AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   95 / 103

282K to 285K   out of 306.8K words

time around Aure mukai na Har abada ba AUREN WATA UKU ba.. Ba Aure sabida wani manufa ba.. Ba Aure dan Daddy ya mallaka min wani project ba. I love you so much Khairy.. And from now henceforth I want you to know that you are my FOREVER.. Mrs Haidar Maitama.

Hawayen da take mak alewa suka digo saman hannun Haidar. Fuskarta Ya kamo yana dubanta  Forgive me Khairy..! Forgive your Sweetmonster.

Murmushi take tana dubansa hawaye na gangaro mata  Na yafe maka.! Na yafe maka mijina.. Na yafe maka tin sanda Aunty Kwaise ta sanar Dani gaskiyar al amarin.. Na yafe maka because I always believed you are a good person.. Na yafe maka because I love you.! Ta k arashe cikin yin k asa da muryarta.

Kallonta yake kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yana duban yanda lips dinta ke furta kalaman so a gareshi. Bai san sanda Ya janyota jikinsa ya rungume ba.

Idanunsa a lumshe yake furta  I love you more.. I love you more.! Ya k arashe yana kuma shigar da ita jikinsa.

Jin zancen na neman canza salo Ya sata k ok arin janye jikinta tana fad in zataje ta duba Baba Ali.

Haidar bai saketa ba yaci gaba da rikitata da kalolin k aunarsa yana fadin  But his Dad needs you more.. Besides Yaa Gumsu is there to take care of him.

Kaman zata sakar masa kuka take fad in dan Allah yai hak uri Ya kyaleta taje ta duba su ta barsu shiru tuntuni.

Shima kaman zai kukan yake fad in idan ta tafi wajen Baba Ali shi waye zai kula dashi.

Ta kuma marairaice fuska  Toh ai shi Baby ne.. Kai fah babba ne.

Yaci gaba da shafa sumarta yana duban fuskarta  But I m your big baby.

Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.

Haidar ya janye hannayen suna duban juna cikeda so da kauna.

" Tell me, am I not your big baby.? "

Ta yunk ura zata kuma shigar da fuskarta cikin jikinsa ya tallafo fuskarta yana tsareta da idanunsa. Ta kuma marairaice fuska zatai magana taji ya kuma had e bakinsu waje guda.

Da kyar Ummul ta samu ta kwaci kanta daga hannun Haidar.

Ya d ago idanunsa da tuni Sun k ank ance yana dubanta. Da kyar ya iya d ago yatsun hannunsa guda uku yana mata alama  3 minutes.. Minti uku kacal na baki.! Ya furta daga nan yanda yake kishingid e yana maida numfashi.

Lumshe idanunta Tai bayan ta fito daga d akin tana mai sauk e ajiyan zuciya. Haidar k arshe ne Ya kware wajen mantar da ita duk wani b acin rai da fushi da Ya jefata ciki a baya. A hankali ta furta  I love you.. I love you so much my bigbaby.

Ta tadda Baba Ali baccinsa yake Yaa Gumsu na bisa darduma da alama sallah ta ida. Bata ko bari Ummul ta zauna ba ta fatattake ta da ta koma wajen mijinta ta karada idan Baba Ali na nemanta zata kirata a waya. Cikeda kunya Ummul ta fice ta koma nata d akin.

Kasancewar bata tadda Haidar a d akin ba ya bata daman fad awa bathroom tayo wanka.

Tsaye Tai gaban wardrobe tana nema tufafi mai sauki da zata sauya. Tana nan a haka taji hannun mutum ya zagayeta Ya rungumeta ta baya had ida manna mata kiss a dokin wuyarta dake da dashi da dumin ruwan da Tai wanka. Tai wani irin jan numfashi a dan firgice.

Ya kaikaito da ita suna duban juna. A dan shagwab e tace  Ka bani tsoro.

"Ya d an Ware ido  Really I scared you..? Yai maganar yana janyota jikinsa sosai. Lokaci guda yai kasa da murya  Tell me, ta Ya na baki tsoro..? By& hugging you.. Or.. by& kissing you.? Yai maganar cikin kashe murya yana kuma shigar da ita jikinsa."

Kaman zata sakar masa kuka tace  All..!

Ya kuma shigar da ita jikinsa yana mai ci gaba da sumbatar wuyarta yake furtawa a hankali  I want you to scare me too.. with your sweet kisses.. Warmed hugs.. And your sincere smile..! Ya k arashe cikin kasheta da wani irin salo mai wuyan fasaltuwa.

Cikin k ok arin janye jikinta take fad in Ya kyaleta ta saka kaya.

Ya tsare fuska yana dubanta  Do you need it.?

