Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ba a dai hada mashi din a ga ko zai sha din.
Shayi mai kauri na hada mashi don ya kama mashi cikin nasa na mikawa mama na kamoshi tare da ita
muka bashi shayin.
Alhamdullahi don yasha sosai ya maida idon sa ya rufe kuma alaman ya isheshi ba zai kara ba a haka
mazan suka shigo suka same mu dashi ina zaune rike dashi na dan dagashi ya fada mai.
Sunyi farin ciki da halin da suka sameshi sai mama ke fadin dama yar nan tace insha Allah maganin nan
datake mashi kwanan nan ance da yardan Allah a cikin kwanaki uku za aga fa,idanshi gashi ko mun gani.
Alama ya nuna wanan matsalan bata asibiti bace ke nan don haka gara in an kara ganin hasken hakan a
mayar da yaron nan gida aje acigaba da neman na gargajiya a gani.
Ya Auwal yace haka kowa ke fada shima Habu jiyan nan yake fadin ance wani zubin idan an rasa gane
kan ciwo kawai mafita abar asibitin da mutum don shedanu da miyagu masu sihiri suna son hakan.
A asibiti suke samun galaba don sunsan babu wani maganin tsari ko riga kafin da zai taresu a nan din
sun daita maganganu a tsakaninsu har yan uwa suka taru asibitin kowa na murnan cigaban da aka fara
gani akansa din.
Lokacin tafiyana gida yayi don ganin matansa sun iso don ina kaucewa duk wani abinda zai iya kawo
muna fitina a tsakanin mu a lokacin tun bayan rabon duty da mama tayi muna a kansa din.
A haka kuma na kan dan samu daman leka school cikin damuwa da farga ban dai fahintar komai a
hakan bayan attendees din da nake dauka kada karatun nawa ya samu cikasa da yawa a lokacin gashi
zamu fara final exam din mu next week.
Abu ya taru yai min yawa a kai ga zuwa asibiti ga karatu duk nabi na fige hankalina ba a kwance ba
umma tazo kusan sau uku tana dubashi.
Hakama mutanen abuja sunzo dubashi din don a gaskiya zance a yanzu akwai sauki sosai saidai na
fahinci kamar hankalinsa ya dan gushe masa kuma bai magana bayan bude idon da yakeyi din .
Gashi kusan satinsa hudu ke nan asibiti har wasu kwararun likito suka consultants aka dauko don shi
suyi duba iya abinda zasu duba a kansa din magana dayace sun kasa gane ainihin abinda ke damunsa
din.
Exam din dana soma yasa sam banda lokaci ga yaya habu dasu mama sunyi min fada cewa na maida
hankalina wajen exam din tunda akwai mutane a tare dashi.
Amma matsala daya shine tunda ya fara dan budan idonsa din nan a ni kadai ake gane wani abin da
yake bukata wani lokacin ko ban kusa zasu kirani in zo in duba masu shi din.
A cikin hakan har exam dina yayi nisa sosai ga jinya ga kuma karatu wata rana ina zuwa mama ke
sheda min cewa tana ganin za a bar asibitin nan don tayi masu bayanin cewa su gwada dagashi daga
asibitin a gani kuma.
Munyi hakan da ita kamar kwana biyu na dawo ina hanya maria take fada min cewa an bar asibitin da
yaya an mayar dashi gida.
Jin abin nayi wani iri sai kuma na barwa zuciyana komai nake tambayan yanzu yana ina ke nan tace
yana gidanshi wajen matansa.
Saidai ance a tsohon part dinsu da suka tashi aka ajeshi ba a kaishi ainihin part dinsa ba don kada a
dameshi a nan din .
Ajiyan zuciya na sauke ina fadin to yanzu yaya zanyi Yanda tace dani ya habu yace dole can zan koma
nima mu kula dashi tare dasu saidai na dinga yi ina zagayen gidana.
Sam banji dadin hakan ba a raina amma na bar zancen kamar yadda tace nayi sai idan sun nemini da
maganan hakan na karaso gida a cikin bacin rai.
Don kuka dai nayisa a yanzu har na daina saidai tunanen zuci kuma dana koma yi wanda yafi kuka
wahala donshi yana cin jiki.
Nashigo nayi wanka tare da alwala nafito ina kimtsawa yaya Habu yayi salma a gidan hakan yasa na
fito daga dakina don ni kadaice yanzu a gidan Biba ta koma wajen uwarta tun faruwan al,amarin nan a
can take yanzu saidai tana zuwa kwana bibiyu da yan uwanta su gyara muna gida suyi min wanki da
sauran wasu aiyukan.
