AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   15 / 103

42K to 45K   out of 306.8K words

san an mari wofi haka naji.. Ya kuma shafa fuskarsa yana lek en bayansa irin yanda marassa gaskiya keyi kafin ya matso da fuskar nasa saitin fuskan  yarsandar  Kinga ita Azeema Ubanta na asibiti rai hannun Allah. Ta tabbatar mun mutuwa zai. Kuma da zaran ya Mutu aka raba masu d an abinda zasu samu zan amshe komai nata. Tana mallaka min zan koreta da kud in gadon Uban nata zan aureki Kurtuwata. Ya k arashe yana wani washe baki yana wani kashe mata idanu  Toh d an yi mun murmushi mana na gani sahibata.. Inye kaga Kurtuwa Amaryar Habibi.. Ya k arashe kaman zai rungumota.

Yatsine fuska ta d anyi had ida turasa baya  Easy mana Alaji wajen aiki na muke.. Shikenan tinda haka kace.. Amma wllhi idan Kai ga gangancin kawo mun bariki wllhi babu abinda zai hanani cin uwarku daga Kai har matar taka kasan sharri na karanta a banza zan maida police station gidan hutun matarka.

Saurin toshe mata baki yai yana  Wllhi bama ta sanki ba har yanzu. Bata san wace budurwar tawa ba.. Kwantar da hankalinki kafin ma ta sanki ta tsufa gidan marigayin mahaifinta. amma sai na tabbata na amshe d an abinda uban nata zai bari mata..

Ta kuma yatsina fuska kafin ta tura k ofar ta fito tana karkad a sandan dake hannunta sai faman d age hanci sama take. Azeema ta bita da kallo dan haka kurum hankalinta bai kwanta da  yarsandar ba musamman da ta hango Habibu ya fito daga bayanta yana fad in  Nifa Rankidade Sam bazan yarda ba wllhi sai an shiga kotu an k watarwa matata hakkinta..!

Azeema ta k araso gareshi ta shige jikin mijinta tana fad in wllhi a tafi kotu kawai.

Sai ya fara kokarin kwantar ma Azeema hankali da fad in idan yana a matsayin mijinta sai an tafi Kotu.

Sergeant d in kuwa banda watsa ma Azeema wani wulak antaccen kallo bata komai.

Da kyar Habibu ya shawo kan Azeema ta amince suka bar police station d in da sharad in case din bai k are nan ba. Sai aika ma  yarsandar mugun kallo take dan ta kula da wani kallan k asa k asa da Habibu ke binta dashi.

**

A can b angaren su Umma kaw d aki maiji da lafiya aka sauk eta. Umma ta zauna saman gado tana lotsawa tana jin taushin latifa ga sanyin AC na bugata. Ai sai Umma ta yab e baki tace  Kai kaji taushi kaman ina saman gajimare. Tirk ashi. Lallai masu kud i suna sha aninsu.

Asshe dake lab e daga k ofa tana karantar duk wani motsin Umma waya manne kunnenta wanda ko shakka babu da Mommy take wayan. Sauk owa k asa tai dan upstairs aka sauk i Umma.

Ta zauna nan parlorn k asa tv na aikinsa waya manne kunnenta  Aunty Kwaise bakida wata matsala fah. Ni na fad a miki na kuma yarda da aikin wann Malamin dan kaman tafiya muke da solution d in matsalar mu. Matar nan dai da muka bige

Ta d anyi Shiru alamun tana sauraro daga b angaren Mommy. Sai taci gaba  A a Haba Aunty Kwaise nasan fah abinda nake. Ai tuni nasa Yunusa yaro na ya binciko mun komai kanta. Duk wani abinda Ke wakana tsakanin ahalinta. Yazo gidan sauki tinda nan cikin Kano ne. Ai bazai yuwu mu d ibo ko wace iri mu jajib a ma Haidar ba

koda kuwa Auren na wata UKU ne kawai. Yanzu zuwa gobe idan Allah ya kaimu zakiji duk bayanan da Yunusa zai kawo mun dalla dalla duk yanda akai. Idan ta kama a miki scanning information d in ne a tura miki ta mail duk za ayi Aunty Kwaise. Haba abu ne za ayisa cikin wayewar kai. A yanda na fahimta bakin aljihu ne kawai zai bayani wann kuma nasan ba matsala bane. Ta d an dara tana kuma kod a Mommy da mata kirari irin na matan Manya. A haka sukaci gaba da tattaunawar tasu.

