Chapter 76 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   76 / 101

225K to 228K   out of 302.2K words

ke kadai kina shanawa ba dole kiyi sheki ba haka
?

Wani anbar mata miji a ina saida aka gama abinda za ayi don dai ita bata san zafin kanta bane ai ina
zan zauna mace na shigo min gida tana min feleke da yanga ana iskanci da sunan jinya wallahi ba a haifi
wanan yar ba tukun .

Komai sukayi ai don kansu saratu balle ma me akeyi duk abinsu dai basuyi da ranana balleni kome
zasuyi yanzu ai na saba da ganin hakan akan mutumiyarki Nusaiba bai kuma daga min hankali ba balle
wanan din.

Sai naji salima tace ballema me akeyi maganan kice dai kawai saratu da wani tashin tashin dinki can
daza ki kawo za,a hanata zuwa duba mijintane kuma ?

Wayace za,ya hanata yanzu don Allah ni dai banson abinda zai hadani da wanan yar kauyen yarinya
dake ganin daidai take da kowa yanzu gidan nan.

Jin nayi shiru ina saurarensu yasa mama soma fadin zaku fara takale takalenku ko ku jawa kanku zagi a
karshe a juya maganan kuma .

Ko yaushe ina muku fadan irin wanan maganan dabai shafeku ba amma baku jin kashedin da nake
maku ina ruwanku da shanawanta yanzu kuma ?

Sallon ku hada wani fadan kuma kenan a yanzu tsakaninsu ana zaune kalau maman tudun wadace take
fadin hakan a garesu rai bace.

In sun jawo magana ai suji dashi ni ina ruwana tunda ban aikesu ba sun daiji abinda yazid ya fada game
dasu ai ya karya yarinya ba wani abu bane wajenshi.
Ballema mama waye zai dauki zancen su tunda ba sakarai nake ba kawai dai magana ce mukeyi sai
kawai saratu din ta mike tana guna guni ta fice .

Ashe fadi take don an mayar da mutum baiyi aure ba za a dinga mashi abinda akaga dama karya ta fada
ba cin amanan akeyi ba inba hakaba ya akayi tayi ciki yanzu ?

Na jima a zaune nayi shiru kaina kasa gaskiya wanan mace tana son shiga min rayuwa duk dana
tattarata na watsar gefe daya iyakata da ita gaisuwane wata rana kuma bamu ko gaisawa din da ita haka
zamu share juna.

Tace ita danyar kai nace na fita muje zuwa sai hakan da nake mata kuma a yanzu ya koma bata haushi
tana jin kamar ta shakeni ta kwantar.

Wai ashe bayan tabar part din takoma nasu shine taje ta kira saiba a waya tana labarta mata duk
abinda aka fadi abu ga mara hakkuri saiga saiba din ta kira Asmau tana zagin ta.

Muna ciki din mukaji Asmaun na fadin ita saratun din tace hakana wai meyasa saratu keda tsegumine
wai ?

Shiru daga ita har mu wajen yayi can ta soma fadin Nusaiba na fada din ina ruwana da duk abinda
zasuyi ke bakiyi min wanda yafi wanan din bane aiba karya na fada ba ko ?

Mama tudu ta mike ta isa tana fadin wai meye kuma yanzu ita yarinyar nan dan maganan nan saida ta
kira yarinyar nan tun ba a bar wajen ba ta fada mata ?

Anya kuwa saratu kanta daya kuwa da wanan halin ke mara kunya an fada din ai idan bakiyi ba ba zata
fada ba ai wanda ya mutu akewa karya.

Mikewa nayi na fara hada kayana don tafiya kallona yayi yana fadin ina kuma zaki yanzu na amsa da
gida rai bace ban yarda na kalleshi ba.

Abin yana ban haushi duk da nasan yana cikin halin ciwone a yanzu amma kuma a yadda na fahinceshi
shine gaskiya duk cikinsu kamar kannensa sunfi raina shi don me zatayi ta min hakan ko watan mu ya
kasa daukan mataki idan kuma ka dauka da kanka abin ya zama laifi a gun mahaifiyarsu.

