AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   17 / 103

48K to 51K   out of 306.8K words

unta. A hankali ya d agota. Kaman wacce akace ta k ara kuka.

Ya d an shafi fuskarsa ganin yanda take kuka sosai tana fad in ta gaza ta ko wani b angare. Ta gaza protecting ahalin. Rungumeta yai ta b angaren jikinsa kad an yana fad in Ya isa ta daina kuka. A haka yai masu masauk i suka zauna saman kujera.

Saida suka d ibi lokaci a haka kafin ta soma fad in  Bazan tilasta maka ka so Haidar ba. But please just this once.. Alfarma nake nema.. Be a father to him..

Ya d an dubeta sai kuma ya kauda kansa kad an  Ban tab a cewa ni ba mahaifinsa bane Kwaise. D anki shi ya zab i ya cire kansa daga cikin ahalin nan.

Ta d an sauk e ajiyan zuciya kafin ta mik e sosai tana gyara zamanta  Aure nake so a masa..

Daddy ya dubeta da mamaki  Aure.? Cikin yaran Business partners dina kike so na nemar masa matan.?

"Ta girgiza kai alamun a a  Na riga na samar masa mata a garin Kano.  Yar gidan mutunci wacce bata da bud ewan ido da wayewa da yawa balle a samu matsala along the way. Ba babban Aure nake so ba, ba auren da za a wallafa a mujalla ko a gayyato manyan mutane ba. No aure nake so ayi a sauk ak e. Kawu na dake can Maiduguri zai iya wakiltanka dan shi na wakilta akan komai. Ga Asshe ma a can Kanon. So dik wani necessary bincike da Ya kamata a gudanar an gudanar.. "

Dakatar da ita yai ta hanyar d aga hannu  Idan keda  yanuwanki kun gudanar da duk abinda ta kamata kuyi so meye nawa kuma. Ni dai kin sani bazan tab a karb ar ma D anki Aure ba Kwaise. Kuma abinda ya shafi rayuwarsa ba damuwata bane. The only alak a dake tsakanina dashi shine abinda ya shafi Kasuwancina. Kampanina da ci gabanta.

Mommy ta rintse idanunta tana jin wani zafi na ratsa cikin k irjinta. Tasan za a Rina haka tinda dai ta jima da sanin duk wani abinda ya danganci Haidar wofi ma ya fisa mutunci a idon mahaifinsa. Ya zama dole ta tabbata anyi auren nan at all cost. Tinda tasan wann ba komai bane face sharrin mugun asirin da aka jefesu dashi. Ta tabbata tinda Malaminsu ya sanar dasu da zaran anyi auren matsalan dake cikin ahalin zaizo k arshe gwara tayi komai domin ta tabbata auren ya yuwu.

Ta numfasa kad an  Auren bazai yuwu ba saida yarda da amincewarku.. Ina nufin kaida Haidar..

Ya kuma dubanta da mamaki  What exactly do you mean.?

" Ina nufin Yarda da amincewarka shine kawai zai karkato Haidar Ya amince da wann Auren. Kasan halinsa za a iya masa auren mu daina ganinsa har abada, bazai yarda ya zauna da matar ba. Yanzu haka ma Gaba yake damu tinda gashi ya daina zama gidan nan. "

 Wanda yafi k arfin zaman gidan iyayensa ne zai zauna ma Auren da zaki masa.? Ke kanki kinsan D an naki baida mutunci bai ganin kowa da mutunci daga ni har Ke.

 Amma yana mutunta aikinsa.! Mommy ta dakatar dashi da fad in haka.

Daddy ya tsareta da ido.

Taci gaba da jinjina kai  Musamman project d in nan da yaketa kai komo akai. Naga yanda ya dage yake matuk ar so Ya jagoranci aikin.. Idan har muna so ya amince da auren zamu iya amfani da wann damar. Ina nufin zaka amince ya jagoranci aikin matuk a zai amince da Auren. Daga baya na tabbata zai so Yarinyar kuma zasu gina family tare. Zai tara hankalinsa waje guda. A yanda matsalar..

