Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
MARFIN JALLO,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
22/12/2024
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
1
1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Hayaniya irin na babban gida shine ya tayar da mama daga barcin data dan samu ta runtsa na
safe ,bayan idar da zikirin safe data sabayi a duk safiya .
Wanan dabi,an kusan ya zama mata jiki akullum idan ta idar da sallah zata zauna tayi zikiri har sai rana
ya foto sosai kafin ta dan kwanta ta ba ido hakkinsa.
Daga inda take kwance din tana jin yadda yaran gidan nasu da manya ke kara,kaina a tsakar gidan
kusan hayaniyar babban gidan nasune ma ya tayar da ita a lokacin.
Salati tayi tana dagawa a kasa inda take kwance saman sallayanta ta dan jima a zaune don gargadin
likitoci dake fadin.
Idan ka tashi tsaye barci kada kayi saurin mikewa tsaye a lokacin don min a daidai lokacin jinin dake
kwaranya a zuciya bata gama sauka ba yana yuyuwa ka mike hakan ya ja maka matsala a rayuwanka a
cewarsu.
Ana son Sai ka dan bada yan mintuna a zaune kafin ka mike tsaye don kariya ga lafiyan ka a lokacin
wanan dokan da mama taji illanshi.
Baga yaro ba baga babba ba dokace da likitoci suka bayar don gujewa fitinan lafiyan jikin bawa daka iya
haifarwa mutum ciwarwutan zamanin nan .
Hakan yasa wanan boyar Allah ta rike wanan akidan ta dan bada lokaci a wajen zaune daidai lokacin
da aka turo kofan dakin nata tare da daga labulen dakin aka shigo ciki da sallama muryan danta na
ukkune yake sallaman tare da fadin ashema baki tashi ba mama ?.
Daidai lokacin ta dago kai tana sauke mai kallo tare da fadin na tashi Habu badai har rana tayi hakaba
kuna shirin fita ?
Rana tayi mama yanzu kusan karfe takwas da rabi ake nema zuwa nayi muyi sallama don yau balaguro
zamuyi har wani kasan ba lalai bane mu dawo a yau ko gobe saidai kun ganmu dai zance.
Kallon mamaki take binsa dashi tana fadin haba Habu wai sau nawa zan maka fadan irin haka don Allah
?
Mutum zaiyi tafiya mai nisa irin haka bazai fada a gida ai masa addua ba ka raina da dan adduan da
muke binku dashi ko yaushe ke nan ?
Zaune yakai saman kujeran dake gefe ciki da kaya yayiwa kansa wajen zama a gefe yana fadin mama
muko muka san amfanin adduan ku akan mu don duk abinda muka dafa muna ganin alheri a cikinsa.
Murmushi matar tayi tana fadin yanzu dai ina kuka dosa Habu ko kudun zaku kuma yau dinma ?
a,a mama wajajen Camero muka dosa wajen wani taron gargajiya da za,ayi a can kinsan aikin mu ya
kumshi hakan sai munje don dauko rahoto.
Shine zamu dauko rahoto akai da zamu yadawa al,umma su gani ikon Allah yanzu habu har camaro
zaka hankalinka kuma a kwance ?
Batare daka sanar da mu ba sai yanzu ka shirya tafiya kazo kana fada min Habu ?
Wai meyasa kudai maza baku mayar da tafiya a bakin komai bane wai ?
Kako san nisan dake tsakanin zaria zuwa camero ? camero din nan da kake ji kawai a baki tafiyace mai
nisa fa daga nan .
Ya amsa da fadin kuma tafiyan mota zamuyi mama saboda kayan aikin mu dole mubi mota zuwa
wajen taron wanan yasa zamu tashi tun yau ai a dai muna addua muje lafiya mu dawo lafiya.
Insha Allahu lafiya zakuje ku dawo lafiya Abubakar alherin dake cikinsa ubangiji Allah ya sadaku dashi
sherin dake cikin tafiyan kuma Allah ya nisantashi daku alfarman Annabi da alkur,ani ya amsa da amin
cikin jin dadin adduan mahaifiyar tasu a gareshi.
