Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ta fada tana aje bowl din data riko
a hannunta ta samu waje itama ta zauna a kusa dashi ta fara gaida iya dake fadin Allah yai maki albarka
yar nan kinji.
Yanzu nake sababi da yaran nan suna daki sun mimike kafa wai sai yanzu zasu dora muna girki ta fada
tana kiciniyar budan kwanan gabanta din.
Nan Sare ta taso tana dariya ta karbe kwanon tana budewa iya ta soma fadin kingani ba, ki duba ba
kunyane dasu ba ai, ace mace na kwance wai tana barcin safe a daidai lokacin daya dace mace ta mike ta
dorawa mijinta da yara girki safe.
Idan baku koya a yanzu ba sai yaushe zaku iya hakan don Allah, irin wanan lalacin shike wahal da
matan shiyan can da yayanku yatara.
Idan baka koya a gida sai bayan kayi aure kace zaka koyi abu yanzu don basu koya a lokacin daya dace
ace sun koyi hakan ba yaushe zasu iyashi yanzu.
Dankalin turawane da kwai shake a cikin kulan da Sare ta bude din take fadin nasan dai wanan har
damune aka zuboshi.
Nasan baza a rasa ruwan zafin da za a hada shayi a nan ba ai shiyasa ban dauko ba maria din ta fada
tana kallon Sare.
Hakan yasa na fahinci ta zubawa kowane harni mu karya a nan din mikewa nayi na dauko plates s
kitchen na fito dashi na zama nayi na fara dibarwa iya dana fahinci tsohuwar tana jin yunwa a lokacin
don fadan da takeyi.
Na zuzuba masu a cikin plate na mikawa kowa nasa lokacin naji ya Habu ya soma magana yana fadin
Iya zankai Maria asibiti a dubata ?
Wani abin kuma ya samu maria din iya ta fada tana duban yar uwar tawa yace a,a iya zandai kaita a
dubatane ko da abinda zasu iya bata asibitin ?
Wani kallo tayi mai tana hade dankalin data tura bakinta dakyat tace Habu kana haukane da zaka dauki
matarka dake fama da laluran jinnu zuwa asibiti ?
Jinnu kuma iya ya fada yana kallon tsohuwar yayinda yar,uwata ta dukar da kanta kasa cikin sanyi jiki
nabita da kallo cikin mamaki jin abinda tsohuwar ta fada.
Kaga mubar zancen nan yanzu ka bari uwarku nasan tana nan tafe gidan nan taje ta shirya wajentane
ta dawo yau din nan don ta fito jiya bada shiri ba yasa ta koma gidan.
Sun dan jima a part din kafin su fita nabi yar uwata da kallon tausayi don na fahinci me iya ke nufi da
zancen ta saboda matar baffa dake fama da matsalan jinnu idan tafara lalura saita ba mutum tausayi.
A yadda naji yan rugga suna fadi lokacin wai saboda matsalanta baffa ya aurota don ta rasa manemi
baffa yace shi zai iya yanzu har ta haifi yaya uku da baffa lokacin da muke rugga din tare dasu.
Tuna hakan yasa hankalina ya daga sosai a lokacin gashi mijinta yana gari bamu samu kebewa da ita ba
tun safe saboda mijinta dake gari.
Misalin shabiyu saura mama ta iso da alama zata kwana biyu a gidan don bata saba zuwa da kaya haka
masu yawa ba idan zatazo.
Balle a yanzu din da taga inawa mahaifiyarta komai mama din ta rage zuwa sosai kamar yadda takeyi a
baya zatazo tayi sati biyu ko wata kafin ta kwasa ta koma gida kuma a yanzu saidai tayi kwana biyu ko
ukku ta koma.
Munyi mata sannu da zuwa nice na dauko ruwa na kawo mata tana zaune iya tana bata labarin yayan
matan mama din yadda suka kwasa dasu da safe.
Daki na koma tunda na fahinci kamar suna boye muna halinda ake ciki yasa na nuna ban damu da
insani ba nima saidai a zuciyana zancen jinnun da iya ta ambata yana daga min hankali.
Yar uwata da take kamar uwa a wajena tun tasowan mu da ita na bude ido yau naga tana son shiga
halin rayuwa duk da ta girme min nisa ba kusa ba amma tare muke komai da ita ko yaushe muna tare
muna gudanar da rayuwan mu.
A bakin iya nake jin cewa wai ashe sun fita asibiti a ranan duk data gargadesu da zuwa asibitin fadan da
takeyi da yaya Habu din a lokacin ya tayar dani daga dan barcin dana samu a lokacin.
Kiran sunana da ya habu din yayi yasani fitowa ina amsawa yake fadin naje Yanda din tana nemana a
part dinsu.
