AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   32 / 103

93K to 96K   out of 306.8K words

fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a sauk ak e.

Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k are mata kallo taga me take dashi haka da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.

A b angaren Asshe kuwa sauk e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb o ta coge kud ad e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had a ba k aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta amaryarsa yarinyar Sa ar Anisa ke cinye kud in harta da yawon k asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d inta da auren d an  yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab a bari Kwaise tasan gaskiyan al amari ba.

Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad ai. Ji take tamkar cin fuska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad an kafin ta nufi sama.

Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had ida juya ido  Seriously.! Da gaske kina nan kina k unk ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab in cincin dan ba mijin da zai bud e wann fuskar naki.! Ta k arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.

Damm! Haka k irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*24*

*©þSameena Aleeyou& *

Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa. Ta sani bata tsammaci farin ciki cikin Auren ba. Kaman yanda bata tab a mafarkin akwai wani rayuwa mai dad i gaba gareta ba. Saidai tafi zaton tashin hankalin daga wajen mijin. Tinda mutum ne da ko saninsa batai ba. Sann shima bata tunanin ya santa.

Ta d ago a sanyaye tana duban Anisa dake ci gaba da aika mata mugun kallo.

Anisa bata daina sakin huci ba ta finciko Ummul ta tadata tsaye  Tashi makira. Sai wani sanne fuska kike tinda kikazo. Irinku kunfi kowa iya makirci. Ta shiga zagaye Ummulkhairi dake tsaye tana k are mata kallo. Sai ta tab e baki dan ido ba mudu ba yasan kima. Dukda nad e take cikin lafaya tasan ko kusa bazasu zo d aya ba. Hasalima Anisar bazata nuna mata komai ba face farin fata.

"Anisa ta rausayar da ido cikeda takaici. Tai tsaye gaban Ummul wacce Har lokacin ko motsawa batai ba  Kar kiyi tunanin zaki tadda farin ciki a wann gidan dan kinyi nasaran saye zuciyar Mommy. Bariki ji na fad a Miki wani abu. Mommy mace ce da take tamkar Hawainiya.. Babu wuya ta canza launi. And Haidar.? Ta kuma sakin murmushi tana ci gaba da zagaye Ummul  Hello, I m sorry to say sai kin gwammaci mutuwa da auren wann miskilin. Bansan dalilinki na amince ma aurensa ba amma ina mai tabbatar Miki Kinyi babban ganganci. You ve made a grave mistake, because Haidar Maitama would never ever fall for someone like you.! Ta k arashe muguwar murmushi saman fuskarta ga wani wulak antaccen kallo da take bin Ummul d in dashi."

Saida ta gama juye ma Ummulkhairi buhu buhun wulak anci kafin tasa kai zata fice.

Ummul ta sakar mata murmushi tace cikin sanyin muryarta  Baki sanar Dani sunanki ba.

Anisa ta kalleta a dak ile  Mai sanin sunana zai miki.?

Ummul ta kuma murmusawa  Sanin suna nada mahimmanci ko dan hakkin zamantakewa. Allah yasa hakan ba matsala bane.

Anisa ta tsareta da ido tana kallon salon makirci daga wajen wann bagidajiyar. sai kuma ta girgiza kai tana rolling eyes  I don t have your time.

Har tasa kai zata fice ta sinkayo muryar Ummul  Ina tunanin tinda har kika tako yanda nake kinada lokaci na. Tai maganar murmushi saman pale face d inta da taci kuka.

Anisa ta kuma dubanta da mamaki. Wanda mamakin Ya hanata magana. Bata tsammaci maganganu irin wad ann daga bakin bagidajiyar Amaryar Haidar ba.

Ganin tayi sakare yasa Ummul kuma murmusawa ta k araso kusanta  Ni sunana Ummulkhairi.. Watak ila nasan kin sani Shiyasa baki tambaya ba. Har lokacin sassanyar murmushi ne saman fuskarta Wanda ba k aramin tunzura Anisa ya kuma yi ba.

