Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
irin namu na mata game da zaman takewan mu.
Alhamdullahi kuma don ance Allah maji rokon bawane duk da abin dai sai a hankali idan ya kwanto
zuciyana ina danjin wani abin lokacin da sauri kuma Allah zai tamakeni abin ya gushe min a kasan raina.
Don haka tunane na farayi da me zanje idan zani barka don dole dai inje mata barka kuma zai kasance
zuwana na farko tunda na auri ya J wanan zuwan zanga irin tarbon da zan samu daga kowa dake gidan.
Bayan mun dawo gida na bude akwatin turamena na dauko wani zani daya dan burgini a ciki na aje
saman gado niyata na kara bude na kayan kamshi in hada mata dashi inkai masu .
Muna kitchen nida biba ne ya shigo har kitchen da ya same mu muka shiga gaidashi da wuni yana
amsawa nake tambayashi maijego yace suna lafiya.
Na karayi mashi barka da arziki yayi godiya ya juya zuwa falo ya zauna a nan na sameshi nakai zaune a
kusa dashi yace a gajiye nake sosai yau banjin zan kara fita a yau da sauri na juya na kalloshi don nasan
ba gidana yake ba da zaice hakan ?
Ban gama mamaki ba ya kara fadin hada min ruwan wanka masu zafi in gasa jikina dana dawo sallah
naci abinci inbdan kwanta in huta.
Sam jiya bam samu barci ba muna asibiti saida ta haihune kusan asuba na samu na dawo gida ban
kuma yi barci ba aka kira sallah na fito haka mutane ke shigowa suna muna barka da arziki.
Tsam na mike zuwa hada mashi ruwan wankan dayace sai dai zuciyata a cunkushe don na kasa fahintar
manufan hakan.
Saidai ban sani ba ko zai kintsa daga nan gidanne ya wuce can din zuwa anjima kada in mai mumunan
zato yasa na kawar da zancen kasan zuciyata.
Har yaje yayi wanka bai kara magana ba nikan na fito naje maci gaba da aiyu kana naji lokacin dayake
fadin shiya fita massalaci.
Sai bayan isha,i yashigo gidan ina daki zaune a inda nayi sallah ina duba sakonnin wayata ya shigo ya
sameni da sallama dauke a bakinsa.
Na amsa tare da dago kai ina gaidashi yake fadin abinci zaki ban na dan kwanta kada in fadi a gajiye
nake sosai yau wallahi.
Na dai mike tare da taimakonshi daya miko min hannu muka nufi falon Biba nasawa kira ta fito daga
dakin da take ta sameni a kitchen ina hada abincin abincin ta na bata don yarinyar nada wata dabi,a
idan ban bata abinci ba komai yunwar da take ji bata taba diba taci sai lokacin dana bata din.
Na fito na jera mashi lokacin har yakai kishingide a wajen yana waya saida na hada komai nayi mai nuni
daya fara ci din yaja ruwa ya dauraye hannunsa ya soma ci ina gefe zaune ya kalloni da alaman tambaya
inci mana na kada mai kai alaman a,a don na fahinci wayan da yakeyi yana da muhin manci a gareshi
lokacin .
Zance na miliyoyin kudi yakeyi don haka nayi gudun nayi interrupts dinsa a lokacin har ya kusa gamawa
yana kan wayab ina jin maishi na tambayanshi abinci yake cine halan naji yace ehh new wife dina ta
hada min delicious nake ci yana dariya yake fadin ko mai nata na bam mamakine ita kamar yadda take
ai.
Banyi aune ba naga ya haskowa wace yake wayan da itani yana fadin kinganta nan yana nuna mata
fuskana nayi kasa da kaina cikin kunya.
Yake fadin ku gaisa mana amma bata jin hausa fa turanci zaki mata zance ranan ya fara jin kalman
turanci a bakina da abin ya bashi mamaki matuka.
Har yake tunane wai ko da gaskene munyi zaman rugga da ake fadin munyi kuwa shifa al,amarin mu
yana matukar daure mashi kai sosai wallahi.
Kafirace na gane hakan ta yanayin shigarta da nagani suman dokin dake kanta daya zubo sai yanayin
rigan jikinta kuma dana kara fahintan ba musilunci a tare da ita.
Muka gaisa da ita take fadin gaskiya ina da kyau matuka dole handsome ya rude a kaina ashe a yanzu
baida zance sai nawa a bakinsa meye sirin abin ne wai ?
Koda yake ga sirin ta gani da idonta ai kurciyata yake diba da yake kara mai karfi take fadin in kara kula
da shi sosai don Allah nayi dariya ina mata godiya ya juya da wayan yana cin nama sukaci gaba da
magana dashi duk a kaina daine har sukayi sallama suka kashe wayan tasu.
