AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   66 / 103

195K to 198K   out of 306.8K words

ba. Abun bai basa mamaki ba tinda yasan shidai tsakaninsa da mahaifinsa Babu komai face tsangwama tsana da kuma kyara. Amma saidai a wann lokacin abun bai masa ciwo sosai kaman a lokutan baya sanin cewa da yai ko Babu komai a halin yanzu yana tareda soyayyar mahaifiyarsa da k aunarta. Uwa uba idan Ya kalli Ummul sai yaji duk wani k unci dake zuciyarsa ke ciki ya yaye.. Bai sani ba ko tsananin sabon da sukayi a yanzu ne ke haifar masa da hakan Wanda a baya idan aka ce zai zauna da ita under same roof zai musa. Sai gashi a halin yanzu Har bacci suke cikin mayafi guda. Ya lumshe idanunsa a hankali murmushi na kufce masa.

A reception wani staff na asibitin Ya bata wani shud in folder mai d aukeda logo na Maitama Builders daga fuskarsa. cewa wani abokin aikin Haidar d in ne ya bari a bashi. Ita dai ta amsa folder d in ta nufi d aki dashi. Hisham Wanda shine ya kawo folder d in yana lab e yana kallon Ummul Har ta shige da folder d in. Cikin zuciyarsa yake furta  Saura kad an.. Saura kad an na d aukeki Ummul.. Saura kad an mu kasance tare.. Saura kad an ki kasance da masoyinki na gaskiya. Yana ida fad in haka yaja Pcap d in dake kansa ya kuma rufe face dinsa dashi kafin ya fice daga asibitin.

Haidar yai zaune yana duban folder d in Wanda ke k unshe da wasu bayanai da wani waje na rattaba hannu gameda babban aikin da suke gab da farawa da zaran ya fito daga asibiti. Long awaited project dinsu. Project d in da yai alwashin kai mahaifinsa k asa warwas dashi. Project d in da yai niyyan ruguza Maitama Builders dashi. Project d in da Ya jima yana tanadin duk wani fansa nasa kan iyayensa musamman mahaifinsa Wanda Har kawo wann lokacin basu fuskanci juna ba.

Shiru yai yana juya folder d in cikin hannunsa a hankali yake furta  You deserve this Daddy.. You deserve this.. I can t backdown now.. Ka cancanci haka Daddy.!

Ummul ta dubesa da d an mamaki ganin irin hucin da yake. Ga wani yanayi da Ya shiga tinda ta kawo masa wann folder d in Wanda ta jima bata gansa cikin irin yanayin ba. Tai k ok arin zama gefensa a d arare. Ta dubesa kaman mai tsoron magana  Lafiya kake..? Kaman naji magana kake.? Ko.. Akwai abinda zan iya taimakawa dashi.? Tai maganar a sanyaye.

"Kallonta yayi, wann karon irin kallon da yake mata a baya kafin su saba da juna . Ya kafeta sosai da ido sosai Wanda Ya soma bama Ummul tsoro Har saida taji dama bata tambayesa ba."

Jiki a sanyaye tace  Kai.. Hak uri.. Ba nufi bane nai maka shishigi a almarinka..

Tana k ok arin mik ewa taji ya kamo hannunta. Ta lumshe idanunta cikin k ok arin saita kanta. Bugun zuciyarta na sassauta a hankali.

Ya dawo da ita Ya zaunar kafin ya kuma d ago folder d in yana gani. Idonsa na kan folder d in yake furta  He sees me as a failure. Yai murmushi da za a iya kira da murmushin takaici  That I create a circus out of his business life. Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  I ve been planning.. To take him down.. To take Aliyu Maitama down.. To ruin him.. To bankrupt his business.. The business he valued all his life more than his own son.. Fuskarsa tai jazir haka idanuwansa sanda yake maganar.

Ya d ago yana duban Ummul dake dubansa cikin wane irin yanayi mai kama da tausayi.

"Haidar yai murmushi yana juya folder d in, irin murmushin nan da ake kira da murmushin takaici  He values this more than everyone around him. Tell me, shin nayi laifi idan nace zan kaishi k asa.? "

Sai Ummul ta shiga jinjina kai tana dubansa  K warai kuwa.. Ka tapka kuskure. Kuskure mai muni. Dik yanda kaje

kazo shine mahaifinka& Wanda kasancewarsa hakan Ya haramta maka fad a dashi..

