Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
nan ya soma fadin tare da iyalinsa ina son kuji ku sani kada ku dauka ban san plan din ku
bane saboda kun daukeni bansan me nakeyi ba.
To ina son ku sani duk ranan da wata daga cikinku naji kona gani tayi fada ko tsangwama akan yarinyar
nan da aka kawo gidan nan zan ba mace mamaki sosai ga matakin da zan dauka.
Babu macen da zata hadani fada da dan uwana ko wani nawa a gidan nan mama ki duba matan nan
basuji kunya ba don Allah idan zanyi magana mama kice na barsu zasu canza.
Yau ace matar Habu ce datazo jiya jiyan don nan tasan tayi girki ta sako maku abinci har nima a saka
min don girmamawa da halarci wai kuma don suna dolaye sun kasa fahintar ma,anan hakan da yarinyar
nan tayi.
Aiko ita bayin kanta bane mijinta ko wani ya bata dabaran ta dinga hakan Saiba ta fada daga gefen
mama wajen da take zaune din.
Ban fada maki idan kina zancen ki kibar sakani a ciki ba habu ya fada a harzuke yana mikewa tsaye zai
dosheta don abinda ta fada.
Kai Habu koma ka zauna kada ka tako wajen nan mama ta fada mama ki bari in koya mata wayau don
Allah wanan yarinyar bata da kunya wallahi.
Kinfa ji abinda ta fada waini na koyawa Maria wanan hikimar idan kuma bani bane wani ya saka tayi
hakan tana nufin ke kenan ko iya ?
Ballema nice ta tambaya jiya da zata zuba ta kirani tace mutum nawane manyan yaya Habu a gidan
nan na fada mata amma wallahi ba wanda yasa tayi hakan a gidan nan .
Na fada mata basai ta saka ba tunda muna girki a nan muma tace a,a idan tayi hakan rashin kunyane
tayi girki iya bakinsu bata ba manyan shi ba da wani ido zata kallesu .
Don ya habu yana mijinta ai bashi kadai zata bawa abinci ba su a wajensu hakan rashin tarbiyane kuma
bayan hakan ina zata da alhakin kamshin da mutane sukaji a kanta.
Sare ce dake rike da labule tana kallon draman da yaninta keyi da matan nasu take fadan hakan amma
wallahi ba wanda ya saka anty maria zuba abincin nan.
Ita tasan darajan mutane tarbiyan data taso a gidansu cikine ta fara nuna muna nan koyin da gidansu
sukai matane take wanzarwa yanzu a nan.
Ai dama ko wani tsuntsu kukan gidansu yakeyi a duk inda yaje haka kuma Allah ke nan ya nuna maku
bakin cikin da kuke shukawa sarakuwarku gata zaune.
Yau ubangijo ya kawo mata yar da zata share mata hawayenta kuna kallo ban taba gani ko ji inba
gareku ba yau ace matar data haifi mijinka baka san darajanta a idanunka ba.
Uwar mijinka tazo ko ruwa baka iya daukowa ka bata balle abincin alhalin kuma dantane ya ya sayi
wanan abincin kika zauna kikaci har kina bawa yan uwanki amma ba zaki iya ba yan uwan mijin ki ba ?
A,a iya mu munga cewa abincin nan duk abinda ya kawo sai an kawoshi nan wajen ki shiyasa aka daina
zuba maku komai idan mun dafa.
Fau ya dauketa mari yana harzuka yace idan duk na kawowa iya ina ruwanku sai in zauna ku kashe
muna tsohuwa da yunwa kome ?
Jafarne ya dauke Asmau dake kusa dashi zaune mari ya mike yana fadin wallahi iya ban taba sanin
cewa basu dafa abinci da kuba a gidan nan sai yau din nan amma babu komai ke kuma zaki dawo ki
sameni ai bari ganin kin boye a bayan mama ya fada a hasale ya juya zai fice daga falon.
Kada ka daki yarinyar nan bai tsaya sauraro ba ya fice fada sosai iya da mama sukai masu Abubakar ya
mike yana fadin indai abincin part din kune na soke dama bansan ta saka maku ba da ban bari takai
maku ba don ku ba mutanen arziki bane kowa kuma ya sani.
Matan dake bakin ciki da yan uwan mijinsu kada wani yazo gidan nan ya ci wani abu daga jikin J basu
kaunar ganin J yaiwa wani alheri a rayuwansa .
Ina son ku sani ba J kadai yake da ikon gidan nan ba gaba dayan mune muke da iko a cikin gidan nan
har Ahmed da yake yaro yana da hakki a cikin gidan don naji abinda kuka fada ranan game da zaman mu
a cikin gidan nan.
Mama gata nan itace mukewa biyayya dagamu har mijinku din don ra,ayin mamane tagan mu a waje
daya haka zaune.