Ganin Anisa tayi Shiru yasa Ummul katse shirun da fad in  Yauwa gwara da Allah yasa kika shigo.. Dan Allah ina ne band aki wllhi tun d azu nake so na tashi nayi sallan isha amma bansan ta ina zan shiga ba.

"Hararta Anisa tai daga sama zuwa k asa  Ina Miki kashedi, kar ki kuskura ki shiga d akin cen. Dan wann d akin d akin Haidar ne. Ta k arashe tana nuni da d akin."

Ummul ta murmusa kad an  Ok haka na nufin wancan kenan zan shiga. Tai nuni da d aya k ofar.

Takaici ya kuma cika Anisa ganin da gaske Ummul bata d auketa da zafi ba. Taja tsaki tana juya ido kafin tasa kai zata fice.

Ummul Tai saurin dakatar da ita  Kinga. Anisa ta juyo tana dubanta a dak ile.

 Na gode. Tai maganar har lokacin kyakkyawan murmushin ne saman fuskarta wanda ko shakka babu k ok arin b oye tashin hankalin dake saman sa take.

Wani tsakin Anisa ta kumayi kafin tasa kai ta fice a fusace.

"Sauk e ajiyan zuciya Ummul tai tana mai hamdala cikin zuciyarta. Dan da dai tai tozali da mijin da aka aura mata, gwara taita karo da wann figaggiyar. Dan idan fad a da tashin hankali ne zata iya cewa cikinsa ta girma. Amma miji bata san mai zata tarar ba. Bata san wani irin k alubale zata fuskanta tare da shi ba. Haka zalik a zuciyarta Sam ya gaza natsuwa dukda kwantar mata da hankali da mahaifiyarsa tai. Ta kuma sauk e ajiyan zuciya a hankali kafin tasa kai ta nufi d aya d akin hagu da wanda Anisa tai nuni dashi matsayin na Haidar."

Kaman mai tsoron shiga haka ta tura k ofar. Zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Sai addu an neman samun salama had ida natsuwa take cikin zuciyarta take. D aki ne mai matuk ar kyau da tsari komai na ciki sabo ne dal da alama. Tai tsaye sororo tana duban d akin dan ita dai bata San ta ina zata fara ba. Abinda ta soma tunowa shine gadon baccinsu ita da  yaruwarta Khulsum. Shikenan Sun rabu. Ta rabu da kowa nata kenan kaman yanda Umma ta umarceta. Shikenan ba ita ba danginta. Wani hali Abba yake ciki.? Yaya yanayin k arfin jikinsa.? Umma ta mata iyaka dasu gaba d aya tace ko a waya kar ta nemesu idan har ita ta haifeta. Sai taji k afafunta Sun gaza d aukarta. Nan ta silale wajen kuka na zuwa mata gadan gadan.

**

Kano&

Har ta kwanta wajajen misalin k arfe shad aya na dare taji ana buga mata k ofa. Ta mik e da kyar tana mamakin waye haka cikin daren nan. Bata kawo kowa ba sai Khulsum tinda ita ce tazo mata cikin dare irin haka a kwanan baya.

Ta k araso tana tambayar wanene lokaci guda tana ci gaba da fad in Khulsum kece nan wajen.

Ga tsananin mamakinta muryar D anta Hisham taji. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa.

 Hisham.! Ta furta a hankali

Hisham yace  Hajja ni ne.

Ta bud e k ofan tana dubansa da mamaki  Lafiya kai kuma cikin daren nan.. Watau bazaka daina irin wann tafiyar naka ba ko.

Murmushi Hisham keyi yana duban mahaifiyar tasa  Haba Hajjata tarban da za a min kenan. Hajja ko shigowa gidan banyi ba fah balle na sha ruwa balle mujega gaisuwa.

K wafa tai tana dubansa kafin tasa kai ta shige tana ci gaba da sababin yanda ya maida tafiyan dare d abi arsa.

Hisham ya maida k ofan ya rufe kafin ya take mata baya yana fad in Allah ya huci Zuciyar Mamanshi tuba yake.

