AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   77 / 103

228K to 231K   out of 306.8K words

yarda kin cika mai k wak walwar kifi Anisa. Ta ya kike zaton zanyi duk abinda kika ce ba tareda Sun zargeni ba.. You must be stupid.! Ya dan numfasa kafin yaci gaba  Look, Daga mahaifyata har Ummul sunyi matuk ar yarda dani bazanyi wani abu da zai rusa wann yarda nasu da na samu ba.. "

Anisa ta furzar da huci  Toh idan ba haka ba ya zamuyi..? Ai gwara mu markade wann cikin ma fiyeda shegen can dake cikin Dareen Wanda muka markade. Dan wann shine babban barazana a garemu.. Hisham duk yanda za ai cikin nan bazai zo duniya Ya tarwatsa mana farin cikinmu ba.!

Hisham Ya furzar da huci  I need to think of something.. Amma banda zubar da cikin.

"Cikeda k osawa Anisa tace  Har kanada wani abinda zakai tunani akai bayan wann cikin threat ne a garemu.. Ta girgiza kai cikin tashin hankali  Hisham, we can t afford any further miscalculation& We need to act now tun munada dama akan cikin nan.. Tun yana k arami.. Yanzu ya kamata mu b arar dashi. Idan ta kama na taho yanda kake ne zan taho just to carry out the job. "

A zuciye yace da ita  I love Ummulkhair kin fahimta.. I want to build my relationship with her based on trust.. Bazan tab a bata wani room da zata zargeni ba.. So tinda nace ki bar min komai ki bar min nasan abinda zanyi.. The bottom line shine Ummul bazata tab a komawa ga Haidar ba..! Bai jira cewarta ba ya katse kiran yana ci gaba da sakin huci.

Ya jima zaune wajen yana sak e sak e cikin zuciyarsa da yanda zai b ullo ma al amarin. Ya shafe fuskarsa yana jin tsanan Haidar na ninkuwa cikin zuciyarsa.

A b angaren Ummul kuwa wani kula na musamman take samu daga Hajja wacce takeji tamkar dai jika zata samu. Duk yanda Ummul ke nuna bata son cikin bai hana Hajja d aukin cikin ba. Sann dukda samuwar cikin ya haifar mata da tuno nata bayan bai canza yanda take ji gameda cikin a zuciyarta ba. Duk wani abinda tasan yanada kyau ga mata masu juna biyu sauri take taima Ummul. Haka zalika duk abinda tasan mata masu juna biyu naso kokari take ta mata koda Ummul d in tana nuna bata so.

**

A parlor Hajja ta tsinci magungunan da aka bama Ummul ko d aya bata sha ba ta ajesu. Hajja ta girgiza Kai ta d auki ledar maganin ta nufi d aki yanda takeda tabbacin Ummul na kwance nan dan tinda suka komo daga asibiti da labarin cikin yau kusan kwanaki uku kullum zama take a d aki tana aikin kuka abinci ma sai Hajja tayi da gaske take ci.

Hajja ta turo k ofan d akin tana juya magungunan kaman mai k irgensu take fad in  Ummulkhair wai baki sha maganin nan ko d aya ba tinda aka baki su..?

Da kyar Ummul dake ta kwance lamo hannunta guda saman cikinta ta mik e tana goge ragowar hawayen da suka gangaro mata tanayi tana avoiding idon Hajja dan tasan bata son kuka da shiga damuwar da take. A hankali ta furta  Hajja ni wari suke min bana so.

D an girgiza Kai Hajja tai kafin ta zauna gefenta kad an  Banda abinki Ummul magani ai ba a shansa dan dad i.. Shi wann maganin folic acid ne kuma magani ne mai amfani sosai ga mata masu juna biyu wanda ake so su fara shansa tin ciki na k arami sabida matuk ar amfaninsa ga jaririn dake cikinsu. Da yawan mata masu juna biyu idan an basu magunguna makamancin wann sai su aje bazasu sha ba Wanda haka barazana ne ga lafiyar jaririn dake cikinsu.

