Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
sai in bata key din ai kayan mijintane itama .
Amma dana fahincesu saina hana key din yaron ya juya ya koma yana fada mata abinda nace game da
amsan key din a wajena.
Fisge fisge ta soma tana nunani ana riketa daga wajen muna tsaye maria na fadin kai Rahama ki mike
mata mana kafin ta tara maki mutane a nan.
Ba zan bata ba don ba ita ta ban ba wasa wasa sai gashi an taru a kanta tana ta zage zage wayana dake
vibration na dauko a jakkata shine akan layi na dauka a fusace sai naji yana fadin.
Kina inane ke nace wajen buki mana yace ance saiba na fada dake a wajen don kin hanata key din mota
?
Au dani take nidai naga tana fisge fisge na zata iska ta hau ai look kada ki yarda kibawa kowa key din
nan idan abin baiyi ku dawo gida kawai don Allah ?
Na zata kin biye mata don ba hankaline da itaba bata duba condition dinki saboda hauka na cika masu
motan da suke amfani dashi tun shekaran jiya yau kuma na basu kudi su kara mai a cikin motar.
Don tana mara mutunci hakan bai mata ba saita karbi key a hannunki don kishin tsiya zata gamu dani
wallahi dif na kashe wayan ina fadin banjin ka yaya.
Munafuncin maza kawai ai baka fada min kayi masu hakan ba sai yanzu nuna min yayi naje da motarshi
kada in hau motar haya zuwa wajen kawai kuma mu kula mai da mota kada in yarda inbayar mashi da
motanshi ga kowa.
Sai kawai mukaga fada ya koma da salima ga saiba can da nata nan kuma ana fada da salima abin ya
bamu mamaki matan yayyunsu suka shiga fadan salima din ana ta cacam baki a wajen.
Bamu san meke gudana ba acan din don muna da dan nusa dasu matar yazid da aka fara fitinan tazo ta
samemu muna tare harda ita.
Saida wata kanwarsu yaya matar aurece ita tazo tana fadin bafulata kin yamutsa wajefa da fitina ga
amarya can na fada dake wai zuwanki taron nan bai mata rana ba ya bata mata buki.
Kishiyarki na fada a dake a barta tazo ta dukeki ana riketa can, nan kuma suna zaginki da mijinku ashe
salima tana wajen ta basu amsa shine shine abinya zama fitina ya barke a tsakaninsu har ana batun
bawa hammta iska a tsakaninsu.
Muryan maria naji a hasale tana fadin Au haka tace ashe, bamu ko sani ba ai ba zata kara ganin mu ba
ai kuwa, koda Rahama tazo wajen nan ba wanda yaji bakinta da wata,
Ta daiyi da wace ta tayar mata da fitina don itace ta bata mata bukinta ba Rahama ba watau Rahama
itace marainiyar tako ?
Mariyace ke fadin haka a hasale taci gaba da fadin tun zuwana naga saratu na harare harare a wajen
nan, sai sun san dai wanda ya bata masu sha,anin bukinsu don ba Rahama ba dai kam.
Dani da mariya din da matar yazid muka bar wajen bukin a ranan ne kuma rana ta farko dana fara jan
mota a garin zaria don ko biba ban tsaya nema ba tunda tana tare da yan gidansu Aminu kuma ya bace
a wajen taron.
Saida na saukesu gida na nufo nawa gidan kai tsaye yayi kiran wayana ban daga ba saboda hayaniya
banko ji kiran ba a lokacin yasa ya nemi Aminu .
Aminu din ya kirashi yana sheda mashi na bar wajen bukin da dadewa kodaya dawo gida ni ya sameni
gidan abinda ya fara tambaya shine waya jawoki zuwa gida ?
Nina jawo kaina mana na bashi amsa ya tsaya yana min kallon mamaki baiyi magana ba ya nufi
dakinshi kai tsaye don a gidan yake sai daya gama ya fito ya fita zuwa massalaci sallah magariba da isha,i.
Ya dawo ina dakina jin shigowanshi gidan yasa na fito daga dakin ina gaidashi abinci na dauko na kawo
mashi falo inda yake zaune yana waya.
Ya harde kafafuwansa a waje daya a mike yana dan jujuyasu yake wayan yana fadin shi gaskiya yasan
dama za ai haka ai wallahi ya fada mata tabar mashi gidansa tunda bataji meyace da ita kafin ta dawo
ba.
Ai ya fada mata datayi kuskuren akan yarinyat nan tace zatayi mata rashin mutunci ba zai kyaleta ba
saurare naji ya tsayayi kafin yace shin mama ana aure dolene ?
Ni dai na kawo yarinyar nan gidan nan yanzu kuma nace ta tafi gidansu tunda basu da mutunci itafa ta
rokeni motan nan banyi mussu ba nax bata key harda kudin mai da zasuyi jigila dashi.