Sallamu Alaikum ga nakiyar baby muryan wata dattijuwa dauke da kwala a kai data shigo babban gidan
Alh talle din ta tsaya daga kofane ya karade gaba daya gidan.
Daga can dakin mama din inda take bankwana da danta taji muryan wanan matar cikin mamaki take
sake zancen da sukeyi da dan nata.
Cikin mamaki take fadin nakiya kuma da safen nan ?
Har yakai a fara tallan nakiya gida gida haka me mutane ke nema da bindan kudine wai nakiya dai a
sanina sai bukin aure ake nakiya don ango.
Murmushi Abubakar yayi yana fadin barin inje mama kada in makara abokan tafiyana suna kirana tun
dazun.
Nan uwar ta dago tana fadin kaje kuyi sallama dasu hjy kafin ka tafi bana son irin korafin su na baka
sallamesu ba din nan.
Insha Allahu ya fada yana mikewa tsaye barin dubasu in dawo mama ya fada yana mai barin dakin cikin
kuzarinshi irin ta namiji mai jin lokacinsa.
Dakin hjy babba ya nufa ya gaida ita tare da fada fada mata inda suka dosa a ranan ba yabo ba fallasa
tayi mai Allah ya kiyayye hanya.
Ya fito yana kokarin shiga wajen hjy Nana ya hangosu gaban wanan matan dake faman kwada sallama
suna leken wani abu a cikin kwalan da matar ta shigo dashi.
Hakan yasa ya doshi wajen saura kiris ya karasa yaga yara da manya sun watse wasu harda faduwa kasa
don tsoro ga ihun da sukeyi suna neman inda zasu shiga saboda firgici .
Wanan ihun ya dakatar dashi yaja ya tsaya yana binsu da kallo fuska daure kafin ya mayar da
hankalinshi wajen matar da sai murmushi take a fuskanta.
Lafiya boyar Allah tace nakiyar babyce na kawo masu gashi kuma sun watse sun barni dashi .
Kallon matar yayi cikin mamaki murmushin yagani a fuskanta yasa ya karasa wajen yana kokarin kallon
kwallan dake gabata bude.
Ido ya runtse lokaci guda don wani katon maciji kalan da sai a cikin film yake ganinsa.
Ya nade a waje daya ya cika kwallan har baki sai kansa daya dora a saman jikinshi yana kiu kiu da
idanuwansa dake bude.
ALLAHU LAH ILLAHA ILLAH ANTA SUBBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZULLUMIN ya ambata a fili .
Muryan matar yaji tana fadin kada kaji tsoro kai namijine kuma sadauki ba asan maza da razana ba
sadauki.
Daga can bayanshi yaji muryan dayan kanwarsa tana fadin yaya Habu kada kaje kusa don Allah
macijene a cikin kwallan nan babba.
Jin sunansa da aka ambata yasa matar fadin Garba sadauki garba gagare kai sadaukine ko a fagen fama
kafiran makka sun buga sun barka sarki rikon amana mai alkawari ya cika har bayan rai,,,,,,,,,,
Dubu biyu ya zaro a cikin aljihunsa ya mikawa matar takai gwiwa biyu tana zabga mashi addua da
neman tsarin ubangiji gaba da bayanshi.
Ya juya da niyar komawa dakin muryan hjy Nana yaji tana fadin boyar Allah aida kin fada kwai a miko
maki abinda Allah ya hore ki tafi .
Yayin da matar tacigaba da fadin da yardan Allah kayi gaba saudaki sara da sassaka bai taba cima a
rayuwa insha Allahu sai dai makiya su buga su barka.
Mama data samu ta mike don ganin abinda ke faruwa a wajen taji yadda matar kewa danta Abubakar
addu,a ta fahinci kudine ya bata yasa ta dauki dari biyu ta fita ta mikawa matar nan ta dasa sabon addua
kuma tanawa mama jam,i ga duk zurianta.