Cikin murya irinta mai kuka ta katse Hajja  Amma ni bana son jaririn Hajja& Bana so na haifosa dan Allah.. Ta k arashe cikin rawar murya

"Hajja ta girgiza Kai had ida kamo hannayen Ummul  Na haneki da fad in kalmar nan Ummul.. Ke din nan bada jimawa ba zaki zama mahaifiya da izinin Allah. Duk abinda kike furtawa ki sani na tasiri Akan D anki. Zama iyaye ba abu bane mai sauk i. Daga zaran ance yau Kin zama uwa toh ki sani rayuwarki ta canza, dole ki zama mai kula da taka tsantsan kan abubuwan da kike furtawa musamman kalaman da suka danganci  ya yanki dan bakin mahaifiya sosai yake tasiri. Sann duk wani decision da zakiyi making da ya danganci rayuwarki ki sani dole wann D an nada wani kaso na hakki a cikinsa.. Ke din wani nauyi ne da amana yake gab da hawa kanki wanda yasa nake tunanin lokaci yayi da zaki waiwayi gida Ummulkhair. "

Ummul ta d ago a d an razane tana dubanta. Sai ta soma girgiza Kai  A a.. Dan Allah a a Hajja.. Bazan iya ba.. Bazan iya tunk aransu a haka ba.. Wllhi bazan iya ba.. Dan Allah ki barni a nan nidai bani so su ganni da wann cikin.. Ta k arashe tana mai kuma fashewa da kuka.

Hisham da fitowarsa kenan da niyyan yima Hajja Sallama dan a ranan yake son komawa Abuja kafin ya ida shirya yanda zaiyi da cikin Ummul nan ya lab e bakin k ofa yana sauraronsu. Cikin zuciyarsa yake fad in wato Hajja ta shirya mayar da Ummul gaban iyayenta kenan. Komawan Ummul gida kuma na nufin Haidar zai sameta. Ai kuwa bazai tab a bari hakan ya kasance ba. Bazai tab a bari Ummul da Haidar su sake crossing path ba tareda ya samo solution d in yanda zaiyi da D an Haidar dake cikinta ba.. He needs to make his move fast kafin Hajja ta b ata masa komai.. Komawa Abuja bata gansa ba har sai ya samo ma Kansa mafita. Sai ya samo makomar cikin Haidar dan bazai tab a bari duk sadaukarwar da yai su tafi a banza ba. Komawa da baya yai yana tunanin abun yi. Dole ya dakatar da Hajja.

Kai tsaye waje ya fice yana kiran Anisa a waya. Nan yake la barta mata zancen Hajja da Ummul da ya sinkaya.

Anisa ta mik e tsaye a firgice tana girgiza Kai  No& No way Hisham& We can t let this happen.. Kaga abinda nake fad a maka ko.. Wann shine abinda nake tsoro.. Idan har Ummul ta koma gida toh kuwa shakka babu tamkar ta koma hannun Haidar ne dan a halin yanzu Haidar baida wani aiki sai zarya tsakanin Abuja to Kano. Bazaka bar Ummul ta

isa Kano da wann cikin ba. Do whatsoever it takes ka dakatar da aukuwar hakan.. Hisham dole cikin nan ya salwanta dan cikan burinmu. Bamu tafi da nisa har zuwa nan da wani d an tayi ya ruguza mana shiri ba.

Hisham ya bud e marfin motarsa ya shige yana shafa Kai had ida furzar da huci  Kaina ya k ulle Neesa.. I don t know what to do anymore.. Knowing Hajja bazatai k asa a gwiwa ba har sai ta damk a Ummul ga iyayenta. Ya kuma furzar da huci yayinda Anisa taci gaba cikin hasala  Toh ai duka laifinka ne. Da ace ka d auki shawarina ka tistiyesa da bamu kawo wann gab ar ba.. Da ba wann zancen muke yanzu ba.

 Are you insane Neesa. Bakisan had arurrukan dake tareda abortion bane ko me.? Ta ya zan jefa rayuwar Ummul cikin had ari bayan duka abinda nake dan na mallaketa ne. Wann banzan Haidar d in ne ya b ata komai da ya kasa hak uri har saida ya tabbata ya d irka mata ciki. Idona idonsa sai na shak esa tinda ya keta gonata dan Ummul tawa ce ni na fara saninta tun kafin ya santa. Ni na fara sonta tun kafin ya sota. Ni na fara niyyan Gina rayuwar Aure mai tsafta tareda ita kafin shi da uwarsa su k ulla Auren yaudarar da yai da ita.. Idan sunana Hisham Haidar ya gama rayuwar Aure da Ummulkhair.!

Anisa ta furzar da huci  Duka wad ann bazasu taimakemu ba Hisham. We are running out of time. We need to act now kafin Ummul ta isa Kano.!

Hisham yai shiru yana sakin huci yana fidda tururi shi kad ai. Idonsa naga kallon gabansa daga nan yanda yake zaune cikin motar. Bai kuma ceda Anisa komai ba sai huci da yake fiddawa har saida Anisa tai tunanin ko ya aje wayar ne.

