AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   83 / 103

246K to 249K   out of 306.8K words

Ya fara yan k anan kuka. mommy ta sinkayo sautin yaron daga cikin waya. Annurinta ya ninku, yayinda k walla ta kuma ciko idonta  Is that my grandson.. Is that his voice..? "

Haidar ma murmushin yake yana duban yaron  Yes Mommy.. It s your grandson.. He wants to hear your voice I guess. I m putting you on speaker.

Yasa Mommy a speaker yana yana duban yaron yake fad in  Guess who s on the line Son.? It s Grandma. Say hi to granny.! Cikeda farin ciki yake maganan gwanin ban sha awa.

Mommy tace  Hello my cutie.. Is that you..? Is that your tiny voice.? How s my little love doing..? Oh c mon don t cry.. Is the little one hungry..? Cikeda farin ciki da ya gaza b uya take maganganun. Haidar sai murmushi yake yayinda Ummul ke saurarensu daga nan yanda take kwance har lokacin hawaye ke gangaro mata musamman da ta sinkayo muryar Mommy tana magana ma jaririn.

Mommy tace da Haidar Ya bata Ummul. Sai Haidar Ya d an waigo kadan yana duban Ummul da ta basu baya. Kuka take maras sauti. Ya d anyi gyaran murya yace  She s.. still asleep Mommy..

"Mommy ta jinjina kai  Kyaleta tana buk atan hutun. Ta k ara da  Haidar, nace ya batun aurenku.. Mecece makomar aurenku da Ummul.? Jikinta duk a sanyaye Tai tambayar cikeda shakkun amsar da zata samu daga gare shi."

Lumshe idonsa yai kad an had ida furzar da huci daidai lokacin wata mata mai sanye da kayan nurses ta dan manyanta matar ta shigo. Ta dubi Haidar dake rik eda jariri ta kuma dubi Ummul. Kallon na mamaki ko tuhuma take ma Haidar ganin bataga mutanen da suka taho da Ummul ba. Kafin tai magana Haidar yai saurin furta  I m the

father. Sai ta saki murmushi matar tace  Ba shakka naga kama.. Congratulations to you. Ya jinjina mata kai had ida mata godiya kafin ya sumbaci yaron Ya mik a mata. Ta amshi yaron tana nufan Ummul.

Ficewa waje Haidar yai yana amsa kiran Mommy. Mommy ta sake nanata masa tambayar da Tai masa.

"Furzar da huci Ya kuma yi yana shafa kansa kad an  All that I m sure Mommy.. Shi ne I won t give up my wife.. I ll never give up Khairy.. I won t give up my little family.. I will do everything I could to make sure ahalina bai tarwatse ba. Ya dan numfasa kafin yaci gaba  If Khairy is the architect of our love Mommy.. Then I ll be the Engr.. If she s the one that designed our love.. Then I d make sure it is well built.. I will be the protector of that love.. I know it won t be easy.. It will be difficult.. But then, I won t give up.. Never..! "

Mommy ta goge hawayen da suka gangaro mata. Murmushi ne saman fuskarta amma can k asan zuciyarta zallan tausayin D an nata ne. Ta shiga jinjina kai tana fad in  May Allah be with you Son& Ina rok on Allah ya had e maka ahalinka kaman yanda Ya had e mun nawa.

Haidar Ya amsa da Ameen Mommy. Yai mata godiya Tai masa fatan alkhairi da nufin washe gari idan Allah yakai rai jirgin sassafe zasu biyo itada mahaifinsa.

**

A can waje kuwa Sadis bai fasa bin bayan motan Hisham ba har saida ya cimmasa. A dole Hisham yai birki yai parking.

Hajja ta soma karanto salati tana waige waige ganin Mota ta sha gabansu ba shiri.

 Hisham meke faruwa.. Waye wann meyasa yake bibiyanmu.?

Hisham da k irjinsa bai daina bugawa ba girgiza kai yake yama kasa ficewa daga cikin motan. Fad i yake cikin rawar murya  I.. Ya.. Yaron Ogana ne a wajen aiki.. Ogana da nake aiki k ark ashin Kampanin sa.. Engr Aliyu Maitama mahaifin Abokina Haidar.!

Cikin wane irin shock Hajja ta d ago tana duban Hisham fiyeda Wanda ta shiga lokacin da taga Haidar.

 A..Aliyu Maitama.. K ark ashin sa kake aiki..?! Ta fad i cikin birkicewa.

