AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   59 / 103

174K to 177K   out of 306.8K words

aka tarbeta dashi  Waye yace miki Dije tana yafiya..?

Ta kuma gyara zama  Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son gani ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!

Asshe ta jinjina kai  Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.! Ta k arashe idonta tar cikin na Inna Dije.

Murmushi Inna Dije take tana dubanta  Maiyasa kika kirani.?

 Kiranki nai mu taru mu had a k arfi da k arfe mukai Suwaiba k asa. Dan bazan tab a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri arta ba. Bazan bari Alakan D ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D ahna ba. Bazan tab a bari D ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab a bari na had a zuri a da Suwaiba ba.! Ta k arashe tana huci.

Inna Dije ta murmusa  Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.

Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D anta Hilal da kudin da ya tura ma  yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata asiri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud ad ensa Har kawo auren da Hilal d in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so ba face  yar Suwaiba.

Inna Dije ta sauk e ajiyan zuciya  Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri arki zab i d aya kike dashi a nan.

Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Wane zab i kenan.?

 Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!

Asshe ta d ago da mamaki tana duban Inna Dije  Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar da Suwaiba ke fad i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!

Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad an daga cikin kujeran  Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak i iskan  yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.! Ta k arashe shu umin murmushi irinta gogaggun mata saman fuskarta.

Asshe tai shiru kaman mai nazari. Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d aya. Zataja layi ma D anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zaiso mahaifinsa yasan cewa ya tura ma  yaruwarsa Anisa kud ad en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk awari baya tab a sab awa musamman tsakaninsa da  yaruwarsa. Yana k aunar  yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fitar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d aure Hilal.

Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai.

 K warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na nufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.

Inna Dije ta jinjina kai  Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma yarda da sakin jiki Dani. A sauk ak e zamu kaita k asa.

Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai da yanda zasu gudanar da komai.

**

Bayan kwanaki uku da faruwan wann al amari Tani ta shak i iskan  yanci. Duk a tunanin Umma Inna Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud ad ensa harda tara.

Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk awarin zama da kowa lafiya.

A b angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad in  Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud ad en yayi amfani dasu wajen d aukar ma surkar Haidar Lawyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d aga koda k adarata..

Katseta yai da fad in  Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud ad en.

Ya dubi Hilal  Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud ad en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d aukesu matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud ad ena. Yana ida fad in haka Ya mik e ya fice yana sab a babbar riga.

Hilal ya sauk e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud esu ya dubi Amminsa cikin mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa.

Kafin yai wani magana ta dakatar dashi  K warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud ad en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba  yar Suwaiba.! Ka nemi  yar gidan ko waye ka aura amma ba  yar Suwaiba ba.!

Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa  Kinyi haka ne dan ki d aureni Ammi..? Sabida haka kika zab i taimaka masu.?

 Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark an Suwaiba da zuri arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi  yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda  yar Suwaiba ehe.!

"Ya girgiza Kansa  Kiyi hak uri Ammi.. You don t have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice."

K arshe dai Asshe ciwon k arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar.

**

Abuja..

Yau kwanan Haidar ak alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk ufa addu a gareshi da rok ar masa sauk i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa.

"Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na urar nasara Sun masa k awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido."

"Mommy taci gaba  A lokuta da dama mukan mance wasu ni imomin da Allah yai mana na d an lokaci ne ba mai tabbata ba& Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman  ya ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk e nauyin da aka d aura maka na hakkoki..? Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni  Ina rok on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok on Allah Ya tashi kafad unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib icin Al amaransa.. Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata  Ina rok on Allah Ya nuna mun zuri ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He s all I have.. I can t lose him..! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka."

"Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k ok arin k arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata  Mommy Haidar zai tashi cikin yardar Ubangiji.. Zakuyi rayuwa irinta D ah da mahaifiya mai cikeda albarka da aminci.! "

Ta d ago tana duban Ummul wacce itama d in Mommyn take duba hawaye fal idonta.