Cikeda kunya ta rufe bakinta da tafukan hannu tana zaro ido.

Kashe mata ido yai kafin yace  Zo muje.?

Ta girgiza masa kai  To where..?

 To my bedroom obviously.. I have cloths for you there.

Zata kuma magana ya duk a gabanta yana mai kwantar mata da gadon bayansa.

Itakam dariya ma abin ya bata ganin Ya duka ya juya mata baya  Wai mai kake ne.. Meye haka.?

 What..? D ale mana. Yace yana nuna mata gadon bayansa.

Murmushi mai bayyana hakwara take. Ta d an girgiza kai kad an tana nuni da kanta  Wai ni ce zan d ale baya.?

Ya d ago gira da ido yana dubanta  Oh mamaki kike.? Of course I ll give my wife a piggyback to my bedroom.

Itakam dariya da kunya duk sai Ya rufeta musamman da ta d ale bayan Haidar d amas ya nufi bedroom d insa da ita.

Saida suka isa d akin ta raina wayonta dan Haidar dai bai aje mata wani kayan sakawa ba kaman yanda yace. Kaman zata masa kuka take tambayarsa ina kayan nata suke.

Ya dan tsuke fuska yana dubanta  It s not.. necessary.. You don t need it.. You ll be fine like this.. Ya k arashe yana kashe mata ido guda.

Kaman zatai kuka take fad in ita dai tak i wann wayon.

Haidar Ya janyota jikinsa yana lallashinta da fad in yayi alk awarin zasu sharing nasa kayan kafin wayewar gari. Nan kuma suka soma sinkayo kukan Baba Ali.

Ummul ta dubesa tana girgiza kai  Ka gani koh.. Yanzu ya zanyi na fita a haka.. Daga corridor fah nake sinkayo kukan nasa.. Wayyo Allah na nasan zagawa take dashi dan yai shiru.. Ta ya zan soma fita a haka.?

Ya kamo hannayenta  Relax Khairy.. You stay here.. I ll go check on them. Ok. Ya karshe yana dubanta.

A hankali ta jinjina masa kai. Ta koma tai zaune tana k are ma d akin kallo.

A haka Haidar ya shigo da Baba Ali cikin hannunsa idanun yaron tar a bud e da alama hira zaiyi. Sai cillasa Haidar yake shi kaw yaron sai k ekata dariya yake.

Haidar Ya diresa saman gado yana ci gaba da masa wasa. Ya kwanta ringingine ya dora yaron saman k afafunsa yana cillasa da k afafu. D a da uban duk dariya suke mai cikeda nishadi. Ita kam Ummul sai suka zame mata tv dan sosai suka birgeta.

Ganin Haidar ya shagala da wasa da D ansa yasa ta fice nata d akin ta sako tufafi mai sauk i.

"Haidar ya dubeta sama da k asa sanda ta turo k ofan d akin. Ya dan tsuke fuska yace  Mrs Aliyu, what s the meaning of this..? "

Ta dan girgiza Kai  Mai fah.?

"Ya mata nuni da bakinsa zuwa kayan jikinta  I mean, do you really have to wear that..? "

Ta dan rausayar da ido dan tasan rigimace kawai irinta Haidar.

Sai Ya dan kashe murya yace  But still.. you look spicy..! Ya k arashe yana kashe mata ido. Ya dan bud e mata hannu yace ta k araso. Cikin tsanaki take takawa har ta isa garesa. Yai mata masauk i zuwa b angarensa guda yayinda Baba Ali Ke cikin d aya b angaren nasa. Ya had esu gaba d aya ya rungume. Ya dan lumshe idonsa kadan  Finally we are together.. The three of us.! Ya fad i yana sumbatar su biyun.

Sosai ta shige cikin jikin mijinta ga D anta daga d aya b angaren. Mai kuma zata nema a duniyar nan. A hankali take furta kalmar godiya ga Ubangijinta da ya cika rayuwarta da d imbin albarka.

Haidar ya dubeta yanda Tai lamo gefen kafad arsa  Mrs Maitama.

Ta amsa murya a mak oshi kafin ta dan d ago ta dubesa.

Haidar yaci gaba  Put him to sleep now.. Let s have our own time.. Ya k arashe yana mika mata Baba Ali. Ba musu ta amshesa ta soma kiciniyar basa abincinsa.

Haidar ya rik e rigar nata yana mai fad in  Allow me.