Na fito muka gaisa na samu wuri na zauna yake fadin bayan ki dazun mun bar asibiti da jafar yana gida
yanzu haka.
Na dago kai na kalleshi yace ehh saboda mun yanke shawaran a mayar dashi gida acigaba da wanan na
gargajiyan tunda duk munsan ciwonsa dai bana asibiti bane.
Don haka zaman nasa a asibitin baida amfani banda zaman kashin kudin da akeyi kawai naso a kawo shi
nan don zaifi jin dadi a nan din sai kuma nayi tunanen cewa mutane ba zasu gane hakan ba zasu dauka
da wata manufa muka kawo shi nan din.
So shiya dai na kaishi can aka bude masa part din mu a nan yake yanzu don haka nazo in fada maki
dole kema din zaki koma can din a yanzu har muga abinda hali zaiyi.
Idan ya kama din mu fita dashi wajene sai mu fita dashi din aje can a gwada sa,a kuma yanzu dai zuwa
nayi na fada maki zuwa dare sai ki shirya zan dawo in daukeki nida maria mu kaiki can din .
Hawaye na soma sakewa yake fadin kiyi hakkuri hakan jerabawan mune mu daku saidai shi dake
kwance ya fimu shiga wani rayuwa.
Don haka ki natsu banson kije ki biyewa Nusaiba kuna saida hali har mutane suyi Allah waddai da halin
ku ki natsu kisa ido ga jinyar mijinki shine abinda zai kaiki gidan.
Ya barni da zulumi ya tafi na rasa abin yi dole maria din na kira ta ban shawara na dauki dan abinda
zanyi amfani dashi a can din tunda ba zaman dindindin zan tafi yi ba gidan.
Hakan ya faru sunzo bayan sallah isha,i suka daukeni bayan yaya yayi gargadi ga maigadin mu na nan
gidan sosai akan ya kula da gida kada ya bari kowa yazo gidan ya shiga idan bani bace na turoshi.
Mun isa mun samu motoci biyu a gidan hakan na nufin akwai baki a ciki lokacin haka muka karasa ciki
da sallama abokanshine suka zo daga abuja dubansa suka samu an sallamishi suka zo gidan.
Suna zaune a falo dasu mama sai yaya ibrahim da zai zauna a na shima tare damu din suna bayani
saiga ya habu don shine a gaba aka gaisa ya kara masu bayani halin da ake ciki nan suke fadin har idan
za a fita dashi waje din ne don Allah su sani.
Da zasu tafi suka kawo kudi mai yawa suka bayar Asmau suka mikawa akai masu godiya suka tafi.
Sai bayan fitansune maman tudun wada ta juyo tana fadin kin iso yar nan sai kikaji shawara ya canza
mun bar asibitin ?
Ai nace habu ya kiraki ya sanar maki tun dazun din yace kina makaranta a lokacin idan kin dawo dai zai
sameki.
Ya habune ya shigo da kayana dan troler ne dana saka kayana a ciki sai sallaya da al,qura,n dina dana
dauko yana shigowa ya nufi ainihin dakin da suka zauna da maria don gadon dakin da komai yana nan a
dakin yadda suka barshi.
Ya fito yake fadin dakin nan zaki zauna ke Rahama mama dubune tace a nan zata zauna ke nan kuma ?
To me zata tsaya yi can mama tunda yana nan sai mama tudun wada ta karbe da fadin inba ita ba waya
san yadda zaibi dashi haka yadda takeyi ai itace dai karfin jinyar nasa ko .
Asmau ta miko kudin tana fadin habu ga kudin nan dasu Mansur suka bada ki bawa mama koda wani
abinda za ayi nan koda yske mu gani nawane ya mika hannu ya karba daga hannunta.
Dubu dari biyune yace ya juyo yana fadin ga dari da ashirin ku raba ku ukku sai wanan su mama kuma
su raba ya mika mata sauran.
Ina waje daya nida yar uwata a takure yake fadin tundazun barcin yakeyi ke nan mama tace ya bude
idanunsa dazun kafin magariba nan dai ya zauna suna hira dasu mama din da iya data shigo .
Saiba ce ta fara mikewa bayan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin aina zata ko mu nan zamu iya jinyarsa
ba sai wata tazo ba don me za a kawo Ramaah ace itace zatayi jinyarsa.
Keko kikan fara abinki ke nan mama dubu ta fada tace a,a mama abinda ake muna a gidan nan yayi
yawa ke nan dai mu bamu da amfani garshi yanzu sai Rahama ko ?
Yanzu meye abin fada cikin zancen nan wanda ke fama da kansa a yanzu har kun ga wajen wani fitina a
nan kuma ?