Anisa ta kuma ce  Hello.. You there.?

Gungun matasa rik eda makamai dangin dogayen wuk ak e da Hisham ya hanga ya sanyasa sakin murmushi. Duk abinda matasan suka gani sai Sun saresa da makami ba mutum ba dabba. Kai ko abin hawa suka gani a layin sai sun rabza masa makaman hannuwansu.

Lokaci guda yace da Anisa  I have a plan. Ya fad i yana mai sakin murmushi kafin yaci gaba  I will surely ruin Hajja s plan of taking Ummul back to her parents.

Cikeda k osawa Anisa tace  Meye shirin naka.?

Hisham ya murmusa   Yan sara suka.!

Cikin rashin fahimta Anisa tace  Yan sara suka kuma.?

Hisham Ya kuma murmusawa  Just wish me well..! Yana ida fad in haka ya katse kiran ya mik e da sauri ya fice daga motarsa.

Aiko yana ficewa daga motar matasan nan suka k araso a guje suka dinga dukan motar da makamai har saida suka farfasa glass. Shi ko Hisham a guje ya shige gida dan kar su saresa ko suyi ajalinsa. Yana shigewa ya sad ad a a hankali ya shige kitchen. Wuk a ya d auka zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya rintse idanunsa yana bama kansa k warin gwiwar abinda yai niyyan yi  I have no other option. Bazan iya barinki ma Haidar ba Ummul..! Ya fad i yana mai dab a ma Kansa wuk ar a gefen cikinsa. Ya rintse idonsa da k arfin gaske sabida azaban zogin da yaji. Ya tafi da sauri cikin d ingishi yana danne gefen cikinsa yanda yai stabbing Kansa jini na fita. Waje ya fito had ida jefar da wuk ar cikin hanyar ruwa har lokacin matasan basu daina ta addanci da tada hankalin Al umma a wann layin ba. (Allah ka shirya mana Al umma.) A gigice ya turo k ofar gidan yana bin garu yana rik e gefen cikinsa yana tamke ido alamun zogi. Lokaci guda yake rangad a ma Hajja k ira da k yar.

Daga Hajja har Ummul a birkice suka fito jin irin yanayin da Hisham d in ke ambato Hajjan sann sunji hayaniya ya kacame unguwar Wanda hakan yasa Hajja zama tareda Ummul a d aki dan kar ta razana.

Jini suka gani na bin gefen cikin Hisham da tuni ya galabaita yana fad in  Hajja.. They stabbed me.. Help me..!

Dukansu jikkunansu rawa ya d auka. Hajja ta shiga salallami cikin tsananin kid ima  Innalillahi wa inna ilaihi raji un.! Mai zan gani.? Hisham..! Sai ta fashe da kuka ta nufesa a kidime tana fad in  Sun caka ma d ana wuk a sun saresa.. Inna ilaihi wa inna ilaihi raji un..!

Ummul ma duk ta kid ime sai aka rasa mai bama wani baki cikin ita da Hajja ga Hisham dake kwance shame shame yana nishi.

 Hajja su waye suka caka masa wuk a.? Mai ya faru dashi..? Sai kuma ta nufi k ofa a guje tana fad in zata nemo agaji. Duk jikinta rawa yake.

Shugaban committee na unguwar ne da wasu maza kusan biyu suka biyo bayan Ummul suka shigo gidan. Duk a rikice.

Suna shigowa suka nufi yanda Hisham yake kwance shame shame ga Hajja gefensa sai hawaye take tana k arfafa masa gwiwa da fad in zai sami lafiya in sha Allah. Shi kuwa sai nishi yake mai nuni da yana jin jiki  Hajj..Hajja ki yafe mun.. Ki yafe mun Hajjah.. Mutuwa zanyi..!

Ta kuma matsan k walla hannunsa rik e cikin nata gam take fad in  Ka daina fad in haka D ana. Zaka samu lafiya.. muryarta Ya sarkafe sai rawa da jikinta yake.. Daidai lokacin yan committee suka ciccibi Hisham da zummar kaisa asibiti. Hajja da Ummul suka take masu baya cikeda tashin hankali.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*52*

*©þSameena Aleeyou& *

A gaggauce aka wuce da Hisham Emergency yanda aka soma kokarin ceto rayuwarsa. Idan kaga Hajja sai ta baka tausayi. Batada kowa sai tilon D anta Wanda bata fata ta rasa shi.

