AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   99 / 103

294K to 297K   out of 306.8K words

zuban hawaye.!"

Hajja Tai k ok arin maida nata hawayen tana jijjiga Ummul take fad in  Ki daina maganganu irin haka Ummul. Ba abinda zai samu Haidar.. Ba abinda zai samesu gaba d aya da izinin Allah. Haidar zai dawo gareki Babu zancen AUREN WATA UKU tsakaninku.. Zakuyi rayuwa mai tsawo tare in sha Allah kinji koh.. Kici gaba da ambaton Allah kinji koh. Da sannu zai kawo mana sauki cikin al amarin.! Ta k arashe hawayen da take ta k ok arin dannewa na zubo mata itama.

Mommy da Aunty Asshe ma an rasa mai bama wani baki Hilal na tsakiyansu Ya rungumesu dukansu biyu shima hawayen yake Ya kasa jurewa. Aunty Asshe fad i take  Ina yawan kiran Anisa shashasha kun sani..? Amma lokacin da akai Aurenta sanda zasu tafi SouthAfrica.. Kun san mai tace min da muka keb e a d aki.? Ce min Tai Ammi ki yafe min.. Nasan na sakaki bak in ciki da dama because of my stupidity..! Asshe yaci gaba da hawaye tana jinjina kai  Sai tace min I ll make it up to you Ammi..! You will be proud of me..! Ammi Ina sonki..! Kice ma Abba ya yafe min.. Kuma kice ma Hilal ina son shi.. And I thank him for always having my back.! Ta k arashe cikin kuka yayinda Hilal ma ta matse hawayen da suka gangaro masa.

Mommy kam bata iya cewa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro mata tana tuna randa ya dage sai an basa matarsa da D ansa Sun tafi.. Ta tuna irin draman da akai kafin ta amince Ya d auki iyalinsa su tafi.. Ta tuna saida ta aje masa mata na tsawon watanni uku kafin ta basa matarsa.. Ta tuna sanda ya shigo ya mata Sallama da kalamansa

na soyayya a gareta. Ta tuna yanda yaita bata hakuri yana fadin bazai tafi ba sai ya daina fushi dashi kuma sai ta saka masa albarka. Sai Mommy ta rintse ido hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata  My prayers are with you Son.. Allah bazai basu dama akanka ba.! Ta k arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Daddy kuwa yana daga waje bakin parlorn shida Alhaji Gimba yanda Alhajin Gimban keta k ok arin kwantar ma abokin nasa hankali.

Duk k arfin hali na Daddy saiga hawaye na gangarowa daga idonsa. Ya kuma d agowa yana duban Alhaji Gimba. Cikin zuban hawaye Daddy yaci gaba  Gimba my two Sons.. Yarana guda biyu wanda nai failing dinsu tin suna yara ko ince Tun suna ciki basu zo duniya ba..! Wad anda Allah ya bani su cikin tausayinsa da jin k ansa da kuma rahamarsa amma sai nai masa butulci ban nuna godiya a gareshi ba.! Guda d aya na sheganta shi da harshena na koreshi tin yana ciki.. Ya girma babu mahaifi..! Guda d ayan kuma.. Ya girma gaba na amma banyi appreciating d insa ba. Ya girma tamkar Babu mahaifi sabida wofantar dashi da nai akan idona..! Yau gashi dukansu biyu suna hannun barayin Daji Gimba.. Su biyun sunyi abota tin basu san sud in  yanuwa bane. Amma abotan Ya koma k iyayya a lokacin da Ya kamata sufi son junansu bayan sun fahimci Sun had a mahaifi guda.. Gimba inaji kaman ni na haifar da conflict d in dake tsakanin yarana guda biyu.. I failed them both.. And now.. Ban sani ba.. Ko dai na sake ganinsu ko ba na sake ganinsu ba..! Gimba kana ganin Har yanzu Ubangijina hukunta ni yake akan laifuka na na baya.?! Ya k arashe yana girgiza cikin zuban hawaye.