"Katseta yai da fad in  You don t know anything.! Ya sassauta murya  If only you knew the kind of hell he made me went through tin daga yarinta na, har kawo girma na.. Har zuwa aiki da nayi a k ark ashin kampaninsa. Ki yarda dani wann aikin da zanyi shine zai zamo aikina na k arshe k ark ashin kampanin sa. Sann shine fansar duk wani wulak anci da cin zarafi da na fuskanta a wann kampanin.! Ya k arashe yana kuma tamke folder d in cikin hannunsa."

 Kar ka bari fushi yai maka jagora.. Bata Kai aya ba ya dakatar da ita.

 O c mon Khairy.!Stop minimising the issue here. Don t act like I m making a big deal out of it.! Yaci Ya k arashe maganar a zafafe.

"Dukda zuciyarta dake bugu hakan bai hanata k ok arin tattaro courage dinta ba, ta d aura hannunta saman nasa, tana dubansa da fuskarta mai cikeda rauni  Duk abinda Ya faru dakai a baya. Na d auka mun riga mun wuce wann. Na d auka ka goge duk wani k unci na rayuwar da ka fuskanta a baya da yafiya.. Su d in iyayenka ne ba ma asumai ba. Girman hakkinsu akanka Ya shige ka nemi fansa akansu.. "

Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa  You always talk about hakkinsu.. Have you ever bothered talking about hakkin  ya ya. Shin su basuda hakki ne kan mutanen da suka zamto sanadin tsintar kansu a wann duniyar..?

Shiru tai tana dubansa.

 Answer me. Basuda hakki.?

 Eh.. Su.. su..

"Katseta yai  Why are you stuttering now..? Kin kasa furta kalma d aya sabida kinsan gaskiya nake fad a. Sunada hakki and they will be questioned kan wann hakki na yaransu. Yaci gaba da jinjina kai  Shin kinsan most of children da suka tsinci kansu a yanayi na Allah wadai are victims of circumstance. Wasu sun fuskanci abuse and negligence from their own parents. And don t you think this can cause behavioural issue in the children later in life.? Yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Idan kayi shuka zaka bashi ruwa zaka kula dashi Har wann shukan ya girma ka girbi amfaninsa. Kaman haka idan kayi shuka baka kula dashi ba zaka samu akasin amfani mai kyau. Kaman misalin haka ne tsakanin  ya ya da iyayensu. Ya dan rage girman idanunsa yana dubanta  Wait a minute, do you really think you can change the dynamic of this family.? "

"Ummul ta jinjina kai a hankali  Bank i maka duk abinda kace ba. Shiyasa na sanar dakai tin daga farko. Iyayenmu ma suna kuskure. Sann kuma idan akwai wad anda zamu fi ma uzuri sune Iyaye. Ta d an gyara zamanta  Jinin Daddy shike yawo through your veins tun a fari.. Sann daga baya da ka samu had ari ka rasa jininka jininsa ke yawo cikin jikinka a karo na biyu..! Ya kaikaito yana dubanta da mamaki. Ummul taci gaba da jinjina Kai tana sakin murmushi. Lokaci guda taci gaba  Zan sanar dakai wani sirri da baka sani ba. Sabida tsananin k aunarka da yake Ya zab i a ajiye hakan matsayin sirri a wajenka harma da Mommy. Bai zab i ka sani ba, sabida yayi ne don soyayyar da yake maka. "

 What do you mean.? What secret are you talking about.? Ya tambaya cikin rashin fahimta.

"Ummul taci gaba  A lokacin da mukayi accident Daddy ne ya bada jininsa aka k ara maka. Cikin yardar Ubangiji, You are alive today sabida jinin Daddy na yawo through your veins. Ta k arashe murmushi had eda k walla tab idanunta."

