AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   74 / 103

219K to 222K   out of 306.8K words

Sheikh Imam ya fahimtar dashi wasu abubuwa. Sai kuma akai rashin sa a Sheikh yau bai fito majalisi ba.

Alhaji Gimba ya jinjina Kai  Wann gaskiya ne Abokina. Ina ma iyaye da yawa zasuyi yanda kayi da an rage wasu mace macen Auren da babu gaira babu dalili. Amma tinda yanzu Sheikh baya nan ni zan zaunar dashi mu d an yi magana ta fahimta.. Kasan kai zai iya jin nauyinka a wasu abubuwan.. Sann idan son samu shima kasa ya dinga zuwa d aukan karatu ko ba lokacin da muke ba.. Akwai lokacin da aka Ware dan samari kaman shi. Lallai yanzu Babu mai zama da jahiltan addini sai Wanda yaso.

Daddy ya jinjina Kai  Wann haka ne.. Toh zan bar maka shi. Zan kira driver yazo ni ya d aukeni.

Alhaji Gimba yace  Akwai driver na ai sai ya kaika. Nan sukai sallama Daddy ya sanar da Haidar shi zai tafi

"A d an wani hut dake haraban gidan suka zauna yayinda Alhaji Gimba ya soma jan Haidar d in da hiran Kasuwanci kafin ya d anyi gyaran murya yace  Haidar, ni aminin mahaifinka ne nasan kasan da wann. "

"Haidar ya jinjina Kansa a hankali. Alhaji Gimba yaci gaba  Kaman yanda musulunci yace abokan iyayen mu iyayen mu ne. Idan sunga munyi wani abu ba daidai ba zasu iya kiranmu su mana gyara.. Idan ma ta kama su tsawatar mana duk zasuyi.. Haka ne. Nan ma jinjina kai Haidar yai. Alhaji Gimba yace  Ma sha Allah. wato Haidar, mahaifinka ya sanar Dani abinda ke faruwa, ba wai dan ya bud e min sirrinka ba sai dan so da yake a samo maslaha. "

Haidar yai shiru yana sauraronsa.

"Alhaji Gimba yaci gaba  Wato shi Aure wani abu ne da yakeda mahimmanci Haidar a rayuwar Al umma gaba d aya. Dalilai da dama suna sawa ayi aure haka dalilai da dama Suna sawa Aure ya mutu Wanda ba a so. Daga cikin dalilan mun sani Aure ibadah ne bautan Allah ne kuma d abbaka sunnnar Ma aiki (SAW) sann duk Wanda ya d auki aure matsayin ibada bautan Allah zai samu dacewa da tsira harma da farin ciki a cikinta. Hakan nan Aure yana sa kamewa daga fad awa tarkon zinace zinace. Kaman yanda yazo a hadisin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara yarda a garesu. Yanda Manzo (SAW) yace yaku taron samari ga Wanda ya samu iko daga cikinku yayi aure. Shi aure yana tsare gani sann yana kame al aura. Har yake cewa ga Wanda bai samu hali ba toh yayi azumi. Shi azumi garkuwa ne.. Sann dalili na gaba samun nagartacciyar Al umma. Ta hanyar Aure ake haihuwa a samu Al umma nagartacciya. Bazamu fad ad a ba amma kaga ko wad ann muka d auka Sun ishemu dalili. Haka zalika shi Auren nan ba a barmu kara zube ba saida aka koyar damu yanda zamu zauna cikinta ta fuskar shari a da koyarwar addini. Ta yanda d aya bazai zalunci d aya ba a cikin zamantakewar. Domin kuwa addinin musulunci addini ne mai kyau da tsari da kuma adalci. Haka zalika idan rabuwar Aure ta kama dole, Wanda ba a fata toh nan ma saida aka koyar damu yanda zamu rabu bisa kyautatawa da mutuntawa. Ya dan gyara zamansa kafin yaci gaba  In Islam, it is believed that married life should be filled with mercy, compassion and tranquility. Sann Zaman aure zo mu zauna ne zo mu sab a.. Ko harshe da hakori watarana ana samun mishkila.. Toh idan an samu sab ani ba haka kawai ake saki ba sabida girman al amarin.. Akwai hikima da musulunci ya saka saki hannun namiji. Dan idan mace ne zakuyi fad a sau d aya amma tana iya cewa ka saketa sau dubu. Kaga tunaninta da naka ba d aya bane.. Hangen nesanka da nata ba d aya bane.. Kai ko a halitta ta fuskar k iran jiki kaida ita ba d aya bane. Ita haka Allah ya halicceta mai rauni kai kuma mai jurewa. So idan al amara irin wann suka taso endurance dinka da tolerance d inka ya kamata yafi nata. Idan an samu rashin fahimta ko matsala a zamantakewa a tsakanin. Kuyi k ok arin samo maslaha tsakaninku ba sai third party ya shigo ba, idan kukai trying a tsakaninku still ba a samu maslaha ba sai a saka manya ciki dan amfani manyan kenan. Bama a fata har takaiga zuwa gaban manya toh amma idan ya zama ba mafita sai a mik a matsalar gaban magabata. Idan ya gagara a mik a matsalar gaban jagororin Al umma wato malamai. Idan shima baiyi working ba toh fah ka sani duk yanda ake son wani Auren rabuwan shi yafi alkhairi. Sann idan Allah ya k addari ba sauran zama dole za a rabu.. Toh sai a rabu cikin mutuntawa da kyautatawa.. Ya dan gyara zamansa  Shin ya ma ake sakin.? Saki yana"