Alhaji Gimba Ya girgiza kai  Kar kayi magana irin haka abokina. Duk abinda Ubangiji Yayi daidai ne. Ba a saka ayar tambaya. Tsarki ya tabbata gareshi mai mulkin sammai da k assai mai juya al amara yanda yake so. Idan yaso Yayi mana rahama idan yaso Ya azabtar damu duka iko nashi ne akan halittunsa. Sann duk halinda muka tsinci kanmu ciki rahamarsa ne. Ya dan numfasa kafin yaci gaba  Ka daina dawo da kurakuren da kai baya kana azabtar da kanka dasu. Mu dukanmu  yanadam ne kuma masu kuskure sann mafiya kyawun masu kuskure cikinmu sune masu tuba. Wanda mukai tuba na gaskiya dominsa Ya sani sann shi d in mai yawan gafara ne mai jin k ai. Ya dan dafa hannun Daddy  Tabbas idan Munyi imani za a jarabce mu.! Kai hakuri abokina kai tawakkali. Ka saka ma ranka wann rajabawa ce daga Allah.. Muyi addu an Allah Ya kub utar dasu Ya dawo mana dasu lafiya..

Daddy ya amsa da Ameen yana mai waigawa ko zaiga Sadis amma bai gansa nan wajen ba.

Alhaji Gimba Ya gyara zama yace  Kuma Haidar kawai suka nema yakai kansa.? Sann meyasa baayi gaggawan sanar da jami an tsaro ba dan a samu a shawo matsalar da wuri.

Daddy yai saurin girgiza kai  A a Gimba rayuwar yarana are at stake here.. Kaga ita Anisa ma cewa sukai juna gareta kaga dole abisu yanda suka buk ata kasan yanda wad ann azzaluman mutane suke gudanar da al amaransu sam babu Allah a ransu Gimba. Yanzu mistake kad an zaayi su hallak a min yara gaba d aya. Watak ila idan Haidar yaje su nemi Ransom mai tsoka.. Ni ko rayuwata suka nema ba Kampanina da abinda na mallaka ba zan basu dan su sako yaran nan Gimba.

Alhaji Gimba Ya tsare Daddy cikeda tausayawa. Sai yana tuna lokutan baya da Daddy ke cewa kampanin sa Ya fiye masa Haidar. Yau gashi yana ce zai sadaukar da komai nasa dan ya ceci Haidar ciki harda rayuwarsa. Ya dan numfasa sai kuma yace  Amma akwai alaman tambaya a nan Abokina.. Meyasa zasu buk aci Haidar Ya kai kansa..? Meyasa Kai tsaye basu nemi Ransom ba.? I m sorry to say this.. Abokina Anya baza a duba maganar Haidar ba.? Banso na saka maka zargi ko shakku akan D anka musamman da shike baku jima da kasancewa da juna ba.. Amma..

Daddy yai saurin dakatar da Alhaji Gimba yana girgiza Kai  Haba Gimba kar kace kaima ka yarda da shirmen Haidar. Haidar zafin kishi kawai ke d awainiya dashi amma d an uwansa bai nufinsa da komai face alkhairi. Masu garkuwa su suka sacesu. Kasan mutanen nan da salo salo na yaudara.. Kar ka mance sukan sace mutum su nemi kud in fansa Wanda yakai kudin ma suyi garkuwa dashi.. Sai ya d anyi shiru kaman Wanda Ya tuna wani abu  Haidar shine in charge na sabon kwangilan titi da mukeyi a jihar Lagos.. Kasan Kampani da dama sun nemi kwangilar basu samu ba.. Kanaga garkuwa da akai da yaran nan nada alak a da wann kwangilar tinda gashi basu nemi ransom ba sai Haidar..!

Alhaji Gimba yai shiru sai kuma ya jinjina kai kad an  Everything is possible here.. Amma Kai tsaye bazamuyi saurin yanke hukunci ba.. Saidai dole mu saka abinda kace into consideration. Allah dai ya bayyana mana su cikin aminci..

Daddy ya amsa da Ameen yana jinjina kai.

**

Kutsawa yake cikin dajin yayi tafiya da baida wani nisa daga bakin kwalta. Kasancewar ba daji bane sosai hakan yasa Sadis bai sha wahalan samun layin Haidar ba. Bakin kwalta Haidar ya bar motarsa Ya sauk a d Ya fara tafiyar k afa. Nan yake sanar da Sadis ya kunna tablet d in da sukai connecting spy camera din dake button din wuyar rigar Haidar d in dashi. Akwai app da sukai installing cikin tablet d in yanda kowa zaiga live streaming abinda ke faruwa. Spy Camera d in dake jikin button d in wuyar rigar Haidar zata dinga nade komai yanda su kuma zasuke gani cikin tablet d in.

Lokaci guda Sadis ke fad in an gama.

