Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
suke kiranta da mai dauraren fuska haka suka gaisa a tsatsaye da
ita .
Gashi kuma tana tsaye ta tare kofa alaman bata son ta shigo daga ciki fuska a daure donshi suke
kiranta mai dauraren fuska bata da saki ko kadan.
Dan uwanta ta tambaya take fadin yana ciki hakan yasa tayi kokarin kutsawa taja gefe ta bata hanya
tashiga gaisawa sukayi take fada mai mahaufiyarsu da kawu ke nemanshi .
Yake fadin yazo ke nan kice ina zuwa daga haka ta juya ta fice duk da kayan dadin dake zube a gabanshi
yana ci da ace marainintane datace wanan fa yaya ?
Shikuma jafar zaice zoki zauna kice kodama batayi magana ba idan ta shigo hakan zaice da ita
bissimillah salima zauna mu karya.
Haka ta juya tana kunduma masu zagi tana fadin yaya J duk yafisu mutunci yan iska masu tsoron
matayensu kawai ?
Ta koma ta shedawa mama cewa yana tafe tashige dakin kwanansu ta bar falon a lokacin iya na can
tare da Jafar a part din da suke jinyarsa don maman tudu tayi tafiyanta gida tabarta dashi.
Saida Yazid ya gama karyawa ya shigo part din dauke da dansa a hannunsa ya gaisa dasu ya samu waje
ya zauna yana fadin fuskatan mahaifiyarsu yace.
Salima tace kina nemana mama kafin ya kaiga rufe baki uwar tace ehh ga kawun ku nan yazo akan
zancen kudin daka sameshi gidansa.
Ok kudin ya kawo ke nan yazid din ya fada yana gyarawa dansa dake gefenshi zama ya kyalla ido a
gefensu ko zaiga kudin sai dai baiga komai ba yasa ya fuskanci uwar dake magana.
Kaida kaje gunsa da zancen kudi kaika bashi kudin da zaka sameshi kai tsaye don rashin kunya ?
Amma ai mama kudinane ko hakkina don naje na sameshi ai ba zai zama laifi ba ko gyara zama kawu
yayi yana kallon yazid din cikin mamaki.
Eeh lallai yazid ni kake fadawa kudinkane ko yanzu da sauri yace haba mama kudinane fa hakkinane na
tambaya ba wani abu ba idan yazo da kudinne sai aban su mana shike nan don Allah ?
To baizo dasu ba mara kunya ko kuma radhin kunya zaka kawo muna yanzu tunda hakkinkane ta yaya
an mayar da abu kaddara zakazo da rana tsaka kace kana bukatansu a yanzu.
Mama ko kaddaranne a nuna min insan yarda na juyasu zuwa kudi don ina da bukatan kudi a yanzu ni
banja ba bance aban na kowa ba nawa nake maganan abina a yanzu.
Kai Yazid kagane ko kudin tun lokacin data bansu nayi dabaran sakasu a kaddara na sai filaye da
gidajen kango sai a sayar a kara sayen wasu a jingine haka nayi da kudin.
Ok to a kaini filin sai na saka nawa a kasuwa don kudi nake da bukata akwai kayan danayo oda zasu
shigo min zuwa wasu sati insha Allah.
Kai habu na fadama ka shiga hankalinka ba zancen kudin nan a yanzu sai ranan da kawu ya sayar ya
kawo maka kudinka idan lokacin hakan yayi.
Mama kudin nan kudinane hakkina da Allah ya wajabta a gareni ba don haka ina bukatan abina a yanzu
ko hannun wa suke kuwa ?
Kawu ina son kudina nan da sati daya kacal kudi ko kaddara a ban abina don ina da bukata akansu
yanzu.
Yazid ni kake mussu dani mama ta fada ya mike tsaye yana fadin Allah ya kara lafiya da nisan kwana
mama ni na isa inyi mussu dake kudina nake bukata kuma shina fada nan da sati nake da bukatansu.