Hisham Ya jinjina kai  Eh Hajja k ark ashinsa nake aiki kuma na tabbata shi Ya turo a kamani a tunaninsu ni macuci ne kaman yanda Haidar yai zato.. Hajja abun is complicated amma na tabbata komai zai fito fili idan suka tabbatar banida laifi kuma ni taimakon Abokina kawai nake.

Innalillahi wa inna ilaihi raji un shine abinda take nanatawa cikin zuciyarta. Bata sake fahimtar komai ba sai tsintar kanta da Tai a station dan tuni an kama Hisham anyi dashi ofishin yansanda.

Hisham Ya kamo hannayen Hajja cikin nasa daga nan yanda yake rufe cikin cell. Ya kwantar da murya sosai  Hajja I m innocent.. Ban sace Ummul ba.. Ban kuma raba Haidar da Ummul ba.. Hasalima ban tab a sanin Ummul abokina Haidar take aure ba har sai bayan da suka rabu.. Sann a wann lokacin na san  yaruwarsa Anisa tana neman rayuwar Ummul da abinda ke cikinta kaman yanda tayi ajalin rayuwar tsohuwar matar Haidar da abinda ke cikinta..!

Hajja bata fahimtar komai sai hawaye dake gangaro mata tana duban D an nata cikeda tausayawa. Ta ya fara aiki k ark ashin kampanin mahaifinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D anuwansa ya zama abokinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D anta ya fad a gidan da taita k ok arin nisanta shi dashi ya fad a cikinsa tsamo tsamo..? Ta ya duka wad annan abubuwan suka faru. This a too much of a coincidence.

Muryar Hisham ta sinkayo yana fad in  Hajja ki daina kuka.. Banida laifin komai Hajja ta.. Your son is innocent.. I m sure Haidar would understand so as his father. Su d in mutane ne masu nagarta.

Hajja ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Silalewa Tai nan wajen tana kuka sosai. Kuka mai tab a zuciya.

**

Washe gari jirgin safe su Mommy suka biyo zuwa Bauchi. Haidar kuwa asubahin fari Ya baro masaukinsa Ya nufo asibitin dan dama bai yarda ya bar asibitin ba saida ya samar ma Ummul da jaririnsu room nurse da zata kula dasu dan ko nawa zai kashe a kular masa dasu tinda shi dai bazai yuwu Ya kwana dasu ba.

Cikin tsananin damuwa mai tattareda tashin hankali Ummul ta kuma tambayar nurse din  Ina Hajja.. ina Hisham meyasa ban sake ganinsu ba tin jiya..? Ki fad a mun.. Haidar ne yace ki rufe ni a nan Ki hanani fita..? Dan Allah Ki sanar Dani.. Ina Hajja da Hisham..?

 Suna yanda Ya kamata ace nan suke.! Haidar da shigowarsa kenan da kaya nik i nik i na jaririn da na mahaifiyar jaririn Ya fad i haka.

Nurse din ta sauk e ajiyan zuciya tana ma Haidar sannu da zuwa. K ok ari taketayi Ummul ta saka ruwan tea a cikinta ko jariri zai samu ruwan nono amma tak i sai tambayarta take ina Hajja da Hisham.

Nurse din Suka gaisa kafin Haidar Ya shiga aje kayayyakin dake hannunsa matar tana sanar dashi Sun sha fama da  yar rigimarsa daren jiya dan cewa Tai saidai a barta ta fice. Ta dubi Ummul murmushi saman fuskarta ta kuma dubi kofin tea dake aje gefe sai ta dubi Haidar tace  Kuma tak i ta saka komai cikinta balle wann babban mutum din ya samu isasshen abinci. Ta mik a mata mug din  Ya kamata ki shanye wann.. Mu a Likitance ruwan nono shine farkon rigakafi ko wane jariri ke buk ata.

Ummul ta galla mata harara. Dariya taso bama nurse din amma ta gimtse tace  Daure dai ki shanye wann.. Ni kinga ma tafiyata. Ta mik e tana ma Haidar Sallama.

Bayan ficewarta Haidar ya maidoda da dubansa ga Ummul wacce ta nannad e jikinta cikin mayafi. Ya dan furzar da huci kad an kafin yace  Kiyi hak uri ki sha.. Take one more sip.. Please.!

Kauda fuskarta gefe ba tareda ta dubi yanda yake ba. Ga jaririn tuni ya soma mutsu mutsu yana cilla k afafu sai tsotsan hannunsa yake alamun yunwa.

Haidar ya kuma furzar da huci yana shafe fuskarsa  Look Khairy.! Idan baki sha ba zan tako har wajen na baki da kaina kuma kinsan zan aikata..!