Bayan sun ida waya Asshe ta mik e ta lek a Suwaiba. Nan ta tadda Umma tuni ta baje saman gado bacci yayi awon gaba da ita harda su minshari.

**

"Hisham yai Shiru yana sauraron mahaifiyarsa. Sai kuma ya girgiza kai kad an  Hajja ba yanda na iya ne. Tafiyar ce ta taso mun babu shiri. Ya d an matso kusanta had ida kamo hannayenta cikin nasa  Na bar amanan Ummul hannunki Hajja. Dama tare na ganku nai maku karambani ko nace zuciyata tai karambani&  Sai ya d anyi fasali  I will come back for her Hajja.. Zan dawo, dawowa na musamman domin Ummulkhair.. Please kici gaba da kula da al amranta har na dawo. Bazan d auki lokaci ba wann karan in sha Allah.. Kinji Hajjata. Ya k arashe cikeda rauni."

Dubansa ta d anyi duka duka yaushe yazo har zai tafi. Ita kam ta fara gajiya da wann aikin nasa.

A hankali ta jinina Kai  Shikenan. Allah yaci gaba da tsareka yayi maka albarka. Bazan dakatar dakai ba koda ina son yin hakan. Ummul kuma ka barta cikin aminci da yardar Ubangiji. Fatana Allah yasa kar ka d auki lokaci mai tsawo.

Hisham ya murmusa cikeda jin dad i yana jin zuciyarta at ease. Fitan sassafe zai wanda ba lallai ya samu ya kuma ganinta ba balle suyi sallama. Amma yayi alk awarin da zaran ya isa zai kira Hajja ta had asu a waya.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..! *

*14*

*©þSameena Aleeyou& *

Mommy ta kuma duban Daddy Wanda fitowarsa kenan cikin shirin fita Squash game. Hannunsa rik e da jakan kayan motsa jikinsa d aya hannun Racket ne na buga wasan. Sunada private court d insu da suke bugawa da abokansu.

"Ta d an sauk e ajiyan zuciya a hankali  Engr, kan maganar namu..? Nasan idan har na bari sai ka dawo ce min zakai ka gaji. Ta k arashe da d an shagwab a cikeda kissa."

Tab e baki yai kad an had ida girgiza kai  Kwaise I thought mun gama magana. Kinga wann D an naki na cire hannuna cikin rayuwarsa. So yayi aure ko kar yayi aure is non of my business. The only thing I care about is my company tareda ci gabanta..  Har ya d an soma tafiya ya juyo  My tea should be ready kafin na dawo.. Please. Ya k arashe yana mai ficewa.

Mommy ta furzar da huci tana girgiza kai  A a Kwaise bazaki karaya ba. You need to do this.. You must.. Ya zama miki dole. Ta k arashe tana neman layin Asshe.

Shi kuwa Daddy zaune suke a court d insu shida Alhaji Gimba suna hutawa daga motsa jikin da sukai.

"Alhaji Gimba Ya d an girgiza kai kad an  Engr Ya kamata kaji maganar iyalinka.. Nima na jima da wann tunanin, inaga Aure shi ya kamata a masa.. Shi zaisa ya tara hankalinsa waje d aya. Kasan meye idan bazaka iya zuwa ka nemar masa Aure ko ka karb ar masa ba. I can represent you then. Zaka iya wakiltani nai komai ma Haidar. After all, nima uba ne a gare shi. "

"Daddy ya d an dubesa, baice komai ba saima k ok arin bud e bottle water dake cikin hannuna da yake."

**

Washe gari Umma ta karya da karin kumallo mai kyau. Ga kaya na alfarma da Asshe ta aiko mai aiki ta kawo mata. Tai wanka ta cancand e cikin atampar da bata tab a mafarkin saka irinta ba. Ta dubi kanta jikin madubi tana mamaki. Ta mik e ta shiga zaga d akin ta yaye lalube tana kallon kyaun gidan da aka sauk eta.

A haka Asshe ta shigo ta taddata. Ta saki murmushi tana dubanta  Maman Ummul har kin shirya abinki& Na aiko

Marka ta tambaya ko akwai abinda kike so.. Tai maganar tana shigowa d akin.

