AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   91 / 103

270K to 273K   out of 306.8K words

ba yau ne rana na farko da na fara neman Aure ana rejecting dina ba. "

Kalamansa sai ya tuno ma Daddy labarin da Hisham d in ya basu lokacin da yaita Neman aure ana rejecting d insa sabida rashin cikakken asali. Wanda Daddyn yake ganin hakan kaman laifinsa ne. Now is the right time for him to be a father to his son.

Daddy ya dubi Hisham yace  Ya isa haka Son. Just don t mind your brother. A hankali wataran zai fahimceka. Idan Kana so ka auri Anisa zan nema maka Aurenta. Ba Anisa kawai ba. Kai Ko ina kake so kaje neman Aure ni mahaifinka Aliyu Maitama zan tsaya maka.. Ko  Yar gidan waye kuwa. Ba Wanda zai sake maka gorin asali.

Hisham ya murmusa cikeda Jin dadi. Kaman zai kuka yake furta  Thank you Daddy..! For the first time in my life.. Naji a raina Nima inada mahaifi kaman ko wani D a.

 Ya kamata kaji haka koda yaushe. Because your Dad will always be here for you kaji koh.

Girgiza Kai kurum Haidar keyi kafin yasa kai ya fice daga parlorn dan bazai jure kallon Kayan bak in ciki irin wann ba. Mommy ta mik e tabi bayansa.

Daddy ya dubi Hisham yace  Amma wani hanzari ba gudu ba.. Kanaga za a bada belin Anisa cikin sauk i musamman yanzu da iyayen yarinyar can Dareen suka bayyana kuma suke Neman hakkin Ran  yarsu.?

"Hisham ya jinjina Kai  K warai Daddy. Da ace Anisa bata amsa cewa da ganganci tabi kan Dareen da mota ba Tabbas da abin yafi zuwa da sauk i. Babban abinda zaisa a bada belin Anisa a halin yanzu shine rashin ganin gawar Dareen Wanda ganin gawar Dareen ne kad ai zai tabbatar da mutuwar ta. Kaga zamuyi amfani da hakan a court. Da taimakon k wararren Lauya kotu zata amince ta bada beli koda za a ci gaba da Shari ar. Daddy ita kanta Anisa da ta bige Dareen batada tabbacin Dareen ta Mutu ko bata Mutu ba tinda bataga gawar ta ba balle ta tabbatar kaman yanda ta fad i a statement dinta. So bazai yuwu a yanke ma Anisa hukunci ba tareda k wakk waran dalili ba. Anisa ta cancanci second chance kaman kowa a rayuwa Daddy. Kuskuren da ta aikata bazai zama dalili da zaisa a juya mata baya ba. Daddy idan ka amince min zan tsaya tsayin daka har sai na tabbata Anisa ta Sami freedom din data cancanta. Dan rashin adalci ne a barta a rufe ba tareda an tabbatar da ta aikata laifin kisan ba. Idan har daga baya wani abu ya bayyana.. Ina nufin aka samu gawan Dareen ko wani k wakk waran dalili da zai tabbatar da mutuwar Dareen.. Ka yarda dani Daddy ni da hannuna zan mik a Anisa ma hukuma, Alk ali yai hukunci koda bayan ta zama matata. Zan kuma d auki hakan matsayin k addara Daddy dan D anadam bazai wuce k addararsa ba. Daddy I believe Anisa ta cancanci Rayuwar farin ciki mai cikeda  yanci a Gidan Aurenta koda na dan lokaci kad an ne. Ina fata ta Sami wann opportunity d in a rayuwa ta samu wann experience din koda na dan lokaci kad an ne.. Balle ma in sha Allah baza a sameta da laifin kisan ba. Ya k arashe cikeda kulawa."

Mommy dake tsaye bayan parlorn duk sai jikinta yai sanyi. Sai ta rasa tausayin waye zataji. Anisa dake tsare ne ko kuwa Hisham d in ne dake kokarin nema mata  yanci Wanda take ji kaman dukkansu sunyi failing Anisar sai Hisham ne zai sadaukarwa mai girma ga d iyar  Yaruwar tata.

Daddy ya dafa kafad an Hisham  I m proud of you Son. Kanada zuciya mai kyau kuma mai yalwa. Allah ya maka albarka da wann sadaukarwa mai girma da kake k ok arin yi. Amma ina so ka fara tuntubar mahaifyarka da batun. Munyi waya ta kuma sanar Dani gobe  yanuwanta zasu mata rakiya zuwa nan Abuja. Yanada kyau kaji nata ra ayin da shawarin.