Ra,ayin uwarkune hadin kanku dana matan ku amma wa yan nan shedanun da Jafaru ya tara da
alaman zasu durkusar da wanan mafalkin na Dubu nason taga kun samu hadin kai tsintsiya daya
madaurinta ku daya.
Iya ta fadi hakan ga shi Habu da ya saura a falon yace basu isa ba iya kuma sunyi kadan mu zuba da
mace a gidan nan a yanzu zasu gane waye Habu ?
Duk abinda akayi ina zaune a gaban idona akayi shi har fitan matan yayan nasa da sukaji fitan mijinsu
suka koma part dinsu bayan sun gama koke kokensu don ranan mama ta nuna masu bacin ranta sosai a
gabansu.
Tunawa nayi da yar uwata da naji ana fadan wai bata da lafiya hakan yasa na mike na nufi part dinta da
sauri na sameta zaune a falo saidai yanayin ta kawai zai sanarwa mutum bata da lafiya.
Sam ban fada mata tashin hankalin da akayi ba balle in kara mata damuwan da na ganta a cikinsa
abinci na dora muna bayan tayi min bayanin abinda zan dafa saidai har lokacin zuciyata tana min
sake,sake.
Na wani irin rayuwa akeyi a gidan nan haka kuma yaya yar uwar tawa zata kasance cikin matan nan
dana hango rashin da,a a tare dasu dolene nima in zage a yanzu in kare yar uwata tako wani hanya .
Can wajensu kuma sai waya kowa keyi nan aka fara fadin mena fada maki saiba tunda kikace
bafulatana kanin mijinku ya dauko ?
Fulani da kika gansu mutane da akewa kallon basu san komai ba amma sunfi mutum sanin duniya kar
suke kallon mutum sun iya sace zuciyar duk wanda suke so su kuma nunawa wanda basu kauna boni a
cikin ruwan sanyi kin fara gani ke nan wanan ma ai kadan kuka gani indai bafalatanin mutum ne.
Wallahi mama saina nuna mata ba kowa take ba a gidan nan ba zan yarda da sherin daduk zatazo
muna dashi ba yar daji da ita kawai.
A dakin Asmau kuma yar ta ke fadi a cikin waya bance kada ki yarda da hadin kan Nusaiba ba Asmau
nusaiba munafukace yar iskace ta karshe irin na bugawa a jarida din nan amma kinki ki gane me nake
nufi ?
Ki zauna tayi amfani dake ta cika burinta a kanki ta fitar dake gidan kila lokacin zaki gane me nake nufi
da kalmana inba kina shasha ba.
Ta yaya zaki zauna yarinyar data hanaki farin ciki a rayuwanki kin sani wai ki dinga bin kaidin ta kuna
musgunawa uwar mijinku da kakanshi ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
1️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wanan case don da akayi shine mafarin komai a gidan har zuwa wani lokaci muna rayuwa dasune kawai
da sunan muna gida daya.
Amma hassada da kyashin duniya sun dauka sun dorawa anty Yanda dani kanwarta a gidan bamu da
da matsala da surukan anty Yanda ko kadan .
Don mutanene su masu mutunci daba zan iya fadan irin halarcinsu ba a garemu don sun rikemu kamar
mu din jininsune .
Haka muma bamu yarda wani rashin hankali ko sabani muyi kuskure a garesu idan mama ta koma can
tudun wada nice zanta hidima da Iya .
Wanda ban daukeshi wani hidima a wajena kafin na wuce makaranta zan tashi kiran sallah farko in
gyara part din tsohowar ko ince part din mu in dora ruwan zafi na wanka dana flask idan akwai
dumame in gyara muna don tafi son dumame ita.
Sai infito in share haraban gidan nan kaf ba zakiga wani datti ba a wajen gidan ko kadan saidai kafin in
dawo zaki matan part din yaya J sun jefo abubuwa sun bata wajen hakan bai damuna.
Don wanan kadanne daga aikin da muka baro a gidan baffa ba yabon kai ba nafi anty na kuzari nakan
gama nawa na hada da nata sai mun gyara garken shanu munyi ma matansa tatsin nono da surfe da
acan muka koya wata rana harda fura mu wuce kiwo.
Sai yamma lis zamu dawo gida mu sakawa shanaye hayaki muna kula dasu wanan yasa ban dauki aikin
gidan nan wani aiki ba a wajena.
Idan na gama inyi shirin school in wuce kuma ban makara tunda karfe hudu nake tashi zuwa
makarantar idan na dawo nayiwa iya dan miya ko abincin da take so taci a ranan kullum cikin saka min
albarka take.