In kuma har aka wuce sati gaskiya za,a samu matsala a tsakani gaskiya don kudina ba zasu wuce wanan
rana ba in sha Allah.
Yasa kai ya fice daga part din kallon juna sukayi tsakaninsu kawu ke fadin kingani ba Dubu aina fada
maki kamar yasha wani abu daya zo min gashi kuma ya maimaita agabanki kuma.
Ai kuwa bai isa ba yaya don na kula bayin kanshi bane don na fahinci an zugo yaron nan ne mai zaiyi da
kudi a yanzu hannunshi ?
Tunda kaf komai na dan uwansu yanzu hannunsu yake suke juya mai komai tunda ya kwanta din nan
dole akwai wanda ke zugashi yayi wanan abin haka .
Mama fa saare data dade tsaye kofan daki ta saurarensu tun shigowan Yazid takara fada hakan yasa
uwar ta juyo a hasale tana fadin meye ke kuma ko kema zancen kudinne zaki tayar min da hankali
kuma ?
Mama in tayar maki da hankali kuma kawai dai nima zance idan za a sayar da kaddarorin a hada nawa
don na fada maki ina son in fara sana,an kayan kitchen ne irin na Fatiq .
Lokaci guda kawu ya debe hulan kanshi yanawa kansa fitara a hankali ga zufa daya tartso mashi a
goshinsa salima tana kallon ikon Allah don ita kadai ta fahinci halin da kawu din yake ciki.
Jin yadda Mama din suke fafatawa da saratu yasa ya samu da kyat bakinsa ya budu yana fadin dubu
barinje sai dai kinjini kuma.
To yaya har zaka tafi kyale yaran nan kada ka daga hankalinka ga zancen nan don Allah rashin
hankaline irin tasu kawai sukeyi.
Ya dai samu ya fice daga gidan amma hankalinshi ba a kwance ba don yasan akwai magana yau ko
kaddaran da yake fadan ya saye baisan inda zaikai Yazid din ba.
Hana rantsuwa dai akwai wani fili daya saya amma karamine da niyar ya gina nasa gidan na kansa su
tare ciki da iyalinsa don wanan din da suke ciki ya tsufa sosai gashi kuma nagadone da yan uwansu dake
jahar Naije zaune saukin abin basu taba bin ta kan gidan ba tun bayan rasuwan tsohonsu da aka dan
samu matsala saboda makwabta sun sheda kudin iya yafi yawa a gidan nasu dasuka gina lokacin.
Hakan yasa suka fitar da ransu ga wanan gidan harma da yan uwan nasu sai Jafarne ma yake yawan
maganan cewa zai kaisu wajen yan uwan nasu shi kuma jiki yaki lafiya a yanzu.
Su din kuma ba wai damuwa da zuwan sukayi ba don kawu ya tsorata mama din akan bin yan uwan
nasu yace su din matsafane zasu iya tsafesu.
Iya kance komai tsafinsu kawu yafisu tsafi ai don zuciyarshi bata da kai zai iyayiwa koma waye mugunta
akan abin duniya idan ff,za,ff,fafamfaaftana masu wraffada kalaminta ke nan ga dan nata.
Kwantar da hankalina da nayi yasa nayi fresh dani nayi kyau farina ya fito fili da kyau idan kika dubeni
sai kin koma ina zaune a falon ummah nida saudatu mun
na kallo da rana.
Ummah ta shigo falon ta zauna tana fadin Yanda ta kiraki na dago na dubeta kafin na bata amsa da a,a
take fadin munyi waya dazun take fada min cewa.
Mijikin yanzy ya koma abin tausayi duk ya kara lalacewa ya rame halama kamar ciwonsa nason ya
dawo mashi saboda rashin kullan da bai samu yanzu sosai dama kece dai karfin jinyan nasa ai ?