"Batai yunk urin hanasa ba. Batai yunk urin dakatar dashi ba har ya saka ma yaron abincinsa a baki da basmala. Haka Haidar yai zaune ya sakasu gaba yana kallon yanda take feeding jaririnsu gwanin bansha awa. Sosai ya shagala da kallonsu suna k ara birgesa Har Baba Ali ya samu bacci. Bayan ta shimfid a Baba Ali Haidar ya umarceta da ta d auro alwala tazo suyi sallah. Haka kuwa akai. Ya jasu sukai sallah raka a biyu kaman yanda yazo a sunnah. Sukai addu o i da duk wani abinda Ya kamata suyi. Bayan nan ne fah ta yarda lallai Haidar na buk atan nasa lokacin. Dukda tsananin son kasancewa dashi take a wann daren bai hanata tuno wahalan da ya bata a kasancewarsu ta farko. Haidar ya kula da hakan. Cikin lallama da dabara yake sanar da ita it will be different from the other time. Gently yake biyeda ita. Saida ya tabbata ta mallaka masa kanta, zuciyarta, ruhinta da gangan jikinta gaba d aya. A haka yai leading nasu zuwa wata duniya da basu tuna kowa cikinta sai su biyun. Kaman yanda yace zai kasance na daban haka d in ne ta kasance. Ta yarda yayi kewarta ya kuma nuna mata tsantsan k aunarsa gareta. He made sure wann daren zai tabbata na musamman a tarihin rayuwarsu.."

A kwanakin soyayya sukaita nuna ma junansu Babu kaman Haidar da gaba d aya ya sake rikicewa akanta. Idan suna tare basu tuna komai basu tuna kowa sai su biyun wasu lokutan kukan D ansu Baba Ali ke dawo dasu wann duniyar.

Sunyi nisa cikin faranta ran junansu suka sinkayo sautin kukan sa. Ummul Tai yunk urin zame jikinta daga nasa tana fad in zataje ta duba Baba Ali.

Rik eta Haidar yai yana kuma shigar da ita jikinsa. A hankali yake rad a  Do you know why he s crying..?

Ta dan girgiza Kai  No.. He s hungry.. probably..!

Haidar ya kuma matseta cikin jikinsa  Cewa yake he wants a sibling.

Cak suka daina sinkayo kukan yaron.

Haidar yaci gaba da rikitata da salon k aunarsa yana fadin  See I can read his mind.. You don t need to go check on him.. Just stay and give him a sibling..

Da dabara Ummul ke zame jikinta Har ta samu ta zille masa. Saida ta kai k ofa taji ya rik o hannunta. Ya manneta jikin k ofa had ida d ago hab arta kad an suna duban juna  I love you Khairy.. I love you so much.

A hankali bakinta itama ke furtawa  I love you too.. I love you my sweet.. sweet..! Bata k arasa ba Haidar yai karaf yace  Your sweet mons&  Bata bari yakai aya ba tai karaf tace  My sweetlove.. Ta k arashe tana mai manna masa kiss a lips d insa. Daga haka ta zame ta fice cikin sauri tana murmushi ma Haidar da tuni Ya daskare yana shafa lips d insa.

**

Tarewarsu da sati biyu ake bikin sunan Baba Ali a nan Abuja. Su Mommy suka hada nasu taron nan gidan Daddy. Ummul tayi waya da yanuwanta duk zasu samu halarta harda Babbar Yayarsu Aunty Salima wacce tuni ta baro yaranta gida wajen Mama Tani dan yaran ne kawai zasu samu halarta banda iyayen.

"Sadis ne Ya tafi ya d aukosu ana gobe taron sunan. Azeema na gaba yayinda Khulsum, Badia da Aunty Salima ke baya. Aunty Salima tana hankalce da Sadis da Azeema tin tasowarsu Har kawo isowarsu. Ko ba ace ba zata iya cewa ta fahimci meke wakana tsakanin su biyun."

Sanda suka iso Salima ta tsare Azeema da ido bayan sunyi Sallama da Sadis Sun nufi cikin gidan.

Salima ta girgiza kai kad an tana duban Sadis dake kuma waigowa yana satan duban Azeema. Itama Azeema sai murmushi take tana waigawa.

Salima ta tsareta da ido tace  Ke Azeema.. Wai meke faruwa ne a nan..?

Azeema tace  Me fah Aunty..?

Salima Tai mata nuni da Sadis da tuni Ya nufi mota tace  Shi nake nufi.

Murmushi Azeema ta saki tana wani juya ido  Laa wai Sadis.. Ba komai fah Aunty Salima.. Kawai mutunci muke.

Salima ta jinjina kai tana fad in  Eh lallai fah mutunci.. Toh idan Tai tsami munji mun gani. Ta k arashe tana take ma Khulsum baya.

Badia kaw dake nan daga waje tin bayan isowarsu tana nan zaune gefen flowers dake jikin k aton shataletalen dake tsakiyar gidan. Wayar Ummul take amsawa yanda take sanar da Ummul d in Sun iso amma Sun sauk a gidan Daddy. Ummul kaman zatai kuka take fad in meyasa basu taho sun sauk a gidanta ba.