Duk da haka kuma zan shiga wajen anty na na gyara part dinta don shigan cikin data samu mai bata
wahala hakan yasa yanzu da mijinta shima dan uwansa ya kadashi cikin business dinsa bai zama sosai a
gari idan bai gari abincin da nayi wajen iya mekeci tare da ita.
Duk ciwon da anty maria takeyi bai sa matan yaya J tausaya mata ba ba ruwansu da ita wai bata da
lafiya balle su tausaya mata.
Haka itama lamarinsu bai dameta ba idan bani gida ina school zata shigo wajen iya su zauna tare har
lokacin dana dawo.
Wani lokaci a nan zamu zauna sai dare zata koma wajenta wanan ya jawo tsegumi saidai ba suyi a
gabanta don ba ruwanta dasu ko abinda sukeyi bata kallon hakan don ita bata da yawan magana
kamata.
Don ni a cikin dan lokaci nasan mutanensu sosai har iya kan aikeni irin gidan Kawu dauda ko can tundun
wanda wajen mama .
Ko acan wajen mama da mukanje mata wuni wani lokacin nayi sabo sai da mutanen gidan don akwai
yan mata sa,anina da wa yanda suka girmemin a gidan.
Hakan ya jawo sabo sosai a tsakanin mu cikin dan kankanen lokaci wata rana na dawo daga school da
rana ina zaune muna hira da iya da antyna.
Anty Asmau ta shigo part din kallo guda zakai mata kasan bata da lafiya gaida ita mukayi na cigaba da
kankare kumbana da nakeyi .
Naji tana fadin iya don Allah nazo aron budurwan nan nakine taje ta taimaka min tun shekaran jiya
banda lafiya .
Girki nakeso dan Allah ta taimaka min har yanzu saiba taki dora girki kuma tasan banda lafiya amma
bata do,,,,,,,,
Jeki ki girka mata din saidai ki sani ba zan yarda da hakan kullum ba haba iya iya yau din nan ne ko
zuwa gobe dai haka har Allah ya ban lafiya.
Koma dai meye banson abinda zai jawo kace nace akan hakan son Allah iya ta fada tana kara kallona
tace min jekiki ki taimaka mata din kinji yar albarka.
Kallon yayata nayi tayi min alama da intafi mana tunda iya tace inje din tare muka shiga part din nasu
ga dai gida kan amma babu mata a cikinsa saboda kazanta.
Wani plate don yakai kwana bakwai a wajen wani cup har yayi huhuna da abinda akaci cikinsa aka
barshi nan kaya saman lafiyayyen kujeran dake falon kayan yayansu da nasu abin ba tsarin fada wallahi.
A kitchen din naga tashin hankali don tukwane abincin ne a girke da ruwa da ruwa duk sun yi babu
kyau gani a wajen hakan na tsaya saidana wanke tukunyan da zanyi amfani dashi lokacin na dora girkin .
Ban iya sakewa kitchen da kazanta haka dole na shiga wanke kayan dake tare a kitchen din ina
mamakin yadda mace zata samu daula haka kazanta ya hanata gyaranshi.
Lafiyayyen shimkafa da miyar kaza na hada masu fridgen din nan nasu dankare yake da nama haka
store dinsu kayan abinci a dankare kamar sun lalace a wajen gyara sosai na tsaya nayi masu tsakani da
Allah ga yarta dake ta kuka na dauketa na goya ta a bayana yarinyar tayi barci haka kuma nake wanan
uban aikin da ita a goye a bayana.
Banji kyashi ko kiuya yi masu aiki tsakani da Allah ba inayi ina gyaran falon ina duba girkin daya
gauraye gidan ba wani abu bane girki kamar mace ta tsaya ta soya kayan miya yadda ya dace .
Haka tayi amfani da sanadarin girki na zamani ko na gargajiya da muka sani wanda nagani a kitchen din
shi nayi masu amfani dashi a lokacin.
Na bude miyar naga ko ya isa daukewa saiga dayan matar ta shigo kitchen din ksllon mamaki take min
kafin ta karaso gabana tana fadin .
Banyi mamakin ganinki a nan ba tunda har ga yar gida a bayanki yau nagani nidai ki gama ki fito muna
dashi in diba na amsa da fadin.
Ba aiki ya kawo ni nan ba zuwa nayi in taimaka mata idan wace ta sani na girka ta fito sai ta baki daga
haka ban kara tankawa ba kuma.
Huumm,ummm kama kanki yarinya bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane nan ba wurin raininki bane
ko yarki bata isa ta kawo min rashin mutunci ba balle ke ?
Muryan Asmaun mukaji a bayan mu tana fadin sannu da aiki Ramaah yauwa sannu anty na kammala
na fada ina kokarin fita daga kitchen din.
Ai da kice min munyi sabuwar yar aiki a gidan nan Saiba ta fada sai naji Asmau na fadin .