Hisham ya amsa da  Shikenan Daddy zanyi kaman yanda kace in sha Allah.

Daddy ya amsa da  Maddallah. Allah yayi jagora.

Hisham ya sake amsawa da Ameen kafin yai Sallama ma Daddyn ya fice zuciyarsa wasai.

Washe gari kuwa Hajja ta samu tarewa zuwa gidan mijinta Engr Aliyu Maitama a nan birnin tarayya tareda rakiyan tsirarun  yanuwanta. Daddy yaso ya raba musu gida ita da Mommy amma sai Mommyn harma da Hajjan suka zab i zaman tare a gida d aya. Hakan yasa tuni aka gyara ma Hajjan nata sashen a nan cikin gidan.

**

Anisa bataji mamakin ganin Haidar ya kawo mata ziyara ba dan tasan izuwa wann lokacin labari ya isa masa cewa Hisham naso ya aureta.

"Haidar ya tsareta sosai da ido kafin ya gyara zamansa yace  Tell me, is it true& Da gaske ne wann D aniskan ya miki tayin aurensa.? "

"Ta furzar da huci kad an had ida rausayar da ido  Believe me I couldn t believe it either.. I mean how shameless of him. Ta ya zai soma cewa zai aureni bayan ukuban da ya jefani ciki..! Ka yarda dani, Ya b ullo ta wann salon ne bayan da yaji an maida Aurenka da Ummulkhair. Na tabbata wani abun yake son shiryawa. "

Haidar yai shiru kaman mai nazari  And you.? What are you suggesting.?

Anisa taci gaba da jinjina Kai tana dubansa  Zan amince da Tayinsa. Zan aure shi.

Da tsananin mamaki Haidar ke dubanta  Did you hear yourself. Kin kuwa ji mai kika fad a.? Zaki amince ki amshi tayinsa.? Zaki amince ki aure shi..? Are you going to let him use you for the second time.?!

Murmusawa tai kad an  You might know Hisham as a friend.. Amma ni na sanshi ne a matsayin mugu. Hisham is a very coning person. Idan yace zai Aureni kaman ya sadaukar da wani portion ne na soyayyar da yake ma Ummulkhair. Knowing Hisham bazai tab a sadaukarwa mai girma irin wann ba ba tareda ya samu wani babban outcome ba. Idan har yace zai Aureni ka yarda dani akwai wani shiri babba da yake kullawa ta k ark ashin k asa. Kar ka mance Hisham ya kawo mace cikin rayuwarka har ta aureka kukai rayuwar aure ba tareda ka ankare ba. Wanda duk zai aikata abu makamancin wann ba k aramin shed ani bane. So na sani Hisham ba mutum bane da za ayi under estimating d insa. Duk abinda yake yi is well calculated. Amma ka yarda dani aurena da yace zai yi wann karon shine babban miscalculation mafi muni da zai tapka a rayuwarsa. Ni ba wann shashashar Anisa da ka sani a baya bane. Bazan Auri Hisham dan na bashi dama yai amfani Dani ba. Saidai ni nayi amfani dashi. Wann karon zai tone ramin da zai rupta ne a ciki da Kansa ba tareda ya ankare ba. Zan tabbatar mishi da cewa ni mace ce kuma yayi kuskuren underestimating dina. Ni yafi cancanta na bayyana asalin waye Hisham sabida Dani yai amfani. Kuma aurensa da zanyi shi zai bani dama na samu duk wani kusanci dashi sann na yaye rufin fuskarsa kowa yasan waye shi. Ka yarda dani Hisham bazai tab a barinku ku samu peace ba kaida Ummulkhair matuk a yana nan a kura lullub e da fatan akuya.