Ta dauki kwallan ta tafi don taga sauran iyalin gidan basu da niyar fitowa balle su sallameta saida sukaji
fitanta suka fito suna mayar da ba,asin zancen a tsakaninsu kowa na fadan abinda yagani a cikin kwallan
hankali tashe.
Mama dai bata gani ba amma ta mikawa matar sadaka don tasan wanan matar banza ba zai fito da ita
gidanta haka basai neman rufin asiri da taga wanan hanyarce mai sauki a gareta.
Zancen mai nakiyar ya hana su mayar da hankalinsu ga Habu da zaiyi tafiya don da tsegumin tafiyan shi
za,a fara sai Allah ya fabeshi a ranan dan shigowan wanan matar mai yawo da macijin maisa a cikin
kwala tana cewa ga Nakiyar baby.
Idan kuma tasan sunan wani gida a gidan zata ambaci sunan maishi tace ga nakiyar wani sai wanan
abin tashin hankalin da mamaki ya tsaya masu a rai har mahaifiyarshi ta fito rakiyarshi da iya kofa ta
tsaya tanawa danta fatan Narsara da Allah ya tsare ya kare wamda sai lokacin hankalin hjy babba ya
dawo garesu.
Daga kofanta take tambayan yau Habu kuma ina za a haka tunda safe ni yazo muna gaisawa hankalina
yana gun wanan bakar matar data tayar muna da hankali da safen nan.
Daga kofa mama din take bata amsa da camero suka nufa lokaci guda matan da yara dake wajen suka
amsa da fadin camero kuma ?
Wasu na Allah ya tsare wasu kuma sunyi gun suna zancen zuci inda sabo ta saba da hakan zaman gidan
yawane duk yadda kayi sai wani yaga bakai masa daidai ba irin wanan zaman.
Ya fito daga cikin gidan yana kallon agogon hannunsa saboda ymshi kansa yasan da ya makara saidai
dole su jirashi sai yaje wajen aiki inda zasu hadu.
Kamar daga sama yayi ido biyu da wanan matar ta sauke kwallan macijinta sai faman murmushi take
zabga mai a fuskanta kai ya kawar da sauri yana barin kallonta.
Habu bakari don ka na tsaya nan duk da dai shigan tsugula zan ma tunda na kula sauri kakeyi ka kula
da addua don kai din kana tare da tsarin Allah ga kuma tarin mahassada a tare dakai.
Nagode mama ya fada yana kokarin wuce ya sake jin muryanta tana fadin ka kula sosai don alherin ka
da nasara yana inda ka dosa .
Kudi dai wanan matar keso gareshi ya nasa hakan a zuciyarshi ya sake cusa hannu a aljihu yana dauko
dubu daya ya mika mata.
Murmushi tayi tana fadin wanda kabani dakai da mahaifiyarka nagode maku Sarkin da akaiwa ya sani.
Naso magana da mahaifiyar ka saidai gidan ku gidan yawane dana fada mata wani magana amma ba
laifi idan tana son ji ko kai ina can gidan hjy indo mai kosai a nan na sauka.
Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin yana aje mata dubu dayan da taki karba a hannunta saman
kwallan yasa kai ya tafi don ya dauka zancen shirme take masa a lokacin don kawai ta yaudareshi yasan
halin mutanen yau da yaudara.[12/26, 2:54 AM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Tafiyace ta mota da zai dauki dogon zango haka suka fara tafiya tun suna dan hira a tsakaninsu har abin
yakai da anyi shiru kowa na tunane a kansan zuciyanshi.
Dosan mabila da sukayine yasa su fara bayana mamakinsu a fili kowa na fadan albarkacin bakinsa ga
albarkan kasan yankin mabila din.
Abin sha,awane da daukan hankali ga bakon zuwa wajen harma wanda ya saba sai yabi dabbobinsu da
kallon shawa yadda suke daban da wanda aka saba gani.
