Chapter 16 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   16 / 101

45K to 48K   out of 302.2K words

don nasan tana kudi ranan kudin da dan uwanta ya bamu da zai tafi ni banko
tsaya duba kudin ba tunda na saka a kasan jakkata a lokacin.

Kayan gyaran jiki ta kwaso su man shafi sabulai turare har ina mamakin hakan yadda ta iya fidda kudi
ta biya kudin ba tare da jin komai a ranta ba.

Saita tuna min da anty Salman Abuja a lokacin har nake mata hiran tana min shige da ita don haka
halaiyanta yake itama.

Bayan mun dawo gidane tace na kwashe wanda take amfani dasu da farko don ita bai mata ba a cikin
murna na kwashe zuwa inda nake aje kayana na jera kamar yadda suka jera nasu gefe daya don kowa
nada inda yake aje kayansa a dakin.

Tun a hanya ta gargadeni da cewa kada in yarda in fadawa anty saare ko nawa aka ban in mace kawai
dubu biyar ne ko goma.

Nayi mamakin hakan data fada amma na share muka dawo gida a falo muka sameta zaune tare da iya
muka zube kayan a nan falon.

Duban kayan tayi tana fadin kasuwa kukaje Salima baki fada min ba aida na baku sako kun sayo min
tana duban kayan take magana .

Kudin ba zasu azu min ba hakana zan iya kashesu ban mora ba ko kuma in rasa me nayi dasu amsan
data bata ke nan lokacin.

Ga mamakina sai naji Saare din na fadin ke Ramaah nawa ya baki halan nace dubu gomane sai tayi shiru
bata sake magana ba sai can take fadin baki sayo komai bane ke nace a,a ban saya ba anty Saare.

Mikewa Salima tayi zuwa daki da ledan kayanta a hannu na dan kai kwance a inda ta tashi ina kallon tv
dake aiki iya ke fadin ki lalubo muna Jafar muji koya sauka lafiya.

Ta dauki wayanta tana neman layinsa din yashiga take gaidashi tare da fadin iya tace ka sauka lafiya ko
yace Alhamdullahi ina kaduna sai yamma zamu shiga jirgin Rivers din .

Muryan Salimace ke kirana daga daki na amsa na tafi ba tare dana san yadda sukayi ba kayane saman
gado ta zuba dana shigo take fadin ki kwashi kayan nan Ramaah kiyi amfani dasu tun wanda yaya ya
sayo muna ne da yaje tafiya da wasu na sallah ba amfani nake dasu ba don ban faye son dogon riga ba
idan zan fitani.

Godiya nayi mata na kwashe kayan zuwa wajena na aje ta mike zuwa gaban mirrow ta kwashe kayanta
kaf ta miko min tana fadin zaki iya amfani da su zai maki kyau sosai ya gyara maki jikin ki don ni bai kara
min wani haske ba.

Na fararen mutanene na kwaso sai daga baya nagane hakan kinga idan ya karbeki kya dinga sayensa
daga baya kina amfani dashi.
Kwasa nayi na kai wajena tunda yanzu a nan dole zan rika amfani tunda yaya Habu yana nan sai
gashima washegari shima ya koma wajen aikinsa .

Duk daya tafi ban koma ba a nan muke kwana saida mama tayi wajen kwana uku asibiti tare dasu
ummah ta fahintar da ita komai game da antyna ta dawo gida ta dan huta.

A ranan ne kuma muka wayi gari da an shiga part din nasu saidai bamu san me aka dauka ba tunda
masu wajen basa nan.

Wanan dalilin yasa ya J daukan maigadi a gidan dama yana da niyar hakan ga iyalinsa din ya kasance a
yanzu muna da maigadi sai kuma mama tace nida salima mu koma kwana a can har ya Habu ya dawo
wanan dalilin yasa muka koma kwana din a part dinsu mu biyu.

Acikin yan kwanaki na kara fahintar waye salima don gaskiya muna zaman mu na lafiya sosai tsakanina
da ita duk da ba wani girma na sosai tayi min ba amma haka bai hana in bata girmanta ba.

Itama din na fahinci tana daukana tankar yar yar,uwartace ta jini don yadda take zama ta fada min
komai nata ta dai sake jikinta sosai dani tunda tasan ba wanda zan fadawa .

Wani saurayi take so sunansa yazid amma iyayyenta da yayyu sunce yayi yaro kwarai a gareta ita kuma
ta nace akan shi take so .

Duk da yazid din zai girme mata da shekara biyar ko fiya da hakan amma sun nuna basu son alakanta
dashi gashi kuma sun shaku sosai dashi din.

Da muka dawo da kwana part din antyna sai hakan yai mata dadi sosai sai sukai wani lokaci dashi a
waya nikan ina kwance ina sharan barci na.

