AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   96 / 103

285K to 288K   out of 306.8K words

 Na tsaneka Hisham..! Allah ya isa fyaden da ka dinga mun.!

Hisham yaci gaba da murmushi yana shafa hab arsa  Daga baya kenan& Na Miki na k arfi sau d aya amma duka sauran da yarda da amincewarki akayi..! Cikeda gargadi yaci gaba  Kuma bari kiji na fad a Miki wllhi kikayi gigin cire cikin nan ko kika bari wani abu ya samu cikin nan..! Sai ya girgiza Kai yana dubanta  I don t know what I might do to you Anisa.!

Murmushin takaici Anisa take tana dubansa  I can t believe I m three months pregnant with your child Hisham. A monster like you bai cancanci zama mahaifi ba.!

Murmushi Hisham ya kumayi yana dubanta kafin ya sakalo hannunta cikin nasa  You won t do anything foolish Anisa..! You will face them and act cool..! Ya k arashe yana mai finciko hannunta suka nufi arrivals.

Can ya hangi Mota mai d aukeda plate number na Company d insu. Ya rik o hannunta yana fad in our ride is here.

Babu wata wata suka shige bayan motar Hisham na kuma jero ma Anisa warnings. Tana fad in yayi kad an ya sakata yin abinda batai niyya ba. Haka akaita shera gudu dasu sai masifa suke tsakaninsu sam bama su kula da waye driver din nasu ba dan p cap ne akansa.

Saida akai nisa sukaga driver ya canza hanya ya d auki wani hanyar.. Hisham ya fara fad in  Lafiya..? Wane hanyar kake bi.. Hey who are you.. Why can t you turn back..! Hisham ya k arshe yana k ok arin fizgoshi saidai tuni driver d in ya murda AC din motar take wani abu kaman hayak i ya gauraye cikin motar. Suka soma tari gaba d aya idan ka d auke driver d in da hancinsa ke rufe da nose mask..

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*62*

*©þSameena Aleeyou& *

"Suna zaune gaba d aya parlorn Hajja a sama, hira suke na yaushe rabo cikeda nishad i. Ga gidan tuni Ya soma cika sakamakon taron da zaayi da yamma. Dan har wasu dangi daga Maiduguri Sun samu hallara. Koda Haidar Ya Lek a yaji hayaniyar mutane sai bai haye saman ba yai zamansa a parlorn k asa. Wayarsa ya Ciro Ya tura mata sak o."

Ana tsaka da hira sak on Haidar ya shigo ma Ummul.

_I m hungry_

Ta karance sak on sai ta soma waige waige. Ta tura masa reply

_Where are you_

Ya mayar mata da amsa

_Downstairs.. Waiting for you_

Mik ewa Ummul Tai da zummar barin wajen Salima tace ina zata suna tsaka da hira. Ummul ta d an juya ido tana mata alama da k asa.

Badia tai gyaran murya tace  Haba Aunty Salima sai kin mata tonon silili ne. Wajen Oga Haidar zata.

Salima ta jinjina kai  Haka kuma. Toh a dawo lafiya..

Murmushi kawai Ummul tai tasa kai ta fice. Tana ficewa kuwa Salima ta dawo kan Azeema tana fad in sai ta fad a meke tsakaninsu da Sadis d in can. Nan Badia ta saka baki tana fad in itama ta kula tsaf da su biyun. Azeema kaw sai cewa take ita ba komai tsakaninsu fah sai mutunci.

Ita dai Khulsum kallonsu kawai take jikinta duk a sanyaye ba tareda tasan dalili ba. Bata san meyasa ba amma haka kurum taji tunaninsa Ya zo mata. Tinda ya koma makaranta bata sake ji daga garesa ba. K ila ma Ya mance da ita. Saurin kwaban zuciyarta tai da fad in  Toh ke ina ruwanki dashi.. Meyasa zakiyi tunaninsa Har haka.. Ya mance da ke kema ki mance dashi. Saurin mik ewa Tai ta bar wajen cikin k ok arin kawar da tunanin.

A parlor Ummul ta iske Haidar. Sanye yake da jampa ruwan k asa harda hula. Ya turo hular saman fuskarsa had ida kishingid a cikin kujeran. Tai tsaye tana dubansa murmushi saman fuskarta. A hankali take takowa Har ta iso kusansa. K amshin ta ne yai masa Sallama. A hankali yasa hannu Ya janye hular. Ya bud e lumsassun idanunsa yana dubanta. Tayi kyau cikin leshi golden brown color. Dinkin sosai yai mata kyau Ya zauna jikinta kaman wacce bata jima da haihuwa ba.

Ya bud e mata hannayensa daga nan yanda yake kishingide  Come here.