Ganin ban kulashi ba yasa shi fadin ke Rahama kada ki bari raina ya baci dake gurin nan badake nake
magana bane wai ko sunyi dakene yanzu ?

Jin abinda ya fada yasa na kara dagowa na dubeshi cikin mamaki banga laifinshi ba kila son yana namiji
yasa bai fahinci zancen daga farko ba.

Ko kuma wata kila baiji farkon maganan tasu bane sai tsakiya yasa yake fadin zancen bai shafeni ba ai ni
dai na hada kayan na koma falo na zauna na barshi nan.

Tunane nakeyi a raina ya zama dole nasan yadda zan daukarwa saratu mataki ta daina aibantani ga
bakinta a yadda na fahinci maganan ta dai shine.
Ina fakewa da cewa ina jinyar yaya ga hakan na shammaci abokan zamana ina kwana da miji ni kadai
har ciki ya shiga ba yau ta fara fadan hakan ba karo na biyu ke nan da irin hakan ya faru.

Wata rana muna zaune a haraba ana hira ake bada labarin wata wai bata da umma asalinta me saratun
zata fada daga inda take zaune tana dakilan waya sai cewa tayi ai ance basu bane shegu.

Shegu suna gidan aure inda ake daukan kwanan wata a samu ciki a haifi mutum wanan dan da aka haifa
ya zama shege sune shegu na asali da akasani ba wai wanda aka haifa a wajen iskanci ba haka ?

Wanan abin ya tsaya min a rai tun lokacin duk da maman tudu ta tsawata mata don ta katseta da fadin
to malama inji wano nafsin ya baki wanan fatawan kuma ?

Kinhanki saratun nan a yanzu kan gaskiya baki iya zama babban gidan mu saidai ki koma rabe rabe a
nan tunda har kin san wanan kikaki kawo miji kiyi aure ki huta.

Ai mama Allah ne bai kawo mijin bata fada cikin tsigar rashin kunyarta datakewa mutane nan mama ta
rufe ido tayi mata tas a lokacin tace sai inci ubanki wajen nan niko uwarki bata fada min maganan banza
haka ?

A wanan lokacin har mama tayi fushi tana fadin gida zata koma bata zama tana kallon wanan fitsaran
haka saida sukai ta bata hakkuri shine yazid ya kusa halakata din a lokacin sai kuma wanan karon da ta
sake maimaita abin shigen hakan.

Tunda na zauna a wajen baiyi magana da kowa a cikinsu ba ga Asmau sai maimaita abinda Saiba ta
fada mata takeyi amma hakan baisa na tanka masu ba don zuciya daya zo min a lokacin.

Ba karya nasan ina da wanan zuciyan wanda idan nace zanyi magana a lokacin tabbas hakan zai iya
jawo muna gagarumin rigima a ranan.

Saidai kashh jin yadda Asmau ta matsa da zancen har take fadin indai don wanan da akeyi yanzune ai
ba ai komai ba balle ko a gabana akeyi hakan bai taba damuna ni.

Ai yin ma isace idan fitsari banzane kaza tayi mana Allah ne sheda ta koda hakan ya faru nasan
kaddaratace a hakan amma a cikin kiyayyewa nake don ni din ba jahila bace kamar wasu nasan abinda
nakeyi ban shiga hakkin kowa ba har na samu wanan cikin .

Da za a zauna ana fada min magana inma shegen ne nayi tare da yayanta muka aikata hakan don ba
zina naje waje nayi ba balle a zauna a fada min magana haka kamar nice farau.

Sai a bari tunda yaya yana kwance nayi cikin idan na haihu aje asibiti a auna dan idan ba nasa bane sai a
ban in tafi da abina .

In kuma nasane zan shayar daku mamaki a gidan nan don sai nayi karan saratu a wajen hukuma na bata
min suna da take kokarin yi a gidan nan.