Idan ko idonshi biyune zata ban waya mu gaisa dashi ya dan jani da fira har in gaji in mika mata waya
don bai gajiya da rokona in kafa masa gwaunatinsa gasu yaya.

Shi baisan banda power hakan ba garesu nima cin arzikin yar uwatane ya hadani dasu idan bashi ba
ina rugga tare da dabbobin mu da baffa ya kwace muna.

Rai da kwade irin na dan adam a zaman mu wajen Baffa saida muka gano shanayen maihaifin mu
kuma muke basu kulawa sosai a lokacin.

Don sai ince yawancin shanayen da baffa ke alfahari dasu na mahaifinmune don sunfi yawa sune masu
dabbara dabaran baki da fari a jikinsi kinsan shanun mu na can suna da babbanci da shanayen ku na nan
mu namu gudale sinfi yawa sunci sun koshi sosai suna bunkasa don hakkin da suke samu.

Yayin da yar,uwata take har lokacin karkashin kulawan likita kuma tayi kyau sosai su mama dabu da
mahaifiyan mu suna kwantat mata da hankalinta.

Hakan yasa jikinta yayi kyau ta murje ba kamar yadda aka kaita asibitin ba ga kuma rubutun da a
kullum sai an wanko mata tasha.
Yauma shiri muke don mama tayo waya da muje gidan malamin bayan kwatancen da tayowa salima
tace tagane gidan zamu karbo mu sameta dashi asibiti.

Zafin ranane a lokacin amma haka muka daure muka fita bayan la,asar dakyat kuma muka sami abin
hawa da zai kaimu unguwar mu karba mukai asibitin.

Gidane mai fadin baranda daga waje sai ciki inda tulin kayan da muka gani ya nuna na almajiran gidan
ne muka karasa ciki kuma zaure biyu ne a gidan nan muka sami malamin muka karba ya tambaye mu
mai jiki ?

Salima tace da sauki idon da bawan Allah ya kura min yasa na shiga tsarguwa da irin kallon da yake min
har dai muka samu ya mika muna mukai mai sallama.

Karfe biyar a asibiti yayi muna mun samu su mama a waje suna shan iska muka gaidasu tare da mika
mata sakon tana ta saka muna albarka.

Nan take fada muna cewa almajirin dake kawo masu kullum yau baida lafiya ita kuma ba dadin jiki ta
tashi dashi ba don saida tasha magani.

Tausayi ta ban don akan ciwon yar uwata ta hade nata ta zauna a asibitin duk akan neman saukiwa
danta take wanan abin mun dan jima a wajensu din.

Nan mahaifiyar mu take min yare da inzo in mata kitso kanta yayi mata nauyi da yawa na bata shawara
akan tazo gida zaifi .

Don ta samu ta wanke kan saboda kitson ya jima akanta idan anyi sabo duk a cikin harshen fulatanci
muke magana da ita don haka basa jin mu.

Inda ummah ke fadin ya zatayi tazo gidan da sunan kitso gara dai inzo nan in lalaba mata kan nata duk
da maman mu yar daji ce amma gaskiya tana da tsabta sosai kafata da kanta basu rabuwa da gyara
kullum.

Mamace ta mike take fadin bari ta duba ko ta falka ta bata maganin ta shiga nan nake fadawa Salima
takaddaman da mukeyi da ummah din wai kada a zageta yarta na asibiti kwance ace tana batun kitso ita.

Lah ummah kizo gida ki wanke idan ba zaki zo ba kuma sai a kaiki sallon a wanke maki a can tunda shi
kitso dole sai anyishi.

Murmushi tayi tana fadin boni jam saloon kuma yar nan meya kaini zuwa saloon a wanan shekarun
nawa kuma yanzu ai garama inje gidan baku aimin a can din.

Itama salima din tayi dariya tana fadin kukan filani Allah yayiku da kunya ummah meye a cikon kunyan
haka kuma tunda ba tsufa kikayi ba ai nifa har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece kika haifi su
Ramaah wallahi.

Don kinfi kama da ace kece yayarsu dai ba mahaifiya ba ummah don sam baki tsufan haihuwansu ba
haka tayi murmushi tana dukar da kai.
Wai meyasa mutane da dama suke fadan hakane garemu bakece kika fara fada ba kowa haka yake fadi
a kanmu idan ya ganmu da ummah din.

Mama ta fito da kayan abincin da anty Yanda taci hakan yasa na tashi da sauri na karbo a hannunta
tana fadin tagode kayan da zamu dawo gida dasu ta fara tattara muna waje daya harda wa yanda zan
wanke masu.

Karfe shidda a gida yai muna ban kuma zauna ba saida na wankewa ummah mu kayan nata dana anty
yanda da ake kawowa gida in wanke ko yaushe.

