Chapter 87 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   87 / 101

258K to 261K   out of 302.2K words

zan manta da cin
mutuncin da kuka so min ne a baya ?

Yau gashi wace kukai min donta itace kuma ta kama dan barakha aitayi amfani gareku kuje kuyi tayi
idan muna funci abin yine ni dai nasan ban hada dukiyana dana kowa ba ?

Yanzu kuma meya kawo wanan zancen ga yar uwarka Jafaru jinin barakha jinin kane hakama naka jinin
natane dole ka rile dan barakha a duniyan nan itama ta rike naka.

Ma tukar ana son ayi zumunci mai,,,,,,,

Wani zumunci kawu irin zumuncin ku da mama kake nufi kome yan uwana dai masu kaunana saboda
Allah zanyi zumuntan dasu .

Kyaleshi kawu wani abu ya hau kanshi nake gani a gaban mu Jafar yake wanan magana yanzu ka
yankesu ka soya so wa yanda baka so din.

Basu dai sona mama ai su suka nuna min hakan ke zan fada maki da ga yau ki fita hanyana da duk wata
iyalina Saratu.

Na fahinci lamarin ki babu alheri a cikinsa ko daya don haka ba ruwan ki da iyalina na fada maki bake
kika auro min mata ba ba a karshinki take rayuwa ba ko gaisuwa na yanke tsakanin kedasu.

Bake kika ban abin hannuna ba balle ki kawo min izza da isa a cikin iyalina na fada maki .

Basu ba harni yar kallon lankwas nayi ina mamakin yaya J a lokacin don irin maganan da yake zarowa a
bakinsa.

Eeh lalai Jafaru yanzu na kara yarda cewa an wanke na fulani kuwa an baka kasha don yadda ka zare
din nan kai da bakinka kake fadan wanan maganan ga yar uwarka ?

Don tayi magana fadan gaskiya da wanan wawa yakasa fahintarta shine kake fadan haka a gaban kowa
yamzu ?

Mama nine wawa kuma sai yayi murmushi baiyi magana ba yazid ke nan ashe akwai abindaya kulla a
ransa ranan.

Shiko yaya yace meta fadawa Rahama yanzu in ita bata da hankali ai ita da iya sun bata amsan daya
dace ina magane akan shiga da tayi part dina jiya tasani meya hadata da Asmau jiya ?

Waini karata ta kawo a wajen ka dama ni kike tambaya karanki aka kawo wajena don kina yar iska ni
zaki tambaya don ban isa a kawo karanki a wajena ba ko ?
Wai meye hakane kukeyi yau zaku tararwa mutum daya kamar kuna hake da ita dama kun zauna baku
barmu munyi abinda ya kawo mu ba kan yaron nan sai zagin yar uwarku kukeyi.

Sakaiyan da zakuyi min ke nan a yanzu na fatana inga kanku ya hadu tun da raina kai jafar kake fadin
wai ka yanke alakarka dasu don mace ?

Ita Asmau ta kasa fada min ko meya sai ta kiraka nan don munafunci ta shiryama karya da gaskiya ko
mama akan me zata kiraki tunda bake kika ajeta ba .

Eeh lalai kuwa na tabbatar a yau din nan haka kace Jafar mama me zance tunda wanan yarinyar bata
son a zauna lafiya itace kadai kika dauka a yanzu kin haifa cikin mu ?

Yaya tashi muje ta fada tana mikewa tsaye cikina duk ya duri ruwa a lokacin don yadda naga ranan ya
rikide min ya koma malam jafar dinsa na gaskiya dake tsayawa ya fadawa ko waye gaskiya.

A,a fa mama nima dana ganta dashi sai da nayi mata magana nace hakan bai dace ba ace ta shiga har
dakinshi ta dauko mai abin amfaninsa haka ?

Tace ina ruwana ai ba nawa bane ni kuma na kyaleta tunda kona fada maki kema zakice aiba nawa
bane ta taba salima ke fadan hakan bayan sun mike din.

Mama ta juyo ta watsawa salima din harara sai kawu ke fadin a,a dubu abin amfanisa fa akace ta dauka
cikin zafin rai tace yaya don Allah ka barni ko ran jafar saratu ta dauka laifineb?

Balle kayansa ai bansan a jirace yake damu ba gidansa ka zauna a gindin mata suna rabaka da yar
uwarka dama ai haka suke so don burinsu ke nan ?

Gaskiya kai Jafar kuma bai kamata ka fadi hakan akan yan uwanka a gaban mu ba don dai kokarin
uwarku duk a kanku yake karewa taga ta kammalaku a waje daya.

Wasu kalamai yazid ya fada a cikin larabci wanda shi yasan meya fadi kai dai fada masu in aya ka jawo
koda yana da hakkon kan iyayyensa don tauye hakki bala,ine ?