Don naba Rahama tawa motan Aminu ya kaisu abinda zatajeyi shine kuma zai zama jidali a wajenta
yanzu a bainan jama,a har ana kamata tana barin a bari taje ta duketa.
Watau bata damu da halin da zara iya shiga ba ko ba ruwanta da cikin jikinta ke nan ita idan an barta
da Rahaman badon ciki ba me zata diba a wajenta ?
Saurare ya somayi na dan lokaci kafin naji yana fadin dole inyi fada mama cikine jikin yarinyar nan fa
mama idan tayi mata illa fa hajan bai shafeni ba ke nan ?
Sai in tsaya tayiwa yarinyar mutane illa tunda ta kudurta hakan a ranta Rahama bata taba damuwa
dame nake masu ba ita dion banyi mata ba itayi fushi
Kuma ta sani tasan ina masu ai ko ita ba mutum bace koba aurenta nakeyi bane itama akwai wanda
yakai nusaiba wahal dani a cikinsune mama ?
To wallahi ki fada mata duk ta kuskura takai hannu a kan wanan yarinyar again na barta har abada ke
nan a rayuwana tunda ita mutumiyar banzane na fahinci hakan sosai yanzu.
Tana magana bai tsaya saurara mata ba yacigaba da fada karshema ya kashe wayanshi yana huci ya ja
plate din abinci zuwa gabanshi.
Yau da ace ina yawan korafi akan abubuwan da nake gani kansu ashe da ban samu wanan shedan ba
daga bakinsa a yanzu ?
Ashe yasan nasam komai nunawane banyi a gabanshi sai in nuna komai banji ba akan harkanshi da
matanshi koda sun bugo mashi waya a yana gidana ban yarda na taba nuna mashi kishin da nake ji kan
hakan ba a fili.
Saida yayi cibi kamar biyu zuwa ukku naji muryanshi yana fadin yaushe kika iya motane ke ban sani
ba ?
Ajiyan zuciya na sauke kafin nace dashi ya jima mana tun ban aureka ba na iya mota lokacin da nake
zuwa Abuja hutu anty salma tasa aka koya min driving.
Lalai kin kai bafulatanan asali Rahama amma baki taba nuna min kin iya ba har nake zancen a dinga
koya maki keda wa yancan kafin Allah ya hore min in sayawa kowa nata ?
To idan na nuna meye faninshi yanzu ai gashi daya kama ka sani kasani din ai, kuma don Allah kabar sa
kanka a cikin zancen mu da matanka don hakan yana kara min bakin jini a wajen yan uwanka na saya
zancen bance mama ba nace yan uwanshi.
Rahama kada in magana ta illantaki don ana tsoronta ita din me har waye Nusaiba yar iskan banza
kawai dama haka mama ke son gani yasa ta takura min sai in dawo da ita.
A zatonsu idan ta dawo zata kwatar masu wani abu dayafi wanda nayi masu a yanzu a wajena kyalesu
nayi naga plan din nasu basu san waye Nusaiba ba har suke tunanen hakan a wajenta.
Yarinyar da bata son taga duniya naiwa wani alheri koda kuwa ita mamane da kanta har inta sani sai
mun samu matsala da ita ta nuna nata iyayyen fa don wauta ?
Wai ita suke sa ran tayi masu abinda ban tashi yi akansu ba yanzu kyalesu daga su har ita jira nake ya
fito a tsakaninsu ai wanan kan dole inyi mata kashedi a kansa tunda bake kadai bace.
Nasan aiba zata iyaki ba tunda sun gwada syn gani yanzu so take tayiwa cikin jikinki rauni a fahintana
shiysa take nemam jidali dake.
Tayi da wani ai nibama zan koma zuwa wajen bukin ba balle ace ga kuma laifina wanda naje din nan ya
isa hakana kuma.
Abinda nayi niya bayarwa zanbawa Aminu yakai masu shike nan a zauna lafiya tunda basu son ganina a
sha,aninsu.
Saboda me ba zaki ba gidantane ko bukin yar uwarta akeyi da zakice ba zaki ba zaki tafi in takai yar iska
ta kara tankawa a kanki kuma ?
Ai baki san Nusaiba bace tayi hakane kawai ta baki tsoro amma komai bata iyawa na gaya maki ita
Asmauce har yanzu bata fahinceta ba.
A,a mai bukin tace munzo da yar uwata zamu bata masu sha,aninsu suna bukinsu a cikin dadin rai
zuwan mu yasa muna son bata mata buki ?
Ita Saratun tace hakana har wani buki bukin da suka sawa kansu karya a kanshi daga ita har mijin bar
yar iska karya yazo ya shimfida masu suka hau suna hauka.
