Chapter 15 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   15 / 101

42K to 45K   out of 302.2K words

, , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Sai da suka shiga part din ya J ita da su mama dubu da mijinta nasan sallama sukayi dasu mijin nasu dake
gari shine kadai ya fito har bakin mota yana fadin gashi nan zuwa asibitin idan ya shirya.

Haka suka daga suka bar gidan duk kokarin dakewana saida hawaye ya zubo min ba lokacin ya J yazo
ya wuce mu zuwa part dinshi lokacin nake jin muryan Asmau na fadin wai har sun tafine ?

Sun tafi Salima ta fada saita amsa da Allah ya sauwaka dama ashe bata da lafiyane take yawan zama
haka lukume a daki ko yaushe?

A daidai lokacin Saiba ke fadin wai har ciwo ma sai an boyewa mutum a gidan nan abu har yakai haka
muna gidan nan bamu sani ba ?
Koda yake ance kowa ya samu rana yayi shanyinsa cikin ne za ace za aje asibiti a zauna har sai an
haifeshi ni ban taba ganin irin haka ba gaskiya.

Na kula da lokacin da Saare ke nuna mata ni da idanu naji tace ai gaskiya na fada Saare shi ciki ai har ka
haifishi baka taba jin dadi a rayuwanka sai ranan daka haihu.

Yadda take magana yasa naji ba dadi a zuciyana itako tacigaba da fadin kudi yayiwa Habu yawa koda
yake ba zafinsa bane tunda Allah ya kashe ya bashi ta dubi kishiyanta tana fadi ita kuma tayi wani irin
meda baki.

Sai naji Saiban na fadi a to mana ke inbashi ba dai naga mu duk lalura baisa munje mun kwanta asibiti
saidai asayo muna magani a hadamu dashi kawai ?

Amma ai kowa da irin yanayisa ko yanayintane yazo mata a haka ai ko ita bada son ranta taje
kwamciyan asibitin ba .

Tunda gashi ta fita tana kuka dadi zaisa mutum kukane Salima ke fadan hakan cikin hasala data karbi
zancen da yar uwarta ta soma yi dasu din.

Zo muje Ramaah kinji mama tace idan sun tafi mu gyaro wajen mu kulle masu ato nidai ga gaskiya na
gani ba za a hanani yin magana ba dai kan bamu tsaya karasa saurarensu ba sai dai muna gab dashigane
mukaji muryan mijinsu na kiran Asmau.

Shiyasa akace matan saure sunfi kishiyar miji daya kishi wanan ba karya bane don matan ya J da suka
fito fili suka nuna bakin ciki ga yar uwata ranan.

Ashe bani kadai naji haushin abinda sukayi ba din har da Salima don ina kitchen ina hada kayan datace
in kwashe zuwa cikin gida naji salima din tana fadin.

Shiyasa suke bakin kishi tsakaninsu ai ina abin dadi a zaman asibiti ga mutum har wanan abin yakai
zancen banza haka ?

Ciwone ai yasan kofan kowa sanda zaizo gunka baka sani ba tunda ba sallama maka zaiyi ba ai
munafuncin banza da wofi kawai ?

Ni dai banyi magana ba amma na rike hakan a raina akwai ranan magana matukar muna raye na nasa
hakan a zuciyata.

Bamu zauna ba nida Salima abinci muka dora don mama ta gargademu da hakan mu hada abinci akai
asibitin da wuri basai na can sunji yunwa ba za a kawo masu .

Kafin sha biyun rana mungama miya da abinci tana zaune tana yanka salad da kayan had iya na zaune
tana jan tasbaha a gefen ta .

Ni kuma ina kitchen na dora ferfesun da mama ta bugo waya tace a hada na kifi.
Ya Habu ya dawo yana tambayan makulin part dinsu da muka rufo masu naji iya na tambayan ya mai
jikin take ?

Naji yace sun bata gado sun fara dorata a dokan sun kuma hana a aita yawan sintiri a wajenta don barcin
da akeson ta dinga yi ko wani lokaci saboda lafiyan abinda ke cikin cikin nata.

Bakaji ba mai lafiya yana zama haka don son rai ka zauna a hanaka mu,amula da mutanen arziki su wa
yancan sakarkarun sun dauka hakan wani abune har suna tsayawa gulmam hakan .

Shi Jafaru ya sameku can ko zai fita don bai tsaya jin zancen nata ba ya juyo yana fadin muna tare dashi
iya shiya biya kudin komai ma har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya.

Ai dama nasan ba zai bi kan matansa marasa kan gado ba tunda shiba sakarai bane irinsu wai iya anyi
wani abin ne ya dakata yana tambayan tsohuwar ?

