Chapter 79 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   79 / 101

234K to 237K   out of 302.2K words

zata haifa ba a rabuba ke nan
dai ?

Barta aiko haka an nunawa yar iska iyakarta don daga kan yarinyar nan yayi yawa tana daukan kanta
ita wata tsiyane kiga tanayi kamar tana jin warin mutane ita gata maidigiri.

Sun jima suna zagin kansu waini a wajen kafin suyi sallama su kashe wayan uwar ta kallo Saiba tana
fadin wa aka saka tace wai amaryan Jafar ce tabar gidan subbahanallahi uwar tace.

Nusaiba wanan zaman gidan baisa kinyi sanyi kin koyi darasi ba ashe ? Na dauka wanan halin da kike a
gida zaisa kiyi nadaman abubuwan da kika aikata a baya ai ?

Yanzu akan abokiyar zamanki kikewa wanan mugun fatan haka har kina fatan Allah ya barar da cikin
jikinta don Allah keda kika haifa wani yayi maki bakin ciki da hakan ?

Sai yaushe zaki hankaline ke Nusaiba irama wace ke turu maki tsegumin tafiki rashin sanin ciwon kanta
ai da zata zauna duk tsegumi da sirin gudansu tana aikawa waje.

To ki guji naki a wajen ta ranan da zata kwaye maki baya tayi maki tonon sililin abinda kuke shukawa a
tsakanin don tayiwa dan uwanta ciki daya balleke ?
Dama sam rayuwan yarinyar ni baimun ba wallahi don na fahinci itace ta shiga tsakanin ki da Asmau
tun farko ta hanaku zaman lafiya duk amintakan dake tsakanin ku.

Duniyace ai ita ke koyawa wawa wayau koda baida fahinta wata rana duniya zata fahintar dashi keda
ya kamata ki natsu a yanzu ki komawa Allah inda rabon komawamki gidan ki komawa uban yarki kin
zauna kina wanan hauka haka ?

Katse uwar Nusaiba tayi da fadin mama ke saiki dinga ganin laifinaita da tayi min fa ta hanani zama
dakina ta rabani da mijina ?

Oho ba zakiji ba kenan ko ta ina ta hanaki halinki dai ya hanaki zama a gidanki Nusaiba waye baisan
halinki ba yanzu ?

Duk hakkurin yaron nan da kawar da idonsa jan abinda kuke mai saida kika kaishi bango ya koma komu
yanzu bai ganin darajan mu a idanunsa kuma ?

Ai duk wanan sherin yaeinyar nan ce da baku son a fadi kaifinta har yaushe za a tsaya goyon bayan
wace aka san itace matsalata amma baku son a fadi laifinta sai saratu dake kaunata ni gabadaya naso
subar gidan ba ita kadai ba don ko Asmau munafukace ta gaske dole sai ta fita tabarni dashi.

Tsuki uwar taja ta juyo tana fadin na yarda abin nan ya tabaki Nusaiba ki matsa harki samu tabin
hankali Asmau dince zaki fitar a gidam jafar ?

Shiko Yazid tun bayan dawowanshi yana part dinshi tare da iyalinshi dan baison yayi nusa dasu sosai
hakan yasa tunda ya shiga bai sake fitowa ba.

Sai washegari daya fito yaje gaida j din suka dan zauna dashi ganin yadda J din yake kwance yasashi
fahintar yana jin jikin nasa ranan.

Muryan J ce ta katseshi da yake fadin yarinyar nan taki dawowa ashe nayi mamakin hakan ban kuma
san abinda taje ta fadawa iyayyen nata ba har suka riketa.

Me zata fada J abinda kuke mata kai da mama da yan uwanka da matanka shine zata fada mana ai
basuce ta fada masu komai ba .

Illa dai tace ba zata dawo bane ita tagaji da abinda ake mata kai baka daukan mataki koda kana zaune
kaga bata da laifi anan .