A kwance na sameta falo da alama sosai tana jin jiki don yanayinta daya nuna hakan sosai a lokacin
gaida ita nayi take fadin in gyara part din in dora masu abinci .
Cikin dan lokaci kankani nayi duk wani abinda ta umurceni da yi a lokacin na jera masu abincin dana
samu taci sosai saida mijin ya shigo wanda kallo daya zakai mashi kasan yana cikin wani yanayi na bacin
rai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
1️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sosai mama Dubu ta bada lokacinta tana kula da yayata haka kuma taja min kunne nasa ido kan yar
uwata sosai ga duk abinda zataci ko zatayi a gidan.
Hakan kuma nake wanan kokarin duk da a lokacin akwai sauran kurciya sosai a kaina amma ban fita
saina tabbatar da nayi komai daya dace a gidan.
Dana dawo kuma zan shiga in mata abinci da gyaran waje saidai indan mijinta yana gari dan yanzu bai
faye dogon tafiya ba sosai.
Koya tafi baifi yai yan kwanaki ba ya dawo saboda laluran matashi a yanzu duk da abin baikai daga
hankalin da kowa zai fahinci akwai matsala ba gareta.
Bayan kamar wasu yan satutuka ya Jafar daya je kasan waje kamar yadda nakeji a bakin matanshi da
yan uwansa ya dawo kasan.
Ranan Anty Saiba ta sauke jin kanta ta samemu a part din Iya zaune muna kallo take fadin Sare zuwa
nayi don Allah muje wajen mu ku tayamu aiki.
Anty Sare na mata ba,a da cewa lalaima ba dole ba maigida zai dawo ana mashi soye suka dan taba
ba,a zata tafi har ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin .
Ramaah har kefa zamuje don aikin yayi muna yawa sosai gashi rana yayi komai bamu hada ba yasa
nake son don Allah kuzo ku tayamu.
Mama dubu ta kalli inda nake zaune tana fadin Ramaah ai bata da matsala ga dai mashiririta nan su da
kika fara gaiyata ba komai zasuyi ba banda surutu.
Saida naje wajen antyna na gyara don mijinta yana iya fadowa ko wani lokaci gidan yasa koda yaushe
cikin tsabtace mata wajenta nake zakice ba wani mahalukin dake rayuwa a part din don yadda yake kal
ko dayaushe.
Nayi mamakin yadda na samu wajen nasu don na kwana biyu banshiga ba saboda exam din da mukeyi
banda lokacin laka part dinsu a yanzu .
Haka kuma iya ta hana wanan aikin da Asmau ke fakewa tana sakani a baya yanzu iya tayi mata gatse
da hakan yasa na samu ta shafa min lafiya.
Don wai ashe shigan cikine da ita lokacin yasa take narkewa haka bata iya yiwa kanta komai a
rayuwanta nayi mamakin yadda mata biyu zasu kasa gyaran wanan katafaren ginan nasu .
Su biyu sai yan yaran su amma part din har wani bashi yakeyi da tsamin dauda tunda daminane a
lokacin aka shiga.
Kitchen na samesu tsaye suna shawaran abinda zasuyi din ga dai kaya abincin nan amma da yawa sun
lalace saboda rashin amfani dasu da ba ayi sun lalace.
Wanan bashin kuma wai daga fridge dinsune wari ke fita haka da ace nice zan kwashe kayan nan kaf in
kyautar dashine in wanke fridge din insaka kamshi ko wani yaro ba zanso yaji wanan warin da fridge din
nan keyi ba balle babba.
Saidai kashh duk sherin da Sare ke zuba masu kwando kwando bai sa sun duba maike wanan warin
haka su fitar dashi ba karshe falo muka koma muka kara aikin ko a nan ma warin bai barmu mun zauna
da dadin rai ba.
A dakin Nusaiba maigidan zai sauka shine dalilin wanan shirin da mukeyi din inda Asmau take dakinta
tana shakar barcinta hankali kwance saida muka dawo falone hayaniyar mu ya tayat da ita ta kuma dan
jima bata leko falon ba a lokacin.
Saida ta bushi iskanta ta fito sabe da yarta a kafada da dan cikinta daya tasa kadan tana fadin duk aiki
ake sha hakane ?
Banza kowa yayi da ita ta samu waje ta zaune don sun fahinci kishine ya hanata fitowa a yadda na kula
su anty Sare sunfi kula Saiba bisa ga Asmau wata kila don kyautantane data dara Asmau din dashi ko
kuma wani abu can dai na tunanensu.
Dukko da cin mutunci irin na Saiba da nuna ita watace kuma matan wani saidai zasuyi fadan kiga sun
dawo sun shirya kuma dasu nidai wanan abin yana daure min kai dasu sosai wallahi.