"Haidar ya shiga girgiza kai  No. no, no way& No, this can t be& You must have got this wrong.. Tsakanina da mahaifina babu komai face k iyayya, kyara da hantara.. I m the last person da Daddy zai baima jininsa. Na sani bazai tab a ba koda mutuwa zanyi.. Ta Ya mutumin da ko zuwa Ya dubani baiba zai bani jini. I almost lost my life amma.. Bai damu yazo Ya dubani ba. Ta Ya zai bani jininsa.? "

 Amma yayi hakan. Idan Har hakan na cikin wani hakkoki naka akansa toh ka tabbata Ya cika wann hakkin. Kana iya karb an hospital report d in and see for yourself. Cewar Ummul.

Haidar ya girgiza Kai  Well I don t need his blood.! Knowing my Dad.. Akwai manufar da yasa yai hakan.! Watak ila to throw it own my face cewa ya bani jini.. I m alive sabida jininsa dake yawo through my veins.! Ya k arashe yana huci.

Ta sauk e ajiyan zuciya a hankali  Bazai tab a zama haka ba sabida Daddy bai zab i wani daga cikin ahalinsa yasan hakan ba. Musamman ma kai. Batai k asa a gwiwa ba ta kuma daidaita zamanta  Dalili shine Ina zaune lambun can na shak atawa dake bayan offices din likitocin kwanakin baya. Nan na tsinci zancen likitan da abokin aikinsa yana sanar dashi kwanaki da suka rasa jini kala kaza a asibitin mahaifin patient d in shi Ya bada jininsa kuma ya zab i hakan Ya zama sirri tsakanin ahalinsa. Sunan hamshak in D an Kasuwa Engr Aliyu Maitama da suka ambata yasa na fahimci kai suke nufi. Ta d an numfasa  Ba nufi bane naji zancensu. Sann banso ka sani ba tinda Daddy ya zab i ya zama sirri. Amma idan hakan zai kawo maslaha cikin ahalin banida zab i da Ya shige na sanar dakai.!

"Jikin Haidar Ya d anyi sanyi Dikda k ok arin b oye hakan da yaketayi, yayinda Ummul ta kuma daura tafukan hannunta bisa nasa  Daddy yana sonka.. Yana matuk ar k aunarka.. Dan Allah ka janye duk wata maganar fad a da d aukan fansa akansa.. Shid in mahaifinka ne& Idan baka zamto jigo na hab aka masa kasuwancinsa ba bazaka tarwatsa ba. Kar ka mance mutane da yawa Sun dogara da aikin da suke a wann Kampanin dasu da iyalansu. Kai tunani idan ka tarwatsa Kampanin mutane nawa zai affecting.? Mutane nawa zasu rasa ayyukansu sakamakon durk usar da Kampanin da kayi. Mutane nawa zasu koma basuda aiki basuda abinda zasu rufa asirin kansu da iyalansu dashi. Tin daga shugaban Kampanin Wanda Ya kasance mahaifinka Wanda yake da girman hakki akanka matsayinsa na mahaifinka koda bai kasance ahugabanka wajen aiki ba. Sauran manyan ma aikata masu hannun jari Har zuwa kan k anan ma aikata& Ina zaka kai girman hakkokinsu.? "

Ya d ago Ya dubeta cikin yanayin da zata iya cewa bata tab a ganinsa ciki ba.

A hankali taci gaba  Nasan kai mutum ne mai saka sharri da alkhairi. Wanda duk yanda Ya zauna Ya tashi alkhairansa bazasu gushe ba. Jajirtacce Wanda jajircewarsa takanyi tasiri cikin duk abinda yasa gabansa. Mai taimakon Al umma ba mai durk usar da ita ba.

 What if duk abinda kika fad a akaina ba haka bane.! What if na aikata kudirina da abinda na jima ina shiryawa.?! Kina tunanin zaki iya dakatar dani.! Just Who do you think you are.?! Ya k arashe yana mai tsareta da ido.

Cikin zuciyarta tace  I call you sweet monster for a reason. You are not like other monsters out there. A fili kuwa cewa tayi  Kanada zuciya mai kyau. Inada yak inin kyakkyawar zuciyarka bazata bari ka aikata akasin abinda na fad a ba.

Haidar Ya kuma d agowa ya dubeta. Sai Ya dan lumshe idonsa kadan  Khairy please get out now. I need to be alone.!

 Amma& 

 I said leave.! Ya katseta a zafafe

"A hankali ta mik e, ta d an dubesa kafin ta soma tafiya cikin sanyin jiki."