Yau dai ko saratu kishiyatace ya tsaya a hakan irin abinda take min kawai ta koma can gidan takama
daki daya mu zauna a matsayin kishiya da ita insan zaman miji daya mukeyi da ita a gidan nan.
Naji ina cin amanan su saidai zaki bada dalilinki gobe gaban Allah don ba yafe maki zan taba yi ba
saratu sai kin fadawa Allah cin amanan da kika sheda nayi masu a gidan nan.

Ke kuma Asmau indau zuwa duban yaya da nakeyi gidan nan ne na daina daga yau ba zan sake leko
gidan nan da sunan gaidashi ba balle na kwance maki mijin ki duk ranan da Allah ya bashi lafiya in zai iya
zuwa gidana yazo idan ba zai iya ba kuma yasha zamanshi nima nagaji da wanan wahala haka .

Na juya zuwa ciki na kwaso kaya ban ko kalli inda yake ba balle su mama get din gidan na nufa na fice
ban sake juyowa na kallesu ba .

Yau nasan yarinyar nan tsatsan bafulatanace ashe haka ai basu iya fada ba ransu bai iya baci ga abu ba
to yanzu dai ankai ga yadda ake so ai ina kula yarinyar nan ko zuwa tayi gidan nan an kama sakin magana
ke nan ana mata haibaici tana sharewa tun farkon lamarin nan .

Shin garekune farau zama da matan yayyu koko kun zama yan idone da ba a kwaba muku ku auren dai
ai kowa zaije yayi yaji abinda ke cikinsa.

Ba yarinyar nan ba koni yau zan bar gidan nan tunda Jafaru ya fara samun lafiya nake ganin abubuwa
daban daban daga gidan nan hadewa kawai nakeyi .

To Alhamdullahi tunda Allah ya bashi lafiya a yanzu Allah ya kara mikar muna dashi lafiya amin daga
kofa ya dogaro yana fadin ta wuce ko ?

Maman tudu tace dole aita wuce tunda sherin har yakai na sheganta mata abin cikin cikinta a gabata
kuma ba a dauki wani mataki ba ko nice ai zanwa kaina gata.

Saidai ku sani yau abinda baku sani ban kan yarinyar nan tayi abinda duk cikin mu nan kaf babu mai iya
yinsa ga yaron nan.

Itace zata hana kanta barci ta kwana tana masa karatun kur,ani tana sallolinta tana bashi magani tana
tofeshi ko yaushe ka falko kana iskata a kan shi tana mashi addu,a.

Tau ku sani idan jinyar yaron nan ya koma kasa kada kuyi kuka da kowa kuyi kuka da kanku wallahi don
daku aka hada kai aka koreta a gidan nan yau.

Dama makiran kishiya tafi mai fitina hatsari don gara mai fitina tana fitowa fili ka fahinceta amma
wace ke sari ka noke itace guba mai cutarwa farat daya.

To yanzu fissabillahi yaya daga dan maganan fatar baki saita kwasa tayi fushi tana fadin magana haka
dama dai ai sallon ta samu hanyar kubucewace tayi don ta nuna ta gaji hakana ?

Yanzu idan bata zo ba sin yadda tace ai zai nade ya bita can din inda ta saba cin karanta babu babbaka
ana kallonta can ko sai abinda taga dama tayi.

Itama yar kauye tasan tayi wanan shirin ga mutane balle muna da aka haifa a cikin gari taje wa
zuwanta ya dama a gidan nan koda ita ko ba ita in Allah ya bashi lafiya sai ya mike da yardan Allah.
Kaico iya dake tafe tana gyara daurin dan kwalinta take fadin haka badai da abokiyar zaman naki ba
kuma kike wanan abin kunyan haka ?

Aa,ha iya badani bace da dai sarakuwartace da yaranta tunda su ba ai masu fada nikan ai kafin nima su
koreni din yau zan koma dakina insha Allahu kar abin ya juyo kaina yanzu kuma ?