Muje yaya mama ta kara fada tayi gaba ya biyota a baya suka fice gidan kallon Aminu yaya J yayi yana
fadin ka tashi ka bisu.

Sai yaron yayi kasa da kanshi bai motsa ba ya kara fadan bakaji me nace bane ka zauna kuma ?

Uncle ayi hakkuri don Allah a barni nan ni ba baeun ka gidan nan ba ban son abinda zai jawo muna
magana kan zamanka nan kaga yar iskan nan yanzu ta fara fadan ba daidai ba.

Ba abinda zai faru ka barshi a nan har aji ta iyayyensa jafaru tunda nan din yake son zama gashi anzo
ba a gane komai ba yar banzan nan mai bakin tsiya ta hana akai ga matsaya kanka ?

Waikai meya farune fada muna muji yazid ya fada aiyo yanzu naji maganan hankali wurin nan nan din
Aminun ya shiga basu labarin abinda ya faru kamar yadda mahaifiyarsa ta fada a waya.
Yazid yace ni yanzu yaya abinda naga yafi tunda har shi yace ya bar masa gidansa kan wanan zancen a
barshi nan ya zauna mugani uban zai dawo hankalinsa ya nemeshi idan bai nemasa ba fine sai a rikeshi a
nan din dama da gida biyu aka sanshi ai.

Yanzu kai ka saurareni kaji abinda yaya ya fada wallahi naji wani tsegumi ko kyam daga gareka game da
zamanka a gidan nan ko yaya bai koreka ba ni zan turaka kabar gidan nan.

In shaAllahu uncle ba za a samu matsala a wajena ba ya fada wanan dalilin yasa Aminu din zama a
gidan mu kuma yake amfani da hudubarsu a gareshi dama halinshine hakan shiru shiru bai magana .

Haka burin da mama taci akan zataci min mutunci nida jafar ya tafi a fushin da takeyi dashi gashi ya
nuna bai ma san tanayi ba.

Zai kira Asmau da safe kafin ya karya su gaisa yaji lafiyansu haka kuma da rana zai kira suyi ta hira da
yara don ita dai za ace gata nan daine da halinta.

Ban faye damuwa da lamarin su ba don haka banyi mamakin rashin zuwanta gidan mu wajen mijinta
ba kamar yadda shima din bai je gunsu ba a cikin sati biyun da yayi a gidan mu.

Duk da dama ba fita yakeyi ba illa iyaka dai idan wasu da baiso shigo mai gida suka zo shine yake fita
kofar gida ya samesu.

Saida yayi sati ukku cur a gidana ranan kwatsam naga ya kira yazid yana fadin yazo ya kaishi gida ya
dubu su daya gama shiri kuma yace min sai ya dawo.

Sai bayan fitansu nake ji a bakin Aminu daya shigo gaida mu da kwana yake tambayan uncle fa nace ya
fita yaje gida yau.

Sai naji yace dama iya tace in fada mashi yayi kokari yazo don rikicin kawu da uncle yazid da sukeyi da
sauri na juyo ina fadin rikici kuma akan me ?

Yace to ni dai naji kamar ana fadin rikicin kudin gadonsu uncle da mama saratu wai kawu din ya cinye
masu kudinsu na gado.

Wanan magana babbane ashe naji iya tace uncle yazid yana da gaskiya ita kuma mama tana fadin
uncle baida mutunci.

Allah ya kyauta nace dashi na karasa da abincin ka yana kitchen ka dauko ya mike zuwa kitchen din ya
dauko a nan falo ya zauna yana cin abincin nasa.

Yake ban labari akan zaman su yaya barakha da kishiyarta shike fada min yadda tayi da kudinta itama
da aka raba ta karba.

Yadda mijinta ya cinye kudin kaf babusu babu dalilinsu a yanzu ga kuma ba zaman lafiya a tsakaninsu
yanzu ya kare da fadin kowa gari ya sani da kudin ya kara aure ai.
Haba dai Aminu haka na yuyuwa kuwa ya dauki kudinta ya kara aure dashi shine ya shiga ban labarin
irin rikicin da akayi lokacin auren.

Yaya bai dawo gidan ba tun safe har dare nina daukama ya koma canne sai gashi wajajen magariba ya
shigo kwatsam kuma na gaidashi ya amsa ya samu waje ya zauna a cikin gajiya.

Na mike tsaye naje kitchen na dauko mashi ruwan gora da kofi na kawo mashi gabanshi ya dube ruwan
yana fadin anya kuwa zansha ruwan nan banci abinci ba tun karin safene a cikina fa ?

Na waro ido cikon mamaki ina fadin garin yaya kaiko kasan fa jikinka ba lafiya ko banza ni magani da
bakasha bama shine nake tunane ai ashe har abinci bakaci ba.