"nufin furtawa. Intention na saki ba saki bane. Idan kace ma matarka zan sakeki, wann ba saki bane.. I intend to divorce you, this is not a divorce. I think we should get separated, this is not a divorce either.. It has to be a statement or a verb. In the sense that Na sakeki, .. Or you are divorced. Shikenan ta saku. Shi da yayi sakin yanada chances na kome guda biyu, idan yayi na uku babu kome Har sai ta auri wani mijin bashi ba. Idan miji ya saki matarsa sau d aya, meaning one down two to go. Sann Anfi so matar ta zauna gidan mijin tayi iddarta. Akwai hikima da musulunci yace ayi hakan. Dan a wann zaman zai iya maida matarsa kuma ta maidu ba sai anje ana biko da sauransu ba. Menene Iddah.? Shine waiting period after the divorce. Ga macen da batada juna biyu iddah period dinta shine 3 monthly cycles.. If she s too old like If she s in her menopause ma ana wacce ta daina Al ada ko kuma yarinya k arama wacce bata fara ba their iddah period is 3 months.. Idan mata mai juna biyu ce kuma iddarta shine ta haihu.. And this may be 2 months, 3months, 7months.. Depending on her pregnancy. Sai ya dan gyara zamansa  Now, it is prohibited for a man to divorce his wife a lokacin da take al ada, or when she s in the state of purity yet he had intercourse with her in that state of purity. An hana saki a wad an nan lokutan. Wann shine saki na bidi a. Innovated divorce. Mafi rinjaye Sun tafi akan it is sinful but valid. Ma ana kuskure ne hakan amma matar ta saku. Idan mutum zai saki matarsa. God forbid, yet they had intimacy few days, few weeks ago. Musulunci yace he waits until she gets her menses. Idan tai tsarki ba a samu intimacy ba sann sai ya saketa. Kaga zai wahala ma yayi sakin idan har zai jira wann lokacin. Amma da yawa hakan baya faruwa sabida mafiya yawan sake sake cikin b acin rai akeyi. Akwai hikima cikin duk abinda musulunci yayi umarni ko yayi hani.. "

Yaci gaba da bayani kan hukunce hukunce da hakkoki Haidar na saurarensa.. Har ya fara tuna nashi sakin da matarsa Wanda sun samu intimacy kafin ya saketa. Ya lumshe idonsa kad an yana karanto istigfari. Har saida ya sinkayo muryar Alhaji Gimba yana tambayarsa  Be open with me Haidar. Shin kana son matarka.?

Haidar ya jinjina masa kai  I love her with my life Uncle& But..

 There s no but if you truly love her..

"Jiki a sanyaye Haidar ya girgiza Kai yace  I choose to be the problem Uncle.. I choose to carry the burden.. Ya dan girgiza kai a hankali  Mahaifiyata ta wahala sosai.. Tanada kurakurenta, but.. I can t let her carry it all alone.. Bazan iya barinta ita kad ai ta fuskanci matsalar ba sabida ita din ta fahimci kuskuren ta kuma ta tuba. Yaci gaba da jinjina Kai  I choose to be her shield in this.. Idan hakan na nufin sitirta kuskurenta, even if it would destroy me.! Ya k arashe cikin yanayi mai ban tausayi."

Alhaji Gimba ya dubesa cikeda tausayawa. Yanada masaniya gameda family issue da ahalin Aminin nasa suka fuskanta. Yau Haidar ne yake sacrificing farin cikinsa sabida mahaifyarsa lallai rayuwa ta sauya kuma Haidar ya cika D an da za ayi alfahari dashi. Sai yaci gaba da jinjina Kai a hankali murmushin saman fuskarsa yake duban Haidar d in.

