AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   2 / 103

3K to 6K   out of 306.8K words

Saidai kafin tace wani abu Ummul ta janye hannunta ta nufi gida cikin saurin wani kukan na kuma b alle mata.

Jiki a sanyaye Khulsum ta take mata baya.

Suna shigowa gidan suka tadda mahaifiyarsu zaune dirshan tsakar gidan sai cazgan kuka take. Ga Mama Tani wato kishiyar mahaifiyarsu kuma uwar gida a wajen mahaifinsu tayi bak e bak e a tsakar gidan sai  yan wak e wak enta na habaici take.

"Ummul ta k araso a sanyaye ta duk a gaban mahaifiyarsu dake cazagan kuka. Jiki a sanyaye, murya na tsananin rawa Khairy ke fad in  Umm..Umma.. Umma.. Kuka ya hanata ci gaba da magana."

Umma ta d ago idanunta masu zuban ruwa. Cikin kuka take duban Ummulkhairy tana nunata da d an yatsa take fad in  Ummul na gaji.. Wllhi na gaji.. Na gaji dake.. Na gaji da wann fashe fashen auren da ake akanki.. Ummul na amso Miki rubutu.. Na Kai sunanki gaban Malamai an baki rubutu an miki addu o i.. Ke k arewa har ruk iya an miki.. Ummul anya ke  yaradam ce.. Ta k arashe tana kuma fashewa da kuka. Yayinda Kan Ummulkhairi ke duk e kukanta na k aruwa da Jin kalaman mahaifiyarta.

Khulsum kaw girgiza Kai kurum take tana duban mahaifiyar tasu cikeda mamaki Jin irin kalaman dake fitowa daga bakinta. Ita kaw Mama shewa tai harda tafi kaman ta samu tv haka take dubansu. Sai dariya take cikeda nishad i.

Khulsum ta aika mata mugun kallo kafin ta maido da dubanta ga mahaifiyarta da kuma  yaruwarta.

 Umma dan girman Allah ki daina irin wann kalaman Akan  yarki.. Ke fah uwa ce Umma.. Khulsum tace ranta na tsananin sosuwa.

A hasale mahaifiyarsu ta d ago tana fad in  Ke dalla can rufe min baki.. Mai kika sani..? Ki bari randa kika zama mahaifiya irin k addarar da ya samu  Yaruwar ki ya samu d iyarki sann ne zakiji ciwon da nake ji.. Wayyo Allah.. Wayyo ni Suwaiba laifin mi nayi aka jarabceni da  ya irinki Ummul.. Ke ba wani tawaya bane tattare dake d an hasken nan baki rasa ba. Ke duk wani abin da mace zatai tink aho dashi daidai gwargwado Allah ya baki amma a rasa Wanda zai aureki kowa da yazo sai Ya gudu.. Haba Ummul..! Ta kuma fashewa da wani kukan..

Idan da sabo sun Saba da dramar mahaifiyarsu. Khulsum ta girgiza Kai. Tinda aka soma amsan kud in auren  yar uwarta Ummulkhairy ana fasawa cikin damuwa da tashin hankali mahaifiyarsu take. Batada da burin da ya wuce taga Ummulkhairy tayi aure ta bar gidan ko ba dan komai ba sai ko dan gori da maganganu da take fuskanta Kama daga kan Abokiyar zamanta har izuwa kan ahalin gidan dama sauran jama an unguwa. Mahaifiyar Ummulkhairy ta kasance irin mutanen nan ne masu saka damuwan maganganun mutane a ransu. A akasarin lokuta mutane suna mata kallon sakarya wacce batada wani wayo ko cikakken hankali. Sann tin Ummulkhairy tana k arama taci burin ta aurar

da ita da k anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k ananan shekaru taita mata wak e tana karanto baitika tana mata rawa tana fad in saura k iris ta aurar da ita saura k iris ta kaita d akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab a mata maganganu da fad in ta jira dai taga girman  yar tata sam bazata tab a tankata ba. Umma Ta kasance irin mutanen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu itada Khulsum yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko.

Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda bata sonsa zatai hak uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d inta tai aure ta tafi d akin mijinta.

Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yara uku gareta kuma duk sunyi aure suna d akin mazajensu. Badi a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d aya daga cikin matan unguwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad in ita nata yaran kaf suna d akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta.

"Mahaifinsu baida wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k ok arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k asan zuciyarsa na damuwa da al amarin  yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum cikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba."

Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da Umma ke ci gaba da yi tana fad in  Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min mafita Wayyo ni Suwaiba.. Ta k arashe tana kuma rusa wani kukan.

"Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai  yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne masu nuna kulawa da k auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan  Ya yansa da danginsa dukda kuwa k annensa dake zaune cikin gidan basu d aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu nasiha da wasilci da zumunci ba."

Cikin b acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad in  Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?

Batace komai ba sai gunjin kuka da take ci gaba.

Ya kuma girgiza Kai  Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k arshe ba tinda dai kink i amincewa  yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d in ke so.

Cikin zuban hawaye ta d ago tana duban mijin nata  Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.

 A ina kika tab a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka nawa Ummul d in take ne..?

Umma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d in take. Tai karaf tace  Ta fah haura talatin Abban Ummul.

Taci gaba  Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k ok arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.

Abba ya kuma katseta  Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d aura Miki ba.. Ko an fad a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Amma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata domin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki keda amfani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..

Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye  Haba Abban Ummul dan Allah ka fad a alkhairi..

 Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad in alkhairi gameda  yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su  ya ya amana ce Allah Ya bamu kuma za a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe. Ya k arashe yana mai janyo kwanon tuwon sa.

**

"A can d aki kuwa Khulsum ce ta duk a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak umi tana fuskantar  yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka."

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU.!*

*03*

*©þSameena Aleeyou& *

"Cikin gunjin kuka Ummul taci gaba  Mai kuma zaki fad a mun Khulsum.. Ba dai kinyi abinda kike so ba kin tari matan nan da fad a har Zubair ya iso ya taddamu a haka.. Toh me kuma yai saura tinda gashi ko wayata bai d agawa.. Khulsum, Nifa burin mahaifiyata kawai nake son cikawa..! Ta k arashe wani kukan na taso mata."

"Khulsum ta girgiza Kai  Adda Ummul dan Allah ki saurareni.. Wllhi mutumin nan bai cancanceki ba.. Ba son gaskiya yake Miki ba.. Da ace son gaskiya yake Miki da ya baki dama ya saurara daga b angarenki, amma baiyi haka ba ya hau kan dokin fushi.. "

 Har akwai Wanda ya cancanceni ne Khulsum..? Tai maganar tana nuni da kanta cikin rawar murya irinta mai kuka.

Khulsum ta girgiza Kai  Dan Allah kar ki bi maganganun Umma da mutane.. Kar ki kaskantar da kanki Adda Ummul.. Wllhi kin wuce gaban duk mazan dake fasa aurenki.. Kimarki da ajinki ya wuce nasu. Shima wann zubair din bai cancanceki ba shiyasa ya kasa ganin kimarki kaman dai sauran.

Ummul tai murmushi mai ciwo  Watak ila banida wani kima da gaske Kulsum.. Watak ila abubuwan da mutane ke fad i kaina gaskiya ne.

 K warai kuwa Ummul mace mai shekarunki batada wani kima matuk a ba d akin mijinta take ba..! Muryar Ummansu ya katsesu wacce tai tsaye tana sauraron tattaunawar yaran nata.

A tare suka d ago suna duban Umma dake aika masu mugun kallo tana huci.

"Khulsum ta lumshe idanunta had ida furzar da huci  Umma wai dan Allah meyasa Baki saka farin cikin yaranki a farko.. Mutanen nan fah tuni sunzo Sun amshe kayansu, wllhi ko Zubair baizo ya tadda Adda Ummul na rabon fad a ba bazasu bari ya aureta ba tinda sunyi furuci kuma sun amshe lefensu.. Haba sai kace ana Neman Kai da ita.. Dik anbi an tsangwameta a gida da waje duk bata huta ba.. Umma auren nan fah ba a ce yana cikin cika cikan musulunci ba.! "

Umma ta danna mata dak uwa  Kinci ubanki Khulsum.. Idan baya cikin cika cikan musulunci ai sunna ce mai k arfi& Ke baki San ko gawan mace mai aure yafi daraja ba.. Cikan mutuncin mace shine a ganta a d akinta.. Ta d an numfasa kafin taci gaba  Kina jina idan baki daina korarwa  yaruwarki mazajen aure da wann bak in Zuciyar naki ba wllhi kinji na rantse zan saka k afar wando d aya dake.. Maimakon ki duk afa Neman naki mijin auren kin tsaya kina lalata na  yaruwarki koh.. Toh ahir d inki Khulsumu aure dai da izinin Allah ina numfashi sai Ummul ta tafi d akin mijinta ko mai zai faru kuwa.! Ta k arashe sai tsuma take.