Yaya sai kinso saka kanki cikin zancen nan gaskiya don wallahi dai bada ke akeyi ba kin sani yaran nan
kuma kin dai san dan yau banice zan turasu sunawa matan dan uwansu haka ba ?

Wai sai meyasa matan jafar ne ko kafin yarinyar nan ta auri Jafar ai yar uwarta habu ya fara aurowa
gidan nan da zaku dauki karan tsana ku sakawa yarinya guda duk kokarinta ga dan uwanku.

Aike Amina baki sani bane dan uwanne nasu basa so shiya kawo haka kiyayyan jafar dasune ya shafi
amaryansa .

Haba iya in antashi magana kiyi ta hadawa dani don Allah ni yanzu mena cewa Rahama anan daga
muna maida maganan zagin da Nusaiba tayiwa Asmau shike nan fa tayi fushi inma maganane ai ita
Asmau itace ke fadin magana da har ya shafeta ni meye nawa a cikin zancensu.

Tun bayan fitana daga gida kuka baizo min ba asalima taxi na tare zuwa gidan saidai inata faman
sakawa da kwancewa a kasan raina.

Ina shawaran barin garin a ranan in nufi abuja ko adamawan cameroom gun yan uwan mu zaifi min
sauki a rayuwata sam ban taba nasa cewa zanwa wani shige shige a wajen boka ko malami da sunan in
kuntatawa wani.

Amma sai gashi ban tsira wajen sherin abokan zama ba kullum duba sukeyi ina da asirin da nakewa
mijin namu yasa bai yarda yaga laifina.

Duk magana idan zai taso nice wai za a bawa gaskiya na sani ai na kuma san irin azaban da Allah zaiwa
mutum.

Nagama komai na shiri kwance na dawo falo don in danci wani abu duk da bakin nawa ba dadi a
lokacin amma haka nake daurewa kamar yadda manyana suka fada min.

Ance in daure ko bakina ba dadi in dinga cin abincin ya kasance ina da kuzarina dan kada na lalace abin
cikin cikina kuma zai wahala .

Fruits din dana sayo a hanya da zan dawo na yanka nake sha naji bugun kofa don munyi da Biba saida
safe zata dawo ranan don haka ni kadai ke nan zan kwana a ranan sai megadin gidan dake waje.

Daga ciki nake tambayan ko waye muryan ya Yazid naji yana fadin bude mune da iya hakan yasa na
dauki gyalena dake gefe na yafa akaina na bude kofan.

Shida iyace sai matarshi da yaransu sukazo na danyi murmushin dole a fuskana ina fadin kune a gidan
yau ?
Ba doleba ance amarya mu tayi fushi harda rantsuwa ba zata sake taka gidan muba murmushi yake na
komayi ban daiyi magana har lokacin.

Muka samu waje muka zauna dukkan mu a falo na mike na dauki sauran fruit din a cikin fridge din na
kawo masu sai bin ko ina na fidan sukeyi da kallo.

Iya ke fadin kagani ko na fadama ko acan din tauye take don laluran nan ne kawai yake kaita amma
yaran nan yau saida suka kure hakkurin yatinyar nan.

Ai tunda nadon su takeyi ba iya ba zatabi ta nasu ba tace bata kara zuwa ganinsa yanzu gashi can kun
barshi ya rikice bayan tafiyan ku ita mama tayi fushi ta wuce gida ke kuma kin dawo nan ke kadai ina
yarinyar da kuke zama da ita din ?

Saidana hade wani malolon bakin ciki nake fadin tana gida yau yar uwarta ta haihu suna suna sam banyi
tunanen zaki bari suci galaba akanki ba ai tunda kinsan da gaiya suke abinsu.

Kowa yasan meyasa Saratu take hakan ni dai na dauka ba banza take hakan ba don ban taga ganin inda
mutum yaki dan uwasa ba haka ?

Amina tun bata kai gida ba nasa aka dawo da ita kema munzone da safe idan Allah ya kaimu ki shirya
yadda kika saba kizo ki duba mijinki kinji na amsa masu tare da godiya.