Badia tace  Ayya  yaruwa kiyi hakuri wllhi tin kafin mu taso Mommy ke ta waya tana fad in tuni an shirya mana masauk i.. Kinsan bazamu iya ce ma Mommy a a ba.

Daga d aya b angaren Ummul kaman zatai kuka tace  Toh shikenan.. Gobe muma in sha Allah da wuri zamu shigo.. Idan mun zo Zan rok i Mommy nasan zata amince mu taho tare.

Badia tace  Toh shikenan Allah Ya kaimu goben. Kinga bara na shige ciki sauk armu kenan. Sukai sallama da

 yaruwar tata a daidai sanda wata k atuwar b akar jeep ta shigo gidan.

Badia ta soma tafiya kenan taji wata murya na babban mutum mai cikeda kamala na mata Sallama.

Ta waigo cikeda girmamawa tana amsawa. Dan idan dai bai kai Abbanta a shekare ba zaiyi kusansa dukda hutu da jin dad i na b oye tsufa.

Bayan ta gaida mutumin sai Ya k arada  Allah sa dai  yar gidan ce ke.?

Ta d an girgiza kai kad an  A a ni ba  yar gidan bace. Amma ciki zan shiga yanzu.

Ya murmusa yana jinjina kai  Toh da Allah idan kin shiga kimin iso wajen Maigidan. Dan nayita neman layinsa bana samu.

Ta d anyi jim sai tace  Toh.. Wanene zance.?

Mutumin yace  Kice Alhaji Gimba ne.

Ta jinjina kai tana mai amsawa kafin ta shige.

Alhaji Gimba yabi bayanta da kallo murmushi saman fuskarsa yana jin wani abu na fuzgarsa.

Koda Daddy ya fito ya tadda Alhaji Gimba tambayar da Ya soma yi ma Daddy shine wacece wann yarinyar da Tai masa iso.?

Daddy ya d anyi jim sai Ya dan girgiza Kai kad an yace  Bansan wacece ciki ba amma dai ina tsamman d aya daga cikin  yanuwan Matar Haidar ne.. Sai Daddy ya dan girgiza kai  Amma meke faruwa..? Allah yasa dai lafiya.?

Alhaji Gimba yai saurin girgiza kai  Lafiya sai alkhairi.. Kawai dai.. Naga iri gidanka ne abokina.

Da mamaki Daddy ke dubansa. Sai Ya girgiza kai kad an yace  A a Gimba.. You can t be serious. Bazaka mana haka ba.

Alhaji Gimba yace  Wllhi I m serious Abokina.. Ai kasan ban tab a zuwa maka da magana makamancin wann ba. Ba irin k ok arin da bakayi ba ganin na sake aure Tun bayan da na rasa iyalina amma banyi ba. Yau nazo maka da irin batun da kake son ji kana nema ka k aryatani.

Daddy ya girgiza Kai  Ni ba k aryataka zanyi ba amma matar d ka d auko d in ne ban tsammaci haka ba. Bayan kasancewarta k aramar yarinya ka fad a mun ta Ya zamuje muna zubda gwiwoyin mu a yanda Haidar keyi. Ta ina zamu fara jera kafad a muna surkunta a yanda Haidar keyi.?

Alhaji Gimba Ya murmusa yace  Abokina kenan. Naga dai ba haramci cikin abinda nake son aikatawa sai alkhairi in sha Allah. Sann Tafiyar Haidar daban namu daban.. Kaman yanda kaje ka nemo ma Haidar haka zaka tafi a nemo min matuk a na samu yarda da amincewar yarinyar.

Daddy ya girgiza Kai yana fad in  Gaskiya Gimba ni baza ayi wann kayan kunyan dani ba. Kaje can ka nemi aurenka ba hannuna.

Alhaji Gimba Ya dan dara yana kuma fad in lallai sai Daddy ya shige masa gaba a neman auren da yake.

Washe gari ta kama ranar taron sunan Baba Ali da Kakaninsa na Abuja suka shirya. Sann ranar mutanen SouthAfrica wato Hisham da Anisa ke dawowa gida Nigeria.

Hisham Ya kaikaito Ya dubeta sanda jirginsu Tai landing a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport. Shu umin murmushin nan nasa ne saman fuskarsa  Mai ciki. Tashi ki daina baccin haka mun iso.

Wani Uwar harara Anisa ta watsa masa tana jin kaman wani haraswan zata kuma dan tayi amai cikin jirgin yafi sau uku.

Huci take tana fad in

95 / 103