Don kaika daukota J yakamata ace ka nema mata daraja a idon kowa gidan nan duk da suna ganin sun
girmewa shekarunta amma dai shi zama tare baice hakan ba ai.

Bsice don mutum yana kasa dakai yana auren danka ka dinga muzantashi kana nuna shiba komai baine
haka kuma kowan ku yana kallon yaran nan da matanka sinaciwa yar mutane mutunci nasan da gidan
nan ne ba zamu taba yarda aiwa kannin mu hakan ba a gidajen auren su.

Shi habu wai yayi fushi don yarinya ta dage akan bata dawowa har saida yakai sunyi musayan baki
dashi don gaskiya inda shine bai yarda aiwa matarshi hakan ai.
Shiru jafar din yayi yana saurarenshi kamar yana tunane kafin ya jefowa dan uwan tambaya yana fadin
atakaice dai yanzu nida mamane masu laifi a wajensu.

Kwarai kuwa bros lafinka anan shine baka tsawatawa lamarin koda kana kusa akayi mata baka daukan
matakin daya dace koda gobe ba za a maimaita irin hakan ba sai yayi murmushi ga dan uwan nasa dake
magana.

Yazid din yace kwarai kuwa bafa wai kai ka nuna mata concern a bangarenka alhalin tana samun
musgunawa a wajen mutanen gida shine kawai abinda zakayi ba .

Yama dole kabata kulawa a ko wani bangare kamar yadda kakeba kowa tunda kaika daukota cikin
gidanka.

Haka kuma ita mama kamar da saninta ake komai ga yarinyar nab banda wanan itama kanta tana
yawan aibantasu a gaban kowa don ko gaida mama sukayi ance bata amsa masu wani lokaci kaga ba
wanda haka zai faru dashi yaji dadi har ya zauna itace uwar mijinsu fa ni nasan halin mama idan ta tsargi
mutum bros ka sani kaima ?

Baiyi magana ba saici gaba da kurawa dan uwan nasa ido yayi kawai a inda yake zaune yayi shiru ya
kafawa kasa ido yana tunane.

Mikewa Yazid din yayi yana fadin yakama a gyara zancen nan abinda na guda kenan da matana kaga
ban yarda ta shiga kwamacalan gidan nan ba don ina da labarin komai a wajen iya.

Yanzu ya rage naka idan kana son matarka saika gyara ka shirya da abinka idan kuma ba yadda zakayi
don Allah bros kabar yarinyar nan ta tafi taje gaba ta samu wani mijin .

Sai a lokacin ya dago kai da sauri ya dubi kanin nasa dake magana Yazid din yace hakane mana ka
sallameta ka zauna da wa yan nan mayayen naka lafiya tunda itace matsalanku.

Ko dai makaho yasan irin hakkuri da sanin ya kamatan yarinyar nan kai kanka kasan ka tauye mata
rayuwa a gidan nan don ba kalan macen da za a dauko a takura haka bace ita.

Yazid idan da bansonta zaunan aureta gashi ka fadi kaima ko makaho yasan halinta na alheri balleni da
kusan a yanzu yarinyar nan itace rayuwanta.

Me nake tsunta a wajen wa yan nan marasa hankalin tunda na auresu sunan nayi aurene amma ba
wani jin dadin rayuwa na ma,aurata a tsakanin mu.

Na tabbatar da Rahama bata tare dani haka ya sameni gaskiya ko kwanana bai kare ba dana
wullakanta ita kanta mama tasan hakan don tun bata aureni ba take dawainiya dani a kwance kan
lalurana.

Na zata dana yanke shawaran aureb yarinyar nan mama zatafi kowa jin dadin hakan a ranta ashe ba
hakana bane a wajen mama don sai gashi ta juya zancen da cewa sihiri sukai min don suci arzikina kawai.
To ashe kasan hakan ka bari ana mata hakan a gaban kowa bama kamar yar iskan nan Saratu da kawu
da sune suka canza muna mama daga nan gidan kawu na nufa zanje amsan gadona dake hannunsa ko
ba zanyi amfani dashi ba ina bukatan abina a hannuna yadda kowa ya karbi nasa .