Sun dan jima a zaune iya ta matsa akan su tafi dare yayi don sam ita bata fitan dare wanan fitowan ma
ya kanane haka.

Nayi masu rakiya akan washegarin zan shigo suka tafi matarshi sai bina da kallo takeyi kawai don
hausan a lokacin take koyonsa.

Bayan sun wuce ina shiga daki na jawo dan jakkata na hada kayan bukatana a cikinsa nayi ready komai
na saka a jakar safiya kawai nake jira a lokacin.

Barci sama sama nayishi a ranan don abinda na yanke a raina gidan ga baki daya ya fice min a rai abin
cikin cikina kuma yana ban tausayi.

Don nasan haka zai taso da kalubali idan ban dauki matakin hakan ba tun yanzu don haka dole in kauce
in samu a daukar min mataki akan saratun nan da kowa ma don har mama gaskiya.

Washegari sallah kawai nayi na zauna addua na jira gari ya dan haska na fito inacewa maigadi zani can
gidan kila in kwana biyu a can din waman zuwan.

Yana ta min adawo lafiya yana gaida maigida shiya tare min keke na hau ina sauke ajiyan zuwa dana bar
wajen muna fita titi nacewa mai keken kaini tasha in shiga motan kaduna.

Ya dauki hanya sai tasha din muna zuwa ga mota saura mutum biyu zuwa kaduna na sallameshi na
biya kudin mota na fada.
Saiga cikon na karshen yazo muka daga na sauke ajiyan zuciya ina jan hijjab dina zuwa hancina saida
muka bar zaria na sake gyara zama ina lumshe idona.

Mai karatu abinda yasa banje abuja ba son zuwan dasu daddy sukayi na nuna masu zan daure da duk
wani abinda zan gani amma yanzu na kasa hakan .

Gara inje wurin ummah zaifi min duk da banson zuwa gidan nasu don yadda mijin nata yake like da ita
kamar wasu yara hakan kan ban haushi idan na tuna da mahaifin mu da basuyi irin wanan rayuwan
barikin dashi ba haka har ya tafi kullum shi yana kofan gida yana tsaro wajen aikinshi ko in daddy yana
gari su fita tare dashi din.

Amma shi wanan ya samu wanan daman da mahaifin mu bai samu ba Allah ya gani ina taya mahaifin
mu kishi a kansa gaskiya.

Ashe yazid ya biyoni zuwa gidan ya daukeni ya samu ban gidan maigadi ke fada mashi ai tun safe na
fita da jakata nace can gidan zani a lokacin.

Gidan mu tace dakai zata ni yanzu daga gidan nake ai fitowana ke nan nazo nan don jikin mijin nata ya
dan tashi subbahanallahi maigadi ya fada ya dora da fadin har da jakar kaya ta fita ai nina saka mata a
mota don tace wanan karon zata kwana biyu a can din.

Waya ya daga ya kira yana tambaya ake ce mai to ban iso ba ya juya ya fita sun kira wayana a kashe
yasa suka kira Maria ta dauka cikin sanyin muryan nan nata suka gaisa bai tsaya ba yace ko amaryan J
tana wajenkine sister ki ?

Rahama ta fada cikin mamaki ta dora da fadin wallahi bata zo nan ba ai mun kwana biyu gaskiya yake
fadin habu bai dawo bane ?

Ta amsa maida yace sai jibi zai dawo bai tsaya ba ya kashe wayan ya karasa gida sun ta maganan
maman tudu ke dadin dama nasan zatayi gaba tamayi kokari tunda har takai war hakan.

Bafulacene zai tsaya ana gardaman abinda yake da gaskiya a kansa tayi kokari dama ta zauna ai tunda
tana son mijinta yanzu dai kubar zancen nan kada yaji don Allah mama ta fada.

Basu sameni ba sai zuwa yamma nayi barci na tashine suka sameni

76 / 101