Anyi mana Abu matan dan uwanka ke gani wai saboda makirci yasa yarinyar nan karyan zuwa asibiti ta
zauna a can don kawai ta,,,,,,

Haba iya ki bar yaya yaji da abinda ke damunsa don Allah matanda basu sawa basu hanawa idan an
tashiyi sune basu san Allah ba cikin zancensu Saare ke fadan hakan ga kakan tasu .

Koya gane me take nufi da zancen ta yasa kai ya fice daga part din bai jima ba ya fito a cikin shirinsa
nan Salima ke fada mai mun hada abincin asibiti yace har angama ta amsa da ehh mama tace kada mu
makara ai da hada abincin.

Ku fito dashi na kai masu don kaduna zan tafi yanzu in sayo wani magani da za ai mata amfani dashi
nan ban samu oroginal dinsa ba.

Allah ya tsare mukai masa bayan mun saka kayan a bayan motanshi din muka nufi cikin gida nikan
Allah ya gani ban iya cin abincin ba a ranan don har lokacin ban fahinci komai ga zaman da zatajeyi
asibitin ba.

Mahaifiyar mu bata iso garin ba sai dare wajajen tara muna daki salima dai waya takeyi ni kuma ina
kwance naji ana mata sannu da zuwa .

Muryan ummah na tsinkayo a kunnena tana amsawa hakan yasa na dubi anty Salima ina tashi zaune
nace muryan ummah nake ji fa ?

Waye ummah ta fada tana kallona nace mahaifiyar mu tare da ita muka fito falon tana zaune suna fira
da iya dake tambayanta hanya ?

Sannu da zuwa muke mata saidai ni a cikin yare nake mata magana ina tambayanta yan uwana tace
suna lafiya taso tazo da umar sanda ai amma ta barshi agidan hardo saboda karatunsa .

Ku kawo mata abinci ko iya ta fada sai ummah din tace sallah zatayi tukun a nuna mata ban daki tayi
alwala na mike tsaye don bansan inane zan kai ta ba sai Salima ke fadin kaita bandakin mama mana ta
sauka a nan.
Lokacin anty Saare na part din ya J bata sanda zuwan ummah namu ba ni dai a yadda na dauka shine
tana zuwa dan hirane part din.

Amma sai inji Salima na fadin don kwadayi da munafhnci take yawan shigewa matan yayan nasu in
bashi ba sau nawa suna masu wullakanci a baya lokacin da yayansu baiyi karfi haka ba?

Amma yanzu wai duk anty Saare ta manta da hakan suta koma tana shigewa don suji dadin
wullakantasu ke nan kuma.

Dakin yana nan yadda muka gyarashi da safe nan ta shiga yayi sallah ta jima bata fito ba salima ta
dauki kayanta takai mata dakin ba wasu kaya bane sosai sai manshanu da kindarmo mai yawa datazo
muna dashi da nama soyayye.

Abinci ma da iya ke magana nayi murmushi ina fadin ummah ba zataci abinci ba nan iya saboda
kunyanki kinsan nan gidan surukintane ai.

Salima tace shine kikai shiru Ramaah ta mike ta suri kayan ta sameta dasu a daki nan ta jera mata har
da jawo kofan dakin don tasan babu mai shigowa hakan yasa ta dan tsankwari abincin kadan ta aje.

Bata sake fitowa ba falon sai washe gari ta fito da shirinta tana dakon yaya ya shigo ya tafi da ita
asibitin da zata zauna.

Inda muke ta kokarin hada masu breakfast da za a kai asibitin haka kuma iya ta lasa muna tare da mu
za,a tafi mu dubasu a can.

Yasa mukai komai a gurguje inda na saka nonon kindarmon a cikin fridge na rakumi datace min don
yar uwata tazo dashi ta dinga sha na diba a cikin wani gora da za akai mata ta dinga sha na kada a kulan
kankara.

Mun shirya tsab koda ya fito yazo gaidasu iya da ummah ya samu har iya din mun shirya muna jiransa
bayan an gaisa muka fito da kayan muka kwasa zuwa asibiti gaba dayan mu yan part din aka rufe shiyan.

Sam ummah bata sake ba har muka kai asibitin cikin nauyi da kunya take don ta shiga motar surukinta
koshi don ba wanda ya santa a zaria ne yasa har ta yarda ta shiga Ya Habu ya jata.

Duk ko da dan wayewan kai da ummah kedashi wanan baisa tayarda akidan mu ta fulani ba don anty
Yanda yar farice a wajenta kuma yarta ta cikinta suruki zai dauka a mota haka ?

Ba laifi gaskiya don ba zakice asibiti bane ba ,a kuma kilance wajen ba dakin masu irin lalurar yar uwata
din itama aka ajeta munje daidai visting hour don haka kofa a bude take lokacin.