Kaina kawar na mayar a tv ba tare danace da ita komai ba a lokacin saidai a zuciyana na fada nakeyi
ina fadin wanan shiya shafa a yanzu don sun fini sonshi ai idan ya halaka sun huta don kowa saiya kama
gabansa.
Haba dau uwata aida kinyi hakkuri kin koma Saudatu ke fadan hakan gareni da sauri na juyo ina fadin
in koma ina saudatu gara dai kowa ya taba yaji a yanzu ai.
Ba komai ya kawo hakan ba don itama maman tudu ta koma gida sati biyu ke nan yanzu kingako inba
iya ba a yanzu ba mai tsayawa ya bashi kulawan daya dace ?
Iyan kuma ba karfine gareta ba sai naji ummah tace mahaifiyarsu saida na juya idon nake fadin in kawu
ya bari ta zauna har ta kulashi ba ?
Ni dai sai ince auren ki da bawan Allah nan uwata auren kaddarane kawai amma ba wani jin dadi ga
hakan sai bakar wahala kana amaryan ka ko haihuwan farko bakayi ba zaka tsaya jinya irin haka don
Allah ?
Haba saudi ai hakan ma bautan aurene tasan irin ladan da zata samu a wajen Allah jinya takeyi fa kuma
na mijin aurenta.
Duk abinda kagani ya faru da bawa da sanin ubangiji Allah kadai ya san dalilin haka ga bawansa Allah
yasa hakan alherine gareta damu baki daya ummah ta katse maganan da hakan duk muka amsa da amin
lokaci guda.
Take fadin ni kingani nan saudi bawan Allah nan tausayi yake ban abu daine na dan yau wallahi da
yarinyar nan da daddy sunbi ta tawa datayi hakkuri ta koma dakinta hakana .
Duk abinda zasuyi ko suce mata ta sharesu kawai ladanta yana ga Allah haka kuma wata rana duk sai
labari insha Allah don gaskiya mutumin nan yana sonta banga abinda zata tsaya duban iskancin wasu ba
dama su ba son ganin ki sukeyi tare dashi ba ai.
Hakan da kikayi kuma ya basu daman samun kafan da zasuci gaba da musguna maki ai mutum in
makiyinkane kada ka yarda ya samu kafan galaba a gareka ?
Ina kurum ban tanka mata ba don nasan indon tasuce ita da yar uwata basuki in shirya kwatsam ince
na koma ba a yanzu din ba tare da anyi min gatan da daddy keson ai min ba.
Ummah kodana koma wanan matar bawai zata canza halinta bane a garemu na sani amma hakan zaisa
na samu dan dama a wajensu ai.
Ita Yanda mijinta yana tsaye garesu shiko wanan fa ummah bai iya katabus ga iyalinsa sai abinda tace
dashi zaiyi haka kanninsa mata.
Saidai hakan amma dai gaskiya ya ban tausayi sosai wallahi zan samu lokaci ai in kirashi mu gaisa inji
yaya karfin jikin nasa.
To hjy idan kinyi hakan ba laifi bane amma ya kamata kowa ya sharesu nan yadda suma suka share
kamar basu damu da itaba yanzu idan kin kira zasuga kamar kina bikonsune suzo nan.
Shiru nayi don gaskiya saudi ta fada ba karya a zancen ta don ko kowa bai fada ba mama zata iya fadin
hakan kuma naga zancen yayi tasiri ga ummah .
Don tace hakan ne kuma tunda matar ba mutuncine da ita ba ta fahinci hakan tun haduwanta da Hjy
Sa,a data hada ummah din da mijinta na yanzu da take aure.
Don yadda mama taso kushe abin sai Allah ya kawo ciwon Jafar na farko a lokacin hankalinta ya dauke
da jinyarsa har aka samu akai auren don hankalinta daya dauku wai a cewanta ga kawu nan ya nuna
yana son ummah din a lokacin.
Ganin yadda ya rame a kwanakin yasa mama din mayar da hankalinta gareshi saidai tafi saka rai da
fadan cewa saboda nabar gidan yake son ya halaka kanshi ga banza ?