Daga ita har mama kallonsu nakeyi itace fa a matsayin ta hudu matansa ukku itace yanzu ta hudunshi
sai taje ido ya raina fata irin gidan nan ne kuma family house zai kaita.
Musu kai kaya ai suna can yaya Ai ta kirani dazun nan tana sheda min sunje sunga abu na daban ba
abinda aka fada masu bane ko kayan basu shiga dakin da aka nuna masu ba a matsayin nata yanzu suna
can dai ai na kirasho yace wai bai gama ginansa bane kiji makaryaci hakan ne daidai da ita yar iska dama
sai mai karya irinsa zai iya kwasanta ai suje can su karata dashi tunda mutumiyar banzace ita.
Wai yaya tana cewa ko za a kama mata haya ni zan kama masu haya ya zauna da matarshi ke nan duk
shekara inbiya ko ?
Shi habibin ashe makaryacine don haka take kiransa da habibi kowa dashi ya sanshi a fanninta.
Ya amsa yace babba kuwa aini da ganinsa nasan mutumin banzane yanayinsa kadai ya nuna min hakan
a kanshi makaryacine yace shine manager a bankin ashe karyane.
Haka akace mana manager ne na bankin manoma ta kasa karya yakeyi ya fada yana mikewa yace
tadaiyi auren shine burin mu a yanzu.
Sai banji dadin hakan ba don za ayi a dawo ana da an sanine a karshe naja bakina nayi shiru ban sake
uffan ba akan zancen shima kuma ya fada min ne don yasan ba za a taba jin zancen a bakina ba indai
nice.
Can gidan kuma ashe labari yazo masu daga yan jere irin abinda sukaje suka sama a gidan hakan yasa
hankulansu ya tashi ita kuma wawiya bata yarda ba wai ai yace dama bai gama gina inda zasu zauna ba.
Shiyasa yaso a daga auren amma su yaya Auwal sukaki yarda da hakan sukace ayi haka dai a wuce
wajen.
Karshe dai dole kowa yayi shiru amma mama hankalinta bai kwanta da irin yadda ina hafsatu ta labarta
mata komai ba har matanshi da yaransa da suka gani.
Hakan yasa ta kirashi take kara fada mata ina shiga dakin naji yana fadin to yanzu mama ko hakan
gaskiyane yaya zamuyi tunda ita tace tana sonshi .
Hakkuri za ayi da fatan zaman lafiya su sauran matan da suke zaune dashi ai basu mutu ba ka saurareni
malam wanan zance abin a dubane tun yanzu.
Mama ba rawan kanta ya kaita ba koma yaya abin yake ai dole dai hakkuri za ayi yanzu tunda ba za a
fasa auren ba.
Ya kashe waya don tunda na shigo na fahinci da ita yake waya na juya zan fice daga dakin yayi min
hannu dana dakata kar in tafi na dawo na zauna don banda jimirin tsayi a lokacin.
Mama ke nan ta fahinci inda saratu takai kanta hankalinta ya daga a yanzu shine suke ganin laifin
mutane kan anki kara kudi ayi karya niko ko a jikina don ita ta kanta ta nace sai shi a barta taje ta gani ai
yanzu.
Nima wallahi na damu irin hakan babu dadi ai maka karya sai kaje ka samu ba haka abin yake ba kuma
babu yadda zakayi an riga da anyi din.
Sherintane yake shirin cita shiyasa ake son bawa da tsarkake zuciyarsa akan kowa nan tace dake ai
tana yarinya karama ba kwadayin da zai jata ya kaita auren mai mata koda gudane ?
To, gashi yanzu ita bako mai mata daya ta aura ba mai mata har ukku itace ta hudu kinga Allah ya
ceceta da irin rayuwan abokan zamanki na kazanta kuma.
Ai, Ba,a kula irinsu anty saratu yaya ni harga Allah ta ban tausayi wallahi don babu walwala ko jin dadi
dai a gareta yanzu gidan yawa ai fitinane babba ya tunkaro ta.
Aita iya makirci sai su saje dasu suyi tayi niko a jikina na jima da sallama lamarin yarinyar nan a
rayuwana tun lokacin da tace da kudin gadon mu nake aure na sallama lamarinta.
Haba dai kai babbane hakkuri za kayi bata da wani gatan daya wuce ku a yanzu ai ko yanzu kuma ta
fahinci kai ba irin mutanen nan bane tunda kai mata komai a rayuwa.
Ke kika fahinci hakan ita ai fushi takeyi dani daga ita har mama na kuma rantse a yanzu dai ban kara
mata komai saita gane kurenta .