Muryarsa ta sinkayo yana fad in  Just.. go home. I don t need you here.! Ya k arashe ba tareda ya dubeta ba.

Ta juyo ta dubesa a sanyaye sai ta jinjina kai a hankali. Lokaci guda tasa kai ta fice cikin sanyin jiki.

"Bayanta yabi da kallo Har ta fice kafin ya maida dubansa ga folder d in kalamanta yaketa k ok arin yakishewa ganin basuyi tasiri cikin zuciyarsa ba. Ya d ago hannunsa yana juywa yana bin veins d insa da sukai rud u rud u sukai kore shar yana tuna kalamanta sanda take sanar dashi Daddy ya basa jini. Jinin Daddy ke yawo through his veins. A hankali Ya lumshe idanunsa hoton abubuwan da mahaifinsa Ya jima yana masa na yawo a kwanyarsa, zuciyarsa da kuma lumsassun idanunsa."

Koda dare yai Haidar kasa bacci yai sabida rashin Ummul. Baisan yayi sabo da ita Har haka ba. Room nurse din dake kula dashi kuwa cewa yai ya fice ya bar masa d aki he can take care of himself. Gaba d aya gani yake room nurse baisan komai ba bai iya komai kaman ita ba. Abubuwa ne da dama fal zuciyarsa. Koda yazo bacci haka yaita

juyi yana tunaninta. Yakai dubansa ga kujerar da suka kwana tare ranar farko da ya farka. Ya lumshe idanunsa. A fili yake furta  I m not the type that share his problems with others.. I don t know how I do it with you. Ya d anyi shiru still yana duban wajen. A hankali ya furta  It feels so empty to go to bed without you.! Ya rasa haushinta ne ko haushin kansa ko kewarta yake.

**

A b angaren Ummul kuwa Mommy taso ta fahimci wani abu musamman da taga Ummul d in bata koma asibiti wajen Haidar ba .

"Washe gari da safe koda Ummul ta shigo gaida Mommy sai Mommy ta dakatar da ita bayan Sun gaisa. Ta nuna ma Ummul d in gefenta saman kujera  K araso nan ki zauna daughter, magana nake so muyi. "

Ummul ta jinjina Kai had ida amsawa kana tai yanda Mommy tace.

Anisa dake k ok arin saukowa downstairs nan ta sinkayo zancensu. Ba shiri ta lab e jikin staircase tana sauraronsu.

Mommy taci gaba yayinda kan Ummul ke kife k asa  Bana so na zamto irin iyayen nan masu kutsa Kai a al amari gidan  ya yansu. But when it comes to Haidar you and I are team. Haka ne.?

Ummul ta jinjina Kai a hankali.

Mommy taci gaba  Kuma zamuci gaba da zama team wajen ceto rayuwarsa daga halak a. Tinda ni mahaifiyarsa ce ke kuma matarsa. Mu duka d in yanada matuk ar mahimmanci a wajenmu. Haka ne.?

Nan ma jinjina Kai ta kumayi a hankali.

Wann karon sai Mommy ta d aura hannu saman nata  Ummulkhair.!

Ummul ta d ago a raunane tana duban Mommy.

"Mommy taci gaba  Nasan kina hak uri da Haidar. Amma dan Allah ki k ara. I have this strong feeling, with you by his side, Haidar zai mending ways d insa. Kuma mun fara ganin hakan cikin ikon Allah.. Ta dan numfasa  Bazan tambayeki mai ya hadaku ba dan wann ba hurumi na bane. Sann dik hukuncin da kika zartar har kawo zuwa lokacin da zaki sauk o bazan tak ura miki ba. And always remember kina tareda yarda da kuma k aunata a gidan nan. Tashi kije, Allah shi muku albarka gaba d aya. "

Ummul ta jinjina kai a sanyaye kafin ta mik e ta fice jiki ba laka.

Anisa da ta gama nad e komai murmusawa tai. Cikin zuciyarta take furta  You are so selfish Mommy. Kedai kawai d anki. Toh bari dai mu gani idan hak arki zai cimma ruwa.

Da dare ta iske Ummul a sashenta. Anisa ta saki murmushi tana duban Ummul  Da alama jikin D anuwana kuma mijinki da sauk i sosai tinda gashi har kin rigashi dawowa.

66 / 103