Ta dube shi a dak ile  Ni kuma sai na tsaya wani k ato ya bani abinci a baki.. Allah ya sawak e mun. Idan ka mance ne dai na sake tuna maka.. Ni Ummulkhair ba matarka bace. AUREN WATA UKU mukayi kuma ya k are.!

Haidar ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa had ida furzar da huci. Yasan dole zai sha fama ba kad an ba. Yakai dubansa ga yaron da tuni ya b ige da kukan yunwa ga Ummul ta had e rai sosai ta kauda fuska gefe. Dik yanda take son ta d auki D anta ta basa abincinsa ta lallashesa yai shiru ta kasa sabida tsananin k iyayyar mahaifinsa dake kuma tunzurata. Sosai kukan jaririn ke mata zafi amma ta kasa koda motsawa sabida Haidar dake wajen.

K arasowa yai ya d auki yaron ya shiga jijjigasa yana lallashinsa. Sai ya saka ma yaron lip d insa na k asa aiko tuni ya capke ya soma tsotsa kaman ya samu abinci. Ummul ta saci kallonsu yanda Haidar ya saka bakinsa ma yaron sai jijjigasa yake. Hawaye suka gangaro mata.

Daidai nan sukaji Sallama a k ofa. Haidar ya bada izinin shigowa.

Wa zata gani.? Mama Tani ce da  yanuwanta guda biyu Azeema da Badia. Suka tafi a guje suka rungume Ummul suna kuka. Yayinda Haidar ke gaisawa da Mama Tani ya mik a mata jaririn yana musu sannu da hanya. Dan dama Tun a daren jiya ya tura Sadis ya tafi Kano d aukosu. Asuba Sun kamo hanya shisa sukayi isowan safiya.

Haidar ya fice wajen Sadis ya basu waje.

Sosai Ummul ke kuka tana tambayan sauran ahalinta. Ta dubi Azeema tace  Ina Khulsum..? Maiyasa bata biyoku ba..? Itama tana fushi dani ko.? Umma da Abba duk fushi suke dani ko.? Hawaye suka ci gaba da gangaro mata tana girgiza kai take fad in  Bazan iya dubansu cikin ido ba. Cikin tsananin rawar murya take maganar.

Azeema ta murmusa tana share ma Ummul d in hawayen da suka gangaro mata  Dukanmu muna fushi dake  yaruwa.. Shin wak e gudun danginsa a lokaci mai mahimmanci irin wann& ? Amma Kar ki damu zamu iya yafe Miki ko dan zuwan Sabon D anmu.! Ta k arada  Kinga d ago ki gani.. D ago kiga da wa muke tare. Ta k arashe da murmushi saman fuskarta.

D agowar da Ummul zatai sukai ido hud u da Khulsum. Rabon su da su saka juna a ido Tun lokacin Auren Ummul d in a gidan Hajiya Asshe ranan da mahaifiyarsu tai ma  yanuwan Farrak u a k ok arinta na ganin Auren Ummul Ya tabbata.

Hawaye suka ci gaba da kwaranya musu.. Khulsum tana k arasowa gaban Ummul kukan Ummul d in Ya k aru sosai. Murya na rawa Khulsum ta furta  Adda Ummul..! Sai sukai bursting cikin kuka sosai su duka biyun. Suka rungume juna suna yin mai isansu. Har saida Mama Tani tace zasu tasa mata sabon maigida da kukan da suke dan tuni bacci ya d auke jaririn cikin hannunta.

Ana haka su Mommy harma da Daddy sukai sallama tareda jagorancin Haidar.

Gaishe gaishe aka soma kan Ummul na kife k asa tin shigowar Mommy da Daddy. Mama Tani ta mik a ma Mommy yaron tana fad in ta rigata ganin angon nasu. Sukaita  yar bankwanci a tsakani Mommy tana fad in ma sha Allah ta sumbaci goshin yaron. Sak Haidar dinta sanda yake jariri. Su Azeema kaw ficewa sukai bayan Sun gaisar da iyayen Haidar.

Mommy ta mik a ma Daddy dake zaune saman farar kujera yaron. Ya amsa yaron kyakkyawan murmushi bisa fuskar Daddy. Haidar yana gani Daddy na ma yaron addu a ya tofa masa. Ya mik a ma Mommy yaron bayan ya jero ma jaririn da mahaifyarsa add u o i. Har kawo wann lokacin Ummul bata iya d ago fuskarta ba.

Daddy ya dubi Haidar yace suje daga waje. Ba musu Haidar yabi bayan mahaifinsa.