A kasale yake fadin kinsan Asmau bata da wayau taga na wuni a gidan ko ruwa ban samu ba a wajenta
balle abinci ina can muna fama da rikicin yazid da kawu tun safe don yazid yakai kawu koto.

Subbahanallahi na fada cikin kaduwa yace wallahi na mike ina fadin Allah ya sauwaka na nufi kitchen
don dauko mashi abincin rananshi dama na aje muci da darene.

Na dawo na zuba mai na zauna a kusa dashi ya soma ci yana fadin kinsan yazid tun ranan da sukazo
nan da mama tace mashi wawa shine yayi fushi ya samu kawu gida sukayi ba dadi zancen kudinsa.

Kudinsa ke wajensa ke nan ya dauki ruwa ya kora ya aje yana fadin duk abin nan baki sani ba a nan ya
koro min kan zancen tun farko.

Shi nake fada maki wanan kawu din ba mutumin kirki bane ya dade yana cutan mu ai yanzu mama ta
gani koda yake duk abin nan kamar bayansa take goyo har yanzu.

Yanzu sunso nasa baki nabawa Yazid kudin don rashin tausayi bayan kudin dayasa mama tayi ta karba
da sunan nema min magani yana debo ganyen banza yana kawo muna.

Shine na nuna masu ni a yanzu banda komai ga yazid ya hau gashi gobe za a koma kotu shine
hankalinsu ya tashi iya kuma taki sa baki a zancen.

Sai cewa tayi yaje ya nemowa yaro kudinsa duk inda ya sakasu jin haka ita kuma saratu ta sawa
mutane kukan banza munafuka kamar bada ita aka shirya hakan ba.

Na salima na fada masu yanzu kudin sun kusa ninkawa don na kara mata kudi a lokacin ake juya mata
abinta lafiya lau.

Lalai yau ashe kunyi shari,a babba ni karshe dai don kada suce zasu jani gobe zuwa kotunsu na nuna
masu banda lafiya don haka ba zanje ko ina ba.

Amma yaya dakasa baki a zancen ko baka bada kudin ba a maida case din nagida zaifi shiru yayi yaci
gaba da cin abincinshi.

Saida ya gama yake fadin nasa baki in biya ke nan hakan ya nuna bansan zafin kaina ba tun lokacin ai
ido nasa masu nasan haka za a kare don nafisu sanin waye kawu ?
Amma ita mama sam kome yayi daidaine a wajenta saboda ya gama da ita shida wanan bakar matar
nasa hafsatu munafuka ke nan ta karshe.

Dazun iya ke fada min ta kamasu suna fadin wai kece kikazo min da farar kafa komai ke samuna a
yanzu nan iya tayi masu tas ta fita.

Wa,iyazu billahi ni kuma nikan me nayiwa mutanen nan haka basu kaunata ina ruwanki da kaunar wasu
tunda ni ina kaunarki.

Nagane nufinsu ba yau ba duk abinda suke kitsawa a kunnena yake basu sani ba Allah dai ya ban lafiya
donsu yanzu a zatonsu duk na koma banda komai tunda basu ganin ina facaka irin da.

Addu,a nayi a raina Allah ya bashi lafiya ya koma harkokonsa da yakeyi Allah kuma ya buda mashi fiye
da baya ubangiji ya fitar dani daga zarginsu.

Ashe in ba a son mutum komai ana iya mashidon kawai a bata mashi suna nikan naga makirci ga
mutanen nan da shekaruna bakai ace ya dauka ba.

Amma nasan na farko mace tasa tsoron Allah a cikin lamarinta na biyu kuma ta rike gaskiya komai
dacin ta ta kama kanta da mutuncinta ta zauna lafiya da kowa.

Mun gama ya mike don yin alwala nikan cike da bacin ran wanan kazafin daya fada min suna min gashi
Yanda tunda sukazo da yara sau daya ta dubani bata dawo ba har wanan ranan ni kuma banje gidanta
ba.

Saidai mukan danyi waya da ita wani lokacin ta kirani ko ni in kirata hakan kuma ban saka komai a
raina ba iyaka na dauka a yadda ta dauka din tana gudun ace mun hade kai.

Ko wani magana ya tasone ace da ita don ita tun muna yara Allah yayita da ruwan ciki sosai a cikin mu
don tsoronta har ya baci donshi yasa ma nasa a raina zan daina biye mata don bafa zata gyara ba.

Anty salma na kira akan zancen ta bani shawara tare da kwantar min da hankalina akan zance na in
sharesu yadda nakeyi su da kansu zasu biyoni.

Indai daure in fita batunsu kada kuma in fasa alheri ga wanda yazo wajena inda nake.

Mun gama na kira yar aikin ummah itama mukasha hiran mu ta fada min wasu dabaru namu na mata
da zan kara dauka.