Da sauri yace da dan uwan nasa No Yazid kokaje kudin nan a yanzu ba samuwa zasuyi ba Yazid don
haka ka barshi kawai don Allah.

Duk abin nan da kawu yake muna sam mama bata ganin hakan a idonta saima idan mun matsa taga
laifin mu zancen iyace datace ba banza suka barta ba.

Kaga na dauka akan zancen nan nawa da kawu keda hannu a cikinsa zaisa mama ta gane waye kawu
sai gashi naga yanzuma suke wani shiri na daban a tsakanin su don haka karkaje ku samu matsala da
mama don Allah.

Dolene inje bros so nake in kawo karshen mutumin nan ai masa iyaka damu yadda zai fahinci yanzu
mun girma ya fita daga tsabgan mu gaba daya.

Mamace yar uwarsa bamu ba ka bari na latsashi na dan lokaci zai shiga hankalinsa kasa muna ido kawai
kaga yadda zanyi dashi don Allah ?

Yana fadan hakan bai tsaya ba ya fice daga falon da saurin binsa yayi da kallo yana sauke ajiyan zuciya
tare da lumshe idanunsa na dan lokaci.

Muryan maman tudu ya dawo dashi hayacinsa tana tsaye take fadin yazid ne ko ina daki nake jin
muryanshi ai shine ya fita ya bata amsa.

Can ya dora da fadin yazone yana fada dani kan tafiyan Rahama wai laifina bani daukan mataki idan an
mata cin fuska koda a ganane ?

Fissabillahi mama wani irin mataki take so in dauka bayan wanda nake kokarin yi mata a yanzu na
rabata da zama nan gidan duk da mama da sauran yan uwanta sun nuna min rashin yardansu da hakan
amma na cije naki dawowa da ita gidan nan .

Abinda take nufin anyi mata ai in Nusaiba tayi mata ita da bata gajiya da lorafin anyi mata ba daidai ba
koda yaushe nakan tsaya kuma nayi abinda ya dace amma duk bata ga hakan ba mama ?

Watau abinne naku yake son natsuwa da fahinta jafar duk wanan laifin na Dubuce data ba dakariyar
yarinyar nan saratu dama da yawa haka a cikin matanka.

Har yaushe zan zauna in sakarwa yarinyar da batayi aure ba dama zama da matan yayyun ta haka
zaman daba na Allah da Annabiba kuma ta sani ta kyalesu suna aikata abinda ba daidai ba.

Har ace kamar Saratu tana kokarin aibanta jinin dan uwanta tun a ciki da nice yarinya tayi min wanan
aikin a dakina ranan danasa yan uwanta sunyiwa ja,ira dukan kawo ruwa da gobe bata komawa .

Amma dubu ina taji fa amma sai kokarin kare yarta takeyi daga karshe wai aiba da ita sukeyi ba
tsarguwane kawai irin nata data sabayi tana kokarin daukan laifi ta dora akan yar mutane.
Irin maganan sherin dake fitowa a bakin saratu kan yarinyar nan ko waye dole ya dauki matakin hakan
tunda ba a gidan nan aka kare rayuwa ba.

Gaba dayan ku kuna da laifi gaskiya yanzu baga habu ba ko ince yazid tayiwa dayan su irin abinda
takeyi tsakanin matanka mana idan gaskiyane ?

Dole har in kana son yarinyar nan ka dage ka kwatar mata ince ga kowa a gidan nan shine mafita amma
baka zura ido haka abubuwa suna faruwa ba ?

Sun dauki karan tsana sun dorawa yar mutane da za a tsayar dasu a tambayesu babu mai kawo wani
dalili mai karfi a wanan zance kishine kawai irin na mata don sunga ta fisu da komai sai kuma samun
wajen iya shege din.