Sukai zaune a parlor suna gaisawa bayan ta gama sillesa tas kan yanda ya maida tafiyar dare jiki musamman duba da yanayin hanoyin a yanzu.

Hisham ya tsareta da ido. Shi sai lokacin yake hango rama tattare da ita.

Ta d an kuma dubansa  Waima mai Ya dawo dakai ne.? Inji baka jima da komawa bakin aikin ba. Kai da kanka kace kunada babban project a kampanin ku zaka tara hankalinka waje d aya. Toh me ka dawo yi.?

 Hajjah.. Ya kira sunanta a hankali.

Sai ta d ago ta dubesa ganin sosai ya tara hankalinsa.

 Wani abu ya faru ne da bana nan.?

Tambayar da yai mata sai taji tamkar yana sane da cewa Ummul tayi aure ne kuma ba kowa ta aura ba face D anuwansa da suke Uba d aya. Ji tayi kaman d an nata Ya riga yasan sirrin da ta jima tana b oye masa.

Ta girgiza kai a d an daburce  Mai ka gani.. Kaga ni bacci nake ka katse min. Ko ma meye mayi magana da safe. Tashi kaje ga abinci a kitchen sai kai warming kaci tinda kai ka so zuwa cikin dare. Idan bai maka ba kasha ruwan shayi dama abinda ka Saba kenan.

Hisham Ya girgiza kai. Tana k ok arin mik ewa yai saurin k arasawa Ya rik e hannunta  Hajjah you look sick. Kinyi ciwo ne sanda bana nan..?

Ta sauk e ajiyan zuciya jin ba Ummul ya tambayeta ba wanda ba grin Allah da zai waye suyi waya bai tambayeta ita ba. Yaso karb an lambar wayarta ma sai Hajjan ta sanar dashi Ummul batada waya. Yaita mamakin ya za ace budurwa kaman Ummul ba waya a hannunta.

 Eh.. eh nayi dan zazzabin nan da ake fama dashi. Amma bai wani tsanani ba. Shiyasa ma ban sanar dakai ba gudun kar ka tashin hankalinka ka d ago k afa kazo. naji sauk i Alhamdulillah.

Hisham Ya girgiza kai  Haba Hajjah. Har kiyi ciwo ban sani ba.. Hajja a duniyar nan sabida wa nake neman duk abinda nake nema. Hajja sabida kece.. Lafiyarki na gaba da komai da kuma kowa. You are my number one priority kin sani.. ya kuma girgiza kai  Da ace wani abu ya faru dake da bazan tab a yafe ma kaina ba. Ya k arashe fuskarsa fal damuwa.

Sai ta k ura ma d an nata ido ganin yanda hankalinsa ya matuk ar tashi a sabida ita. Koda duka duniya zasuyi rejecting d insa zata so shi ta k aunace shi domin kuwa Hisham d inta definition ne na d a na gari a idonta.

Ta d an dungureshi  Silly. Ba abinda zai sameni da izinin Allah sai naga  ya yanka.

Ya murmusa yana duban mahaifiyar tasa cikeda so da k auna  And very soon zaki gansu in sha Allah. Dan wann karon na d au d amaran neman aure da gaske. Bazan koma ba sai na tabbata an bani ita. Ya k arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.

Zuciyarta yai wani irin tsinkewa. Take annurin fuskarta ya d auke cak. Ta soma k ok arin kauda fuskarta dan bata so su had a ido. Hasalima bata san ta yanda zata soma sanar dashi labarin Auren Ummul ba. Shin da wanne zata fara.? Cewa Ummul tayi aure ko kuma D anuwansa da baisan yana dashi ba ta aura. Shin mahaifinsa tasowa yai daga kabari kokuwa dai yana raye tintinin.

Zata mik e Hisham yai saurin dakatar da ita ganin gaba d aya yanayinta Ya sauya tashi guda  Hajja na fad i wani abu ne da bai dace ba.?

Girgiza masa kai tai  Hisham kaje ka kwanta dare yayi. Tana fad in haka ta mik e ta shige d aki ta barsa nan wajen yana sak e sak e. Fatansa Allah sa dai lafiya ba wani abun bane ya faru. Jiki babu wani kuzari Ya mik e Ya nufi nasa d akin.

