AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   78 / 103

231K to 234K   out of 306.8K words

shigo ta tadda shi tareda  yan committee suna jajanta masa abinda ya faru da tambayarsa yanda abin ya kasance.

"Hisham dake kwance da d inkakken ciki nan yake labarta ma yan committee cewa yaje taimakon wani yaro ne suka soka masa wuk a. Hajja ta lumshe idonta tausayi da k aunan D an nata na ninkuwa cikin zuciyarta. Allah sarki, shidai kamar ko Yaushe cikin taimakon Al umma yake. Ashe silan tsautsayin da Ya auka masa taimako yaje kaman yanda tai tsammani."

Ta k araso suna gaisawa da shugaban committee yanda yake sanar dasu ana kan k ok arin kama yaran dan a hukuntasu sabida rashin hukuntasu da ake yasa suke abinda suka so cikin Al umma.

Hajja ta girgiza kai tana amsawa. Ta k arada  Allah dai ya shirya mana zuri a amma al amarin dad a ta azzara yake.

Shugaba ya girgiza Kai yace  Sai ka rasa ina matsalar take. Shin iyayen ne ko kuwa dai halin yau da muka tsinci kanmu ciki ne. Wai nan abinda suka fito sunayi na tada hankalin Al umma sunansa shara. Ko mai suka gani sai Sun lahanta.. Yara k anana samari da basu wuce ace suna makaranta ba.

Hajja ta jinjina kai  D an yau ne ka haifesa baka haifi halinsa ba.

Ya jinjina Kai  Tabbas akwai jarabawa a wasu lokutan kuma sakaci na iyaye. Mutum karma ka haifo yaran da bazaka iya kula dasu ba yaran da bazaka iya basu tarbiya. Tarbiya Ya k unshi kula da d aukan nauyi tareda sauk e wasu hakkoki da suka ratayu wuyan iyaye. Sai kaga mutum matansa hud u d akuna hud u gareshi wani ma gidan haya ne. Kai shekaran jiya aka kawo mana wani case d aki d aya aka raba da labule aka aje mata biyu labule ne kawai Ya rabasu. Ina addini cikin wann al amarin. Ga yaran nan haifo su ake ba mai zuwa makarantan islama balle na boko.. Ta ya za a ce kana mutum mai hankali da Allah Ya halicceka da k wak walwa bakada tsari a rayuwarka.? Haka zakiga yaran Sun girma wasu ma a mak ota suke kwana dan babu d akin kwanansu a gidan mahaifinsu. Yarinya budurwa ace ita zata nemo ma kanta abinci ubanta mahaifi na nan da rai amma baisan yaya d iyarsa take cin abinci ba. Kuma zaki samu bai fasa aure ba bai fasa haifo wasu yaran ba.. An bar yara kara zube an jefa rayuwarsu

cikin garari Tun suna k anana. Ta ya za a tsammaci Al umma mai nagarta da irin wann tauye hakki da ake ma wad ann yaran da tuni Sun zama victims of circumstances.

Hajja ta jinjina Kai  Haka ne Suhaga.. Da yawa an sha afa da hakkin yara na iyayen kawai ake hangowa. Tabbas iyaye sunada girman hakki akan  ya yansu wanda bayan biyayya ga Allah da manzonsa sune suka biyo baya. Amma sai muna mance kafin mu Gina irin wad ann yaran sai mun fara sauke nauyi da hakki nasu dake rataye wuyanmu Wanda za a tambayemu akai. Dole mutum yai k ok arin Gina yau dinsa da kyau dan gobensa Ya inganta. Allah ya iyar mana da tarbiyar yaranmu ya bamu ikon sauke nauyi na zama iyaye da ratayu wuyanmu gwargwadon iko.

Suka jinjina kai suna amsawa da Ameen.

Ummul dake mak ale daga k ofa ta juya da baya a hankali ta nemi waje ta zauna tana tunanin nan zuwa wani lokaci kadan wann nauyin zai hau kanta. Cikin zuciyarta take addu an Allah Ya iya mata Ya dafa mata Ya bata ikon sauke nauyin dake gab hawa kanta.

**

Gaba d aya hankulansu ya karkarta ya koma ga jinyar Hisham. Daga Hajja Har Ummul Sun aje zancen tafiyar Ummulkhair Kano. Zuciyar Hisham fari tas dan dama wann dalili yasa yai ma kansa abinda yai. Ya d auki wann risk din dan ya karkatar da tunaninsu da hankulansu. Sunyi waya da Haidar ya sanar dashi cewa Sun tafi da mahaifiyarsa can wani k auye ne garin magani Shiyasa bai samu komowa bakin aiki ba. Sam Hisham bai sanar da Haidar cewa shine baida lafiya ba.