Haidar ya girgiza Kai kad an  No.. No Anisa. I won t let this happen. Ina nufin bazan bari ki jefa rayuwarki cikin had ari ba dan kawai asirin Hisham ya tonu. Kin kuwa san mai ake nufi da kalmar Aure.? Ta ya zaki amince ki auri mutumin da ke kanki kinsan ba mutum bane. Anisa Aure is a life time commitment.. Ke  Yaruwata ce kuma k anwata. Koda ace bamu had a alak a ta jini ba bazan bari wann devil d in ya kusanceki ba balle har akai ga maganar Aure. Aure is serious commitment. Na d auki al amarin Aure da wasa a farko naga yanda ya juya mun. Bazan barki ki d auki wann path din ba. Bazan bari kiyi gambling da rayuwarki ba dan kawai kina so ki tona asirin Hisham. Ya dan furzar da huci yana jinjina Kai kad an  Akwai ways da yawa da za a Kama shi. Yanzu haka nasa ana bincike kan iyayen Dareen.I believe a hankali through wad ann mutanen zamu samu wani haske gameda gaskiyar al amarin mutuwar Dareen ko nace b acewarta. If she s alive ita kad ai ce zata iya kawo k arshen yaudarar Hisham.

Anisa ta murmusa  And what if she s dead.? Zan tabbata ne kawai a nan gidan yari babu ranar fita. Sann Hisham bazai tab a biyan duk abubuwan da ya aikata ba. Uwa uba bazai tab a bari ku Sami kwanciyar hankali ba kaida Ummulkhai. Ta dan numfasa  Na gode da kulawarka a gareni D anuwa. Amma Hisham ya wuce tunanin mutum.. Bana tunanin akwai wani bincike da zaisa a Kama Hisham dumu dumu dan shi d in k wararre ne. Sann baya barin wani shaida da zai tracing back to him. Abu d aya da zaisa a Kama Hisham shine abi ta hanyarsa. Ina nufin makirci.! Aurensa ne kawai zaisa na samu kusanci dashi. Taci gaba da jinjina Kai a hankali  I might not be innocent. Kuma nasan in one way or the other dole zan biya abubuwan da na aikata a rayuwa. Tabbas ni nake driving motar. Ni na bige Dareen da Mota but under the influence of Hisham. Ka yarda dani bansan ina hankalina yake ba lokacin da na bige Dareen maganganun Hisham ne kawai suke yawo a kwanyata. K ok ari kawai nake na dakatar da ita kar isa gareka kaman yanda Hisham keta tunzura ni da na dakatar da ita. Dan idan ta isa ta sanar dakai komai zaka tsaneni koma ka hukunta ni. Ashe amfani kawai yake Dani dan na zame masa garkuwa na aikata laifin da zai amfani ya rufe bakina dashi. While I m stuck here Hisham bazai tab a biyan abubuwan da ya aikata ba. Ina buk atan ficewa a nan dan na tabbata ya biya duk abubuwan da ya aikata.

Haidar ya furzar da huci kad an yana jinjina Kai  Idan haka kika zaba. Fine.! Kowa yanada  yancin yin yanda yaso da rayuwarsa. Amma bana so ki saka ma ranki sabida ni Haidar zaki sadaukar da farin cikinki da rayuwarki ki auri mutum irin Hisham. Idan duk abinda kike fad a gaskiya ne Anisa. Then Do it for yourself.. For your own freedom.. For you to clear your name...! Yana ida fad in haka ya mik e yai ficewarsa.

Anisa ta bisa da kallo har ya bace mata. Ta lumshe idanunta hawayen nadama suka gangaro mata.

**

A cikin satin maganan Auren Anisa da Hisham ya kankama. A b angaren Hajja sai bata kawo komai a ranta ba tafi alak anta hakan da Jin k ai da taimako da D anta ya saba tsakanin Al umma tinda d abi ar taimako shaidarsa ce. Sann hankalinta ya kwanta da maganan Ummulkhair musamman da yake an maida Auren Ummul d in da D anuwan Hisham d in wato Haidar. Ga Hisham ma zai nasa auren ya samu natsuwa. Itakam maganar Auren sosai tai na am dashi dukda can cikin zuciyarta bata Jin wani abu mai Kama da farin ciki gameda auren. Sann Sam bata samu natsuwa hundred percent ba sai kawai tai k ok arin kawar da tunanin dan tasan bazai shige aikin shed an ba tinda shi Sam baya fatan a k ulla alkhairi musamman a batu irin na Aure. Bugu da k ari bayan series of Aure da D an nata yake nema a baya ana hanasa idan tak i wann sai ya zama kaman tayi butulci ne ma Allah. Tuni ta bar ma Allah lamarin ta kuma nema zab insa ciki. Ko wane aure yana zuwa da nasa k alubalen. Waye zai tab a tunanin wai ita Fannah D anta zai auri d iyar Asshe k anwar Hajiya Kwaise.? Waye zai tab a tunanin zata dawo gidan Aliyu Maitama suyi rayuwa mai tsafta da Hajiya Kwaise.? Lallai rayuwa cike yake da sauye shayen lamra. Allah ka sauya mana sharri zuwa alkhairi. Ameen.

