AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   88 / 103

261K to 264K   out of 306.8K words

zan k ara amma sai idan kece kika samo min matar.

Mommy ta dan ware ido  Ina ka taba ji an nemo ma miji mata.?

Daddy ya murmusa daga d aya b angaren  Za a fara akanki.. Na baki wuk a da nama Kwaise ta.

Hajja Fannah da gaba d aya ta gaza sukuni daga nan yanda take duk e. K afafunta Har rawa suke.. tana k ok arin mik ewa taji Mommy ta kamo hannunta gam ta hanata barin wajen.

Mommy ta d ago ta dubeta bayan sun gama waya da Daddy.

" Fannah nasan nayi kasalandan ma rayuwarki.. Amma bakida gidan da Ya wuce gidan Aliyu Maitama. A baya nayi zaton cewa zamana ni kad ai a gidan Aliyu Maitama shi zai kawo min dawamammiyar farin ciki Shiyasa nayi duk yanda zanyi naga na rabaku.. Ashe abun ba haka bane.. Sai gashi bayan tafiyarki na rayu ni kad ai amma Babu farin cikin da naci buri.. Ba abinda yafi komai kawo farin ciki a rayuwar nan kamar ka tsarkake zuciyarka.. Ka zauna da kowa tsakani da Allah.. Shi kuma Allah sai Ya saka maka nutsuwa farin ciki,harma da kwanciyar hankali a zuciyarka..! Ta kuma kamo hannayen Hajja Fannah  Kaman yanda na zamto silan raba Aurenki da mijina a baya ina so ki bani dama na zamto silar maida Aurenku a yanzu.! "

Hajja ta d ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Mommy yayinda Mommy taci gaba da jinjina Kai murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta  Na san bazaki ce a a ba dan mijina d aya ne tamkar da dubu. Ki yarda Dani.. Ina son mijina.. Ina matuk ar k aunarsa& This is the hardest decision of my life.. Amma bazan ja da hukuncin Ubangiji ba. Ina rok on Allah Ya had e kawunan  yayanmu Ya bamu ikon kyautata ma juna tareda yima mijinmu biyayya. Sai suka rungume juna kukan Hajja Fannah na k aruwa.

Asshe dake kallonsu daga nesa murmushi Tai tana mai goge hawayen da Ya gangaro mata.. A cikin zuciyarta take cewa ina ma ita da nata Abokan zaman zu zamto haka.

Bayan da Haidar Ya dawo wajen Mommy sai Tai masa tayin abincin da Hajja ta kawo masa. Tab e baki yai kad an had ida girgiza kai  I m good Mommy. Ya kuma duban Mommy da kyau  Mommy nace are you sure this place will accomodate you all..? Yai maganar yana daga ido yana duban gidan cikin wane irin yanayi.

Mommy ta jinjina kai  Eh mana. K warai kuwa.. Kaga dukanmu mata ne haka nan zamuyi squatting.

Da mamaki Haidar ke duban Mommy  Mommy keda kanki kike using word din squat.?!

Mommy ta kuma murmusawa tana duban gidan  Mamaki kake Hajiya Kwaise Maitama zata kwana cikin gidan da bai kai darajan d akunan ma aikatan ta ba..? Ta kamo hannayen Haidar cikin nata  Haidar my Son. Shi dan adam bai gane cewa shi ba koman komai bane until life humbles us.. Mu d auki rayuwa da sauki dan mu d in daga turb aya muke kuma cikinta zamu koma.

Haidar ya jinjina Kai a hankali  Haka ne Mommy.. sai karada  But Mommy.. Kinaga Khairy da Baby zasu iya kwana a nan..? I mean anyi yawa a gidan.. The place is too crowded.. Plus I don t like the vibe here..

Mommy ta saki baki tana dubansa. Sai ta dunguri keyarsa wann karon  Rufe min baki ban son iyayi. Kai a dole kayi D a ko.. Aiko dukanmu nan daka gani haka dai zamu kwana a nan har Allah ya wayi gari da izininsa. Naga ta yanda zakai kinibibin idan ka bud e ido ka ganka Abuja Baba Ali na wajen uwarsa a Kano.

Ya dan furzar da huci kad an  Mommy ni fah.. Gaskiya bazan iya komawa Abuja ba tareda an maida Aurenmu da Khairy ba..

Shiru Mommy tai tana dubansa. Sai ta girgiza kai kad an  Haidar ni a nawa shawarin. Da ka bar maganar maida Auren nan ba yanzu ba.. Ummul bata jima da haihuwa ba& Ga abubuwan da suka faru.. Ga iyayenta can gida da zataje ta fuskanta.. Give her some time to recover.. Sai ai komai cikin lumana.