Haidar yai shiru yana saurarensa sai kuma yace  Amma.. Meyasa baza a kawo ta nan Abuja Asibiti ba Hisham. Idan ta kama a fitar da ita meyasa bazaa fitar da ita ba..? I see no reason da zaisa ka dauki mahaifyarka ka kaita wani jeji da sunan neman magani.. Meye amfanin karatun ka ne wai.?

Hisham Ya k ak aro murmushi  Engr kenan. Kasan ku yan bokon nan kunyi imani da boko amma ita Hajja tafi son na gargajiyan kuma kasan ance magani dace. Yana maganar yana tamke fuskarsa sabida zogi da yake ji.

Haidar Ya jinjina kai ba tareda yace komai ba.

Hisham ya k arada  Nace.. Ya labarin Ummulkhair kuwa..? How have you been coping..?

Haidar ya dan lumshe ido had ida furzar da huci kadan  Every minute passes by feels like a century& 

Cikeda nuna kulawa Hisham yace  Haidar I m sorry.. I m so sorry brother bana tareda kai a irin wann lokaci mai matuk ar wahala.

Haidar ya katsesa  You have your own problems to deal with Hisham. Ya danyi fasali kafin yaci gaba  Abu d aya da nakeda yak ini is that I will find Khairy& I will definitely find her no matter the cost& I will never give up.!

Yanda yake maganar with so much courage and determination sosai ya haifar ma Hisham fad uwan gaba. Ya had iyi miyau da kyar kafin ya k ak aro murmushi yace  I trust you Abokina. The word giving up has never been in your vocabulary.. Keep searching until you find her.

Haidar baice dashi komai ba sai duban Anisa dake tunkaro yanda yake da yai. Taci Uwar ado kaman mai zuwa gidan biki. Sai yace da Hisham  We talk later.. Daga haka sukai sallama ya katse kiran.

Anisa ta k araso tana ci gaba da k wark warsa hannunta rik eda k aramin paranti.

Fuska d aukeda murmushi Tai masa sallama. Ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta aje masa tray din tana fad in

 Sannu da hanya. Mommy tace yanzu sauk ar daga Kano.. Ya hanya..? Ya ka baro su Ammi.?

A tak aice ya amsa mata sai gani tai ya mik e yana amsa waya Wanda ga dukkan alamu aiki Ya Shafa. Baiko bi takan ta ba ya fice yana amsa kiran.

Anisa tabi bayansa da kallo kaman zata rusa ihu. Ko kallo fah bata ishesa ba.. Tazo tana tarbansa amma ko kallanta bai ba balle yaci abinda ta kawo masa. K atutun bak in ciki Ya tokare mata mak oshi sanda ta waiga ta kalli k atoton hotonsu shida Ummul Wanda akai masu a ranar bikin tariyarsu an kafa a parlorn kaman ka kirasu su zo. Nan taji k walla ya ciko idonta ta mik e ta isa jikin hoton. Cikin zuciyarta take fad in  Meye ta fini dashi Haidar.? Meyasa bazaka mance da ita ba.? Meyasa bazaka hak ura da ita ka so ni ba. Wllhi zan maka komai matuk a kaso ni.. Ni Kai kawai nake so.. Dan Allah ka fahimce ni. Ta k arashe zancen zucin nata tana Shafa hoton daidai fuskar Haidar.

Mommy dake daga jikin staircase tanata kallonta tana karantarta daga nan yanda take tsaye.

A hanakali Mommy ta soma takowa cikin parlorn.

Anisa ta waigo da sauri tana duban Mommy. Murmushin da yafi kama da yak e ta sakar ma Mommy. Mommy ma ta maida mata Martanin murmushin.

 Sannu da sauk owa Mommy. Anisa tace tana risinawa.

Da murmushi saman fuskar Mommy ta amsa  Sannu Daughter. Sai takai dubanta ga parantin dake aje saman side table  A ah! Ina Aliyun.. Har ya fice ne wai.?

Anisa ta jinjina Kai Jiki a sanyaye  Ya fice ko ruwa bai sha ba Mommy.. Ta marairaice fuska  Mommy I m worried about him.. Bakiga yanda ya fice ba duk bashi a hayyacinsa. Ina fata a samu Ummul very soon.. Ta k arashe tana kai dubanta go hoton Haidar da Ummul fuskarta fal damuwa.