Khulsum ta d ago tana duban mahaifiyar tasu da mugun mamaki. Lokaci guda ta girgiza Kai kad an tace  Umma dan Allah a dinga Neman zabin Allah dai.. Kuma a dinga k ok arin furta alkhairi.. Auren nan duk yanda aka so bazafa ayi shi ba sai lokacin da Allah yace kuma yaso.

 Aw Nima rashin kunyar zaki min.. Toh bismillah.. Nace bismillah Khulsumu.. Tai k wafa tana mai k arawada  Rikakkiya kawai.. Bazan dai Miki baki ba dan bana fata ki Kai shekarun Ummul a gabana baki tafi d akin mijinki ba.

Ita dai Khulsum bata ma ce komai ba dan tsanar mazan ma tai balle wani aure tin bayan abinda ke faruwa da

 yaruwarta.

**

ABUJA

"Akasarin gidajen da kake iya hanga tapka tapkan benaye ne masu tsananin kyau da tsari. Yanda aka tsara su aka kuma inganta gininsu zakace a k asar turai kake. Tapkeken gida ne da ya amsa Sunansa, ga korayen shuke shuke da ciyayi masu d aukan idanu da ban sha awa. Komai na gidan fari ne k al tamkar fadar White House."

A hankali yake Jin hasken ranan hantsi yana haske masa fuska sakamon baccin da ya d aukesa a balcony d insa saman wasu kujeru na shakatawa tin bayan da ya gabatar da sallar asuba. Sautin motoci da tsuntsaye jifa jifa suka soma gauraye masa kunnuwansa da bai cika shiri da hayaniya ba. Nan take kuwa suka katse masa baccin nasa.

Tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu kana ya mik e zaune yana duba agogon dake fuskar wayarsa. A kasalce ya jefo k afafunsa k asa ya mik e tsaye yana kuma stretching gabb ansa.

Kai tsaye bathroom ya shige bayan ya tura k ofar glass da ta raba balcony d insa da d akin nasa.

Cikin mintuna k alilan ya shirya tsaf ya fito cikin black business suit d insa. Kallo guda zaka masa ka tsarkake Ubangijin da ya tsara halittarsa.

Koda ya sauk o k asa yana iya sinkayo muryar mahaifiyarsa tsakanin ma aikatan gidan ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Ya d an furzar da huci had ida girgiza Kai. Wann morning routine d in mahaifiyarsa ce. Idan da sabo duk mai rayuwa cikin gidan ya saba da wann. D an girgiza kansa yai ba tareda ya nufi cikin gidan ba. Lokaci guda yasa Kai ya fice cikin sauri ya nufi yanda motarsa ke ajiye. Nan da nan yaja motar ya fice daga gidan a gaggauce dan Sam baiso yai arba da mahaifiyar tasa a safiyar.

Bai zarce ko ina ba sai wani makeken building maiji da tsawo da kuma girma had ida tsari. Daga saman ginin anyi rubutu da k araffa masu ruwan zinari *MAITAMA BUILDERS*. Rubutun anyisu ne da Manyan bak ak e.

Cikin sassarfa yake taku a katafaren ginin mai k unshe da ma aikata sahu sahu. Waya manne b angaren kunnensa na hagu. Dik yanda ya shige kaw sai ya d ibi gaisuwa Dikda ba amsawa yake ba.

"Lift ya shige ya diresa a third floor. Wani hamshak in office mai tsananin girma da tsari ya nufa, still waya yake. Nan da nan wata mata cikin shiga cooperate ta biyo bayansa."

"Cikin muryarsa mai cikeda k warjini Yaci gaba da furta  You find a way to fix this Hisham& Honestly, I m highly disappointed. I did not expect my team members to be so unprofessional like this& Iyakacin abinda na sani shine we must cover the deal by all means possible. Yana Ida fad in haka ya katse kiran ba tareda ya jira amsar Hisham ba."

Matar da tin isowarsa yai mata alama da hannu da ta biyosa sakatariyar mahaifinsa ne Wanda kuma ya kasance mammallakin wann shahararren Construction Company d in wato Maitama Builders.

Ta d an risina tana gaidashi  Good morning Sir.

 Morning Jane. Ya

2 / 103