Ba fitina bane mama akan so a raina muna wayaune wani lokaci aiba a gidan nan take dashi ba saita
zauna gidanta tunda ba nan take ba.
Don me za a mayar damu yan kallo ace wai itace tasan kan jinyar sa to ai sai mu barta dashi tundaan
kawotane ita data iya ta kuka dashi.
Umm,uhmm duk abinda zakuce saidai kuce amma ba inda yarinyar nan zata a yanzu tunda itama
mijintane don haka wace bata hakkuri ga hanya nan mama ta fada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[4/12, 10:13 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to
join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kasamcewar manya a wurin hakan yasa na rakube gefe daya kokai ban dago na kalleta ba mama ke fada
da ita sosai hakan yakai ga tace da iya .
Lamarin yarinyar nan dole in kasance a gidan nan tare dasu don abin nata ba hankali sam a cikinsa .
Ga yaron nan kwance amma yarinyar nan bata saduda ba sai banzan haukan kishi da take kokarin
nunawa mutane ina ita din dai matarshice ko ?
Ko har da hakan baki yarda dashi ba na taba ganin wanan rashin hankali wanan ba kishi bane haukane
ai har yaushe mijiki yana kwance haka sharkaf a hannun Allah kika samu bakin kishi ?
Koda yake bata da laifi laifin Dubuce dake kama mata duk abinda tayi yarinyar ko yar gidan uban waye
aini bata kai min hakan ba na rasa meke damun Dubu akan wanan yar ?
Irin haka ai dole ta dauka kowa baida daraja a nan tayaya zan zauna matan dana tana wanan iskancin a
gabana ban dauki mataki ba ?
Har idan an barki dashi din uwar me zaki tsinana masa a nan din banda fitinan da kika saba don kinga
Dubu tana kama maki kafan iskanci.
Mama ba sai kin tanka mata ba ai ku barta muga abinda zatayi din a nan Rahama zata zauna har zuwa
lokacin da Allah zai bashi lafiya to ai shike nan mama ta kara fada.
Da farko banyi niyar zuwa dakin da kayana suke ba don wata zuciya dake dibaba akan na koma gidana
kawai in zauna yafi min sauki da zama nan tare dasu din da zanyi.
Sai kuma nayi tunanen idan nayi hakan ban kyautawa yaya habu dasu mama din ba wanan yasa naja
bakina nayi shiru saida aka rage a falon na shiga dakin komai a gyare yake tsab a dakin.
Sai yar jakata dake saman gado aje na dauka na bude wardrobe na saka a ciki na shiga bandakin nayi
akwala na fito sallah nafila nayi na roki Allah ubangiji ya tsare ya kareni daga duk wani fitina daka iya
tasowa a gidan.
Muryan mama dake kirana a falon yasa na fito take fadin zoki gyara muna wajen kwanciya ita wanan
mai sababin da a haka zata barmu mu kwana a zaune ke nan ?
Na gyara masu shimfida don a kasa sukace zasu kwana ni kuma na zauna a saman dogon kujeran da
aka bari a falon don zama don an kwashe sauran kujerun falon ankai ta bayan ginan .
Asmau ce ta fara shigowa da yaran ta ta zauna an dan jima kuma saiga saiba din ba wanda yayi magana
don kowa ya gane manufarsu a nan zamu kwana dukkan mu dasu ke nan abindai ba tsari gaskiya.
Ni dama ace rabawa akayi akan duk ranan da girki ya dawo kaina sai inzo nayi aikin da zanyi in koma
amma ba ace in dawo nan din in zauna haka a tsakaninsu ba.
Na dan jima a zaune na mike zuwa dakin bancewa kowa komai ba na kwanta don duk a gajiye nake
addua nayi na lumshe idona ina tunanen duniya.
A hakan barci ya daukeni ban sani ba barci ko sosai nayi don ban falka ba sai tsakiyan dare sosai da
fitsari ya tayar dani dana kewaya na dauro alwala na fito.
Ina sallah nake jin muryansu a falon sama sama hakan baisa na fito ba don ina son kama kaina don
gudun zargin kishi .
Har yakai ina jin muryoyin nasu sosai hakan yasa na daure nafito don na fahinci akwai matsala a
lokacin shina sama yanata kwara amai daga kwancen da yaken wani irin bakin amai kamar an wanke
bayan tukunya ga yawan yunkurin da yakeyi din sai ya baki tausayi don da gani cikin wahala yake
zuboshi.
Daki kamashi ya dago mama ta fada saita juyo ta dan dubi mama din tana fadin ni yaya zanyi in
kamashi haka mama ?