Abinda ke ban mamaki yadda na kula da matan gidan basu damu da zama yar uwata asibiti ba irin
yadda na sani idan dan uwanka yana kwance ka dan rika lekasa din sam basa sunayin hakan gareta ba su
?

Hakan yasa na kara nisantar lamarinsu iyakata dasu gaisuwame tun bayan da naje neman magani in
hade saboda ciwon kan daya kamani ta dalilinsu suka hana min magani saida mijinsu ya sawo min har
yanzu kuma ina amfani da sauransu wajena.

Iya taje asibitin ta zauna da matan kawu dauda a ranan don su karbawa su mama zaman su dan dawo
gida su dan sarara hakan yasa na samu daman banyewa ummah kai nayi mata kitso irin wanda na saba yi
mata a gida.

Sai wanan ranan yan gidan suka san dana iya kitso sosai har salima na fadin zan mata idan ta banye
kanta.

Port,harcourt rivers state ya J ne ya gama shirinsa na tafiya ma,aikatar da zaiyi singnig don kayansu su
samu shigowa arewa a cikin wanan watan.

Don sun gama duk wani proces din da akeyi dashi da maigidansa yana shiga wajen yana kiyasta irin
dukiyan dake kasan nan ta Nageria da Allah ya bamu.

Amma dan arewa yana zaune a cikin kunci yake rayuwansa zai iya rantsewa a wajan nan ba wani
bahaushe saishi kadai duk da suna bat da kama da irin shigar mutanen wajen a yanzu.

Don shine ba zai rantse da hakan ba a lokacin a madakatar da zai sadaka da wajen da za a sakama
hannu din ya samu mutane birjit dake jiran su gana da babban mutumin .

Wanda kowa da laluran daya kawoshi wajen bai dade da zama ba wani ya fito daga office din yana
kiran sunan company nasu hakan yasa ya mike don ba wanan ne zuwansa na farko ba.

Mutumin dake zaune a barin hangunsane ya bishi da kallon mamaki don a iya saninsa baisan mr Okah
da wanan mutumin daya canjesa ba a baya.

Wanda a yanzu shima yazo ganawa da wanan mutumin ne ta yadda zai samu ya dan jona ya fara
business din don abubuwa da suke kokarin tsaya masa a yanzu din tun bayan barinsa wajen mr Okah da
abayansa yake yana ci yanasha yana duk wani biyan bukatansa cikin mutunci har duniya ta sanda shi a
lokacin.

Saidaga baya da ya yaudareshi ta hanyar cuta mr Okah din ya watsar dashi na har abada da a yanzu bai
aikin komai kuma sai dan buga buga don ya kare mutuncin kansa.

Lalai babu tamtama wanan yaron mr Okah ya aza a matsayinsa na baya amma wanan yarone sosai
anya kuwa tunanensa ya zo a gaskiya yasan halin mr Okah da kyau kamar yunwar cikinsa fa ?

Mr Okah mutum ne da zai sakar maka dukiya kayi komai a kai kamar bai damu dasu ba sai ranan daya
bukaci sanin kan dukiyan zai waiwayeka akansu.

Wanan karon ma haka yaiwa Jafar din da kanwarsa tillo daya ta gabatar mai dashi kuma ya yaba sosai
da hankalin yaron da baiwansa bai taba tsamanin zai samu yaro karami haka da zai rike wanan amanan
da zuciya daya ba don yaron akwai basira da hazaka ga zafin nema.

Haka hasken taurarinsu yazo daya kusan ma yace na yaron yana gab da taushe nasa yadda masana suka
fada mai akan yaron.

A bangaren jafar din kuma dashi da kaninsa Abubakar suke tsaye sai yan uwasa biyu daya yaba da
halaiyansu sune suke gudanar da wanan sana,an dayanzu darajan gidansu ya soma farfafowa.

Irin jajircewan Jafar din da taka tsantsan akan dukiyan mutane yasa idonsa yana kan komai yasan shige
da ficen da yan uwan nasa sukeyi da dukiyan bai yarda ya shagala a kan dukiyam mutane ba yana hasaso
masu jin dadinsu gaba.

Har kawu dauda ya dora a wanan harkallan a yanzu a wasu jahohin dake kusa da kaduna din shima
sai tubarkallah a yanzu.

Nace ashe da zamu samu irin jafar goma a arewa ba za a barmu a baya ba indai dan uwa zai samu ya
tunane saura azo aci tare a tsira tare da mun rage raddin talauci a nahiyar nan ta arewa.

Saidai mutane a yanzu kansu suka sani sai iyalinsu mutum bai tunane zai iya mutuwa ako yaushe yabar
baya da Kura ga magadansa.

Har jafar din ya fito wanan kafirin yana zaune yana jijiga kansa a wajen ya fice abinsa ba zaka taba
daukan wani abu maimuhinmanci yayi ba a lokacin.