Ni kan harna mike ina tattara kayan abincin zuwa kitchen na dawo ya mike yana fadin a ina yarinyar
nan take kwancine da cewa habiba yake tambaya ?
Tare muke kwana da ita a dakina na bashi amsa yace to a dakina ke nan zamu kwanta ko mu bar mata
waje ?
Anan zaka kwana ke nan ya kalloni cikin mamakin da ni yakamata ace nayi mashi tunda nasan bai gama
kwanakin da zaiwa matanshi a can ba tunda na fahinci two two days ne kwanan namu kamar yadda
akasarin musulman hausawa sukeyi a gidajensu wajen raba kwana a tsakanin matayesu.
Shi da kansa ya koma ban amsa da anan zan kwana tunda kikaji na fada ai ko akwai matsala da hakan
ne ?
Nayi lau da idanu ina rausaya kai nace gani nayi dai baka idda kwanakin ka bane a can ai tunda kwana
biyu kawai kayi a wajensu ?
To anan din da baki son in kwana zan kwana din ya mike ya nufi dakinshi kai tsaye yana barina wajen
dana bishi da kallo marata dake dan yankawa ya kara yankawa alaman dai period yana gab da zubo min
don haka yake min idan na kusa period akarshen wata.
Daki na koma na kimtsa duk da dare baiyi ba sosai a lokacin saida na gama na nufi wajen biba dake
takure daki kasancewar shi a gidan na samu har ta soma barci da littafi a hannunta.
Dan bugun ta nayi ta tashi nake fadin tashi kije dakina ki kwanta uncle fa ya tafine anty naji ta
tambayeni ?
Sai nayi dan murmushi nace ba a nan zai kwanta ba yana dakinsa jin hakan yasa ta mike sai kuma tace
da dai kin barni nan din in kwana anty ?
Bazaki kwana a can din ba shiya kwanta tun dazun ai yana dakinsa hakan yasa muka fito tare zuwa
dakin nawa da ban fita ba saida naga ta kwanta na rufo mata kofan bayan na kashe wuta.
Dakinsa kodana shiga har ya kwanta kamar yadda yace barci ya soma dibansa na kashe wuta na rufo
dakin na kwanta a gefen shi .
Na zata barcin nasa yayi nisa sosai yasa nake komai a hankali don kada in tasheshi amma me banfi
minti biyu da kwanciya ba naji ya mirgino guna yana rugumana tare da ajiyan zuciya.
Saida ya shaki suman kaina dake a daure don ko kitso ban samu yi ba niyata sai zai dawo gidana zanyi
kitso din da dan gyare gyare sai gashi abin ya zamo min bambarakwai ban fahinci meke gudana ba a
yanzu gidansa.
A yadda daina fahinta shine dole akwai matsala tsakaninshi da saiba har ya kawo haka kuma dole
wanan matsalan babbane duk da ko suna hakan a da can ba fahinta zanyi ba irin yanzu dana shigo
cikinsu dole a yanzu in fahinci hakan a tsakaninsu duk daba hiransu mukeyi dasu ba dashi.
Kiss yakaiwa wuyana yana fadin I love you Rahama ina son kamshin nan naki sosai yana min dadi a
raina nakan ji kamar bani bane idan na kasance dake haka a yanzu ?
Cabdi jam watau gaskiyane anty salma da malam mu na vocatinal center da sukace wasu mazajen
kamshi tsabta da iya girki ko iya magana yana sa su kasance da mace har a dauka kamar asiri macen take
masu suke rikicewa haka akansu.
Anty Salima da saratu sun taba hira mai kama da gulmanshi a gabana ita saratu take fadin takan rasa
yaya yake kasancewa da matansa yadda yake dan gaye din nan su kuma san gasu kazamai tun dai Asmau
dako wanka yake zama mata aiki koda yana gari zata iya maimaita kaya guda a kwanaki acewanta wai
wankin ne yake mata wuya yasa bata saka kaya lokaci lokaci.
Sai salima tace ni banga gara ba a dukkansu duk halinsu daya shiyasa sukai abota a school lokacin don
kazantarsu iri dayane wallahi.
Nayi dan murmushi ina juyowa gareshi nace a cikin muryata dake kara rikitashi love you too yaya J.
Naji ya kara kameni yana fadin really ?
Uhumm na iya fada don sallon daya saukowa jikina a lokacin haka muka samu raya daren dashi duk da
nasan hakkin wata ya dauko ya kawo min amma sanin halinsa nasan yana da dalilinsa nayin hakan a
lokacin.
Washegari daga school naje gyaran jiki don nasan dole koda yamma ko washegari zanje gidan don
haka dole in gyara jikina yadda zan fuskancesu don ba zan yarda inje masu a yakuce ba su samu abin
kushewa a jikina duk da kishiya komai haduwan ki saita hango muni a jikin ko cikin shigarki.