Duban Mommy ya d anyi fuskarsa duk a dame  But Mommy..

Ta katsesa  No buts Haidar.. This is the right thing to do.. Yanzu ma ni abinda nake so da kai ka kira can station din da Anisa ke tsare ka bada umarnin a saketa.. Kawo wann lokacin nasan ta gane kurenta.

Ya d anyi jim yana duban Mommy. Sai Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa  Mommy kiyi hakuri.. ba wai bana so a saki Anisa bane.. It breaks my heart seeing Aunty Asshe like this.. Mommy akwai Wanda nake so na kama ne.. Kuma through Anisa kawai zan kama shi.. But I promise you da zaran bincike Ya kammala Anisa will be free.

Ta jinjina kai a hankali tana dubansa. Sallama yai ma Mommy kafin ya tashi ya fice ya nufi nasa masauk in.

**

Washe gari kaman yanda suka tsara sassafe Sadis ya kwashesu suka d auki hanyar Kano.

Tuni Daddy ma Ya tasa kan  ya yansa Haidar da Hisham suka bi jirgi zuwa Abuja. A Cewar Daddy akwai gabatarwa na musamman da zaiyi a Company gameda  ya yan nasa musamman Hisham Wanda daukacin ma aikatan Kampanin suka sansa da ordinary employee a baya. A halin yanzu zai koma ne matsayin D a ga mai jagorancin Kampanin.

Ba yanda Haidar ya so sabida Daddy dole yabi umarnin mahaifin nasa ya tafi tareda su.

*

Umma na zaune tsakar gida taji Sallama Ya kacame ko ina. Ta mik e cikeda farin ciki tana ganin masu shigowa. Mama Tani dasu Azeema ne suka soma shigowa.. Su Azeema dasu Khulsum suka haye jikin Umma suna fad in sunyi kewarta.

Umma ta dubesu jiki a mace ganin bataga Ummul tareda su ba. Cikin rawar murya take tambayarsu  Ina Ummulkhair..? ina  yaruwarku.?!

"Bata rufe baki ba ta hango Ummul na shigowa cikin matuk ar sanyin jiki, kanta kife ga jariri sabon haihuwa nad e cikin hannunta. Mommy da Aunty Asshe na biye da ita."

Umma ta mik e cikin matuk ar sanyin jiki tana duban Ummul dake shigowa. Tuni Umma ta soma tafiya ta nufi Ummul. Tana k arasowa gareta taja ta tsaya kukan da taketa k ok arin dannewa yana kuma fizgarta   Yata..  Yata Ummulkhair..! Sai Umma tai bursting cikin kuka yayinda Ummulkhair ma kuka ya kufce mata.

Asshe ce ta amshe jaririn daga hannun Ummul wacce tuni ta zube k asa gaban Umma tana kuka sosai.

Sai Umma ma ta duk a ta rungumeta  ya da uwan suka b ige da kuka mai ban tausayi..

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*58*

*©þSameena Aleeyou& *

Kan Ummul bisa cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata yayinda Umma ke ci gaba da Shafa kanta a hankali itama d in hawaye ke gangaro mata.

 Nayi kewarki& Nayi kewarki sosai Ummata.. Dan Allah Ki yafe mun..!

Umma taci gaba da Shafa kanta a hankali murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta  Baki na goma kenan kike neman gafara na Ummul.. Ni mahaifyarki ce kuma na yafeki tun kafin ki nemi yafiyata.. Babu abinda yake tsakanin  ya da uwa face yafiya da afuwa.!

Sai Ummul ta sake bursting cikin kuka mai tsuma zuciya. Daidai nan Mama Tani ta shigo da Baba Ali dake yan k anan kuka tana sanar da Umma tafiyar su Hajiya Kwaise da Hajiya Asshe.. Umma ta amshi jaririn tana lallashinsa lokaci guda take ce da Ummul maza ta mik e ta kintsa kanta ta kula da yaron kafin Abbanta ya shigo.

Ummul ta d ago ta dubi Umma tana goge ragowar hawayen dake fuskarta. Murya a sanyaye tace  Umma da gaske Abba ya samu lafiya Har ya fara fita kasuwa.? Tai maganar tsantsan farin ciki na nunawa a fuskarta.

Umma ta murmusa  K warai kuwa. Abbanki ya samu lafiya.. Nan bada jimawa ba zai shigo da yardar Allah.

Sai Ummul ta mik e jiki a sanyaye tana tunanin yanda had uwarsu da mahaifin nata zai kasance.