**

Washe gari Inna Dije bata Ida warwarewa ba sai a cikin mota bayan Sun d auki hanya sunyi nisa. Ita kad ai sai layi take dan baccin bai saketa ba. Haka Asshe da Anisa suka turata cikin mota. Ko zarafin Sallama da Ummul basu barta tayi ba.

Saida sukai nisa Abadan kafin Inna Dije ta ida warwarewa. Ta dubi Asshe dake gefenta da mamaki tana kuma duban cikin motar.

Asshe ta karyi goron dake hannunta dan galibi idan zatai tafiya mai tsawo da goronta cikin jaka. Ta murmusa tana duban Inna Dije  Barka da safiya K awalliya.

Inna Dije ta kuma dubanta da mamaki sai lokacin take tuno duk abubuwan da suka faru.

Asshe ta murmusa had ida mik a mata goro  Karb i ki karya kumallo.

Inna Dije kallon mamaki kurum take ma Asshe Har lokacin. Ta dubi goron da take mik a mata  Kin bani k waya cikin dare yanzu zaki had a min da goro ki k arasa kasheni. Makira algunguma.!

Asshe ta dara kad an  Haba K awalliya wasa fah ake bugawa. Da sauran lokaci ai ba a gama ba. Kika sani ko anjima ki lallasa ni.

Inna Dije tace  Ina muke..?

Asshe ta kuma karyar goronta  Kar ki damu mun kusa isa gida nasa a shirya Miki karin kumammalo mai kyau gudun kar kiyi mutuwar bakin al muru.

Inna Dije ta girgiza kanta Wanda Har lokacin nauyi Ya mata  Yanzu sabida rashin imani naki Asshe shine kika bugar dani ko sallan asuba banyi ba kika nad oni kika saka cikin mota.. Toh ina jakan kayana.?

Asshe ta tab e baki  Buhun tsummokaranki zakice. Wari suke min a mota nai watsi dasu. Kar ki damu sabbi suna jiranki idan mun isa. Yanzu bari a samu waje a tsaya kiyi sallah tinda kin dawo hayyacinki.

Inna Dije sai kallon mamaki take ma Asshe dan ta fara zarce tunaninta.

Koda suka iso Kano kai tsaye gidan Asshe suka nufa. Inna Dije ta samu ta saka abu cikinta sann tai wanka aka bata tufafi ta canza.

Asshe ta k araso tana dubanta lokaci guda tana tinda ransa Suwaiba ta soma zuwa gidan.

Murmushi ta sakar mata ganin ta shirya tsaf  Ko kefa K awalliya. Kin ganki kuwa..

Inna Dije ta d aga mata hannu alamun dakatarwa  Ke ni fah ba Suwaiba bace. Babu wani makircinki da zai bani tsoro. Bazan bari na sake fad awa tarkonki ba. Mijina baisan nayi tafiya ba a nasa tunanin ina tare ne da d a uwana. Ni ba ballagaza bace kaman Suwaiba.

Asshe ta murmusa  Ashe duk kanwar ja ce.

 Mai kika ce.? Inna Dije ta katseta.

Asshe ta kuma murmusawa  A a K awalliya cewa nai idan kin gama Hilal sai ya kaiki masaukin ki.

Zata fice kenan Inna Dije ta janyota. Saitin kunnenta take rad a mata  Kinyi kuskure tinda kika kaini naga gidan. Watak ila kin lashe wasan a wann karon. Amma ki kiyayi karawa na gaba. Abun bazai miki da kyau ba. K walliya. Ta k arashe harda kashe ma Asshe ido.

Sai Asshe ta murmusa su duka biyun suna k are ma juna kallo.

 Kar ki damu na Miki alkawarin babu had uwa na gaba. Dan kafin wann lokacin zan tabbata  yarku ta fice daga rayuwar D anmu. K awalliya. Asshe tace tana mai ficewa. Lokaci guda ta kira Hilal Tai masa

32 / 103