" Idan na fahimceka Haidar, kayi komai ne sabida mahaifiyarka. Kuma duk d a nagari irin haka zaiyi.. Ba ina nufin sakin ba. Ya d anyi gyaran murya  Ka zab i ka sadaukar da farin cikinka sabida mahaifyarka.. Amma rabuwa da iyalinka bazai zama mafita ba. Bansan menene wann kuskure na mahaifyarka da Kake son sitirtawa ba, ka sani duk Wanda Ya rufa asirin wani musulmi Allah zai rufa nasa ranar gobe balle Mahaifiya. Saidai akwai hanyoyi da dama da ake bi dan shawo kan matsala. You can t let yourself be destroyed in the process.. Because Destruction is not the solution and it will never be. Mahaifyarka sai tafi shiga tashin hankalin idan har hakan yai destroying d inka. You are a man, and you supposed to act like one.. Be brave enough to face your problems..Kar ka guje ma matsalolinka dan idan ka guje masu zasu bibiyeka ne har k arshen rayuwarka. Ya dan numfasa  I ll ask you this question again, do you love your wife.? "

"Dubansa kurum Haidar keyi, ya shiga jinjina Kai ba tareda ya iya furta koda kalma ba."

"Alhaji Gimba ya jinjina Kai  Then what are you waiting for, go and reconcile with your wife. Kaje ka dawo da iyalinka. "

Sai Haidar ya d anyi shiru yana tunanin irin k iyayyar da ya hango a kwayar idanun Ummul. Ya sani a halin yanzu Babu abinda tafi tsana Watak ila sama dashi.

Jin yayi shiru yasa Alhaji Gimba murmusawa yace  Bansan Aliyu da rashin k warin gwiwa ba dukda ance rauni na cikin soyayya. Ya k arashe cikeda barkwanci.

"Sai Haidar ya d an k ak aro murmushi yana jinjina Kansa  In sha Allah Uncle, zan dawo da ita. Kuma bazan tab a sarewa ba. Na gode k warai.. Allah ya saka da alkhairi ya k ara girma. "

Alhaji Gimba ya murmusa  Yanzu naji Zaki na magana. Allah ya maka albarka ya mana jagora.

Haidar ya amsa da Ameen had ida k ara godiya ma Alhaji Gimba.

Alhaji Gimba ya mik e suka jera zuwa motan Haidar a tare tamkar yana ma Haidar d in rakiya.

"Haidar bai tab a tsammanin rana irin wann zata zo ba. Mutumin da a baya yake masa kallon tarayyarsa da mahaifinsa babu wani alfanu. Mutumin da yai masa mummunar fahimta a baya. Sai gashi yau wann mutumin ya zamto tamkar mutumin da ya jefa masa igiya cikin rijiya mai duhuwa yace ya kama ya fito. Tabbas zaka k i wani abu wann abun alkhairi ne a gareka, zaka so wani abu wann abun sharri ne a gareka."

Fatan alkhairi Alhaji Gimba ya kuma yi ma Haidar d in. Ya kuma ce a duk lokacin da wani abu ya shige masa duhu ko yake nema shawari his door is always open yazo ya samesa matsayin Uba a wajensa. Godiya Haidar ya kuma masa cikeda girmamawa kafin ya wuce.

Tinda ya fito daga gidan Alhaji Gimba yake ji kaman ya k ara masa k warin gwiwa ne.. Yayi alk awarin zai jira Ummul Har tayi healing koda zai d aukesa tsawon shekaru ne.. Amma yau da Alhaji Gimba ya nusar dashi zai iya wasa da damarsa sai yaji bazai iya jira ba. Zai tafi yayi yak in dawo da Ummul cikin rayuwarsa da taimakon Allah.

Washe gari sassafe yai shiri da zummar d aukan hanya garin Kano. Ya shigo ya gaida iyayensa sann ya k arada

" Daddy, Mommy.. Ina so zan tafi garin Kano yanzu.. Zanje na dawo da Khairy. "

Farin cikin Mommy ya gaza b uya. Duk a  yan kwanakin ta kula ko zancen Haidar baiso a masa sai gashi yau yace zaije ya dawo da matarsa. Suka saka masa albarka tareda fatan alkhairi.

Daddy ya dakatar dashi.

Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yace da Haidar ya jirasa a mota yana nan fitowa.

Mommy tace  Engr. Ya naga ka tsayar dashi..?