Aka gagaisa da juna tsakanin ummah da mama ana satan kallon juna a tsakaninsu sukaiwa juna jaje
akai tayiwa ummah yaya hanya da mutanen gida.

Gadon da anty Yanda take mukaje gaida ita ga kayan more rayuwa nan an baza gwanin ban sha,awa
zakice ba asibiti bane na fada a zuciyana ina kara bin wajen da idanu.
Munkai kamar minti talatin matan ya J suka iso tare dashi suma da nasu abincin nasan shine yasakasu
yi dole saidai yadda suka samu yar uwata din akwance haka ya tabbatar masu bata da lafiya dai kan
saidai ba wani sosai ba.

Ban da sakin jiki dagani har ummah a wajen su dai keta hiransu da kuma baza ido suna gulman wasu
mata da muka hango dan nisa damu masu irin matsalan nata.

Shigowan yaya J dakin da ya Habu ya sa duk akai shiru inda suka karaso bakin gadon yana gaida ita nan
yake tambayan mama ko anzo an mata alluran da safe mama tace anya basuyi ba kan.

Ya juya yana fada ya habu yabi bayanshi suka fice daga dakin sai lokacin saiba tayi magana take fadin.

Wani kan ba zan yarda in kwanta a dinga surbuda min allura haka ba gaskiya daga can inda mama take
zaune ta bata amsa da fadin itama ta kwancen ba da son ranta hakan ya sameta ba ai ?

Komai da ya samu bawa mukkadarine nata kaddaran haihuwan ke nan yazo mata a hakan kuna
magana kamar baku taunawa wani zubin duk wanda kika gani a nan ba dadin rai ya kawoshi wurin nan
ba asibiti fa akace ba gida ba ?

Shiru tayi don tasan abin ya taba zuciyar mama din don ba wanan karon suka fara tsegumi kan matan
Habu din da mama din ba.

Suna fadan mama tafi son matar Habu dasu tana nuna banbanci a tsakaninsu ta fifita matar Habu
alhalin duk wani moriya a gidan mijinsune .

Taba wace suka gulman da ita sakon da take kyautata zaton yakai masu da cewa ta fifita din don ance
ka kyautatawa wanda yasan darajan ka.

Kuma da sauki tunda ba habu ta fifita akan jafar ba ai idan sune aida sauki suyi mata yadda matar Habu
din ke mata idan basu ga canji a wajenta ba.

Wanan yasa suka kama bakinsu don ta fadawa yar sakon cewa su shiga hankalinsu don lokaci guda zata
iya fyacesu gaba daya a gidan kirsis take jira ga hakan.

Don saita sa ya j ya sakesu ta aura mashi masu hankalin ya zauna dasu tunda basu iya cin arziki ba su
kuma su tambaya suji ita a ratuwanta bata gaji tsiya ba ko jafar din da arzikinta yake barazana.

Aiko da J din yaji yai masu tsiya sosai lokacin har yana barazan sakinsu run wanan lokacin suka shiga
hankalinsu da mama din ta samu lafiya dasu .

Sai a yan kwanakin ma suke dan ganin fuskanta idan tazo gidan wanan yasa a yanzuma sukai gum
kamar ruwa yaci su a dakin.

Tare da likita suka shigo dakin hakan yasa muka fice waje sai mama aka bari a wajen nan muka zauna
saman babban tabarma a wajen .
Mai hali dai baya barin halinsa akace don ko a nan gulman wata mace mai tsohon ciki sukeyi ina
mamakin yadda halaiyansu ya kasance a hakan.

Banga abin tsegumi ba a nan duk da yake basu irin hakan ya sama ba a yanzu dole su mayar da abin
kishin tsakar gida su da yar uwata da suke ganin ta shiga rigan arzikin mijinsu a yanzu.

Don ni a zatona shine mai dukiyan gaba daya don bansan cewa dukiyan yan uwansa kaf da suka gada
yana hannunsa ba lokacin.

Sun dan jima ya fito yana fafin muje ko kafin ya juya wajen iya yana fadin to iya ni yau zanyi tafiya fa
zan koma port,harcurt wajen sana,ata .

Ayya Jafaru zaka koma yau ke nan sai kuma yaushe eeh to iya saidai kun ganni yanzu kam amma insha
Allah kafin azumi zan dawo na dan fara azumi a nan din.

Hakan na da kyau Allah ya tsare ya kare ta fada gabanta ya gurfana yana fadin to muka hannun ki mana
a cikin hijjab dinta ya dunkula mata kudi sai murmushi iyan ta sake a fuskanta tashiga mashi sabon
addu,a kuma.

Ya mike tsaye yana kallon kannesa yana fadin to ku yaya za ayi nifa zan tafi yau din nan ana nemana a
can .