Yar aiki kuma ina take kafin ta gano me take nufi sai tace haba dai kanwar tamuce kuma yar aiki daga
taimako ?
Ninaje gun yar uwarta na rokota tazo ta kama min kaina yana damuna da ciwo ga zazzabi kada mu
zauna da yunwa.
Ki duba irin aikin da yarinyar nan tayi muna kamar ba mutum yayisa ba cikin dan kankanin lokaci haka
ga kuma gitki .
Yarinyar tayi kokari gaskiya wanan matsalankice Asmau banga abinda zaisa na ja wa yanda sabodasu
akaci min mutunci a gidan nan.
Kitchen din na dawo ina fadin karbeta zanje nayi sallah ta mika hannu ta karbi yarta daga bayana zan
fice take fadin zoki dibi abincin mana ?
A,a akwai abinci wajen ,,,,,
Dakata don Allah Asmau nifa ban son kaskanci ki bari in diba inyaso idan na diba sai ta diba din wani
kallo nayi mata na wuce zuwa part din iya din.
Koda na koma suna zaune da anty da Yanda a falon suna hira na shigo na fada saman kujera sai iya ke
fadin har kin hada nace nagama iya.
Ai yanzu dai sunga ranan dan mutum ke nan yaro dama ba a haifeshi don mutum daya ba yau da babu
zaman mutunci ai ba zata zo neman alfarma haka ba.
Ina jin tsohuwar saidai na kasa magana saboda maganganun da Saiba din ta fada min duk da ban
kyaleta ba nima amma sai nake ganin ta shammaceni ai a lokacin data fada min magana irin wanan .
Asmau ta shigo da abincin a cikin kula tana fadin ga abincin Ramaah kinki tsayawa ki dauko a,a ba zanci
ba na fada ina gyara zama .
Tace saboda me ko akan maganan da saiba tayi zakiki karban abincin aiba ita ta sakaki ba nuce na roka
kiyi min kuma nagode da abinda kakai min.
Ita haka halinta yake bata da tunane sai ta dauka kowa bai isa ba ita kadaice ta isa a gidan nan shiyasa
ko yaushe kuke jin fadan mu da ita a gidan nan ai.
Ba ita ta sakani ba ai balle ta dameni na fada ta dan juyo tana kallona sai kuma tayi murmushi a
fuskanta tace.
Yadda kikayi ai naji dadin hakan Ramaah tayine don kada gobe ki kara taimaka min kiyi fushin zuciya
akaina haka take min wallahi.
Duk wanda taga ina abin arziki dashi duniyan nan Saiba na bakin ciki da maishi ko gaisuwa batayi da kai
indai ina hurdan arziki ki da mutum.
Aiko zata wahala wallahi indai Ramaah ce dama bata nuna hakan ba da dukkanku kunji dadinta antyna
ta fada tana dariya.
Daga wanan ranan da haka ya faru muka dan fara shiri da Asmau a gidan har antyna suna dan biye juna
sama sama .
A cikin wasa Asmau zata jani zuwa wajenta muyi gyaran daki haka yarta a yanzu yarinyar tayi mugun
sabo dani sosai idan ta ganni ta fara washe baki ke nan tana miko min hannu tana son in dauketa.
Idan na bushi iska zan shiga wajen anty Asmau din mu dan taba hira sama sama da ita wanda hakan
tun yana ba Saiba haushi har tazo takan dan saka muna baki a cikin maganan mu din wani lokaci.
Wani lokaci kuma kamar bata san da Allah ya ajeni ba takeyi ranan da yan iskan nata suke kai saidai
tayi ta jan tsoki tana jin haushi ta nuna cewa bata son zaman mu a lokacin.
Wanan yasa ban faye damuwa da ita ba ban kuma fasa shiga ba idan na bushi iska ranan da ba karatu
sai hakan yasa shakuwa sosai yashiga tsakanin mu.
Saidai matsalan ta shine kazanta da kuma rowa tana iya hanawa mutane abu koda ba zatayi amfani
dashi ba zata bar abin ya lalace saidai ta zubar dashi a karshe.
Amma yana da wuya tace maka gashi a cikin dadin rai saidai in rabon mutum ne ya ratsa a gareta sai
dai kuma anan saiba gaskiya a dan shigan da nakeyi ita saiba tasha bamban da Asmau din.
Don saiba ko bakaga abu ba zata iya cewa dake idan zakici abu kaza akwaishi a kitchen ko kuma idan
kun zauna kuna hira ta dauka abin ta mikama shi a gadarance ta juya bambamcin su ke nan.
Sakin fuska sai Asmau kyauta kuma Nusaiba amma wajen kazanta gaskiya a ganina kamar suna
kwatawa duk da ance wai Nusaiba tafita dama a wanan fammanin.
Nasan matan hausa sun