"Ya murmus  With your permission Rankidad e, I m going with him.. I want to be a father to my son.. "

Har k walla saida suka ciko idon Mommy. Ta tuna farkon Auren Haidar da Ummul d in Daddy cewa yai ba hannunsa ba ruwansa tayi yanda take so da rayuwar D anta. Yau sai gashi ya saka kansa tsamo tsamo a al amarin Haidar d in.

Ta murmusa tace  Toh kodai nima nayo muku rakiyar ne.?

Daddy ya girgiza Kai yana d aura wristwatch d insa  A a wann tafiya ce tamu ta maza. Daga baya sai kiyi naki.

Murmushi kawai Mommy tai ta musu fatan sauk a lafiya baida dacewa.

**

Koda suka isa garin Kano sun samu an kaisu Har k ofar gidan Malam Isubu mai Manja kaman yanda aka fi saninsa.

"A farfajiyan gidan aka saka masu tabarma daga nan k ofan su Ummul d in dan Tani bata bari  yanuwan Mahaifin Ummul da suke uba d aya Wanda suka amshe kudi hannun Asshe farkon Auren Ummul d in sun shiga cikin maganar ba, sanin abinda ka iya zuwa yazo. Dukda maganan na maza ne amma kamawa take Shiyasa tazo wajen tinda tasan da cewa akan kudi ba abinda su d in bazasuyi ba. Sann basu san da mutuwar Auren Ummul d in ba. Bayan sun gaisa Nan take sanar dasu Daddy har kawo wann ranan basu saka Ummulkhairi a idonsu ba. Sun bincika duk yanda ya kamata amma babu labarinta."

Haidar ya dubeta cikin shock  Khairy bata nan..? Toh ina take.?

Tani ta sauk e ajiyan zuciya  Duk yanda ya kamata mu bincika gidan  yanuwa da zuri a mun bincika amma Babu labarinta. Tin a lokacin naso mu koma mu sanar daku halinda ake ciki amma mahaifiyarta tak i hakan. Ta d auki duk laifin ta aza ma kanta..A cewarta wann hukuncinta ne take karb a.. Sannan har rana mai kaman wann Mahaifin Ummulkhairi dake cikin jinya baisan Aurenta ya mutu ba.. An dai sanar dashi tayi Aure a haka yana jinyar amma baisan da wann labarin ba dan jinyar tashi abu ne da ya danganci zuciya. Likitoci suna bada shawarin ba komai za a sanar dashi kai tsaye ba duba da irin yanayin jinyar. Sann baisan da cewa mu kanmu bamu san yanda Ummulkhairi take ba.

Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban Daddy  This is all my fault Daddy.. Duka laifina ne.. Daddy idan na rasa Khairy.. Bansan ya zanyi ba.. Ya k arashe cikin tsananin nuna damuwa.

Daddy bai kaiga furta kalma ba Azeema ta fito da murmushi saman fuskarta. Kai tsaye ta furta  Bazaka rasa  Yaruwata ba Sirkinmu Dangayu. Domin kudin kuna son junanku.. Naga haka a k wayan idonku..  Yaruwata.. Bata kai aya ba Khulsum ta fito da sauri dan dama tin baya dawowar su Umma daga Abuja suka d auko Khulsum da Abba daga gidan Inna Dije. Tani ta kuma d inke bakin Inna Dije da fad in idan taji fit wani abu ya fita daga bakinta ya karad e dangi gameda Auren Ummul toh ta tabbata itama nata Auren ya Mutu kenan sann itada D anuwanta Malam Isubu har abada.

Khulsum ta girgiza kai tana duban Azeema  Kiyi shiru Azeema..

Duk sai suka maida dubansu ga Khulsum da Azeema.

Azeema tace  Khulsum ki k yaleni na sanar dasu.. Baki gani ne Yayanmu naso ya maida matarsa.. Meyasa bazaki bari a sanar dasu ba..

Khulsum na huci tace  Sabida  Yaruwata tace bata so a sanar dashi.. Sabida ita d in bazata tab a komawa gareshi ba. Ta k arashe hawaye na gangaro mata.

"Haidar da baisan tuni ya mik e tsaye ba ya isa gaban Khulsum yana girgiza kai  Kinsan yanda Khairy take..? Tell me, where is she.. Where can I find her.? "

Ta dubesa sai ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye.

"Haidar ya kuma jefo mata tambaya  Please tell me, kinsan yanda take..? Ina take.. Dan Allah ki sanar dani.. "

Azeema tace  Bazata sanar dakai ba. Dan nima bata sanar Dani ba.. Kaf gidan nan

74 / 103