Mommy taci gaba da takowa tana jinjina Kai a hankali. Ta isa jikin pic din itama. Idonta naga hoton take fadin

 Wherever she is. I hope she s safe.

Anisa ta jinjina Kai. Cikin zuciyarta tace  Tana d aukeda jaririn ciki. Jikanki da bazan tab a bari ki sani ba. A fili kuwa sai ta kuma marairaice fuska tana duban Mommy cikeda kulawa  But.. Mommy mai zai faru idan bata dawo cikin rayuwar Haidar ba. Haka nan.. Zai k arashi rayuwarsa a gantale Mommy..? It s been three months now. Tai maganar kaman zatai kuka.

Mommy ta tsareta da ido sai ta d an girgiza Kai kadan had ida furzar da huci  I don t know Anisa.. Bayan yarinyar can da tai masa asiri bana jin Haidar Ya taba son wata mace except Ummulkhair.. Ta danyi fasali  Ban sani ba.. Kodai zai so wata a gaba kodai ni ce zan sake aura masa wata.

Anisa tai sauri ta dubi Mommy  Mommy kina nufin zaki sake aura ma Haidar wata matar idan Ummul bata dawo ba..?

Mommy ta dubeta sai tace  Why not.! Idan har a baya lokacin da bai daukan magana na da mahimmanci Ya amince da zab ina Maiyasa yanzu bazan sake zab ar masa mata ba. Matsalar kawai ban san wace zan zab o masa mai hankali kaman Ummulkhair ba..

Anisa ta sha jinin jikinta kanta a k asa.

Mommy ta kafeta Da ido sai ta gyara zama tace  But.. I have someone in mind already.. Saidai ban sani ba ko zata amince dukda itama inada iko akanta..

Anisa ta d ago a zabure tana duban Mommy. Murya har na rawa take furta  Mommy.. I don t think akwai macen da zata guje ma auren Haidar duk had uwar ta da isarta.. He s every girl s dream.

Mommy taci gaba da dubanta murmushi saman fuskarta tace  You think so.?

Anisa ta jinjina Kai  Hundred percent sure.!

Mommy ta kuma jinjina Kai  Anisa what if.. Kece wann yarinyar da nai sha awa ma D ana Haidar..

K iris ya rage Anisa bata yanki jiki ta zube k asa ba dan a bazata taji maganar Mommyn.

Tama kasa yarda da abinda kunnenta yaji mata. Ta girgiza Kai cikin rashin yarda tana duban Mommy  Mommy&

Ni..? Kike so Haidar ya Aura.?!

Mommy ta jinjina mata Kai  Why not.! Mommy tace cikeda kulawa. Ta k arada  You are his cousin sann ko da ace Ummul ta dawo gidan Haidar nasan baza a samu matsala daga wajenki ko wajenta ba.. I m sure ku biyun zaku fahimci juna& But I d have to ask you this question. Do you love Haidar..?

Anisa wacce ta koma tamkar statue baki sake take duban Mommy. Ta kasa gaskgata abinda ke faruwa. Mommy ta kuma jefa mats tambayar sai Anisa ta fashe da kuka.

Mommy ta kamo hannunta tana girgiza Kai  A a Anisa meye kuma abun kuka. Kinga idan baki sonshi bazan tak ura ki ba zan nema masa wata can daban..

Mommy bata Kai aya ba Anisa ta shiga jinjina Kai tana murmushi  Mommy kukan farin ciki ne.. I never thought a day like this would come& I mean& Not this soon& Mommy I.. I can t believe it& My dream is finally coming true.

Da tsananin mamaki Mommy ke dubanta sai ta girgiza Kai kadan tace  Do.. You love Haidar.?

 I ve always loved him Mommy.. I love him since childhood& 

Mommy tace  Aw..! wai so kike kice tuntuni kina son Haidar..?

Taci gaba da jinjina Kai yayinda farin cikinta ke ninkuwa. Tin ina yarinya nake son shi Mommy.. Kawai kun kasa fahimta ne.. But he s the love of my life..

Mommy taci gaba da jinjina Kai tana dubanta  Does your Mom know..? Asshe tasan kin jima kina son Haidar..?

Sai a nan ne Anisa ta d an ja jinin jikinta.. Sai ta girgiza Kai alamun a a  Kawai.. Ni kad ai na rik e abuna cikin zuciya.. Ko Hilal bai sani ba.

Mommy ta jinjina Kai kaman mai nazari sai kuma ta sakar ma Anisa murmushi  Yazo gidan sauk i had aku aure bazai wahala ba.