Shiru yayi yana sauraren zancen da mama din take kwararo mashi a lokacin shi dai a iya sanin sa ai
yana kyautatawa zamantakewan mu dashi ba zaci zance abindake faruwa tsakanina da mama ko saratu
da matanshi zai zama laifi a wajenshi ba.

Wanan yasama bai yarda ina yawan zuwa gidan ko shiga wani harkansu da bai zama dole ba amma
kuma duk bai tsira daga hakan ba a wajena.

Da mama ke zancen idan har yana sonta ai itama tasan yana kaunar yarinyar nan saidai ba zai iya cewa
yana fito na fito da magaifiyarshi ba kan abubuwan da suke mata din.

Yasani ba a kyauta mata amma yasota da yin hakkuri da kullum yake bata kan wata rana sai labari
tunda har mama ta kasa hango alherin yarinyar a yanzu yasan ba zata taba hangowabane kuma.

Yau duk wanda ya tsaya yayi maka haka akan naka aiko komai yayi ma zaka iya masa ragowa don hakan
amma sam sunki su fahinci hakan ita mama tana ganin komai takeyi tanayinsane don ta mallakeshi da
abinsa.

Har ta ina Rahama tayi wayau haka duk ance kabar mace indaka ganta amma yasan halin matanshi
yarinyar da komai kankanta abu ya batashi zaiga farin ciki a wajenta bata taba raina hakan.

Nan ko zai basu kuma a raina a kumazo a wullakanta abin daga karshe yana kallonsa an nakasashi baida
bakin magana kan hakan har ya gaji ya saba don ba zai sayo abu ayi amfani dashi yagani yaji dadi ba.

Shawara sosai masu amfani mama ta bashi wanda yaji dadin hakan sosai har cikin ransa ya kuma
godewa mama din don yaji dadin wanan shawaran data bashi a lokacin.

Shigowan mama dubu yasa suka canza zancen take tambaya bayan sun gaisa ta tambayi karfin jikinsa
da Yazid ya fitane ta shiga part dinsa bai nan ta dauka yana nan wajensune ai ?

Anya kuwa Yazid bai fita ba don yace min daga nan idan ya fita gidan kawu dauda yake son zuwa ya
gansa ina ganin ya tafi can din ne ?

Gidan yaya kuma da safen nan baiko fada min can zai tafi ba yau ya tuna dashi ke nan shima yaya din
yanata korafin tunda ya dawo baije gidansa ba.
Yaran nan zumunci yanzu bai damesu ba akan zumunci sai Allah ya hana maka alheri suna yawan wasa
da zumunci a yanzu wanda basu sani ba yana cikin abindake habka rayuwan dan adam sosai.

Yanzu sai kika ko kana da zumuntan sai a sarema gwiwa a zaci saboda wani abin hannun mutum kaje
gidan don a baka akama daurema fuska don gobe karka dawo.

Haka kuma zakiji mutun yace ko naje banda abin bayarwa don haka ba zani ba duk wanan halaiyan su
suka kawo koma bayan zumutun a yanzu.

Kedai bari yaya irin fa hakan ke bata zumunci a yanzu ko baka mutum komaiba yaje wurinka ai ya
kyautama haka kuma kai da zaka ai ba ace sai ka rike komai ba da zaka dashi.

Har iya ta shigo ta samesu a dakin aka zauna ana hira a nan wanda hirane akan lamarin ciwon shi jafar
din da mama dubu take fadin yanzu kan jiki yayi dama daba zancen yarinyar nan daya saka a ransa ba
aida sauki ya kara samuwa mashi sosai ?

Dole ya saka keko Dubu ance ka samu da wanda ya damu dake kodana munafuncine kuwa yarinya
data san yakamata yau ta tafi ta barshi ace ba zai damu ba ?

Ki duba da gari ya waye din nan yanzu karfe nawa don Allah amna ba a kawo mashi abin karyawa ba
har yanzu fa aiko wanan ya isa mutum ramewa haka ba sai ciwo ba ?