Wanka sukai ita da jaririnta dan tuni Mama Tani ta d aura ruwa bisa murhu tin isowarsu. Yaron Ya samu bacci da yaji ruwan d umi. Umma ta saka yaron gaba tana kallonsa sassanyar murmushi saman fuskarta. Yau ga D an Ummul dinta nan tana gani za kuma ta sab asa a baya ta goya da izinin Allah. A haka Mama Tani ta shigo ta taddata. Su duka biyun suka tasa yaron gaba suna kallo. Mama Tani Tai saurin bud e net d insa tana k ok arin rufa masa Umma tace  Yaya naga dare baiyi ba da an kyalesa da gidan sauron nan tuk uri ne dashi.

Mama Tani ta rufe gidan sauron ruf tana fad in  Um um Suwaiba gwara dai mu killacesa jikan Manyan mutane ne wann.. Ina mai baki labari gobe zakiga Hajiya Kwaise sassafe gidan nan matuk a tana garin nan.. Muddin taga alamun cizon sauro jikinsa na tabbata bazata bari ya kuma kwana gidan nan ba. Ta gyara zama tana kame hab a  Umm Suwaiba am.! mu muka sha kallo yanda ake taltala yaron nan da kyar Ubansa Ya amince a taho dashi nan. Ta k arashe tana gyara zaman net d in sosai.

Umma ta murmusa tana girgiza kai kad an. Sai suka dubi juna itada Mama Tani sanda suka hangi  ya yansu ras zaune daga parlorn Umman.

Mama Tani ta girgiza kai tace  Wato Al amarin Allah sai a bar masa kayansa Suwaiba. Duk Wanda yace zai shishigi ko k atsalandan a hurumin Ubangiji toh fah Tabbas sai Allah Ya nuna masa iyakarsa. Yanzu dai ki duba kiga yaran nan yanda muka ci musu burin zaman gidan miji gasu nan ras a gabanmu yanzu. Ba wai basu je gidan mijin ba sunje amma sai Allah Ya dawo mana dasu gabanmu dan mu hankalta mu kuma dauki darasi. sabida a lokacin da mukaci musu burin zama gidajen mazajensu bamu nemi zab in Allah ba sann mun zata iyawan mu shi zaisa su samu mazajen aure kuma su natsu a gidajen Aurensu. Ashe ba iyawan mu bane ba kuma wayonmu bane.

Umma ta jinjina Kai  Wann gaskiya ne Yaya. Allah yasa hakan ya zamto izna a garemu da masu hali irin Wanda mukayi a baya.

Mama Tani ta amsa da Ameen Suwaiba.

A b angaren Ummul kuwa sabon tashin hankali ta shiga dan tinda Abba ya dawo daga kasuwa yak i ya dubi koda yanda take balle ya amsa gaisuwarta. Ko jaririnta bai kalla ba balle ya amshe sa.

Tai kwance lamo saman cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro mata  Umma Abba yak i ya min magana. Yak i amsa gaisuwata.. Yak i ya dubi jaririna.. Umma Abba bazai tab a yafe min ba..! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya.

Saurin toshe bakinta Umma tai  Kul Ummul. Kar ki sake magana irin haka..Kiyi ma Abbanki uzuri dan tinda ya farka daga jinyar nan nasa al amarinsa sai a hankali. Musamman idan ya hau dokin fushi. Masana sun alak anta hakan da magunguna masu k arfi da yake sha ga kuma ya hadu da girma. Ki basa lokaci a hankali zai sauk o ya huce kinji koh. Maza tashi ki daina kukan nan haka.. Kici abinci ki sha ruwan d umi kafin Babban mutum ya tashi a nasa barcin.

Ummul ta mik e zaune tana goge hawayenta tana tunanin irin soyayya da shak uwar dake taakaninta da mahaifinta yau an wayi gari itace Abba take gaishesa ya juya mata baya ba tareda ya dubi koda yanda take ba balle ya amsa gaisuwarta. Jiki a matuk ar sanyaye ta nufi band aki nan cikin d akin Ummanta. Dan a gyaren gyaren da Haidar yasa akai ma gidan harda band aki akai masu gaba d aya kowa cikin d aki aka kuma kawata ginin gidan kaman ba shi ba.