Gara dai dakace sai gaba don duk yadda akayi saika saka hannu a wani abin shi dan uwa ai MURFIN
JALLO NE don ko wakake a duniya wata rana sai dan uwa ya taimake ka.
Rahama mu bar zancen nan idan munci gaba kina tuna min abubuwa akan yarinyar nan yarinyar data
dafa min mugun ciwon da kowa yake gudu a duniya wani murfi take gareni a rayuwa ?
Shiru nayi ban kara cewa komai ba washe gari tunda safe yasa kai ya fita gidan nasan hakan nada
nasaban kiran da mama din take ta mashi tunda dare yaki daga wayan.
Wani abu sai mahaifa don kuwa ko yaya ranka ya baci da hukuncinsu dole kai hakkuri idan kana neman
rahaman ubangiji.
Saratu dai tun bata yarda da zancen da ake fadi ba har ta soma yarda gashi washe gari daurin aure
saida maza suka nuna ikonsu akan mama ta yarda ta amince aka daura aure a washegari.
Duk cikin sarakan mama mu biyar ni kadaice na bada gudun mawa a harkan bukin aiko yaya barakha
tana ta yabawa tana fadin kin gani ko ita da nasu baizo daya ba da saratun itace ma ta bada abin arziki.
Aini tuni na gano yarinyar arzikine na daina biyewa zugin mutane akan zancen duniya ba dole ki daina
ba tunda tana ma danki rikon munafunci a yanzu ?
Komai zaki fada kan wanan yarinyar wajen malam da mukaje dazun cewa yayi hannu akasa aka
dambala mijin don ba haka yayi niya ba da farko ?
Haba mama don malam yace ansa hannu sai ace kuma Rahamace tasa mata hannu yanzu don Allah me
ta tsare mata inma hannune ai saidai tayi wanda zata tafi ta zauna dakinta har abada.
Don Allah mama a yanzu ya kamata ki rage irin wanan magana na malamai shekaru fa sunja mama ke in
kin fada ai ba za aga laifinki ba ni wanan halin wallahi yana damuna sosai komai ace a je wajen malam ba
a barwa Allah lamatin komai yanzu gidan nan.
Can Saratu ta dauki mama sukaje wajen malaminsu da Nusaiba yace wai sai Nusaiba ta dawo
abubuwa zasu kamkama ga zance kasan hadin bakine amma mama ta yarda da shirmensu.
Salima ke fadin hakan aiko mama tayo cikinta da zagi na bacin rai tana batun tsine mata saida anty
barakha ta kare tana fadin nikan mama zan kira Jafar yazo kan zancen tunda banga abin zagi ba a nan ?
Ai gaskiya salima ta fadi ni yanzu na gane malaman nan macutane wallahi don suci kudinta sai su
kakaro karya su sharawa mutum don hankalinsa ya tashi a banza.
Haka dai akai komai har daurin aure ba tare da sun samu yadda suke so ba din salima kuma tunda ta
fita har ranan buki bata leko part din ba tana wajen iya zaune har yan kai amarya suka wuce da amarya
bata fito ba.
Anje dasu yaya barakha da maman tudu sai mama hafsatu matar kawu wace zuwanta din yaso ya jawo
matsala tunda taje wajen jere don kawu yace amayarsane zata kai amarya.
Su yaya suka tsaya sukace da inna hafsatu za a dole ya kyale ya bari ta tafi mutum biyar dai suka je
raka amarya dakinta a ranan.
Duk daba gida daya muke ba saida baji shakat da tafiyan nata don nasa an rage wani annoba a yanzu
matar yazid ce ta fara magana ta soma fadin.
Wai an rage wani kaya a nan wanan matar batayi min ita sam kamar ba ciki daya suka fito da yan
uwanta ba ta fita daban a cikinsu komai nata baida kyau wallahi.
Muna wajen iya har yamma nidai koda aka fito wai aje a sallami mama kin zuwa nayi na zauna nan a
barandan iya har suka fito muka fice daga gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/3, 9:39 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ba cewan da akayi kauyen sokoto za akaita bane abin mamaki sai irin gidan da mota ya tsaya dasu a
garin tambuwal.
Daga wajen gidan kawai zaka fahinci inda sukazo gidane na gandu irin gidan yawa din nan mai dauke
da tun kaka har jikoki a cikinsa in akwai.
Haka aka fito da ita zuwa cikin gidan wanda ko gidan gadonsu dasu mama ke zaune a cikinsa yafi don a
can family house dinsu shimfide yake da siminti lungu da sako na gidan ga baki daya har bayi a shimfide
yake da siminti.
Sun samu dakin nata saboda kayanta tsohuwan gidan ta tashi daga dakinta an gyara dakin an hade
mata shi da nata ya koma ciki da falo mai kama da babba da jakka dakin nan da tsawo can ta