Jafar mutum ne daya bude ido da neman kudi tun yana karami suna bin mahaifinsu kasuwa suna ganin
yadda ake harkan kasuwanci da har yazp kuma kawu dauda ya kara dorashi kan wata sana,an .

Hakan baisa yayi sake da karatunshi ba don har masters yayi saboda daman da yake dashi na magani a
ganan yaron don ga tushen ilimin a cikin garinsu.

Hankalinsa yana kan tukin da yakeyi duk da a yan kwanakin hankalinsa gaba daya ya koma gida saboda
azumi dake karatowa yaso a satin nan yashiga arewa saidai hakan ba zai samu a wajensa ba don kayan
su dabasu daga daga kudun ba har lokacin.
Wanan yasa bai samu shiga gida ba sai dole an fara azumi badashi ba ke nan hakan yasa ya jawo
wayanshi ya soma kiran layin mahaifiyarsu dan yaji ya za ayi ke nan ?

Tana dauka yaji muryanta da alaman ba lafiya ko barci kuma ta tashi a lokacin hakan yasa hankali
tashe yake fadin lafiya dai mama ?

Dan murmushin dole mama din ta kakaro a fuskanta kamar yana gabanta take fadin ba komai jafar
yau dai na kwana da dan ciwon kaine kawai amma da sauki.

Kina asibitin ne tace a,a gamu gida iya da matar kawunkune can da ita yau mun dawo gida mu dan
huta muryoyin mu yaji a lokacin yace taba saratu waya take fadin bata kusa tana can wajenka.

Salimace da Rahaam suke magana yace ta bashi salima din nan ta karbi wayan tana gaidashi ya amsa
yake tambayanta idan ciwon mama din sosai ne don yasan ba zata fada mashi gaskiya ba ita.

Gaskiya tun jiya take kwance da muka sameta asibiti amma dai kuma yau da sauki tunda tasha magani
fada ya fara yana fadin shine baku kirani kun fada min ba salima ?

Me saratu takeyi can bayan mama na nan kwance bata masan halin da take ciki ba yanzu zan turo
Lawal yazo ya gani idan zai kaita asibitine ?

Hakan yasa ya fasa fadan zancen da yake sonyi da mama din a lokacin ba a dauki lokaci ba mukaji
sallaman lawal din yazo duba mama din da jiki .

Abokinsa ne nasanshi sosai yana yawan zuwa gidan idan yana gari wajensa haka kuma sukanyi tafiya
tare indai yana arewa.

Shiya shigo ya dubata har sukai dan hira da mama din duk da ina kitchen ina hada girkin sara lokacin
amma ina jiyo hiransu daga kitchen din.

Ya fita bai jima ba ya dawo tare da wani ma,aikacin jinya ya dubata ya bata maganunuwan da zata sha a
raina nace gata ke nan mai karami shike da babba akace.

Anty yanda muke sa rai a cikin mu yanzu ta nunawa mama damu wanan gatan sai dai karfin mijinta bai
kai ba amma duk da hakan Alhamdullahi gaskiya.

Abinda yasa nace hakan dole indai da nagarine kai kaga yadda iyalan mama suke gudanar da
rayuwansu dole abin ya baka sha,awa.

Don ko ya Habu saida ya kira yana fadin zai taso ta hanashi tace ya zauna yayi abinda ke gabanshi ita
lafiyanta kalau Jafar daine ya tayar da hankalinsa.

Shima ya Salis ya kira cikin damuwa donshi yanzu yana ghana yana karatune daga can kuma ya kira
yana gaida ita da jiki me zai hana bakaji sha,awan hakan ba yadda diya keba uwarsu kula.

Bansan ya akayi ba saiga matan yaya din har saare sun shigo suna fadin mama ashe bakiji dadi ba yau
yanzu sweet j yakira yake fada muna.
Aina fada mai ni zaune nabar mama tana banyewa maman su Raamah kai da za aiwa kitso fadan hakan
yasa na kalleta don nasan mahaifiyar mu zataji nauyin hakan data fada.

Sun dai dan jima kafin su fice daga part din lokacin har na hada komai da za akai asibitin na shiga
wanka don nice zanje nakai masu abincin .




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC




MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,1️



1️⃣8️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Bayan kwana hudu ya sauka garin da tarin alheri mai yawa dan tab motar dayazo dashi take da tsaraba.

Mu mukai ta jidan kayan zuwa cikin gida dasu part dinshi muna tarawa a tsakar falo koda muka gama
kwanciya nayi lokacin.

Saida asuba da muka tashi yin sahurne nake jin yar wajensu anty Saare na fadin dama tasan zai dawo
da alheri haka mai yawa.

Don tana zaune yake tambayan su dame dame zai sayo a lagos don a rage kayan sallah suka lissafa
mashi yace saura sai idan yazo nan zai saya.

Anan na

16 / 101