Ta d an fito da ido tana dubansa. Sai ta soma  yan waige waige.

Haidar yace  What..! Taho mana.

Ta d an langab e kai kad an  Wasa kake.. Ka mance ina muke ne.

Gyara zamansa yai kad an had ida furta  Fine.. Kin sama min mai zanci.? Yai maganar yana mai janyo hannunta.

Ta d an girgiza kai  Gidan gaba d aya cike yake.. Barin kira kitchen naji mai suke dashi.

Tabe baki yai kad an  Banson abincin Chefs din gidan nan.. Sun Faye cika yaji& 

Ta d an marairaice fuska  Toh ya kake so ayi Rankaidade.? Mu fah bak i ne a nan. Kai hakuri kaci haka.. Idan munje gida sai na girka maka abinda kake so. Cikin sigan lallashi take maganar.

Sosai suka birge Hajja har taji dama bata sauko parlorn ba dan kar ta katse musu soyayyarsu.

Ummul ta d an matsa baya kad an daga kusan Haidar tana ma Hajja sannu da sauk owa. Haidar ma gaisar da Hajja yai kafin daga bisani Hajja ke musu tayin Burabusko miyan taushe da ta dafa ma Daddy. Ta k arashe tana fad in Ummul ta taho ta kawo ma Haidar.

Haidar ya dan shafa kansa kafin ya katse hanzarin da fad in  But.. I don t eat Burabusko..

Hajja ta dan murmusa tace  Lallai kace zamu maida Kai Yerwa Haidar. Ya zaace Kanuri bai cin Burabusko.? Kuma naga favorite din Daddy kenan. Ya kamata ace ka iya ci.

Daga k ofa suka sinkayo murya na fad in  My brother is more Shuwa arab& Abincin larabawa yake ci.

Gaba d aya suka waigo suna duban mai maganar ba kowa bane illa Hilal.. Ya kara girma da k warjini kaman ba shi ba.

Ya k araso cikin parlorn yana gaida Hajja da Ummul lokaci guda Ya k araso ga Haidar suka gaisa Hilal na hugging d insa kad an na yaushe rabo.

Hajja ta shige ta basu waje abinta bayan tayi ma Hilal lale da zuwa.

Haidar ya dubi Hilal  Kai kuma daga ina kaman an jefo ka.?

 Daga gida Kano.. Tare muke da Ammi.. I arrived in the country yesterday.

Haidar ya jinjina Kai yana tambayarsa ya sch. Allah sa dai ya tab uka abin arziki wann karon. Ya k arada  Kasan ban tab a ganin unserious human being irinka ba. Gaba d aya baka d auki rayuwarka da mahimmanci ba Hilal.

"Hilal ya Dara kad an  Sanin da ka mun da ne D anuwa. Well, I can finally say it with full chest.. I m a graduate now. Kana magana da cikakken accountant ne a nan. "

"Jinjina Kai Haidar yake yana dubansa  Idan gaskiya kake fad i, I ll hire you. "

Suka dan murmusa gaba d aya. Hilal na fad in Lallai shi D angata ne gashi daga dawowa ya samu aiki.

Ummul da ta b ace b at kaman bata a wajen muryar Hajja ta sinkayo tana fad in maza ta taho ta shige kitchen dinta dake bangarenta ta samar ma Haidar abinci. Dan ta kula kaman abincin matarsa yake son ci.

Hilal yai karaf ya dakatar da Ummul da fad in  Addarmu ina Baby yake.? Ni fah shi nazo gani.. Naji ance takwara akai ma Yaya na Haidar. Meyasa ba a min ba.

Haidar ya dalla masa harara  Waye zai maka takwara.? Ba dai ni Haidar ba.

Hilal na murmushi yake Shafa Kai  I m a changed person fah.. Zaka sha mamaki. Ni fah yanzu na zama responsabile Human being.. Na jima da daina sallah ba alwala..

Haidar ya kuma aika masa wani duba dan baiso a d ago yarintar su gaban Ummul.

Murmushi Ummul take tana fad in bari ta kawo masa yaron. Saidai kafin tai shiru ta hangi su Khulsum dasu Badia suna sauk owa downstairs ga Baba Ali cikin hannun Khulsum d in. Sam Khulsum bama ta kula da mutumin dake zaune gefen kujeran Haidar ba.

Shi kaw Hilal mutuwar zaune yai yana dubanta. It s been long.. So long rabonsu da su saka juna a ido.. Ta k ara masa girma da kyau.. Saidai ya hangi wani abu mai Kama da salihanci saman cute grumpy face dinta.

Sam bata kula ba sai wasa take ma Baba Ali. Bataji sanda Ummul ke introducing Hilal masu Aunty Salima. Bata Ankara ba sai sinkayo muryarsa tai yana fad in  May I please.. see him..