Halin Asmaune baki sani ba kuma iya yanzu haka tana can tana barcinta na safe sai tayi mai isanta tace
zata tashi ta dora abinci ko kuma an dora din an koma an kwanta ana jira.

Dukkansu haka suke har wacan data tafi indai kinga an karya da safe gidan nan to yarinyar nan ce ta
tashi tayi muna dabara lokacin da take nan din tana kwana samu .

Shine zata dan samo mana abu mai sauki da zamu karya dashi suna zancen Asmau ta shigo da kayan
abincin da missalin tara da rabi na safe .

Mama din ke fadan cewa wai meyasa suke haka suna da mara lafiya amma ba za a daina wanan barcin
safen na lalaci ba sai lokacin da akaga dama a dora girkin abin karyawa ?

Wayanta ya shiga kara tana fada tana dauka tana jin muryoyi na tashi a cikin wayan wanda yasa
hankalinta tashi har ta furta Yazid da yaya kuma me yayi zafi haka kuma ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/10, 10:11 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



8️⃣0️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Idan nace dake ban shiga damuwa ba karyane don dole akwai damuwa da kadaici balle yanzu dana
shaku da yaya haka ko yaushe muna tare.

Sai naji dan kwanakin da nayi gida ya zama min daban a rayuwata ga wayana na kashe don kadama ya
kirani in kulashi.

Kusan kwana shidda a gidan ummuh inda na sake raina kamar yadda kowa ke ban shawara ina samu
ina barci haka kuma babu aikin komai duk da nakan dan shiga kitchen wani lokaci da Saudatu mai
aikinsu.

Haka yaran daddy mata su anty Baby su ukku duk sunzo gidan dubani kamar yadda mahaifinsu ya
umurcesu dasuyi min din mun zauna na fada masu damuwa ta suka kuma ban goyon baya kamar ta
mahaifinsu da inzauna sai sun kawo kansu in kuma sake jikina na kama harkokin gabana kawai ba a sa
zancen namiji a zuciya don sai ka lalace a banza.
Naga karamci a wajen mutanen nan sai yanzu da zamana ya dawo gidansu na fahinci halinsu ashe ban
fahincesu bane da farko mutanene masu halarci da sanin darajan dan adam.

Inda ko wacensu take a gidan hutu gwargwadon hali don basu cikin wahala ko talauci kadaram kada
ham a rayuwa .

Gashi a fahintana suna nuna kamar mu kanninsune na jini haka sai naji kunyar kaina ya kamani a ranan
na yadda bamu kullasu duk da suna bin mu amma ya dace ace ai muma muna maida kara a garesu shine
mutunci.

Ina kwance daki ranan misalin karfe biyar na yamma saiga ummah da wayanta a hannunta ta shigo
dakin tana fadin wai barci kikeyine Rahama ?

Na dago ina fadin a,a ummah na dai kwantane ta miko min wayan tana fadin mijinki a layi na dago na
kalleta nace mi zan mashi kuma ni ina ruwana dashi ummah ?

Ki karba saiki fada mai ta fada tana dangwaro min wayan a hannu na da sauri na cabe ina karawa a
kunne yana kan layin naga ta juya ta fita daga dakin ta barni da wayan.

Na manna a kunnena naji yayi murmushi yana fadin baki san me zaki fada min bama Rahama shiyasa
kika kashe wayarki kenan ashe don kada indameki ko kiji muryata ?

Shiru nayi ina saurarenshi na sake jin ya furta are with me na amsa da ina jinka mana rai bace cikin
wani yanayin murya a daure.

Naji ya sake murmushi yana fadin fushin hardani ke nan akeyi da nayi maki me kuma Rahama bawan
Allah dake kwance haka har zai iya batawa wani rai don Allah kiyi hakkuri please ?

Nace da kai fushi nakeyi ni kawai nagajine da cin mutuncin da akemin kuma a hana mutum ramawa ba
a kuma daukan mataki a kansa.

Ba gaskiya bane

79 / 101