Ya shigo ya sameni kwance muna waya da ita yake fadin na zata barci kikeyi naji shiru ga danki nan ya
shigo yana neman ki !

Hakan yasa na fito falon a ranan na fahinceshi sarai so yake mu kasance tare dashi dama tunda na
dawo haka yake min idan yana son kasancewa dani da daren.
ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/26, 9:50 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



8️⃣8️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Wajajen shadayan rana muka iso gidan nida Biba da Aminu dana jawo yazo yaga gidan don ya sani irinsu
Yanda sune marasa marmari irinsune masu batawa fulani suna.

Sam bata da sabo ita bata da sakewa da kowa abu daine idan ance so to shi hana ganin laifine a wajen
wanda aka jefa da wanan kalman.

Don ko son da habu kewa yanda yasa shi bai ganin wanan halaiyan nata na daban da mutane ke fadi
kamar ace komawansu gidansu su kadai a yanzu din nan .
Ya kara nisanta ta da kowa yara kawai muka samu a falo suna waaansu ita kuma tana dakin kwananta
muka tsaya nan muna sallama yaron ya ruga daki ya kirata shi mai wayau din kaeamin kuma ya tsaya
yana kallon mu.

Haka ta fito sinkinkin da ita tana ganina ta dan yi murmushi tana fadin ashe kune tafe sannunku da
zuwa nima kwana biyun nan kina cikin raina wallahi.

Ban kulata ba na juya harshe da yare inawa danta Abba yaron baima san inayi dashi ba don bai san
abinda nake fadi da yaren ba na juya ina fadin amma kinyi sakaci da baki koyawa yaran nan yare ba nan
gaba zasuji haushin hakan.

Take fadin babansune bai so a koya masu yana fada idan yaji ana masu yare nace filatancine bai so
kome ?

Bata tanka min ba take fadin bari ta kawo muna ruwa ki barshi saidai su nikan a koshe nake ta dai mike
zuwa kitchen dinta wajen fridge dinta sai gata da gora biyu na ruwa ta aje muna .

Nan suka fara gaisawa da yaran kamar mintuna goma na mike da gaiya ina fadin zamu tafi dama
munzo kawai mu duba sune.

Haba Rahama tun yanzu ko zama bakuyi ba ina ce a nan zaku wuni ai a,a nazo duba yaran nan ne
kwana biyu bangansu ba.

Suma suna kewanki baba yace in ya dawo zai kaisu which means bada ita ba take fada min hakan kai
tsaye to ni zan tafi zamu biya gidan yaya Ai mu gaida ita.

Sai lokacin take tambayana waya kawoni nace Nape muka hau take fadin kuma yaya ya yarda to yaya
zaiyi tunda ba zai hanani zuwa in dubaki ba matukar ina da lafiya ?

Idan kinga ya hanani fitowa ya fahinci banjin dadin jikina shi kadai zaisa ya hani zuwa gidanki ko kuma
yana jin jalin maza a lokacin.

Dan kame kame ta farayi don itace ko yaushe take fadin mijintane yake hanata zuwa dubana ko tayi
mashi magana.

Daga gidanta gidan yaya Ai muka tafi saida mukai azahar muka fito zuwa family house dinsu mugaidasu
maman tudu.

Takuwa ji dadin zuwan mu din sosai don sabo a yanzu ya shiga tsakanina da ita duk da munci wani abu
gidan yaya Ai amma saida mama tasa mukaci dambun shimkafa a wajenta.

Ta sayo muna sobo mai sanyi mu kora sai hira take jana dashi bandai yarda na fadi wani abu mai muni
game da mijina ba ko mahaifiyarsa.

Mun jima na bata alherin dana rilko mata koda muka dawo gida mun samu ya rigamu dawowa halin
mazane don ko yayi fadan dadewan mu sosai.
Har in kaga yayi fada akan abu ransa ya baci da abin donshi nayi shiru na shige daki na sauya kayana
zuwa kitchen don yamma da yayi muna lokacin.

Har dare bai sauka ba yana fushi dani nidai ya dawo daga sallah na hada mai abincinsa na aje mai daki
na koma nayi sallah dana idar kuma na kwanta abina.

Daga falo ya kwala min kira nasan abinci zan zuba mai lokacin na fito na sameshi nima fuska a dare
nazo gareshi ya dago ya dubi fuskan nawa yana fadin abinci zaki zuba min ?

Nan ma banyi magana ba na duka na soma zuba mai abincin har lokacin ban cikin sakewa sai naji yana
fadin kin san bake kadai bane zaki fita tun safe har yamma haka ?

Idan jigila yaja maki wani matsala fa tunda jikinki ba karfine dashi ba har yanzu gashi ance ba,a son mai
ciki fitan yamma ?

Gidansu mama muka fito fa mun jima a gidan yaya Ai har kusan la,asar muna can

87 / 101