Munyi cake dunut milk pop wanda a karshe aikin ya dawo nawa suka koma tayani don da ban wajen
shirme zasu tabka da hasara don basu iya kwabin bama balle .
Wasa wasa saida muka kai yamma don suyan kajin da muka tsaya yi wanda yayi ja gwanin sha,awa
dashi sai bayan magariba muka samu kan mu da aikin muka kammala .
Ni dai ina mamaki rashin ganin sun gyara falon gidan tsab da sauran part din gidan kosu Sare banji suna
masu tunin hakan ba a lokacin a kasan raina nake mamakin hakan sosai a lokacin.
Wanka na shiga antyna tana falo zaune tana azzakar Saiban ta shigo part dinta tana fadin ina Ramaah
ga dan abin da mukayi na debo mata.
Tana wanka Anty maria ta fada ta aje saman table suka danyi gaisuwa sama sama da yar uwar tawa da
sai bin wajenta takeyi da kallon mamaki don ko kai waye shiyan yar uwata dole ya baka sha,awa kome
tsab yake ga kamshi.
Ita Saiba zance baifi sau nawa ba duk dan zaman mu gidan data shigo part din sai wanan dalilin daya
kawota yanzu din.
Kodana fito wanka ta fice antyna ke nuna min nake fadin kici donni ya hau min kai tun a wajen suyan
da mukayi din na koma nayi sallah.
Saida na fito take fadin ina ganin Habu yana hanya Ramaah kallon ta nayi ina fadin ya bugo ke nan tayi
dan luuuu da ido tana fadin haka dai naji a jikina kawai kamar shima zai zo dai yau.
Hira muke jefi jefi da ita wanda hiran zaman mu na Abujane wanan abin da mukayi ya tuna muna idan
wani zai dawo gidan yadda akan wuni ana gyaran waje da aiyuka saidai su banga hakan garesu ba ko
kadan.
Karan wagale get din gidan da akayi ya katse muna hiran mu wanda mazan gidan ne suka iso lokacin
ashe zancen antyna gaskiyane ya Habu shine yaje ya dauko dan uwansa da yai wajen wata uku bai
kasan .
Ta window part din anty na muka leka mukaga tare suke ashe dukka su ukku har da wasu mutum biyu
a lokacin.
Ya Abubakar ya jima bai shigo part dinsa ba don sun tsaya a na sauke kayan yayan nasu zuwa part
dinshi na tsaya jiransa mu gaisa sai gashi ya shigo mukai mai sannu da zuwa.
Shi mutum ne wanda baida sakewa da kowa haka yake dunkunkun dashi ni ina mamaki ma yadda suka
hadu da yar uwar tawa haka.
In har kinji muryan yaya Habu yana tare da iya ne ko mahaifiyarsu saiko idan ransa ya baci zai tsaya yayi
fada akan abin ko kuma ya barka a cikin zullumin abin.
Bayan na gaidashine na shige na dauko abinda zan dauko nafice na koma wajensu iya a zaune na
samesu ga kayan tsaraban da aka shigo dashi part din tsofin a gefe daya an tara.
Ban zauna falo hira ba saboda gajiyan dake jikina na shige dakin kwanan mu nan ma ba kwanciya nayi
ba saida na dan tsabatace dakin har ban dakin kafin na kwanta.
Can cikin barci nake jin maganan su Saare dake fadin dama nasan wanan abin sai yaya yayi fada
wallahi idan ya iso ya samu waje haka.
Warin ne yayi yawa Salima ta fada tana hawowa saman gadon da muke kwana tare da ita tace na bude
fridge din aina duba naman kaine yake wanan wari haka.
Makin su zubar amma wai sun aje basu fitar dashi ba duk part din ya dume da warinsa ga kuma
kazantan dake falon koshi ai takaicine.
Banfa sa sunda yau zai shigo garin nan ba Saare ta fada nan nasa masu baki nace kuma gashi munyi aiki
ba a gyara falon ba saukin abin ita Saiba ta dan gyaro wajenta dazun din don kodana shiga na samu tana
gyaran dakinta ai.
To ai a banza Ramaah duk fa cikinsu babu mai tsabta a raina nace kamu na zagin koko ke nan kuma ai
halin kuka dauka na fada kasan zuciyana.
Sai gashi Salima na bata amsa da fadin abinda iya ke fada muna ke nan kullum wallahi nima dai
zagewa zanyi da koyon irin na Ramaah ina dan aiyuka a gidan nan don in saba.
Tabe baki Saare tayi tana fadin ko ita dake hakan ai halittance hakan bawai yin kanta bane muryan ya J
ya dakatar damu don tabbas a falon iya yake wanan tsawan.