Zama tai ta saka abincin gaba ba tareda taci ba. A haka Umma ta shigo d akin ta taddata zaune saman pillow kaman yanda ta shirya mata wajen zaman. Umma ta soma da lallashi amma Sam Ummul bata iya cin abincin ba har dai Umma ta dan soma mata fad a maimakon taci abincin kawai sai ta b ige da kuka. Ta kasa yarda wai ita Ummulkhair d in Abbanta Abba ke fushi da ita irin haka. A haka Khulsum ta shigo rik e da waya tana fad in  Adda Ummul ga Ya Haidar a waya yace a baki.

Ko sauraron Khulsum batai ba balle ta amshi wayar.

Khulsum ta dan furzar da huci tace dashi  Tak i ta amshi wayer.

Umma ta tsare sosai tace maza ta amshi wayar. Ba don taso ta amsa Umma da Khulsum suka fice suka barta rik e da wayar ba tareda tace dashi komai ba. Mugun takaicinsa ne ya kuma taso mata. Ita gani take duk laifinsa ne Abba ke fushi da ita. Watak ila da bai amince da Auren Wata Uku da yai da ita ba tun a fari da duk wad ann abubuwan basu faru ba. Duka laifin na Haidar ne da ya amince zai AUREN WATA UKU da ita.

Maganan duniya Haidar ya mata tak i ta amsa. Yayi magiyar yayi lallab in duk bata amsa shi ba har saida suka sinkayo kukan Baba Ali alamun ya tashi a bacci. Dan ta k ara basa haushi sai kawai ta barshi yanata suararon kukan D ansa cikin wayar. Har lokacin ba abinda tace sai kukan yaron dake k aruwa.

Zuciyar Haidar yaci gaba da masa zafi. Ya sani intentionally ta kyale yaron yana kuka dan yaji zafi.

A zuciye yace  Khairy wai ina karatunki ya tafi ne.? Ta ya kike punishing k aramin yaro for his Dad s mistake.?!

Bata amsa shi ba har lokacin sai hawaye dake gangaro mata.

Haidar ya jinjina Kai yana Jin zuciyarsa na masa zafi sosai  Fine Ummulkhair.! For the first time da taji ya ambaci sunanta kai tsaye ba kaman yanda Ya saba fad a ba. Haidar yaci gaba  Do as you wish.! Mommy tana nan cikin garin Kano bata dawo Abuja ba.. Zata zo ta d aukar min D ana zai iya rayuwa da baby formula.. Bazan bari tarihin abinda ya faru Dani ya maimaita Kansa Akan D ana ba..! D if ya kashe wayar ba tarda ya kuma cewa komai ba. Aiko yana kashe wayar kaman ance nan ta b ige da kuka sosai jaririn nayi itama tanayi a haka Umma ta shigo ta taddasu.

**

Washe gari kaw su Mommy da Aunty Asshe suka zo duk a tunanin Ummul sunzo su tafi da Baba Ali ne kaman yanda Haidar yace. dan tayi zaton Haidar ya sanar da Mommy kaman yanda yace amma sai bataga hakan daga Mommy ba. Kayyaki ma taga ta kawo musu ita da jaririn da wasu abin buk ata. Nan take sanar dasu washe gari zata bi jirgin safe ta tafi Abuja kafin ran suna. Umma sukaita mata godiya da san Barka.

Mommy ta dubi Ummul dake zaune daga mazauninta kanta a k asa. Ta murmusa tace  Toh Daughter ni zan wuce gobe in sha Allah. Na samu urgent call daga Daddynku. Duk dai bazai wuce magana akan yaransa ba ga kuma case din Anisa da ba a warware ba har yanzu. Naso na tsaya ayi suna kafin na koma.. But still idan na samu dama zanzo ayi suna Dani idan kuma ban samu Aunty Asshe zata wakilceni in sha Allah.

Ta jinjina Kai a hankali ba tareda ta iya cewa komai ba.

"Mommy ta kuma murmusawa tana duban jaririn dake baccinsa peacefully tace  Gameda batunku keda Haidar.. You have the final say here.. Kin cancanci hakan. Dan a baya an Miki dole. Idan aka sake Miki dole wann karon ba a Miki adalci ba& He s my son.. Ina son shi fiyeda komai a rayuwar nan.. Amma hakan ba yana nufin zan sake fifita shi sama da komai kaman yanda nayi a baya ba. Mommy ta dan numfasa kafin taci gaba  I couldn't manage to change him for years.. Amma cikin buwayan Ubangiji you came and changed him.. Ina nufin kece sanadi. Mommy taci gaba da jinjina Kai tana duban Ummul  Ki sani, You are the most precious truth in his life.. But still zab i naki ne Ummulkhair.. Bazan sake tilasta Miki kasancewa da D ana ba kaman yanda nayi a baya.. Sabida ke d in ma  ya ce a

88 / 103