Bayan ficewar su Mama Tani ma ta zame jiki ta fice tana ce da Mommy bari ta barta ta gana da sabon Angonta dan gashi da alama har ya kori Daddy.

Mommy ta murmusa tana jinjina barkwancin Mama Tani.

Mik ewa Mommy tai rungume da yaron cikin hannunta ta dawo kusan Ummul wacce tinda Mommy ta nufota k irjinta ya tsananta bugu. Ta kasa koda motsawa balle ta dubi Mommy tin bayan gaisuwa Wanda shima da kyar ta iya. Ta sani tana fara magana kuka ne zai biyo baya.

Mommy ta kwantar da jaririn cikin baby crib d insa dake gefe. Ta kuma matsowa sosai kusan Ummul. Sai Mommy ta d aura hannayenta saman na Ummul. Ummul na ganin hannun Mommy saman nata hawaye suka shiga gangaro mata.

Mommy ma kuka ne taji na zuwa mata. Sai kawai ta rungumo Ummul cikin jikinta tana fad in  Taho nan  Yata..!

"Mommy ta rungumeta sosai cikin jikinta yayinda Kukan Ummul ya k aru, Mommy na ci gaba da lallashinta."

**

A can waje kuwa taryan taryan Haidar ya karanto ma Daddy komai gameda Abokinsa Hisham da irin cin amanar da yai masa bayan ya aminta dashi. Sann ya sanar da Daddy baida haufin duk wani scandals da failures da Kampaninsu ta fuskanta da saka hannunsa ciki. Daddy yaita jinjina lamarin domin kuwa zai iya cewa bai tab a tsayawa ya tantance kamannin matashin ba cikin employees d insa dukda kuwa cewa suna tareda Haidar kusan ko Yaushe a company. Ya dubi Haidar yace ai sai su wuce police station din snn ya kuma ce da Haidar d in ya kirawo company lawyer d insu cikin gaggawa. Dole Hisham nada Ubannin gidan da suka turosa kampaninsu domin Ya musu zagon k asa.

Tuni Sadis ya jasu suka nufi station yanda Hisham ke gark ame.

*

Hajja na gaban Kanta tana magiya ma  yansanda da su saki D anta dan bata fata Aliyu Maitama ya tadda su a station d in. Alk awari tai ma kanta bazata tab a jingina ma D anta sunan Aliyu Maitama ba koda kuwa shine abu na k arshe da zatai a rayuwarta. Ba yanda batai su bata belin Hisham ba amma sunk i sunce sai Wanda yai filing complaint akansa yazo idan D anta nada lawyer yana iya kiransa.

Hajja ta kuma marairaice fuska  Rankaidade ka dubi girman Allah ka min alfarmar nan.. Ka dubi soyayyar dake tsakanin D a da mahaifiya ka bani belin D ana.. Ko nawa zan kokarta na biya in sha Allah.

"Shi kaw Hisham addu a yake daga nan cikin cell yanda yake gark ame kar a bada belinsa har sai mahaifinsa Aliyu Maitama yazo station d in. Aiko kaman daga sama ya hango Haidar da Sadis ga Daddy na biye dasu. Hisham ya saki murmushi da gefen bakinsa. Cikin zuciyarsa yake furta  Bingo.! Daga k arshe dai, korarren D an zai had e da mahaifinsa. Bari dai mu gani Aliyu Maitama.. Ya zakai da wann D an naka da ka sheganta& The Son you never noticed dikda jimawansa yana aiki k ark ashinka.! "

A haka suka k araso cikin station d in waya manne kunnen Daddy dake magana da company lawyer dinsu.

Cak Hajja ta had iyi kalamanta. Tai mutuwar tsaye nan wajen. Ta ina zata mance wann murya dukda muryar ta manyanta a halin yanzu.. Ta tuno muryar a lokacin da ya jajanta mata rashin mahaifinta kuma leburansa a Kampaninsa. Ta tuno muryar a lokacin da yai alk awarin Aurenta bayan rashin mahaifinta. Ta kuma tuno muryar a lokacin da ya furta mata kalman saki ya kuma sheganta jaririn cikinta. Ta tuna sanda ya turata kurkuku har ta haife D anta a gidan yari. Yau gashi nan zai kuma tura D an da yai sanadin haihuwarsa a gidan kasu zuwa gidan kasu. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa cikin sauri.

"Cak Daddy ya ja ya tsaya, ya dakata da wayan da yake a daidai sanda ya shigo cikin ofishin yana jin bugun zuciyarsa na k aruwa ba tareda yasan dalili ba."

SameenaAleeyou

83 / 103