Tsit mukayi a dakin muna saurarenshi yana fada ina zan iya kwana cikin wanan kazantar haka iya sai
doyi da bashi wajen keyi a nan dakin yusuf zan kwana yau.
Muryan mama naji tana mashi fada akan ya koma ya kwana wajen matanshi ai dole su gyara tunda ya
nuna masu bacin ransa a fili.
Can dai muka daina jin muryanshi a haka barci ya daukeni sai washe gari na falka don akwai gajiya
sosai a jikina na mulkan fulawan da mukayi jiyan.
Hakan bai hanani fitowa nayi aiyukan dana saba yi ba anan suka dawo suka sameni part din iya suka
nufo gaba dayansu shida ya Abubakar din.
Wanan ya hanani komawa part din na nufi wajen yar uwata bayan mun gaisa na karbi aikin da takeyi
din nacigaba ita kuma ta koma dakin kwanansu tana gyara.
Har inda na gama bai shigo ba dakina na koma nayi wanka na gyara jikina lokacin naji muryan shi ya
shigo yana fadin .
Bansan ya matan can suke son mayar da kansu ba gidan nan miji ya dawo tun jiya yake bala,i dasu
akan kazanta ki shiga ki saka hijab dinki kije wajen iya zamu zauna a nan.
Ma,ana dai a fahintana zasu dan yi magana da dan uwan nasa nan part din antyna ke nan hakan yasa
nayi sauri karasa shirina a gurguje na fito daga dakin kusan lokaci daya muka fito a dakin da ita.
Muna gaisawa dashi take fadin naje kitchen na fito mashi da kayan karyawa ita kuma naga ta koma
dakinta na dauko muka aje muka fito tare da ita daga part din.
A wajen muka samesu shida kawu suna magana muka gaidasu tayi mai sannu da dawowa muka shiga
ciki wajen su mama din dake falo suna duba tsaraba.
Shi tsaraba ga iyali wani abune mai daraja dana sanshi tun ina kankanuwa a gidan hjy Fannah Abuja
idan wani daga cikin iyalinta yaje tafiya ya dawo haka zai bimu da tsaraba gaba daya gidan ba wani raba
kai ko nuna muba yan gida bane a wajensu haka zasu kawo muna tsaraba mai yawa da sunan mu.
Haka kuma zamu dunguma anawa wanda yakawo din godiya group group yadda muke gidan tana
saka muna albarka gaskiya don in tuna da wa yan nan mutanen arzikin a rayuwana.
Naso antyna ta barni naje ko nidaya na ganosu tace min sai idan mijinta ya yarda da hakan dana kara
tuna mata kuma sai cewa tayi dani wai yace tare zamu gaba daya da ita tun lokacin ban kara magana ba
kuma.
A wajen su mama din gefe muka koma sai can mama din ke fadin idan kin tashi maria ga taku tsaraban
nan ta nuna mata wasu kaya harda na abinci shi yaya Habu din yazo ya kira mama din da kansa .
Sun jima a can har iya yayin da antyna ta kwanta a nan falon tana barci don maganin da take sha a
yanzu barci yake sata da zaran tasha maganin da safe.
Lokacin da suka shiga falon Habu din Jafar ya shakin kamshin da falon keyi ya dan lumshe ido yana
sauke ajiyan zuciya bin ko ina ya farayi da kallo komai gwanin ban sha,awa awajen, irin falon da yake
muradin samu duk da part dinsa ya kusan ukun wanan din amma kazantar matansa ya hanasu tsayawa
su gyara din.
Duk da komai na zamani na more rayuwa ya zuba a falon gwaunin ban shawa amma komai yazo ya
koma masu shara a yanzu don rashin kulawansu.
Yana mamakin irin halin da matan nasa suka dauko yi mashi a gidan gaba dayansu ba wace zai buga
gaba da ita a wajen tsabtan muhalinsu wanan abin yana matukar kona mashi rai.
Nan ya Habu din yake gabatar masu da abin karyawan da aka aje mashi din a tare su ukkun suka karya
a nan mama tazo ta samesu a part din don zancen dasuka zauna suke son magana da yaran nasu baki
daya.
Zama sukauyi na fahinta yadda ya dace din a tsakaninsu kan matsalolin da malami ya fada a zancenshi .
Wanda kusan abin duk kamar akan shi yaya jafar zancen ke nufi da magauta suna binsa sosai bayansa.
Sam bai dauki zancen da wani ma,anaba a wajensa don bai faye yarda da irin zancen malaman nan
bashi kawune ma ke kokari ko yaushe akansa baiki yake karba.
Yanzunma bai ki ta bakinsu ba don yasan dolene irin wanan harkan nasa ya samu irin hakan bayan sun
gama kuma sukayi zance akan matsalolinsu inda harda zancen yayata ya fito cikin zancen.
Don asibiti suna son su riketa