Daddy yana gefe nan cikin parlorn yana amsa waya bayan Alhaji Gimba Ya fice zuwaga majalisunsu zai sanar dan a tayasu da addu a. Ga security ya kuma zama very tied a gidan. Har lokacin su Mommy jigum jigum suke. A haka Sadis ya shigo parlorn rik eda tablet d in yace dasu gaba d aya Haidar yana so suga abinda zai kunna musu.

Take hankulansu ya dawo ga Sadis. Daddy ya katse wayan da yake ya k araso yana tambayar Sadis meke faruwa.? Mai Haidar yake so su gani.?

Take Sadis ya kunna tablet d in ya kam video na sirri da Haidar ke nad a Wanda ke mak ale gaban rigarsa kaman button.

A haka Haidar yaci gaba da kutsawa. A daidai jikin wata bishiya yaji alamun fito. Yaja Ya tsaya yana waige waige. Can ya hangi wasu k artai guda biyu Sun fito daga bayan wata k atuwar bishiya.

Daga nesa sukai masa umarni da  Hands in the air.

Haidar ya d aga hannayensa sama alamun surrender.

Kartan suka k araso guda d aya yai searching Haidar dan ya tabbatar bai d auke da makami. Yayinda guda d aya yake lek en bayan Haidar d in dan ya tabbata shi kad ai yake babu jami an tsaro.

Ya dubi Haidar yace  Are you sure you are alone.?

Haidar ya jinjina Kai  You can be sure I m alone.!

Suka amshi cell phone d insa kafin sukai blindfolding d insa.

Tafiya kad an sukai idanun Haidar suna rufe. Sai yaji alamun kaman ba mutanen wajen. Abinda kunnuwarsa suka soma sinkayowa shine gurnani da kuka kaman na mutanen dake cikin azaba.

Anisa wacce ita ta soma hangosa fad i take  Haidar..! Haidar please help.. Help me.. Zasu kashe ni& !

Cak Haidar yaja Ya tsaya ga idanunsa a rufe.. A hankali Ya furta  Anisa..! Cikin sauri Ya zame abinda suka rufe masa ido dashi. Ya nufo Anisa dake kwance jini na bin k afarta. Cikin tsananin shock yake furta  What happened to you..? Mai Hisham ya aikata Miki..? Ina Hisham yake..? Su waye wad ann..? Come.. I ll save you.. We need to leave this place.. Ya k arashe yana k ok arin d agota. Saidai bai rufe baki ba ya sinkayo muryar Hisham dake baje cikin chakwabi na laka. Sam bai ma zata mutum bane wajen Ya zata curin k asa ne ko wani abin. Da kyar Hisham Ya d ago hannu yana fadin  Brother please don t leave me here.. Dan Allah kar ka barni a nan.. Zasu kashe ni wllhi..!

Girgiza kai Haidar yake yana duban Hisham cikin rashin yarda  Wai meke faruwa ne haka a nan..? Meye kake shiryawa ne Hisham..? Meye ka aikata ma kanka.. Mai ka aikata muku.. Mai zakai gaining cikin duka wann wasan.?

Cikin murya irinta mai kuka Hisham ke fad in  Ka yafe mun Haidar..! Ka tausaya mun ka fitar Dani a nan.. Wllhi kasheni zatayi..?

 Zata kasheka..? Ita wa..?

Daga bayansa Ya sinkayo murya tana fad in  Banyi alk awarin kashe ka ba Hisham Har sai kayi confessing duk wasu abubuwa da kayi ma Haidar da ahalinsa.!

Cikin wane irin yanayi Haidar ke juyowa Har ya sauk e idanunsa tsaf akanta.  Dareen.! Ya furta cikin tsananin shock yana duban Dareen dake zaune bisa wheelchair.

 You.. you are alive.? Haidar ya kuma fad i yana dubanta.

Dareen ta saki murmushi  Im alive Haidar my love.. I am very much alive.. Burin wad ann azzaluman na ganin sun kashe ni sun rufe baki na bai cika ba.! Sunyi k ok arin takeni da mota dan kar na isa gareka na tona asirinsu wajenka.. Sunyi nasaran takeni da mota amma basuyi nasaran kasheni ba kaman yanda sukai nasaran kashe mana jaririnmu mai watanni uku a ciki..! Haidar I was carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. The only abu da zan dinga gani na tuna soyayyarmu.. Wad ann azzaluman Sun kashe min shi.. Kaman haka nayi alk awarin tatse tsinannen D ansu dake cikin Anisa dan su d in basu cancanci zama iyaye ba.!