Har yakai ranan ya bata amsa da fadin mama koda tunanenta nakeyi ai hakan ba laifi bane ki duba
yadda aka barni haka ba gyara ba komai kamar mara gata mama ?
Ace Asmau bata da lokacina saidai kwanciya idan anyi magana tace aiki yayi mata yawa a hakan kuma
take son in barta ita kadai ba tare da wata ba ?
To ai tasan hakan ba zai yiyu ba ita dai waccan mara hankalun idan ta gama shashancinta ai dole ta
dawo a zauna tare ai yanzu tayi hankali hakan ?
Wa kike nufi yarinyar nan Rahama kowa iya ke tambayan mama din tace Rahama kuma uwar yarsa dai
ta dawo ta samawa yarta abokan shawara hakana.
Bako a gidan nan ba mama don na gaji da fitinan Saiba hankali a kwance yake banson abinda zai raba
min hankali biyu yanzu kuma.
Rahama dai nake Habu nake son ya dawo daga legos zuwa jibi inbi bayanta in dawo da ita bakai kadai
zaka tafi ba dole uwarku taje har yaran nan suyo maka bikon matarka kamar yadda mijin uwarta ya fada.
Iya kikanso kamawa karya yanzu don ance sai naje shine zakice har dani zasu tafi in yabi ta tawace ai
ko zuwanma ba zaiyi ba shi balle aje zancen wai nima in shirya inje din.
Anya biyu kina kaunar dan nan kuwa duk cikin yayanki na kula Jafarune baki damu da damuwansa ba
dubu ?
Yau da kina da tunane da yarinyar nan batakai wanan lokacin ba a gidansu zaune da akace kece
matsalan dake da yayanki da tuni kin tasa keyan yaran nan kun dawo mashi da matarshi.
Amma da yake haka rayuwanki take kamar mara kwakwalwa Dubu baki san mutanen nan tarko suka
dana maki ba don su gaskanta abinda yarsu taje ta fada.
Ki barshi ya taka a hakan har kaduna tunda sakariya kike baki da lissafi kiga abinda zai biyo bayan
hakan a karshe.
Don ke da kanki zakiyi dana sanin rashin zuwa din duk ranan da tunane ya kara turmuze yaron nan har
ya kwanta a gidan nan don saura kiris a kai ga hakan yadda yaron nan ya koma don tunane.
Matukar kika bari har ya taka yaje bikon matarshi aka hana masa ki saurari naki bakin cikin da zaki tara
akan hakan tunda yaran nan suna son junansu.
Har yanzu kina wani zancen wanan mara hankalin ta dawo ta dawo a yanzu tayi mashi me yarinyar da
bata san Annabi ya faku ba har yanzu.
Matukar Rahama taki daaowa gidan nan dubu bake ba harmu ga baki dayan mu sai abinda zai biyo
baya gidan nan ya shafemu kaf a gidan nan .
In kuma kince a,a kada kije tunda kece sauniya mara hankali kawai ina mamaki matuka sauyawan
yanayin ki dubu ?
A yanzu kowa ya zuba maki idone yana kallon wautanki dubu kinsan farin cikin yaron nan kin kuma san
komai game da hakan ?
Ke yanzu ba abin kunya bane a gareki dubu yadda kowa yasan zancen da irin dawainiyar yarinyar nan a
gidan nan kan yaron nan amma ace wai har kin yarda haka ya kasance da ita akan yayanki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 9:31 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ya kasance jumma,ace ranan hakan yasa nayi kwaliya na dan gyara fuskana duk da ba inda zan fita don
tun zuwana ban fita ko ina ba.
Duba ga zancen daddy a gareni hakan yass na kara kama kaina ko marmarin fita daga gidan banyi dama
ba gwanar fita irin haka baceni.
Wasu material da ummah ta saya min duk da nace da ita kayana suna nan banyi amfani dasu bama a
lokacin saidai hakan bai hanata ta saya min ba.