Cak ta dakata da abinda take bugun zuciyarta na k aruwa. Ta ina zata mance muryarsa. Ta d ago a hankali tana dubansa. Shi d in ne dai.. Saidai wann karon ya k ara mata girma fiyeda sanin da tai masa a baya. Wann sumar tasa mai laushi da tsantsi irinta asalin k abilar shuwa arab ya tara shi wann karon. Harda jiki ya k ara saidai girman yasa ya k ara duhu kad an. Har Hilal ya amshi Baba Ali daga hannunta bata dawo daidai ba. Sam bama ta kula har su Azeema Sun wuce sashen Mommy ba. Gaba d aya sai ta daburce.. Ga Hilal kusan k ofa yake tsaye rik eda Baba Ali yana fad i ma Haidar yaron dashi yake kama ba da Haidar ba. Harda cewa za a basa yaron he s his Godfather.

Ai kawai sai Khulsum tabi bayan Ummul ta nufi kitchen.

Ummul ta dubeta da mamaki yanda ta shigo duk a daburce  Ke kuma fah.? Mai kikeyi a nan.. Na zata kun tafi sashen Mommy gaba d aya..

Kasa amsata Khulsum tai sai ma dibi dibi da take. Ummul dai d an tabe baki tai kadan Ta d auko carrots zata pilling Khulsum tai karaf ta amshe tana fad in zata fere mata.

Ummul ta tsareta da ido yanda take komai sauri sauri ba natsuwa. Ta aje chopping board din dake hannunta tana kuma tsare Khulsum da ido  Khulsum. Ta k ira sunanta cikeda kulawa.

Khulsum ta amsa tana dubanta.

 Fad a mun.. Meke faruwa ne.?

Khulsum ta d an girgiza Kai  Ba.. Ba komai.. Mai kika gani Adda Ummul.?

Ummul ta jinjina Kai  Idan zaki b oye ma wani nidai kinsan bazaki b oye min ba.. Ki fad a min meke faruwa.?

 Da gaske ba komai fah Adda Ummul..

Daidai lokacin suka soma sinkayo kukan Baba Ali daga parlor.

Ummul ta zame apron din dake jikinta tana nuna Khulsum  Ni dake bamu gama ba.. K arasa fere mun carrot d in ki yankasu k anana ina zuwa.

Daga haka Ummul ta fice sauri sauri.

Ta tadda Hilal ya mika yaron ma Babansa yana fad in ya kamata ya sanshi dan shine Godfather d insa. Ba maganan k iwa tsakaninsu.

Haidar ya amshe yaron yana fadin  Come to Paapa. Ya shiga jijjiga yaron yana fad in yai shiru Maama is here. Daidai sanda Ummul ta zauna gefen Haidar tana k ok arin amsar yaron.

Yanda gaba d aya attention d in iyayen ya koma kan yaron sosai hakan ya birge Hilal ya kuma basa sha awa. Sai ya dan murmusa yana k ok arin barin parlorn. Hanyar da yaga ta nufa yabi. Nan ya hangeta tsaye cikin kitchen din tana dicing carrots. Ya jima yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa kafin Ya soma takowa cikin kitchen din a tsanake.

Sam bataji alamun mutum ba sai taji gyaran murya daga bayanta yana fadin  Hello.. Excuse me..

Ta dan razana Wanda hakan ya sata saurin aje knife d in da take yanka carrots din dashi had ida rintse idanunta alamun ta razana.

Hilal ya dan leko yana duban fuskarta. Murya a hankali yace  Sorry..! I didn t mean to scare you.

Huci Khulsum keyi ba tareda ta dubesa ba. Lokaci guda tana dunk ule knife din cikin hannunta. A fusace ta waigo tana fad in ya kuwa bazataji tsoro ba mutum yana shiga waje ba Sallama kaman goyon yahudu. Tana maganar a fusace tana juya wuk ar dake cikin hannunta.

Kallon yanda take juya wukar kawai Hilal yake ya d ago hannayensa sama alamun surrender lokaci guda yake jada baya yana fadin  Easy.. Easy..! Yanda yake ja da baya kaman zai auna a guje sai ya kuma tsorata Khulsum. Ta soma waigawa baya tana duba mai ya gani yake shirin guduwa. Hilal bai daina jada baya ba ai kawai sai itama ta nufo k ofa a guje dan ta zata wuta ne ya gani a kitchen din ko wani abu mai Kama da haka.

Kafin tai aune Hilal ya tare k ofan kitchen d in wanda hakan ya hanata k arasawa. Bai daina nunata ba bai daina daukan saiti na gudu ba bai daina furta easy ba.