Kishiya bata taba hango abinda miji ya gani ya auro ki saidai akasin hakan agareki da zata rike a kamin
yakarki wajen miji.
Ni kaina nasan gyaran yayi ba laifi a shagon yazo ya daukeni zuwa gida sai sambatu yake duk da da
farko na hango damuwa a fuskanshi amma muna hada ido dashi duk bacin ran dayayi dakon ya gushe a
fuskansa din lokaci guda.
Ina zama yake fadin nawa kika biya matan nan Rahama ?
Saida na kalloshi nace dubu biyar suke karba sai naga ya bude mota yana fadin ina zuwa ya fita kai
tsaye shagon ya shiga na bishi da kallon mamaki ko me zai masu kuma ?
Sai gashi tare da matar tana gyara lafayanta zuwa kai tana gyara rufe jikinta tazo gabana tana dariya
tace amarya oga ya kara muna kudin gyara fa.
Kinga sako yakai ke nan shine na fito inyi godiya a gabanki don gobe ki dawo mu kara cancara mashi ke
dakyau fiye da hakan ya shigo motan yana murmushi tare da gyada kai.
Har da musayan lamba mukayi da ita a gabanshi yaja mota ya tafi sai wani kallo yake jefo min can yake
fadin gaskiya matar nan ta iya gyara sosai Rahama kinga yadda kika kara fitowa fresh dake don Allah
meye sirin da suke maku ne anan wai ?
Kin ganki kuwa kin koma min yar filonki sak dake haka har yafi irin ganin dana fara maki Allah a ranan
dana fara ganin ki haka kawai naji gabana ya fadi duk da a lulube jikin ki yake da wanan katon hijab din
da kike sakawa lokacin ?
Amma saida naji gabana ya fadi sak ke din na dade ina nema a rayuwata saidai a lokacin wallahi ban
kawo komai game dake ba a raina tunda naga kamar Habu yai muna shinge a tsakanin mu ba yadda zai
kasance in sameki ?
Sannan kisan me wallahi duk lokacin da zan ganki sai dabi,un ki sun burgeni a lokacin don haka nidai
kawai kina burgeni duk lokacin dana ganki amma saboda Habu mijin yarkice bantaba kawo komai a
tsakanin mu ba dake irin haka ?
Ashe ke dinma rabotace kedin daice mafalkin rayuwata Rahama sak yanayin ki da komai naki kalan
dana dade ina mafalkine Rahama macen dana mallaka ta kasance a hakan cikin tsabta da sanin darajan
kowa na tare dani ta kasance mai biyayya da dokokina Rahama .
Sai gashi Allah ubangiji ya kawo min ke a saukake ba tare da wani shan wahalan komai ba Allah ya duba
min kuncin da nake kwana dashi nake wuni dashi yaban ke a cikin ruwan sanyi.
Wai ace mace don ta haihu ai irin gyaran nan da miji zai shigo yaji dadi amma ina babu shi Rahama yau
saida nayiwa Asmau kaca kaca a gaban mutane.
Wanan ai sai a zageni wallahi sai ace kaina kawai nake gyara na barsu a wullakance haka idan kai
magana kuma ace mutum ya faye fitana.
Zasu gyara ka barsu kawai ka daina fadan dan nan da kake masu a gaban mutane don Allah yayi tsuki
kawai ya maida hankalinshi ga tukin da yakeyi din saida muka shiga get din gidan nake tambayanshi ?
Yaushe zaka kaini inyi barkane yaya kada ace banje ba ko ina bakin ciki da haihuwan yasa ban damu
ba ?
Saida ya parker mota naji yace gobe baku fita gobe sai ki shirya in kaiku ku wuni can keda habiba ko
daga can idan kun gama zaku dawo in biya daku gidan mu ku gaidasu mama can din.
Naji dadin hakan yasa nace har gidan yaya Ai sai muje da anty Rukkaiya yace duk a goben Allah ya
kaimu lafiya idan da lokaci sai mu biya ai ku gaishesu.
Wanan yarinyar ma ai taso taje taga mahaifiyar ta don ban tsamani ai ta tafi tunda tazo gidan nan ko ?
Gaskiya bataje ba tunda tace min ta zata ba haka halina yake ba da tazo da niyar komawa gidane sai
taga ashe ba haka abin yake ba ?
Aina sani ya fada yana bude mota ya fitar da kafansa daya waje yana fadin koda naje daukanta ai da
kuka tafito bata so zuwa nan din ba.
Sai gata ta fito daga cikin gidan da dan murnanta tana dariyan ganin dawowan mu tana gaidashi ya
amsa yana fadin Habiba dagani dai ba zancen komawa gida yanzu ko anty ta karbewa yaya ke ke nan ?