Girgiza kai Haidar yake yana dubanta tashin hankali k arara saman fuskarsa. Lokaci guda Ya daga hannaye sama a hankali kaman mai surrender. Fad i yake  You don t need to do this Dareen..! You don t need to torture them like this.. You don t need to kill their child.. Just let them go please.. Let Anisa go.. She s bleeding..!

A fusace Dareen ta katsesa da fad in  No Haidar.! They killed our child..! These two monsters killed our child.. Na kiraka ne kaga fansar d aukan ran D anmu da sukayi sann wann Devil din yai confessing duk abubuwan da Ya maka. Wanda ya hana na sanar dakai ta hanyar amfani da Anisa ta bigeni da mota..! A yau shi da bakinsa zai fad i komai akan fuskarka Haidar. Zai fad i duk abinda yai maka da ahalinka..!

Ta mik a hannu ta cakumo Hisham dake layin azaba  It is game over for you.! Start talking Bastard.! Ka fad a masa yanda ka kawoni cikin rayuwarsa ta hanyar sihiri dan ka tarwatsa tsakaninsa da iyayensa.. Talk.! Ta k arashe tana turasa gaban Haidar yanda Hisham Ya zube gaban Haidar yana nishi.

Zamu iya cewa ba D anadam guda dake motsi parlorn Daddy.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*64*

*©þSameena Aleeyou& *

Har lokacin duk e Hisham yake gaban Haidar yana fidda numfashi da kyar. Ya kaikaito yana duban Dareen dake zaune saman wheelchair gefensa. A hankali yake jinjina kai yana dubanta  So this is your plan..? To exact revenge.?

"Cakumosa Dareen ta kumayi tana huci  No, this is not revenge but a Karma.. This is exactly what Karma looks like..! When you feel you are at the lowest of your life..? Ta murmusa  You think you are Smart Hisham.? Well I m ten steps ahead of you.. Filthy Bastard..! Tell him now.. Tell him everything.! And when I said everything.. I mean every.. Thing..! "

Haidar yaci gaba da duban Hisham yana girgiza kai da idanunsa da tuni Sun kuma kad awa  I know you ve always known& Ka jima da sanin cewa kai din.. d an mahaifina..? Sann dalilin da Yasa ka shigo rayuwata kenan.. Haka ne..?

Hisham Ya jinjina masa kai yana dubansa. Murmushi saman fuskarsa  That s right Haidar.

Haidar ya jinin kai kad an  But why me.. Meyasa ni..? What have I done to you..?

 Because ta hanyarka ne kawai zan kutsa cikin ahalin ka na kuma tarwatsa ku..! Nayi rantsuwa matuk a ina numfashi your family will never be whole.. I vowed to be shadowing each and every step you take in life.! Nayi rantsuwa sai na tarwatsa ku.! Yaci gaba da jinina kai yana duban Haidar  Na kawo Dareen cikin rayuwarka dan na samu saukin tarwatsa ku.!

A fusace Haidar Ya katsesa  But that family you tried so hard to break has already been broken.. Wann ahalin Ya riga Ya tarwatse tin kafin zuwanka.. Kuma kasan mai..? I ve paid the price..! Na girma Ina biyan wann farashin.. Ka sani.?!

Hisham yai saurin katsesa No Haidar baka biya komai ba..! Baka biya komai ba kan irin rayuwar da na fuskanta..! Hisham yaci gaba da hawaye yana duban Haidar d in  I grew up in a misery..! I grew up watching my Mom suffering.. Suffering from the misery your parents inflicted on her..! Before you judge me.. Ina so ka saurari nawa b angaren labarin.!

Cikin huci Haidar ke dubansa  Nothing justifies what you did Hisham.. Kai dan adam ne kaman kowa and you had your chance to do what s right..!

"Hisham ya girgiza Kai  Mai zakace ga D an da aka haifesa a kurkuku..? Mai zaka ce ga yaron da Ya taso cikin kyama da tsangwama..? Mai zakace ga yaron da Ya taso ba tareda yasan mahaifinsa ba.. Mai zaka ce ga yaron da aka turasa kurkuku sabida rashin galihu sann a wann kurkukun yasan cewa a nan aka haifesa..? Mahaifinsa shi ya jefa mahaifiyarsa a wann kurkukun da Ya zamto tushensa.. Sann..

99 / 103