Umma ta girgiza kai tana washe baki  A a babu abinda nake buk ata.. Kin ganni na d age labule kallon Aljannan duniya nake. Ire iren gidajen nan saidai kaita hangosu daga kwalta ashe Inada rabon bacci cikinsu.

Asshe ta murmusa tana jinjina lamarin Umma  Ai wann gidan ba komai bane gaban gidan  yaruwata Hajiya Kwaise dake birnin tarayya. Wann saidai a kirasa da gidan sauk an bak insu ko ma nace miki na ma aikatansu.

Umma ta zaro ido waje  Gida kaman wann za a kira gidan Ma aikata..?

Asshe ta kuma murmusawa  K warai kuwa.. Kinga kalli nan.. Tai mata nuni da fuskar wayarta. Umma tai k uri tana duban hoton matar da Asshe Ke nuna mata wacce tai mata lak abi da Matar manya cikin zuciyarta.

Asshe tace  Da wa ta miki kama.?

Kafin Asshe ta rufe baki Umma tace  Da Matar marigayi tsohon shugaban k asa Maryam Abacha.

Asshe ta jinjina kai tace  Toh wann sunanta Hajiya Kwaise Maitama.  Yaruwata ta ce da muka fito ciki guda. Ke da ganinta ba sai ance miki Matar manya bace.

Umma ta jinina Kai  K warai kuwa babu shakka.

Asshe ta jinjina kai tana mai kuma gyara zama  Kaman yanda na fad a miki Aure take so d anta yayi kuma ta bani wuk a da nama na zab ar masa Matar kirki a nan gida Kano dan bata son ya auri matan dake rubibinsa a bariki wanda akasarinsu girman Turai ne. Ni kuma a yanda kika bani labarinki na tausaya miki. Dake da  yarki kuna cikin yanayi na k unci da damuwa. Watak ila Allah ne ya dubi halinda kuke ciki. Da duk abubuwan da kuke fuskanta kama daga kan kishiryarki har izuwa jama an unguwa. Ya share miki kukanki. Zanso  yarki tayi Aure na gani a fad a.. Auren da za a bigi k irji a kirasa Aure. Auren da duk masu jifanku da munanan kalamai sai sunyi d an da na sani. Domin kuwa Ummulkhairinki ta amsa sunanta Uwar Alkhairi.. Ta kawo miki alheri da ma danginku gaba d aya. Dan nayi imani katafarin illahirin danginku Ke harma da jama an layinku babu budurwar da tayi irin Auren da Ummul zatayi. Babu wacce tai dacen miji irin na Ummul d inki. Yaro d an gata d a d aya tilo ga Attajirin d an kasuwan da kasuwancinsa ya zaga gida Nigeria da ma k asashen k etare. Ta kuma gyara zama  Ke Maman Ummul duk yanda zan miki bayanin dacen da  yarki tayi bazaki fahimta ba. Ke kanki guje gujen rab arki za a fara yi ba ma Ummul da ake gudunta ba. Domin kuwa kin zama sirkar Manyan mutane. Mutanen da ake haskosu a manyan mujallu da talabijin. JINKIRIN Ummul d inki ya zame maku alheri. Ke fah Maman Ummul wllhi Kakarki ta yanke sak a.

Ta d an numfasa  Amma fah ni taimako nai niyyan yi sann tun had uwa na farko naji na yarda dake na aminta dake. Bugu da k ari labarinki da kika bani ya tab a min zuciya dole duk mai imani ya tausaya miki daga Ke har  yarki. Kuma yanda Ummul d inki ta juri kyara da tsangwama baisa ta lalace ba ko ta bijire ma iyayenta na kuma aminta ta

cika yarinyar kirki wacce kowa zaiso ta zama Matar d ansa. Amma idan kinaga kunada wani zab i ko ita Ummul d in tanada wani bazan tak ura ki ba sai na nemasa wata dukda na masa sha awar Ummul.

Ai kafin Asshe ta rufe baki Umma tai tsalle ta toshe mata baki  A a haba Hajja Asshe.. Har wani zab i Ummul kedashi.. Ina laifin wanda yaso taimakon ka ya tasamma rufa maka asiri. Ni damuwana Allah yasa  Yaruwar taki da d anta su amince idan sukaga hoton ita Ummul d in.