Ta kuma waigawa cikeda tsoro wann karon  Wai meye ne.. Meye ka gani.?

Ya nuna mata hannunta mai rik eda knife  Pleae keep that away.. Yai maganan yana rik eda k ofar kitchen din gam. K afarsa d aya na waje d aya na kitchen din.

Sai ta d ago wukar dake cikin hannunta tana kallo. Gajeren tsaki tai had ida sauk e ajiyan zuciya kafin ta koma bakin aikinta.

Hilal ya murmusa kad an kafin ya kuma takowa gareta. Wann karon Sallama yai. Kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa da kyar.

Hilal ya k arada  You haven t changed a bit. Ya fad i da murmushi saman fuskarsa. Bata ko dubesa ba balle ta kulasa. Saima ci gaba da tai da abinda take.

Ya dan langab e Kai yana dubanta  Wai ko darajan gaisuwa bazan samu ba balle sannu da zuwa.?

Ta dan dubesa a dak ile sai ta tabe baki had ida janye idonta  Wanda yai Sallama idan zai tafi shi ake ma sannu da zuwa.

"Hilal ya dan murmusa dan ya tuna sanda zai tafi bai mata sallama ba. Dikda lokacin itama tana Jigawa gidan Inna Dije amma ko a waya bai kira ya sanar da ita tafiyarsa makaranta ba. Sann tinda ya tafi bai sake nemanta ba. Alk awari yai ma Kansa zai natsu yai abinda ya kaisa once and for all ya k arasa karatunsa ko dan ya share hawayen Amminsa ya kuma tabbatar ma Abbansa bazai sake asaran kudi Akan karatunsa ba. Above all, zaiyi ne ma Kansa ta yanda idan yazo ma Abbansa da batun Aure zai tsaya ya sauraresa."

Gyaran murya ya d anyi yace  Lallai ban kyauta ba amma kiyi hak uri. Ya d anyi shiru kafin ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da ya haifar mata da sanyin jiki.

 Khulsum.

Ta d ago ta d an dubesa. Hilal yaci gaba  Tafiyar da nai ba Sallama yanada dalili wanda nasan idan muka samu time na miki bayani zaki fahimta.Ki yarda Dani nayi hakan ne for us.

"Sai ta d an kuma dubansa. Yayinda Hilal yaci gaba da jinjina Kai  Believe me, Ban manceki ba daidai da dak ik a guda. A koda Yaushe kina nan a nan..! Ya k arashe yana nuni da b angaren k irjinsa yanda zuciyarsa take bugawa. Yayinda Khulsum taci gaba da dubansa jiki a sanyaye. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Hilal yaci gaba  I never stopped loving you my cute cute miss grumpy.! "

Daidai lokacin sukaji alamun ana shigowa kitchen d in.

Khulsum tai saurin juyawa tana ci gaba da yanka carrot din sanda Ummul ta shigo kitchen d in.

Shi kaw Hilal saurin daukan glass cup yai yana fadin  I.. I will have a glass of water.! Ya k arashe da murmushi yana daukan ruwan gora dake wajen. Ya dubi Khulsum ya kashe mata ido yayinda Khulsum d in ma ta bisa da wani kallo sihirtaccen murmushi saman fuskarta.

Ita dai Ummul dubansu kawai take. Ta dubi wann ta dubi wancan har Hilal ya fice sai waigowa yake yana duban Khulsum.

Bayan Hilal ya fice Ummul ta tsare Khulsum da ido wacce ke ta faman sakin murmushi a hankali.

Ummul tai gyaran murya tace  Toh ai ya fice sai ki daina wann murmushin da kike.

Khulsum ta dan zaro ido  Na am Adda Ummul..!

Tsareta Ummul tai da ido sai ta murmusa tana aje Kayan miyan dake hannunta cikin roba a sink  Zama kimin bayani ne dalla dalla yarinya. Bari dai mu k arasa da kitchen din nan.

Dan darawa Khusum tai tana fad in  Adda Ummul ba fah abinda kike tunani bane.

Ummul tace  Toh ni mai kikaji nace.. Kin Kama kanki tin baaje ko ina ba yarinya..

Khulsum ta sanne Kai tana dariya.

Bayan Sun gama girkin ne kuma suka soma shirin shagalin. Tuni masu kwalliya Sun iso sunyi mata light make-up da ya matuk ar mata kyau. Shima Haidar d in saida ya k ara shiryawa sabida pictures da zasuyi da jariri. Haka kowa ya dinga santinsu dan ba k aramin kyau sukai ba. Daga bisani Ummul da jaririnta sukaita hotuna da  yanuwa da abokan arziki.

**

Wasa wasa har rana ta kusa

96 / 103