Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
nadi cikin buhun irin na da da ake amfani dashi sai
wasu kwanduna da aka rufe da ganye zakice gorone a cikinsa aka rufe ta shiga budewa .
Yayin da iya da su Habu din suke hiran yanayin kasan Cameron da irin mutanen dake rayuwa a cikinsa
muyan mama dubu sukaji tana cewa Habu wanan ai ba karamin kaya bane ka dauko ?
Meye a ciki mama Jafar ya tambaya yana mikewa mama ta juyo tana fadin wallahi nono ne da danyan
madara wanan kuma kindarmo wanan wara da ake kirada (wagashi ) warar fulanice ta ainihi da aka sani
da ainihin nonon kindarmo za,aita dafashi har ya cure a waje daya kana a dauko buhu ko abin tsama a
matseshi yadda akeson girmansa saidai nasan akwai sauran fasahan wanan abin da ban fada ba a bayani
amma dai nonoce zalla ta kindarmo sabon tatsowa ake wanan wari din dashi wanda akecinsa danyensa
ko kuma a yanyankashi kamar nama a sayo da mangyada ko manja.
Shi wanan abin yanzu soyashi za ayi Jafar ya tambaya mama Dubu tace kwarai kuwa sai kace a karo
maka idan an soya din ai ana amfani dashine kamar nama zaka iya zubawa a cikin miya a dafa miyar
dashi ko kuma ka watsa saman shimkafa kamar nama.
Ban taba ganinsa ba Jafar din ya fada nima dai gaskiya bansanshi ba Yaya J , kawai dai naga ana sayane
nace nima aban na sayo wasu mama mashi nazo dashi.
Mama Dubu dince ta katse su da fadin wanan kuma chikwi nefa Habu sai ta mike tsaye tana fadin
amma kasha kudi a wajen nan bari nazo na dibawa yan gida akai masushi a mutuncinsa tun bai tabu ba
don in suka kai kwanakin da zanyi a nan suna iya lalacewa.
Kallon juna diyan nata sukayi wanda ta fahinci nufinsu tace meye duniya Malam idan kaba wani ya kare
idan baka bayar bama karewa zaiyi gara ka bayar din kaci moriyansa can inda bakai tsamani.
Ai bamuce komai ba mama zuwa anji zan shiga na gaidasu da yamma sai a zuba na fita masu dashi don
naga shi Habu kamar da sauran gajiya a tare dashi.
Duk wanan nono shanune a cikinsa ya nuna sauran jarkan dake rufe mama din tace ina gani tana kallon
danta habu ko zai masu bayani maimako ya bada amsa sai ya juya ya koma saman kujera a daidai lokacin
mama ke fadin ikon Allah man,shanune haka cike har jarka.
Kai habu wanan lissafin dariruwan kudi akeyi fa ina kasamo wanan kaya haka kamar na gara Iya ta fada
tana mikewa zuwa wajen taga man shanun da aka fada din.
Sai fadi take saidai wani lokacin suyan manshanun fulani kamae harace don basu irin suyan mu na
mutane gari a saka albasa da gishiri don yayi kamshi haka suke soya abinsu ba komai a cikinsa.
Kada kisha idan bai hadu ba Habu kai kaji iya tun bataci ba fara kushe abin murmushi yayi kafin can
yace ba manshanu ba ai har mai man shanun zan dauko maki gidan idan ta girka ta baki kada kici tunda
basu iya suya ba.
Au to kinji abinda ya fada shidai ke nan bafulatanan kasan can da sukaje zai auro sai ki shirya Iya kishi
da balatana kuma yanzu.
Barni a Iyata da nake yayan hauawan ma gasu gaban mu na kasa gane kansu yara kamar kansu aka fara
kishi yara kanana da bakin kishin tsiya irin ta hauka.
Ai ba dukansu bane basu da hali iya habu ya fada don gara Asmau ita tasan darajan kowa batawa
mutane rashin mutunci ita.