"Asshe tai murmushin cin nasara. Lallai wann matar ta tabbata shashasha yanzu take kuma gasgata duk bayanan da Yunusa ya kawo mata akanta da  yarta. Wann ko ta fad a mata mak asudin auren ba damuwa zatayi ba. Ta murmusa a fili kafin tace  Karki damu  yaruwata batada matsala ita burinta kawai D anta ya samu mata ta gari ba wad ancan  yanmatan dake sonsa dan kwad ayin abin hannun iyayensa ba. Shima D an nata yaron kirki ne mai biyayya mai bin umarnin iyayensa. Na miki alk awari baza a sami matsala daga b angarenmu ba. Amma saidai kinsan ance Aure d an bincike ne, yanar gizo kawai zaki d ale ya tantance Miki komai. Kinsan su manyan mutane a yanar gizo ake bikcikosu. Ta k arashe tana kuma dulmiyar da Umma."

Umma ta shiga girgiza kai  Wllhi ni na yarda dake d ari bisa d ari na aminta dake sabida a zamanin nan samun mutanen kirki irinku yayi k aranci.. Da ace Ke mai cutarwa ce tin a lokacin da kuka bigeni da mota da kunyi tafiyarku Kun barni wajen. Bakiyi haka ba kika d aukeni kika kaini asibiti kikayi d awainiyata kika kuma kawoni gidanki. Idan ba kin aminta dani ba na tabbata bazakiyi haka ba.

"Asshe ta murmusa  Alhamdulillah, na d auki haka matsayin yarda da amincewarki. Yanzu ki sake kwana ki sake samun sauk i da hutu. Mu kuma ci gaba da tsara abubuwa da yanda zasu kasance. "

Umma ta katseta  Ko dan sabida idon masu ido da hassadan masu hassada

Asshe ta jinina Kai  Kinga zuwa gobe ko jibi idan na tuntub i  Yaruwar tawa aka samu matsaya sai muje asibiti a biya duk wasu kud ad en jinyar mijinki. Sai ki kaini kuma naga surkata Ummulkhairi. Cikin satin nan da yardar Allah magabata zasu taho daga can Abuja sai ayi maganar tsaida ranar Aure. Nafi so ayi komai a gaggauce kafin masu mugun ido su kuma jifan al amarin da idonsu.

Umma tai Shiru kaman mai nazari sai kuma tace  Tooh amma Hajja Asshe wani hanzari ba gudu ba. Kinga shi mahaifin Ummul yana kwance asibiti baisan yanda kana yake ba. Anya baza a jira ya farka daga wann jinyar nashi ba.

A dak ile Asshe take dubanta kafin tace  Haba Maman Ummul ya kike magana haka saikace ba k arni na ashirin da d aya muke ba. Na Miki ta bakin bature yace 21st century. Shin ita Ummul batada dangin mahaifi ne da zasu iya bada aurenta. Yaushe za a tsaya jiran tashin mahaifinta dake tsananin jinya. Waye yasan yaushe Allah zai tada shi. Yarinya ta samu miji shikenan sai ace sabida mahaifinta ba lafiya bazatayi aure ba. A ina ake haka. Yanzu fah mazan wahala suke Shiyasa da zaran an samu gwara a kauda. Baki ganin akasarin Auren da ake yanzu daga zuwa tambaya ba bakin kowa sai kiji an d aura ai duk sabida gudun masu neman jifanka da sharri ne balle wani abu ya gifta a fasa auren. Kinga  Yaruwata yanzu take so D anta yai aure dan a cewarta yaro da kudi hannunsa ba mata had ari ne. Kinga bazai yuwu mu tsaya jiran mahaifin  yarki dake jinya Ya samu lafiya ba kafin ayi auren. Kinga bazamu bari namu yaron ya lalace ba. Kawai idan wann aure bazai yuwu ba..

Saurin mik ewa Umma tai ta daka tsalle ta tumu gaba Asshe. Ta d ago hannaye biyu  Ki rufa min asiri kar ki k arasa maganarki. In sha Allahu fashin auren Ummul ya k are. An daina k irga mata fashe fashen aure. Za ayi aure da zaran magabata sunzo. Ayi tambaya take a d aure tun kafin mak iya suji labari. Sai kuma ta fashe da kuka wiwiwi babu k akk autawa.

Asshe ta dafata kad an  Lafiya Maman Ummul Ya da kuka kuma keda zakiyi farin ciki burinki zai cika Ummul d inki zatakai ga d akin miji.

Umma

15 / 103