idon da ya tsura min na wasu yan lokaci hakan yasa na dukar da kaina kasa cikin jin nauyin shi yadda ya
kura min ido din a lokacin.

Akwai damuwa sosai a yadda na kula da irin kallon da yake min din a lokacin don yanayin annurin nan
nasa da babushi shimfide a fuskansa lokacin.

Har tsawon wani dan lokaci muna zaune a hakan ganin wanan yanayin yasa na zamo saman kujeran
nakai zaune kasa ina mai sada kaina.

Ganin hakan yasa ya soma magana a cikin murya mai taushi kamar ansa shi dole ya furta ya soma fadin
Rahama meyasa kika taho Abuja kika zauna ?

Me zaisa ki bar gida ki dawo nan ba tare da sanin mu ba kina ganin hakan da kukayi ke da maria kun
muna adalci ke nan ga amanan ku da aka bamu riko ?
Fuska na dago na dago da hanzari na dan kallesa yace yes amana kuke a wajen mu don hardo bai boye
muna komai game da kuba ya kuma roke mu da mu rike masaku amana kuma mun karbi hakan.

Sosai naji hankalina ya tashi ga kalaman nasa dayace sunyi alkawari da hardo akan mu don nasan
hardo zai iya hakan don yadda

30 / 101