Cikin k ank anin lokaci aka aiwatar da komai dan tinda akazo da batun auren sai Anisa ta samu sassauci daga wajen iyayenta musamman Abbanta Wanda dama shi yaima Amminta iyaka da ita matuk a tana tsare a police station. A cewarsa bai haifi  yar da zata d aga masa hankali ba. Ba kaman da Abban Anisar yaga D an Aliyu Maitama ne mijin Anisar. Abun duka gida ne.. Hakan yasa babu wani dogon bincike balle jan lokaci. Balle ma shi ina ruwansa baijin ko kashi Anisa ta kawo zai fasa aura mata da dai ta zame masa masifa da tashin hankali cikin gidansa. Can Kano gidansu Anisa akaje ka d auro Aure ko gida Abbanta bai bari taje ba daga cell yace a wuce da ita d akin mijinta. Taron biki ma bai bari an masa a gida ba. Mommy ce ta had a yar k aramar biki can Abuja. Da kyar Abban Anisa ya bari Asshe ta halarta bikin yar nata.

Bayan biki da kwanaki biyu Daddy yace da Hisham wann karon shi zai tafi SouthAfrica dan ya kula da kasuwancinsu na can. Ya d auki matarsa su tafi can musamman da yake an dage sauraron k aran Anisar har sai bayan watanni hud u masu zuwa. Sam Hisham bai k i tayin Daddy ba. Sati guda kawai sukai a Nigeria ba tareda Anisar ta tare da angon nata ba tinda sud in ma tafiya ne. bayan bikin suka tattara suka nufi southAfrica. Tafiyar da zai d auke su tsawon watanni uku.

"Da wutsiyar ido yake duban Anisa sanda suka zauna saman kujerun jirgin. Ya saki wann muguwar murmushin nasa kafin ya rank wafo kad an cikin k ok arinsa na d aura mata seatbelt  Babe, I can t wait jirgin nan tai landing. A hannu zan sureki na fara nuna miki soyayyar da ban samu daman nuna miki a Nigeria ba. "

Banbarakwai haka taji abun. Ta watsa masa wani irin mugun kallo kafin tai  yar bazawarar murmushi na nuni da takaici  Kar mu raina ma kanmu hankali Hisham. Nida Kai munsan babu komai cikin auren nan face k arya. So we shouldn t expect anything from this marriage. Dan ina mai tabbatar maka ni Anisa bazan tab a barinka ka tab a koda d an yatsana ba cikin watanni uku da zamuyi tare. Kuma ka saka ma ranka.! AUREN WATA UKU shi mukayi. Ina cika watanni uku a lokacin da muka dawo Nigeria zan rabu da k addararren aurenka.!

Hisham ya tsareta da ido. Sai ya murmusa yana daidaita zamansa saman seat din. Irin Wanda ya kware a shed ana yake fad in  A naki wauwautan Anisa kinyi zaton wasa da hankalina kike..! Kinyi zaton kin Aureni ne dan Ki samu dama akaina ki bankado duk wasu sirrika na. Haka ne..? Kina tunanin a watanni uku da zamuyi matsayin mata da miji zaki iya samun dama akaina ki bankad o duk wasu sirrika nawa.? Har haka kike son Haidar.? Dan na tabbata sabida shi kikai sadaukarwa mai girma kika amince da aurena.! Yai maganar yana shafe hab arsa yana mata wane irin duba. Har lokacin murmushi ne saman fuskarsa  Lallai kin tabbata sokuwa Anisa idan har kikai tunanin zaki iya outsmarting dina by marrying me.! Ya k arashe yana kamo hab arta suna fuskantar juna. Murmushin itama ta sakar masa dan bazata bari ya gane ta karaya ko abu mai Kama da haka ba.

Ya dan girgiza Kai yana dubanta  Bazaki tab a yin hankali ba balle wayo Anisa. Idan amfani dake a karo na farko ya fi min sauki a lokacin da ban Miki farar sani ba. Meyasa amfani dake a karo na biyu lokacin da na sanki kaman tafin hannuna zai min wahala. Ya d anyi gajeren tsaki had ida yin  yar bazaurar dariya irin Wanda ake ma Wanda aka raina masa

91 / 103