To yaya zancen kudin da nayi maka fa Saare ta fada yace ban manta ba saratun mama ba kince sai next
mont bane saiki tuna min ko ina can din in turo maki.

Ya dago ya kalli Salima yace yan mata nasan kedai na shan ice cream ne ko ko yanzu kin dainane tayi
murmushi tana fadin ban daina ba yaya yanzu kan harda na powder da jan baki .

Ya nunata yana fadin see you nine zan baki kudin jan baki ina saurayin ki dan karya ta kebe baki zakice
wata karamar yarinyace kudi ya mika masu .

Kamar zai wuce sai kuma ya kallo inda yake yana fadin nakan manta da sunanta fa Ramaah ko ka kirata
da Rahama wai dama sunanta ke nan aka sauya da wanan din.

Ke kuma kudin me zan baki ya fada yana kallona murmushi nayi ina fadin nagode yaya yace shike nan
kin hutar dani ?

To ku kunji yadda akeyi ba kamar ki ba Saare da kullum kedai a baki kudi nakan rasa me kikeyi da kudi
haka wallahi yana magana yana kokarin cusa hannunsa a aljihunsa na gefe daya.

Sweet J muje mana kasa mun taso kuma ka tsayar damu haka a rana ya juyo ya dan kalleta hakan bai
hana ya fasa abinda yakeyi din ba Salima naga ta kebe baki data fadi hakan tana magana kasa kasa tace
akgunguma duk ranta ya baci ana bamu kudi.

Nice kusa da ita a zaune ninaji hakan data fada ya miko min kudin yana fadin kin gani ko kin fisu sa,a ke
yan dubu dubu kika samu.
Na karba da hannu bibiyu ina godiya rakasu mukayi har bakin mota suka shiga ko anan ma din saida ya
tsaya da kannesa suka dan taba barkwanci a tsakaninsu suko duk sun sha toka a motan .

Nice na fara juyawa ganin ya tayar da motan tare da mamakin irin zama da naga sunyi a tafiya
dukkansu suna zaune a bayan motar shi kadaine a gaba da yake jan motar.

Suka tafi su kuma suka dawo inda nake zaune da tsohuwar kakan tasu dake kiciniyar boye kudinta
cikin lalitarta dake manne a jikinta.

Kai yaya ho daga shi dai sai matansa shike nan sunyiwa kansu tsiya babu wace zata shiga gaban mota
ta zauna tare dashi don jidalinsu din.

Ai maganinsu ke nan yan iska masu fitinan tsiya kawai haka kawai akan shiga mota su kama dabe a
gaban mutane sun zubarwa mutane da mutunci.

Ni na rasa yadda mutum irin yaya jafar mai hakkuri da kirki yake iya zama da wa yan nan matan da
basu son suga wani komu nan mun rabeshi.

Jifa yanzu kudin nan da Saiba taga zaibawa Ramaah shine ta kasa hakkuri take fadin wai yazo su wuce
ya shanyasu a rana wai ita yar iska mai wayau banza.

Ai shima ya gane me take nufi bakiga ya fita batunta ba ko kwanaki daya dawo tafiya ta aikawa part din
ya Habu da tsaraba suka ki saida ya dawo ya diba da kansa bayan yai masu cin mutunci yabani na kai
masu.

Tsam na mike na nufi wajen mahaifiyar mu dake can dan nisa damu a zaune cikin damuwa nasan ba
komai bane sai halin data samu yar uwata a cikine ya daga mata hankali.

Ina isa naji salima na fadin ummah kin zauna kinyi shiru kamar baki wajen tayi murmushi tana gyara
mayafin jikinta da ya rufe mata jiki lif har kasa.

Idan kinga Ummah duk da wahalan da take ciki zaki rantse kice ba itace ta haife mu ba sai kice ita din
yar muce ba mahaifiya ba.

A cikin yare take tambayana da shi wanan din yayan Abu ne ko na amsa da ehh shine babban yayansu
namiji amma suna da yaya mace tana aure a wani gari ita.

Ayyo suna ko da kama sosai da Abu din saidai haske dashi ya dan dara Abu din dashi nace shi Habu din
kebiwa shima dan mamane su kuma su Salima da Saare kanne sune duk uwarsu daya.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC




MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,



1️⃣7️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Nan muka bar mama da ummah muka dawo gida saboda abincin da part din yaya suka kawo mama tace
ba sai munyi wani abinci ba a ranan mu barshi kada ya zama barna.

Hakan yasa koda ya Habu ya sauke mu gida barci sosai mukayi sai wajajen la,asar muka tashi mukai
sallah Salima tace zan rakata kasuwa .
Banyi mamakin hakan ba

15 / 101