Babu gara kana ina suka watsawa uwarku abinci saman jiki ga hijjabin can ta jika yaki fita har yau don
iya shige irin nasu .
Abinci kuma suka watsawa mama a jikin garin ya haka ya faru mama kai ya jafar wani mataki ka dauka
akai yanzu ?
Shine nan ka ganni zaune ina son iya tayi min bayanin abindake faruwane sai gaka ka shigo aka kawar
da zancen da muka soma.
Ai bada sani hakan ya faru ba nan dai mama ta kwashe yadda abin ya faru wanda ta sani ta mayar
masu ran yayan nata ya baci sosai da hakan tunda Abubakar yafi daukan zafi akan zancen.
Ya dago kai yace mama shine kuma kike cewa a kyalesu har su iya wanan abin kuma a saka masu ido
gobe su kara wanda yafi wanan ke nan ko idan an kyalesu.
Kaiya ita wanan mai shigar cikin bafa laifinta bane na fada maku yadda zancen yake ya juya wajen dan
uwan nasa yace kai kaji bros ya lumshe idanunsa don baida abinda zaice kuma tunda mama ta hanashi
daukan mataki akai tace rashin sanine ya jawo hakan yayi hakkuri da matanshi ya dai tsawata masu kan
hakan.
Gaba daya falon yai shiru saiga Asmau tashigo da sallamanta ganisu haka a zaune yasata dan tsarguwa
tana kuma mamakin ganin har Habu da bai faye zama dasu ba yau duk suna tare hat dashi.
Sun dai amsa mata gaisuwan saidai ta tsargu duk da wancan kaifin ita bata sashi a zuciyarta ya tsaya
mata tunda ba itace tayi laifin take gani.
Sai bayan ta gama gaidsune ta dubi mijin nasu tana fadin yaya J an gama breakfast don haka ta taso
ana ce masa a cikin unguwa kaf manya suce dashi malam din gidan Sanda .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Lokacin da Ya J ya fitar da nasa tsaraban kai tsaye part din Iya yace Abubakar ya kai mashi a can wanan
yana daga cikin sallon horon da yake son yi masu a mumuke .
Bai tsaya ya karya kamar yadda Asmau ta bukataba gareshi wanka yashiga har yafito duk a cikin
kyankyami yake haka ya shirya a cikin wani yadi fari na maza dayasha dinki kayan sun matukar karban
jikinshi sosai ga ogogonsa daka kalla kasan bana ranke ranke bane.
Haka takalman kafansa baki masu dan igiya daga baya amma ya taushe igiyan da dudugenshi ma,ana
bai kaunan saka belt din takalman ke nan a lokacin.
Turarensa ya dauko ya fesa a jiki abinka ga farin mutum nan kyauwonsa na asali dake rudin jama,a ga
kuma jin dadin da jikin nasa ya nuna tare da wayewa sai hakan ya taru ya karawa jikin nasa ma,ana sosai.
Duk cikin yaran mama Dubu ya jafar yafisu haske sosai duk da kaf diyanta fararene masu matukar kyau
sosai sun biyo sashen mahaifinsu da yake shima farin bufulatanine daya bar gida tunda karanta don
mutumin yolane zama ya kawosu Zaria shida iyayyensa amma komai nasu yanzu a cikin zaria suke
rayuwansu da komai don yan bayama basu san gida ba.
Part din Iya ya nufa inda ya samu mama tana kwashe dan abincin ranan data dafa masu yayi sallama ya
shigo yana gaidasu da aiki nan yake fada mata zai fita yakai wankin mota ya kuma leka kawu dauda don
sun shaku sosai da kawun nasa.
Kusan duk wani motsin Jafar kawu dauda yasanshi shiya rike a matsayin mahaifi tun ma mahaifinsu
yana raye kafin ya rasu.
Cikin jin dadi mama take fadin ashe bari a bada tsarabansu saika mika masu daga can yace yayi mama
yana zama yake fadin akawo nasu umma na mika masu don har can nake son shiga in gaidasu.