Tayi murmushi tana boye fuskanta nace tazo ta dauki kaya a bayan mota lokacin ta juya da sauri zuwa
wajen bayab motan ya bude ta kwaso kayan da nake gani kamar na baby ne yaso lokacin.
Saida tayi gaba yake fadin abokina ya aiko minsu daga kaduna yau saidana biya na karbo naje daukoki
ai nace dama bai wahal da kansa ba tunda ba amfani zasuyi dashi ba sai dai a jibgesu don basu gyara
kansu ba balle yaransu.
Ni dai nace rabon sune don haka abar zancen nan ai saida naje dakina na rage kayan jikina na fito na
hada mashi abincin da muka girka don rana wanda har lokacin yana da zafinsa saboda kyau warmers din
nake amfanin dasu.
Banyi wani girkin dare ba fruit salad da nama shi muka sha muka hada da naman muka kwanta ni dai
ido na kawo na saka kawai ban kara magana ba tunda na fahinci bai son maganan a lokaci amna dole
nasan akwai masa dayasa hakan .
Washegari ko tunda safe mukayi aiyukan mu don fitan da nasan zamuyi din yana daki yana barcinsa
shigowan kawu gidan yasa naje tmna tayar dashi daga kwana.
Hakan baisa mun zauna ba shirin mu mukaci gaba dayayi bayan na gabatarwa kawu da komai na koma
kitchen don mu rage aiki tunda nasan sai yamma lis zamu dawo gidan kila ranan .
Daga kitchen din na ke dan fahintar abindake faruwa zuwan kawo kan matsalansa da Nusaibane don
naji yana fadin ai na fada mata saita gane kureta kawu.
Ta dauka da wasa nakeyi ko wanan karon ba zanji ta kowa ba tunda ni ba mai tausayina akan matsaloni
dasu sai zance ya tashi ace nayi hakkuri don haka in zata zauna ta zauna tunda zaman mama takeyi ni ba
zan koreta amma ba ruwana da ita kowa ya sani.
Banyi wani abin asha ba don na tare a nan gidan Asmau ce ta haihu don haka ina da inda zanje in huta a
yanzu babu takura a gareni kuma kun gani.
Kawu din ya tausa murya yana fadin abinda nake son ka gane tunda har mahaifiyar ka ta nuna hakan
bai mata ba kayi hakkuri kai Jafar ka shirya da matar ka kada ka shafawa wanan din laifin daba itace ta
sakaka yin hakan ba.
Sai naji yace kawu ina yarinyar nan dai nine ke auren ta ba wani ba kuma zamana takeyi a gidan nan
don haka ina rokon kowan ku daya saka min ido da ita don Allah ?
Nidai har kawu ya tafi banji sunyi maslaha akan zancen ba tsakaninsu saidana gama na fito kitchen din
nasawa Biba kira daga dakina.
Ta shigo ta sameni kayan dana dinka mata don gudun kada a girshemu haka na fitar mata da kala daya
komai set da gyalensa da takalma har yan kunne na mika mata ina fadin taje tayi maza ta shirya nasan
yanzu yaya zai fito mu tafi.
Ta karba da murnanta tana min godiya murmushi kawai nayi ta juya zuwa dakinta don ta shirya din .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/3, 10:22 PM] Zainab Idris Makawa Writer: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wasu jajayen atamfan super wax mai dan surkin flower yellow a jikinsu da akai min wani dogon riga yaji
kwaliya har yagaji don kyau zakice jallabiyace rigan don yadda aka fitar da shi.
Takalman kafata kuma half cover ce ta mata mai duwatsu new design sai gyale yellow mai duwatsu
dana yafa hakama kunnena fashion na saka dayai shige da kayan sai agogo a hannuna da yar karamar
jakkata yello.
Ki firhita kishiya ga shiganki ko ta yaya yafi ace sai mace tagani ga kishiya taji haushi inji anty salma
take fada min hakan ko yaushe.
Donshi na tsaya na gyara yadda ya kamata ga wani kamshi da nakeyi na ban mamaki a haka na fito na
rufe dakina kamar kullum idan zan fita daga gidan duk da muna rufe falon da ko ina amma ban yarda
saina kulle dakin nawa kuma hankalina yake kwanci.
Ya fito yana waya mukai arba dashi ya sake wayan yana fadin dankari wanan kwaliya haka Rahama ai
sai ace yau din ne sunan ma ga baki daya.
Yau ba suna bane yaya amma yau din ya kasance rana mai muhinmanci ce a gareni na juya wajen Biba
ina fadin dauko basket din da muka shirya ki fita min dashi waje sai ki dawo ki dauki sauran ledojin nan
kuma.