Bata kai aya ba ya katseta  A a dakata dakata Kwaise amma ba dani Aliyu Maitama za ayi wann shiriritar ba..

 Engr dan Allah ka min wann alfarmar a rayuwa.. Just this once..

Ya gyara zama sosai yana dubanta cikin rashin yarda  Seriously.. Wann ai hauka ne.. Kwaise a ina kika tab a jin anyi abu makamancin wann..? Are you asking me to put my company at risk here.?

Mommy ta silalo daga saman kujera ta duk a gaban Daddy saman gwiwoyinta. Ta shirya sadaukar da komai domin ta ceto ahalinta.

Cikin muryar kuka take furta  Zanyi ko menene Engr.. Zan duk a a gabanka na rok eka sabida inada yak inin Auren nan zai zama silan shiriyar Haidar da kuma kwanciyar hankalin ahalin nan cikin yardar Ubangiji..

Saurin d agota yai yana fad in  You don t need to do this Kwaise.

 A a ka kyaleni na duka gabanka idan har hakan zaisa ka amince da buk ata ta.

"Daddy ya soma girgiza kai  Kwaise, babu abinda zakiyi da zaisa na damu da d anki ko na damu da al amarin shi.. Kaman yanda ban d auke shi da mahimmanci ba haka ban d auki wann auren da kika dage sai kin masa da mahimmanci ba. Amma idan har haka kika zab a ki sani I won t get myself involved cikin nema ma d anki aure. Sai ya d auki wayarsa ya shiga dialing layin Haidar. Haidar yana d agawa Daddy ya sanar dashi yazo gida ya samesa yana jiransa."

Koda Haidar Ya k araso zaune ya taddasu a parlon. Iyayensa guda biyu. Yayi zaton magana zasuyi da Ya shafi Kasuwanci shida mahaifinsa tinda har wann ranar baice komai ba gameda proposal da Haidar ya kawo masa the other day. Har k uri a akai a company kan waye ya kamata ya jagoranci aikin wanda yake har kawo wann lokacin pending matter sabida shugaban kampani baiyi nasa zab en ba. Idan Har mahaifinsa a matsayin shugaba a Kampanin Ya zab esa ko shakka babu ya lashe k uri u mafi rinjaye. Idan har mahaifin nasa ya hau kujerar nak i dole haka yana Ji yana gani aikin ya tafi k ark ashin kulawar waninsa. Duk shirinsa na son ganin bayan mahaifinsa da Kampanin zai tashi a banza.

Like always he s not welcome. Ya bud e murya Ya gaishe su cikin rashin tabbacin za a amsa masa ko baza a amsa ba.

Daddy ya jinjina masa kai had ida nuna masa kujerar gefensa  Have a seat.

Ba musu ya k rasa ya zauna yana satan duban b angaren mahaifiyarsa dan a yanda Ya gansu jikinsa ya basa wani abun ake shiryawa akanshi. Ya jima da sanin su biyun tarayya suke wajen k untata ma rayuwarsa.

Daddy ya dubesa  Are you sure you can handle the project.?

Haidar yaji tambayar a bazata. Ya d ago yana duban mahaifin nasa. Maimakon ya basa amsa kai tsaye sai ya girgiza kai yace  Do you still have your doubts.?

Mommy ta tsaresu da idanu jin Daddy ya tambayi Haidar amma sai Haidar d in Ya amsa masa da tambaya. A cikin zuciyarta tace like father like son.

Daddy ya jinjina kai  The project is to be commenced in three months time. Idan har ka shirya kuma kana so kayi da gaske zan sauk a daga kujeran veto and give you and your team the green light& But on one condition.

Haidar ya dubesa da mamaki sai kuma ya dube mahaifiyarsa wacce tin shigowarsa ta kafesa da idanu. Ya maidoda dubansa ga mahaifinsa  What s your condition.?

Daddy ya dubi Mommy  Go ahead Kwaise. Tell your son the condition.