Ke yar nan amma baki da kunya dazun nan kike fada akan wata tazo ta taimaka yanzu kuma kice ke
baki san ya zaki kamashi ba ?
Duk yadda zaki kama ai kin sani tunda wace ke iyawan kin yakinceta da zuwa kusa dashi din yanzu ki
dagoshi kada ya sarke don Allah ?
Tayi kamar zata dagoshi din sai kuma ta fasa ta juyo gun mama din tana fadin sai wani ya taimaka min
hakan yasa mama tashi ta kamashi a hannunta ya karasa aman saida ya gama ta wanke mashi bakinsa.
Washegari kuma dai haka mama tasata gaba akab tayi mai wankan magani din a wahalce ta karasa
kwana biyun ta sai gashi wai ta kwanta bata da lafiya tunkan lokacin ta ya kare Asmau ta karbeta din .
Dole mama tasa na kama don Asmau ko wahalan goyo ya isheta haka dai ake rayuwan a jigirce don
kowa mama bata bari ba a cikin mu wanan zaman sai gashi an daina zuwa kwanan da aka fara saidai
wace zata karbeshi itace zata shigo koshi na dolene nikan da rana bani wuni dasu ina wajen exam dina .
Wani lokaci kona fito da wuri zan wuce can gidana in huta sai yamma zan dawo sun wahala lokacin don
mama zaune suke suna bada command kuma dole ayi din .
A hakan na gama exam din na a wahalce abin farun ciki amma yazo min da rashin walwala don ba wani
farin cikin da nayi da hakan asalima nasan dai faduwa zanyi ga jerabawan nan don banyi karatu ba .
Dole na mayar da hankali gun jinyar yaya don yadda ko ganina yayi na gitta ya kafawa wurin ido ke nan
bai kawarwa sai idan ya daina ganina .
Don a yanzu yana gani saidai ba magana ba kuma wani motsi jikinsa a sake yake kamar jikin ya mutu
nakan kebe in samu wuri inyi kuka mai isata in fito.
Tun dai ranan da Saare da Saiba sukai min habaici a cikin magana da Saiba ke fadin kwadayin wasu
baiyi rana ba don an kare a wahala.
A dama ai ance kuda wajen kwadayi yake mutuwa wanan kudan da alama kan a kwadayin za a mutu
don an fada ruwa tsundum .
Kudaje dai don ba kuda bane kawai mai kwadayi akwai sauro mai dafi yasha jinin na tare dashi acan
ake makeshi wajen kwadayinsa .
Wanda bai ko fara allon sa ba balle ya biya shikewa mai sauka shagube ai gara da wanda ya sauke yafi
wanda bai gwada saukan ba.
Ai Gara da kudan ya san dadin kwadayi don dai ya lasa din koda pdll
Qwya mutu, don ba duka kuda bane suke mutuwa a wajen kwadayi.
Balle shi wanda ko masunsuni bashi da yaje zagin mai kamshi,daji bai ga ma cin wuta balle aiwa
kututure barka da arziki.
Me kike nufi da hakan amsan zancen ku na baki indai kwadayi ya shigo dani gidan dan uwanki ai gara
dani na lasa keko dako gidan da zaki baki sani ba fa ?
Kina nufin bata aure ke nan kome duk yadda kikace inma haka kuka dauka don ba wace zatace cas
bance da ita kule ba a cikin ku.
Salatin da Anty barakha ta saka yasa mu kallon kofa ta karaso tana fadin wanan wani irin rashin
hankalone mijin ku na kwance haka a wani hali kuke haka a gabanshi don Allah ?
Anty yarinyar nan yar rainin wayauce daga muna magana da ta sako muna baki a zancen mu tana son
fadawa mutane maganan banza don tana ganin yanzu daidai take da kowa a gidan nan ?
Haba dai kamar ya daidai take da kowa dama ai daidai taken da kowa tunda itama aure take kamar
kowa a cikin gidan za ace ba zatayi magana ba kuma idan ya shafeta ?
To shike nan dama kuke nuna mata hakan shiyasa take kokarin dagawa mutane kai bar ganin a
kwanaki kin shanmace mu kina ganin kamar kinci galabane a kan mu lokacin ?
Ko zaku gwadane a yanzu ko zaku rama duk macen datace zata sakani gaba a gidan nan mu zuba da ita
ban shiga tsabgan kowa a cikin ku ba balle mace tace zata fada min magana na kyaleta ?
Abinda kowan ku ke takama dashi shine miji nima ina takama dashi a yanzu don haka kikai min ba
daidai ba sai dai muji zafin a tare dake wallahi.
Ramaah ki kyale zancen nan ku duba bawan Allah nan a kwance a