"Ummul ma karfin hali kawai take dan sosai daga Hajja har Hisham sosai suka bata tausayi. Mutane ne masu mutunci, karamci da sanin darajan D an adam. Bata fata wani abun tashin hankali Ya samesu. Suna tareda ita a lokutan k uncinta da tashin hankalinta dan haka Ya zama dole ta aje nata damuwar da tashin hankalin ta ji da nasu damuwar. Fatanta Allah ya tashi kafad un Hisham ya bashi lafiya sann ya sassauta ma Hajjah."

Jiki a sanyaye Ummul ta k araso yanda Hajja ke zaune bayan an shige da Hisham surgery. Hajja ta d ago ta dubeta sai ta k ak aro murmushi na karfin hali tace  Ya kamata ki koma gida haka nan ki huta kema ba k oshin lafiya ne dake ba. Stress ba naki bane.. Ya kamata ki samu hutu.

Ummul ta kamo hannayen Hajja tana girgiza kai  Bazanje ko ina ba Hajjah.. Ina nan tareda Ke in sha Allah.. Har sai munsan halinda Yayana Hisham ke ciki.

Hajja ta k ak aro murmushi tana duban Ummul d in. Sai ta goge hawayen da Ya gangaro mata  Shi d aya Ya rage mun.. Yazo cikin rayuwata a lokacin da nai zaton Babu wani k ofa na haske da zai kuma budewa cikin rayuwata.

Sai ta d an murmusa  I named him Hisham. Meaning generous. Sabida Ina so ya girma da zuciya mai yalwa. Zuciya mai son bayarwa da taimakawa cikin duk halinda ta Sami iko..

Ummul ta jinjina kai cikin kokarin k arfafa ma Hajja gwiwa  Shid in ya dace da sunansa Hajja. Tabbas yanada zuciya mai kyau mai kwad ayin taimako ba tareda ta nemi wani abu in return ba. Ni shaida ce akan irin taimakon sa a gareni.. Shid in D a ne da ko wace uwa zatai Alfaharin samun irinsa. You are blessed to have him as a child Hajja.. A lokutan da wasu  ya yan sukan zama jarabawa ga iyayensu wasu  ya yan abun alfahari ne da sanyin idaniya ga iyayensu. Ked in Lallai kinada sa a Hajja.. Babu abinda yafi buk ata daga gareki a halin yanzu face addu o in ki gareshi. Ta k arashe murmushi da siririn hawaye saman fuskarta.

Hajja ma murmushi take tana hawaye tana jin dadin kyawawan shaidan da akai ma tilon D anta musamman idan ta tuna mahaifinsa ya ciresa daga cikin ahalinsa Tun baizo duniya ba. Sai jikinta ya d anyi sanyi. Ta soma jinjina Kai a hankali tana fad in  A koda Yaushe fata na shine na kasance mahaifiya da zai alfahari da ita. Mahaifiya da zata sauk e nauyi da hakkinsa da ya ratayu wuyanta.. Sai Muryarta ya soma rawa  Ina tsoro Ummul.. Ban sani ba.. Ko na gaza a wani fannin domin shid in Ya girma baisan mahaifinsa ba..

Tausayinta ke ninkuwa cikin Zuciyar Ummul. Tai saurin girgiza kai  Ke mahaifiya ce da ko wani D a zai alfahari Ya kirasa da mahaifiya Hajja. Sai ta murmusa  Meyasa ma Ya Hisham bazai zama mai kirki ba bayan ya kasance D anki.?

Murmushi Hajja Tai dan ta kula so take ta dan kwantar mata da hankali.

Ummul ta matso jikin Hajjan tana kuma fatan sauk i ma Hisham. Tana kwance jikin Hajja takai hannu a hankali tana Shafa nata cikin. Batasan labarin Hajja ba. Sann bata san abinda ya faru da mahaifin Hisham ba. Amma Hajja ta zama tamkar inspiration d inta. Ita d in ta raini D a kaman Hisham. D an da kowa zai alfaharin samun kaman shi. Sai taji k warin gwiwa na shigarta akan cikinta. For the first time da taji tana so ta haifo abinda ke cikinta koda bazata tab a sanar da mahaifinsa ba. Koda bata k aunar mahaifinsa.. Zatai komai ma D anta da izinin Allah. Zata zama masa uwa ta zama masa uba kaman yanda Hajja ta jajirce akan D anta.

Anyi aiki ma Hisham kuma aiki yayi kyau cikin ikon Allah. Hajja ta

77 / 103