Lokacin da suka zo wajen wanan hawan kusan kowansu hannushi a gaba yake yana ganin kamar ba
zasu iya hawan nan ba don yadda sukaga wajen.
Sai gashi cikin yardan ubangiji sun hau lafiya sun gangara kuma lafiya a sannu suka fara barin cikin
nahiyar kasan Najeriya zuwa cikin kasan camero dake da iyaka da Nageria.
Abin sha,awa don basai ka tambaya ba alakansu da addinin musulunci don har yan wani addinin
shigarsu shigen na musulmaine su a kasan sukeyi.
Tafiya dai tayi tafiya don shi driver yasan yankin da za ayi wanan taron wanan yasa basu damu da yada
zango ba sai tsatsaya ko ina ba.
Saidai idan lokacin sallah ya riskesu sai kuma shan man a hanya sukama hanya amma sam basu tsaya
kwana a hanya basu kamar yadda wasu da yawa suka yada zango.
Hakan yasa sukai wa wanan yankin shigar safiya duk da alokacin wurin sha dayan ranane a lokacin duk
wani mai lalura ya fito a lokacin.
Sai wanda ke gida baida abinyi sannu a hankali yake bin garin da kallo daga bayan motan yayin da
driver ke aikin kutsawa acikin garin zuwa babban filin da za,ayi taron gwajin na gargajiyan shekara.
Suna wanan al,adanne bayan ko wani shekara goma idan ya shige in rayuwa ya kewayo ake haduwa
wajen wanan shagalin nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya.
Abaya kasan Nageria tana irin bukukuwan nan na nuna amfanin gona da sauran al,adun gargajiya
wanda yake kawo dankon zumunci da habbaka sana,an mutane da cigaban kasuwanci harma da
zumunci a tsakanin yan garuruwa na nisa dana kusa.
Sai a yanzune da abubuwan kasan suka tabarbare wanan al,adan ya mutu mutus a arewancin Nageriaa
sai dan abinda ba,a rasa ba dai kawai da akeyi yanzu.
Sai dai al,adan kamun kifi da wasan ruwa da sauran al,adun har yau har gobe mutanen kasan kebbi a
garin Argungu kabawan asali basu daina hakan basu a wajensu.
Don suna raya garinsu basu bar al,adansu da suka gada tun kakanin farko ba da kakani baya, don
manyansu sun rike da wanan abin sosai tare da kawo cigaban nahiyar tasu ta Argungu din har gobe.
Wanan kadai za ace an saurayi a yanzu cikin arewancin Najeriya da har wasu kashe duniya suke zuwa
kallon irin al,adunmu na hausawa tare da fasahan malam bahaushe dake tafiya da al,adanmu na
Nageria.
Bayan shishi din a gaskiya yana da wuya ace an saura wanan habbaka al,adan da sauran kasashen
africa dake kewayen nageria irin su Niger, ghana, camero kwatano da benin da sauransu su basu yarda
sun bar al,adunsu ba kamar mu.
Zama ya gyara daga bayan motan yana sauraren Sahabi mai daukan photonsu dake wanan sharfin
akan nahiyar ta arewacin Nageria da yanzu abubuwa suke ta kara lalacewa a kasan saboda sanyi da
rashin sanin ciwon kan malam bahaushe a yanzu.
Ai baka sani ba malam Sahabi zance dakai wanan abin tun lokacin da aka ragewa gidan Redio Kaduna
karfi da power abubuwan da dama duk suka shiga tabarbaremuna kai in maka na mahaukaci kamar anyi
wanan abin da manuface zance dakai.
Don wallahi ba karamin koma baya haka ya mayar da Arewa baya akayi ba da hakan hakan ya taba kima
da mutuncin arewa sosai a kasan nan.
Dama sune masu haskawa suna yadawa amma tunda wanan ya faru sai sannu a hankali kaga
abubuwan sun fara ci baya.