Ka kyauta malam abinda zance ke nan ka rigani Allah yai maku albarka ta juya don taje dauko mashi
sakon kafin ta juyo tana fadin ina ai matan naka sun gama abinci wajensu ko ?
Sam baiji dadin zancen ba amma haka ya daure yace cikin bata fuska mama su ai basu gaj gama abinci
da wuri ba banma jin sun dora yanzu gaskiya.
Ikon Allah wanan waani irin sakacine da yaran nan miji da ake murnan zuwanshi amma su sam ba
hankalin gane haka ai wanan shine kishi na asali ba wanan haukan da sukeyi ba.
Yanzu sai ka dawo kaci ke nan yace ko karyawa banyi ba mama saidai idan na fita zan tsaya wani shago
nan gaba kadan in karya.
Sam malam ba mutuncika bane kana da mata biyu ka koma cin abincin layi wanan zubar da kimar
namijine da matansa bari dai inzaka iya cin namu na zubo ma ka dan hada da ruwa.
Murmushi ya sake a fuskansa daidai lokacin Habu zai shigo part din don shima fita zaiyi to ga sadauki
nan sai in diba maku kuci gaba dayan ku ta wuce zuwa kitchen din kai tsaye.
Abunci ta zubo masu plate biyu shimkafa da miya da ganyen kabeji yaji hadi sosai sai nama yanka
bibiyu a cikin ko wani plate ta direwa kowa a gabansa.
Yaso ya basar amma aiya muda ya busar da iska yana fadin yaya naga plate biyu mama matansa fa
basu ciyar dashi bane halan ?
Yayi kamar baiji mai dan uwan nasa ke fadi ba sai wayan shi dayake faman dakila cikin basarwa kafin
ya aje yana jawo plate din abincin zuwa gabanshi.
Mama Dubu data dawo dauke da goran kunun ayya sai ledan pure water ta aje Habu ya dago yana
fadin is not right mama yana da mata a cikin gidan nan yazo nan kuma yana ci muna abincin mu.
Murmushi mama din tayi kafin takai zaune tana fadin Habu dole ya kama in bashi son da yafita yana
tonawa kansa asiri yaje saye shago gara kawai in diba mashi yaci a nan din.
Duk zancen da sukeyi Jafar sai aika abincinsa yake a cikinsa Abubakar din ya dan kalleshi ya jawo plate
dinsa shima ya soma ci kafin can ya dago yace.
Cikin gari kayi ina son nima zan fita ka saukeni saiga iya ta fito daga daki tayi wanka ta sauya tufafi
yadda takeyi idan mama tana gidan tare dasu ka,idace wanka a rana gareta .
Habu ai gara ka bari yaci abincinsa a nan kada yunwa ya illantashi nima tsohuwa ba iya cin abincin
yaran nan nakeyi ba balleshi matashi haka da harshensa yake da kaifi a yanzu.
Amma iya gaskiya ba zasuji dadi hakan ba idan sungani shiya kamata ya tsawata masu koma meye su
gyara amma haka gaskiya bai dace ba karshema zasu iya dora laifinne ga mama.
Kamar yadda kace din ya kara tsawata masu dai hakan yana da kyau amma wa yan nan shedanun ba
kan gadone dasu ba balle su gyara din.
Tsuki Abubakar da takaici ya kumshi yaja goran kunnun ayya Jafar ya mika hannunsa ya dauko ya kafa
baki ya korawa cikinsa kaf ya aje yana gyara zama yace.
Ita Asmau ki barta da kazanta da saurin fushi yanzu haka dakinta wallahi iya baya shakuwa don kazanta
kayane ako ina watse a dakin kamar wata wace ta tara yara goma.
Itako Nusaiba aikinma bata san kansa ba barta kawai da in za a fita sai kice zakizo gidanta ki samu abin
kwarai duk babu mai tsaba a cikinsu ga rashin kunya kamar tashin tasha bakinta ko yaushe baya gajiya.