Anisa ta d an dubeta. Fuska dauke da alamun tsoro  Amma.. Mommy what if Haidar rejects the idea.. What if yak i aminta da Auren.?

Murmushi Mommy ta kuma sakar mata  Kar ki damu. Yarona Haidar mai biyayya ne.. Ko a baya baya sab a umarni na balle yanzu.. Kawai muyi fatan naki iyayen su amince musamman ma Amminki tinda har yanzu bamu koma kaman da ba.

Anisa ta waro ido tace  Haba Mommy dani da Ammi fah ke d in duka uwa ce a wajenmu.. And a halin yanzu Ammi dalilin da zaisa zumuncinku ya sak e k ulluwa take nema kinga kuwa zatafi kowa farin ciki da wann had in.. Abba kuma kinsan baida matsala tinda ba kudinsa zaa karb a ba.

Mommy taci gaba da duban Anisa mamaki bai saketa ba. Lokaci guda take jinjina Kai  Shikenan.. Zan samu Asshe da maganar..

Cikeda zak ewa Anisa tace  Toh Mommy shi kuma fah..? Ina nufin Haidar.. Ta k arashe cikeda sakarci.

Mommy ta jinjina Kai  Haidar bazai zama matsala ba dan haka kar ki samu damuwa kinji.

Anisa ta daka tsallan murna ta nufi hanyan kitchen a guje tana rangada ma ma aikatan kitchen k ira tana fad in duk su fice zatai ma mijinta abincin dare.

Mommy ta bita da kallo har ta shige kafin ta jinjina kai kadan tace  Sannu a hankali.

Daren ranan Anisa bata sama bata k asa. Sai kai komo take da sunan tana shirya ma Haidar dinner. Mommy ta shigo kitchen din tana dubanta fuska d aukeda murmushi  Iyye lallai.! Ashe d iyar tawa gwana ce wajen girki. Mommy tace tana bude dishes din da Anisa Ke shiryawa.

Anisa ta wani murmusa tana sadda kai alamun kunya.

Mommy ta kuma murmusawa  Yau kuma Mommyn taki kike jin kunya..? Kinga ni ba wata surkunta tsakaninmu ki saki jikinki Dani fiyeda yanda muke a baya.

Anisa ta kuma murmusawa  Shikenan Mommy.. I ll be open with you.. Ina so ki kaunaceni kaman yanda kika k aunaci Ummul koma fiyeda ita.

Mommy ta jinjina Kai  Ko ba Haidar ni mamarki ce Anisa. You shouldn t be hiding things from me haka ne..?

Anisa tai saurin jinjina Kai cikeda jin dadi.

Mommy tace  Good. And if you want anything.. Don t hesitate to let me know kinji koh.

Nan ma da sauri Anisa ta jinjina kai kafin Ta k arada  Mommy ni kin gama min komai a rayuwar nan& Ina jin babu wani abu da zan nema kuma da Ya wuce Auren Haidar. Duk duniya ke kadai kika fahimci mai nake ciki. For so long Ina dakon soyayyarsa Babu Wanda Ya fahimta. Sai Allah Ya share mun hawaye yasa kika fahimta.. Thank you Mommy.

Mommy ta dafa kafad arta  Anything for my Daughter..

Anisa na wangale hak wara tasa kai zata shige cikeda jin dadi.

Mommy ta tsareta da ido sai ta dan riko hannunta alamun dakatarwa  Ina kuma zakije Daughter..?

 Zanje na sake kwalliya ne kafin Haidar ya shigo.

Mommy ta girgiza mata Kai alamun a a  Bana so kina rawar k afarnan a gabansa sai ya rainaki. Ki dinga jan ajinki matsayinki na mace. And kar Ki mance Haidar baisan da zancen ba tukuna.

Anisa tai raurau da idanu had ida tab e fuska kadan. Ta dubi Mommy kaman zatai kuka  Amma Mommy zaki sanar dashi.?

Hannunta Mommy ta kamo  Taho nan kiji.

Suka zauna saman kujera. Mommy ta dubeta tace  Anisa nasan kinsan al amarin aure ba abin wasa bane. Balle Haidar dake fuskantar k alubalen rashin Ummul. Matuk a muka tunk aresa da irin wann batu a daidai wann gab ar za a iya samun matsala ne. Kinsan sa yanzu sai ya kwance mana ya koma Haidar d insa na da. Sann Daddy ma bazai yuwu muzo masa da batu irin wann a daidai wann lokaci ba. Kowa zaiga rashin dacewar hakan musamman da yake Mahaifin Ummul na nan asibiti a Abuja. Ya kamata mu bar komai har

78 / 103