"Ta kuma kamo hannayen Ummul cikin nata  Na fad a zan k ara fad a, kin amsa sunanki Uwar alkhairi.. Kinzo da d imbin alkhairi cikin ahalinmu.. Ummulkhair.! Ta ambaci sunanta cikin wane irin siga mai nuni da yarda da aminci. Ummul ta d ago ta dubi Mommy a sanyaye jin yanda ta ambaci sunanta. Mommy taci gaba  I entrust my son to you.. Please take care of him.. Be patient with him.. Don t let go of his hand.. Help him find his way.. Nasan zaki iya.. Allah ya zama maku jagora Ya albarkaceku rayuwarku da zuri a ta gari. "

Sai Ummul ta sadda idonta k asa cikin jin nauyin Mommy.

Mommy ta murmusa kad an tana dubanta kafin tace  Tashi ki shiga alwalanki.. Ni zanje na samu Daddynku naga sak on sa yana jirana a reception.

Ummul ta jinjina kai a hankali tana mai amsawa kafin ta mik e ta nufi bathroom.

Koda Mommy ta mik e sai ta nufi jikin gadon Haidar.. Ta dafa goshinsa tana dubansa. A hankali ta furta  My handsome Boy. Allah ya baka lafiya. karanto masa addu o i samun sauk i tai. Ta sumbaci goshin nasa cikeda so da k auna kafin ta fice.

Tana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idon Haidar.

A hankali yatsarsa guda ke motsi.. Ya soma k ok arin bud e idonsa da suka masa nauyi. A haka Har ya bud esu tar yana kallon sama.. Komai ya soma dawo masa gameda had arin da sukai.

Ya tuna sanda motar ta sauk a saman shoulder.. Ya tuna tsallen da yai ya rufe Ummulkhair gudun kar wani abu ya sameta. A hankali ya kai hannunsa ya zame na urar dake hancinsa lokaci guda ya furta  KHAIRY.!

A daidai lokacin Ummul ta fito daga bathroom.

Haidar na jin an tab a k ofa ya kuma lumshe idonsa kif.

Ummul takai dubanta garesa. Batasan ko idonta bane amma sai taga kaman ya motsa daga kwancen.

Ta nufi jikin gadon nasa Tai zaune saman kujeran da take kusan yini akai tana dubansa dake nan jikin gadon. A

 yan kwanakin da sukai asibitin..

Tagumi tai da hannayenta biyu had ida tsura masa ido daga nan yanda yake kwance. Ta shiga tuno kalaman Mommy a gareta wanda tamkar amanar Haidar d in ta damk a hannunta. Sai ta tsinci kanta da shakku da kokonto musamman da ta tuna kafin had arin ya faru ya furta mata cewa he d set her free.. Zai sawak a mata. A b angaren guda ga Mommy tace don t let go of his hand..! Mai zai faru idan k addara bai bata daman sauk e alk awarin da ta d aukar ma Mommy ba.? A wani b angare na zuciyarta tana tunanin aurenta ya k are a daidai wann gab ar bayan ta d aukar wa mahaifiyarta alk awarin bazata waiwayi gida ba har sai ta cika watanni uku da aure. Wani k alubale zata fuskanta bayan ta koma gida.? Shin ta Ya zata fuskanci Umma da sauran ahalin gidansu idan har aurenta Ya Mutu. Auren da ga yanda Ya kasance Tun farko.. Tabbas batasan yanda zata fuskanci Umma ba muddin aurenta Ya k are kafin aje ko ina.. Ita duk ba wann ba. Ko kiran waya Umma ta haramta mata mai zai faru idan ta koma da sunan auren ta Mutu.? Ta lumshe idonta a hankali tana furtawa cikin zuciyarta  Allah duk yanda kayi daidai ne.! Ka shiga al amari na ka zamto majib icin lamrana.!