Nayi mamakin hada kawancesu da Asmau don ita ba yawan son maganane da ita ba amma ta iya zama
da ita haka da wanan rayuwan na banza.
Sam ban taba zaton haka rayuwanta yake ba harna yarda na fada tarkonta dariya sosai Abubakar ya
kwashe dashi jin abinda dan uwan nasa ya fada inda sabo ya saba da halin Abubukar na kyata don a haka
suka taso dashi.
Daga can kusurwan kitchen mama ke fadin ina aika diban ma matanka nasu tsaraban ko kada azo a
kwshe a nan ?
Kafin yai magana Iya tace zai shigo dashi baikai masu nasu bane ai baya kawo nan baki daya yakan fitar
masu da nasu tuncan hakan yasa taci gaba da fitarwa kawu dauda da abokan zamanta indai ankai can su
raba a tsakaninsu .
Saida ya mike yake fadin gari iya na sawowa shi don kune masu son jan garin kwaki da manja aina gani
malam saida nayi tunanen hakan Allah yayi albarka amma wanan ai yayiwa Iya yawa bari a dibawa
mutane suma susa albarka.
Baiyi magana ba don ko yayi tunda mama tayi niyar hakan saita diba din donshine basu tsaya bata
bakinsu ba ta fitar da wanda zaikai gidansu dana gidan kawu din Abubakar ya tayashi kwasa zuwa cikon
mota saida suka cika mota fam suka tafi.
Gidansu ya fara tsayawa aka sauke kayan zuwa cikin gida kafin su shiga don gaida mutanen gidan
shigansu Abubakar ya kalli part din mahaifiyarsu dan kwana biyun da tayi wajen yai kura an rasa wanda
zai share mata shi don mugun hali irin na dan Adam.
Da ace mama mutuwa tayi ashe gidan ma ba zai basu sha,awan shigowa bake nan kilama wanine zai
gaje wajen ya zauna aci albarkacinsu.
A gurguje aka gaisa suna masu sannu da hanya tare da godiya kan tsaraban da aka kawo din agaida
mama da dai sauransu.
Basu tsaya ba sukai sallama suka fice daga gidan kai tsaye suna fita inna ta kalli yar uwar zamanta tace
mena fada maku yaya indai yayan Jushuce sai ta aiko muna dako kwarane a gidan nan yanzu ji wanan
kaya don Allah haka.
Tsuki mama taja tana fadin meye a cikin ledojin nan sabira bude muga abinda ke ciki inda kowa na
gidan ya fito ya tsaya ganin abin arzikin da aka shigo dashi din don basu yarda a shiga ciki dashi don
gudun rage masu kwantiti dinsa da suka san za a iya hakan don an sabayi masu hakan kuma ba daman
suyi magana a kai.
Mama duba wanan abin ta fada bayan ta bude ledan inna takai ido ta kalla tace nasan wanan sai yayan
jushu ita kadai takai can a gidan nan.
Kaico waike karima baki kishin kankine wanan katobara haka da nuna zalama a filin Allah kamar wata
mayunwaciya dake ?
Nidana nuna a fili za,acewa hakan ba amma kowa anan ai yana so don ban taba ganin wanda akabawa
ya marya ba a cikin mu.
Nidai don Allah ku bari sabira ta fada cikin dan hasala ga iyayyen nata dake son nuna halinsu fadane
akulum sai anyisa kuma a shirya haka ake zaune a gidan tsakaninsu.
Mama Dubuce yana da wuya kaji harshenta a cikinsu tunko mijin nasu yana a raye kafin ya kwanta
dama haka halinta yake ita bata son yawan hayaniya .
Sunyi mamaki kwarai da irin abinda mama Dubu ta aiko masu dashi nan gidansu su raba ke nan yana
can gidansu baja baja ke nan tunda har ta iya basu haka ?