Hakane kwarai malam ibrahim maganan ka dutse wallahi wanan abin ya taba arewa sosai don kashe
wanan gidan redio da sauran waje irin masakan kaduna su gidan kada da wajen fata wanan abin ya kawo
muna cibaya sosai a arewa yanzu don da suna raye matasa zasu samu aikin yi a kasa.
Salatin Abubakar ne daga bayan motan ya dawo da hankalin driver ya maida hankalinshi sosai ga a
saman dan wani tsukaken haya da suka biyo inda wasu yan mata ke gara amalanken shanu.
Wanda saura kiris su gwauro da juna Allah dai ya gyara ya takaita masu wahala dole sukaja burki suka
tsaya suna maida numfashi.
Malam ibrahim ne ya soma fitowa daga cikin motar yana fadin kaga min almuran yarinya kawai Allah
ya kawomu lafiya saida mukaga mun shigo gari muna murna zaki ja muna tsiya.
Allah dai ya gyara malam ibrahim barta ta tafi kawai itama kauyancine bata sanda mota a bayanta ba
sun dauka sai masu kafa kawai suke tafe a hanyar.
A daidai lokacin da hakan ya faru uwa mai kulawa da yawan addu,a ga yayanta takanji wani yanayi na
daban aduk lokacin da wani mumunan abu zai samu danta.
Irin wanan yanayin ne ya ziyarci mama a lokacin sai ta shiga maimaita innalillahi a kasan zuciyanta da
sauran addu,oin da zasu aikawa yayan ta dake cikin duniya dama wa yanda ke kusa da ita kariya.
Kasa hankalinta gida biyu tayi tana tunanen Abubakar ko Jafar mai yawan tafiye tafiye don shi ko
yaushe a hanya yake dan kasuwane bai tsaya ga aikin gwaunati ba ya aje ya soma kasuwanci da yake
ganin yafi mai aikin gwaunati a rayuwansa.
Alhamdullahi kuma an samu cigaba sosai a wanan harkan da yanzu har yakai lamarinsa ya fara tsone
idon makiya.
Su ukkune diyanta maza da Allah ya bata da marigayi din sai mata ukku shidda ke nan matan biyu
kananane koda mahaifisu ya kwanta dama autar ta ko yayeta batayi ba a lokacin.
Wanan yanayin daya bakunceta yasa ta fita da sauri ta yafa hijjab dinta dauke da kwalin sugar a
hannunta wanda ta saya a cikin hijjab dinta.
Kofan gida ta nufa akwai tsangaya gaba dasu kadan can takai a rabawa yara sadaka shi kuma malam ta
bashi naira dubu sadaka.
Tun kan tayi nisa take jin an fara raba sadakan sugar tana tafe da dan saurin don ba fita sukeyi haka ba
don wai mijinsu ya rasu suna cikin gida ko yaushe zakice mijin nasu yana rayene.
Don komai da akeyi gidan ba a fasa ba don ko wani daki na gidan yayansu suna rike da uwayensu da
kannensu da wa yanda basuyi aure ba.
Rayuwan gidan marigayi Alh Sanda rayuwace ta ba yabo ba fallasa ga iyalinsa daya bari duniya don ko
yabar masu abinda zasu duba kansu ko bayanshi.
Daidai wadata gwargwadon hali dai ba cancan ba kowansu ya samu kaso daga abinda marigayin
fitacen dan kasuwan tsohon yabari.
Wanda bayan rasuwansa duk kokarinsa da yake raye wajen ganin ya tsaya ya hada kan iyalinsa koda
bayansa ba wani matsala ko barakan rashin hadin kai da zai biyo bayan hakan .
Sai gashi a karshe bayan Allah ya karbi rayuwansa an samu dan matsala a tsakani iyalin nasa saidai
ankai zuciya nesa da wasu bangare sukayi don kawai a zauna lafiya.
Haka din ne kuwa ya biyo baya a yanzu masu zaman hakkuri sunayi yan bamu damu da gado ba ko
dashi ko babu