Ta bud e lumsassun idonta ta zuba su tsaf akan Haidar dake kwance.

Sosai k irjinta ke bugu sanda Takai hannunta dake tsananin rawa mai d aukeda damshin ruwan alwala tana shafa goshinsa zuwa sumarsa a hankali. Abunda tasan ko bindiga za a saka mata idan idonsa biyu ne bazata tab a iya yin hakan ba.

Tamkar electric shock haka Haidar yaji sauk ar hannun nata saman goshinsa. Har lokacin bai nuna alamun farkawa ba.

"A hankali taji tana samun natsuwa, bugun zuciyarta na daidaita bata daina abinda take ba."

Ta tsinci kanta tana mai sakin Murmushi a yayinda take dubansa. Har lokacin bata daina shafa goshinsa zuwa sumarsa ba  Kasan mai..! Ta furta a hankali had ida gyara zamanta. Ta d aura hannunta saman yatsunsa a hankali  Kanada sa a. Kai d an gata ne.. Ina nufin kanada mahaifya da take matuk ar k aunarka..! Ta k arashe maganar cikin sanyin jiki tunowa da nata mahaifiyar da tai da kuma irin rabuwar da sukai bayan tayi aure. Ta jinjina kai a hankali tana share hawayen da suka gangaro mata. Sai ta d an tsura masa ido kad an  Kanaga zan iya sauk e nauyin alk awarin da na d aukar ma Mommy.?

Sai ta d an girgiza kai  Na tabbata da idonka biyu zaka ce.. Ke! Get out of my face.! You don t want to have a monster for a husband.! Tai maganar cikin tsarewa ita a dole tana kwaikwayonsa.

"Sai kuma ta bama kanta dariya. Ta murmusa kad an tana mai tsura masa ido tsananin tausayinsa kwance cikin k irjinta. Tai raurau da ido Kaman mai shirin kuka tace  Watak ila You are a bit of a Monster, but you are also sweet.. So sweet& . Sweet Monster.! Taci gaba da sakin sassanyar murmushi tana dubansa  Na gode da ka ceci rayuwata.! Na gode da rayuwata ta kasance mai mahimmanci a wajenka. Allah ya baka lafiya.! Ta k arashe tana k ok arin mik ewa. K ok arin zame hannunta daga nashi take amma mai .? Sai ji tai gam Haidar ya tamke hannunta cikin nasa."

K irjinta yai wani irin bugawa. Ta zaro ido waje tana jin bugun zuciyarta na k aruwa. Ta kasa juyowa ta dubesa sai rawa da jikinta yake.

SameenAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*41*

*©þSameena Aleeyou& *

Duk sai ta daburce ta rasa mai zatai. Ta kasa furta komai sai duban juna da suke su duka biyun& A haka aka turo k ofan d akin.. Ba kowa bace face Mommy. Ganinsu a haka yasa Mommy saurin k arasowa murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. Farin cikinta ya gaza b uya.

" Haidar. My son.! Alhamdulillah.. Haidar ka tashi..! Sai kuka ya b alle ma Mommy. Ta d aga hannayenta sama tana fad in  Alhamdulillah.! Allah na gode maka da ka tashi D ah na. Allah na gode maka..! Hawaye na gangaro mata tafukan hannayenta tallafe da fuskan Haidar din duka b angare biyu taci gaba  I can t believe you are finally here with us again son.. You know, I don t mind losing everything.. But.. Amma bazan iya rasaka ba Aliyu& Bazan iya jure rashin ka ba..! Ta daga hannayenta guda biyu sama  Allah na gode maka daka tayar min da D ahna& Allah na gode maka for giving me such a blessed opportunity to be with my son again..! Ta k arashe tana mai rungumo kansa daga nan yanda yake a kwance. Dole duk Wanda ke duban Haidar da mahaifiyarsa su basa

59 / 103