Kai tsaye ya Jafar motarsa yabada wanki a nan kasan unguwarsu ya hau mashin zuwa gidan kawu
Dauda da sakon tsarabanshi cikin buhu.
Ya samu baba din ya fito zai fita ganinsa hakan ya dakata yana fadin malam kaine tafe yaushe garin ?
Yace jiya da dare kawu yana fada yana kokarin dauko buhun da mama ta bashi ya shiga masu dashi
cikin gida kai tsaye nan suka tsaya gaisawa da matarshi tana mashi yaushe gari ?
Sai bayab sun gama gaisawa yake fadin mama tace a shigo da wanan au ka biya ta gidanta ke nan kawu
ya tambaya yace tana wajen iya ai.
Kace tayi tataki zuwa kwasan lada nimafa yau nake zancen naje nagonasu na kwana biyu ban lakasu ba
kawu ya fada ya kara da yaya wajen iyalin naka suna lafiya Jafar ya bashi amsa.
Fita sukayi tare da kawu din dake tambayanshi baizo da mota bane wanan karon yace nazo da ita kawu
tana wajen waki nakaita can tudun wanda.
Ai hakanma na dakyau wuri suka samu suka tsaya daga kofa kawu din ke fadin naga kamar kazo da
magana a bakinka ?
Yadan kara rankwafawa kafin ya fuskaci kawu yana fadin nazo dashi kawu shawara nazo nema akan
wani harka da nake son fadawa shine nace barin nemi shawaranka muji indan hakan zai yuyu ?
Nan ya kwashe yadda sukayi da Meiambe ya fadawa kawu din shiru kawu yayi inda Jafar din yaga yana
kokarin tsugunawa kasa shima yabi sahunsa suka kai kasa din.
Can yanisa yace tau malam Jafar bakin wanan abin ba son hanyar karuwace saidai ina tsoron harkan
kudi a yanzu .
Don rikon amana haka abune dake son taka tsantsan duk da banda shamakin hakan a kan Jafar saboda
kai ko ince har yan uwanka kuna da natsuwan zuciya sosai kan duniya don gwargwado kuna da kamun
kai har yau Allah ya tsare ya kara karewa babu dan daya taba dauko muna magana a cikin ku.
Don haka Jafar ba zanki shawaranka ba tunda hanyace ta samu amma shawaran da zan baka shine
kafin muyi komai ya kama mu binciki idan ba wani matsala ka bari zanje gidan yaya sale na kusfa na fada
mai a roka muna Allah a cikin lamarin .
Saida Jafar din ya sauke ajiyan zuciya kafin ya karawa Kawu haske akan yadda abin zai gudana da kuma
irin yadda yake so shima a ta bangarenshi abin ya kasance kawu yace ya fahinta insha Allahu zaiyiwa
yayansa magana zaiji komai da yardan Allah kafin ya tafi da haka suka rabu da kawu din kowa ya kama
gabansa.
Suna fita daga cikin gidan nasu ya kama fabanshi yafi ganewa wanan unguwan daya taso a cikinsa don
ana kowa nasu yake wancen wajen a yanzu ya zama kamar sabon wajene garesu.
Abubakar din shagon sanusi ya nufa sukai daidai da sanusi din yana shagon nasa ta sayar da waya a
kofa ya tsaya bai shiga daga ciki ba duk da ya saba shiga din amma a yau daga kofa ya tsaye.
Sanusi yaji dadin ganinsa sosai sai faman washe baki yake yana fadin kai mutumina kace min har kun
dawo ashe tafiyan bamai jimawa bace dama ?
Tafawa sukayi suka soma hiran bayan rabo inda shi sanusi din ke bashi labarin abinda ya faru cikin
unguwa sai yaga hankalin Abubakar din baya tare dashi lokacin sai waya hannunsa dayake faman
dannawa hankalinsa ya dauke dashi.
Yasan halin abokin nasa don haka ya bashi lokaci tun safe yake faman kiran layin ta amma baya shiga
sai kuma hakan ya daga mai hankali a zatonsa