Suna dauko na saka ance yaba kyauta tukwici kayan sun karbi jikina sosai zaune nake muna shan
ferfesu kwatsan muryan salima ya daki kunnena.
Wani irin faduwan gaba ya ziyarci zuciyana lokaci guda a daidai lokacin data tsaya kofan dakin tana
kara kwada muna sallama akaro na barkatai ana kuma amsawa tare da fadin tashigo mana.
Anty salima don har lokacin ina saya sunansu a yadda na saba kiransu dashi da farko tashigo ta sauke
idonta a kaina inda nake zaune kasa saman carpet tare da bin plate din dake gabana da kallo wanda
yake shake da koda zallah da saudatu ta gyara muna.
A,a kune a tafe salima tace eeh tare muke gaba daya ai harsu yaya da mama jin hakan yasa naso tashi a
inda nake zaunen .
Saidai na makara da hakan don sun riga da sun fara shigowa falon ko da sallamansu anayi masu sannu
da zuwa tare da dan kauce kaucen abubuwan dake gaban mu duk daba muni a cikinsa.
Saare da tayi zuwan dole tana ta faman mede muna fuska tana wani dube dube a falon suka zauna
kafin ta mayar da hankalinta a kaina.
Kallo daya nayi mata na fahinci ranta a bace yake wai ashe tun shigowansu kaduna ta soma fadin
amma mama yakamata mu leko su mami muga lafiyansu.
Shine ya yazid ya bata amsa da fadin ke saratu nan makirace watau kin kulla gulma duk wanda kikayi a
waya bai isheki ba sai kinyi na face to face a gabanta toba zamuje ba din din ba shi ya kawomu ba .
Saratu ai zaki iya sauka ki karasa idan kin gama saiki samemu mami kuma idan suna son mu ganta ai
sunsan hanyar gidan mu ko ?
Yatace mami amma bakin jinin dake zuciyana na uwarta ya sa a yanzu har ina mantawa da ita a yanzu
daga inda mama take zaune ta sake wani sallati tana fadin subbahanallahi kanka daya kuwa Jafar kake
fadan haka ga yarka.
Yarkace fa koma me uwarta tayi ma karka manta yarkace ai dinshi nace ina mantawa dasu a yanzu ya
sake fadan hakan.
Ita kuma mama sai cewa tayi lalai kanka ba daya bane Jafar na yarda akwai abindake damun
kwakwalwanka a yanzu to sai ita,,,,
Haba dai dubu don yaron nan ya fadi haka ai kinsan bacin rai yakaishi ga fadin hakan ku bar wanan
zancen tunda ransa har yanzu a bace yake game da yarinyar nan Nusaiba.
Ai don jan magana munafukar nan ta dauko zamcen Nusaiba din don irin haka tunda tasan abinda ya
kawomu garin nan .
Tasan ba wurin Nusaiba muka zo ba munzo bikon yar mutunci da sanin ya kamatane wacce tasan
metakeyi ba wace son abin duniya ya dama ba Yazid ke fadan hakan.
Wanan abinda yazid din ya fada shine yasa ta shigo gidan tana fushi duk gaisawan da saudi ke masu
fuskanta a daure yake ita.
Kafin komai har saudi din ta cika masu gaba da abincin karyawan mu da akayi hakan ba karamin
daukaka saudi din ta ja min ba duk da sunsan ba gidan ubbana bane nan din amma ko hakan yayi min
dadi har cikin raina.
Mazan suna waje basu shigo ba daddy ya fito suka gaisa dashi shi yayi masu jagora zuwa cikin gidan
nasu inda suka samesu a falo suna karyawa nan yazid ya hau masu sheri da sunshigo sun buge da cin
abinci.
Saudatu ce ta shigo take fada min yaya Jafar dashi akazo yana nan yana baza ido yaga ta inda zan fito
a gidan ai sai ya matsa na