AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   48 / 103

141K to 144K   out of 306.8K words

Fannah yai ba tareda kowa ya gansa ba.

Fannah da fitowarta kenan daga band aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet da gajeren wando. Jikinta ya d auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had ida toshe bakinta da k arfin gaske. Fannah tana kuka tana k ok arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta.

Daddy ya dawo cikeda d oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b angaren ta d aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k ato rungume da matarsa dake d aure da towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa.

Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amincewarta ba fyade yai mata.

Daddy ya shak osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d aure jikinta. Ta dawo ga Daddy tana fad in  Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba.

Daddy ya dubeta da mamaki  Dama ya Saba zuwa.?!

Mommy ta jinjina Kai kaman gaske  Ai idan Baka nan yakan zo. Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa.

Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace  A ah.. Wann mutumin ai mak ocin su k awata Baana ce. Kuma ta&  Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana.

Mommy tace  Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?

 Ta sanar dani shi d in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu& Hasalima mahaifin

Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!

Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k arfin ta  Haka ne.? Wann D an iskan saurayinki ne.?! Ya tambaya yana dubanta.

Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa  Ki amsa min..! Haka ne..!

Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad in  Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk ar so. Kuma mahaifinta ya min alk awarin bani ita.. Amma  yanuwanta Sun karya wann alk awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..! Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka.

Daddy ya ci gaba da huci  Ga b arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk a sa ma shayibu yana fad in bari yaje ya duba section d insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d insa na cikin gidan an kwashe kud ad en ciki.

Koda aka mik a Auwalu ma  yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud ad en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud ad en dan su gudu su bar gari.

Daddy bai saurara daga b angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar.

Sosai take kuka duk e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari. Yana ida fad in haka ya mik e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari.  Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k ila da an fara k irga ma abinda ta haifa watanni.

"Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu."

Sam bata San Daddy ya shigo ba take b arin zance.

Daddy ya dubeta da mamaki  Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!

Sai Mommy ta mik e tana girgiza Kai  A a Engr dan Allah ka saurareni.

 Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!

Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai  Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba..

Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa.

Mik ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab akar da tai sabida halin k unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k unci hopping idan ta haihu zuwan D an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa  See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d an da zakai alfahari dashi.

Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin.

Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik e cikin hannunta baiba balle ya karb e sa. Sai ma mik ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D anta sai hidiman bunk asa Kasuwancinsa da yake. K unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D anta da Daddy yai

take. Ta duk ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d an matsayin D a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta allak a ga bunk asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab a ganin k ok arin Haidar ba har kawo girman sa.

Wann kenan.

(Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan  ya ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da  ya yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa).

*

Ci gaban labari..

Haidar ya share hawayen da suka zubo masa  So that s the reason why he hates me.! Ya fad i haka Kansa a kife.

Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata  No Haidar.. Your Dad doesn t hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That s just.. his way of punishing me.!

 Well I don t care.! Ya fad i haka yana mai buga teburin gabansa da k arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad in  I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.! Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake.

Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai  I m sorry my Son.. I m sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!

Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa.

"Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta  Serving jail sentences won t be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won t rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don t want to see your face ever again.! Ya k arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik e ya nufi k ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k ofa ya fice cikin tsananin huci.."

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*35*

*©þSameena Aleeyou& *

Bayan Daddy ya turo mata lawyer d insa aka basu waje dan su gana.

"Lawyer ya dan dubeta sai ya jinjina Kai yace  I don t want to say this, but a halin yanzu farkawar matar D anki ne kawai zamu iya cewa zai kub utar dake Hajiya. Sabida ba zargi ake ba keda kanki kika tabbata kin bata wann turaren. "

Mommy ta girgiza kai  Kana so kace baza a iya granting bail dina ba a halin yanzu.?

Yai shiru kaman mai nazari  I m afraid yes. Laifin babban laifi ne.. Kuma akwai evidence a hannu. Zai matukar wahala. But still nothing money can t buy in this country. Akwai hanyoyi da dama da za a bi dan a rufe case din. Amma abun shine kince baki so ai amfani da kudi wajen siyan freedom d inki.

Bai Kai aya ba tai saurin jinjina masa Kai  It will only complicate the situation even more. Ni a halin yanzu bana son duk wani abinda zai hadani fad a da Haidar. Idan har nai amfani da kudi ko wani k arfi nawa D a na zai k ara k ina ne kan wanda yake. I want to make things right with my son..Ba wani hanya da za a bi wanda rashawa bazai shiga ba.

Lawyer yai shiru sai kuma ya girgiza Kai  Saidai idan ita yarinyar ta farka tayi withdrawing charges. Let s pray she wakes up soon.. Shine kawai mafita.

Mommy taja gauron numfashi had ida jinjina Kai. Ta k udiri niyyan bazatai wani abun da zai kuma b ata ta a idon ahalinta ba.

A haka dai sukai sallama da Lawyer aka kaita detention cell dinta. Ta d ago ido tana duban cikin cell d in. Sai ta tuna lokacin da tai ma Fannah sharri itama kurkuku aka kaita. Hawaye suka gangaro ma Mommy. Tabbas ta kuma yarda duk abinda ka shuka a rayuwa zai dawo maka harda riba. Sai gashi nata D an ya turata kurkuku bayan ta tura Fannah da jaririn da baida laifin komai kurkuku. Dirshan Mommy ta duka wajen hawayen nadama na gangaro mata.

Anisa ce ta k araso k ofan cell d in hawaye tab idonta. Ta duka tana duban Mommy  Mommy..! Anisa tace cikin murya irin ta mai kuka.

Mai ta dago tana duban Anisa. Yayinda Anisa taci gaba da share hawaye tana fad in  Mommh you will get out of this place soon. I m sure of it.. Zaki fita in sha Allah. We all believe you are innocent. Ta k arashe tana mai kamo hannayen Mommy.

"Mommy ta murmusa tana duban Anisa  I hope so Anisa. Muyi addua Allah ya tashi Ummulkhair na tabbata bazata barni a nan ba, ita d in tanada zuciya mai kyau. "

Wani k atutun bak in ciki ya tokare ma Anisa mak oshi Jin Mommy na yabon Ummulkhair dikda kaman itace sanadiyar kasancewarta cikin halin da ta tsinci kanta ciki.

Anisa ta jinjina Kai sai kuma tace  But Mommy Meyasa abubuwa suke faruwa tinda Ummul ta shigo cikin ahalin nan. I don t want to think about it amma I couldn t help.. Tinda ta shigo cikin ahalin nan problems keep piling up.. Misfortune after misfortune.. It s like she brings bad luck with her& Mommy I m only concern about you..! Ta k arashe wasu hawayen na gangaro mata.

Ganin Mommy tai shiru kaman nazari yasa Anisa ci gaba  Mommy what if.. What if she s a curse or something.. hasn t this crossed your mind..? Mommy Ammi ce kawai fah tasan asalin Ummul..

Mommy tai shiru tana nanata maganar Anisa cikin ranta. Kuma fah

48 / 103