Mommy da idanunta Ke a k ek ashe kaman ba ita ce taci kuka a while ago ba tace  Sharad in shine Aure.. Zaka auri matar da muka zab a maka kuma ka zauna da ita matsayin matarka.!

Tamkar sauk an aradu haka Haidar yaji batun. Ya dubi mahaifiyarsa da tsananin mamaki Ya kuma dubi mahaifinsa. Lokaci guda yake girgiza kai alamun maganan tana kuma ringing cikin kwak walwarsa  Unbelievable.! This is unbelievable.. What is this.. Aure.. Sharad in Aure..? Mommy seriously..?! Ya k arashe yana duban mahaifiyarsa. Har lokacin ya kasa yarda.

Mommy ta jinina kai  Eh Haidar.. Aure shine sharad in idan har da gaske kana so ka jagoranci aikin..

Ya kuma juyowa yana duban mahaifinsa yana jiran ya k aryata amma sai yaji Shiru bai ce komai ba.

 Wann shine kiran.? Ya tambaya yana duban mahaifinsa.

 Abinda mahaifiyarka take so kenan. If it was to me kaima ka sani da yin aurenka da rashin yin Aurenka duk ba matsala ta bane. Talkless of wacece zaka aura.  Yar waye.? Daga ina take.? Duk wann ba matsala ta bane.

Meye yake ji kaman hawaye na neman cika idon shi.. Anya wad ann mutanen sune suka haifesa? Anya akwai iyayen da zasuyi ma d ansu mugun k iyayya irin wann.? Abinda yakeda mahimmanci a cikin ahalin kasuwancin ahalin ne kawai Wanda za a yi komai domin bunk asarta. Amma duk wani abinda ya shafi ahalin baida mahimmanci musamman ma shi in particular.

Muryar Mommy ya kuma katsesa  Idan an maka aure a yanda ka d auke mu nasan zaka iya cewa an d aura ma wofi ba lallai ka zauna da matar ba tinda yanzu ma ba ganinka muke ba. Wann dalili yasa muka zab i gindaya maka sharud a.

 Ki gyara zancenki Kwaise kika zab ar masa dai. Amma bani Aliyu Maitama ba. And one more thing.. I can t gamble my company away. Idan kuma har company na zai shiga ki sani naki AUREN ma zai shiga.

Mommy ta dubesa da tsananin mamaki  Aurena kuma Engr.. Mai hakan yake nufi..?

 Hakan yana nufin it will be the end of our marriage if things go wrong with my company.. Kuma wann fake family d in zai watse& Ina nufin babu sauran ahali.. So think carefully for the repercussions of what you are about to decide.!

Zuciyar Mommy yai wani irin bugawa kaman an sauk e mata guduma jin irin hukuncin da mijinta Ya yanke. Yayinda Haidar ke ci gaba da dubansu cikin tsananin mamaki.

Mommy ta nuna kanta tana duban Daddy  Kana so kace my marriage and the family that I spent years Ina iyaka k ok arin naga bai ruguje ba zai lalace..?

 Of course yes.! Mijinta ya bata amsa. Yaci gaba  So before you make your final decision sai ki tantance wanne ne yafi mahimmanci wajenki.. Auren D ank i ko naki Auren.!

Haidar yaci gaba da girgiza kai yana dubansu. This is unbelievable! Ya kasa aminta wad ann mutanen sune wai iyayensa. Ya tsaida idanunsa wanda suka rine zuwa ja kan Daddy  Really Daddy.. Is this what s like to be born into wealthy and influential family..? Everything is about business and making money..? Da gaske Daddy..? Shin ba wani abinda yakeda mahimmanci ne cikin ahalin..? Ya d an d aga murya wann karon  What are we to you..? Is that what you think of your family..? Like we are some sort of business ventures..?

Ya mik e tsaye jijiyoyinsa na kuma tashi yana duban duka iyayen nasa  Are we supposed to..

" Shut up! Mahaifinsa Ya katsesa kafin yaci gaba  Don t you dare raise your voice at me.. Da kai da rayuwarka babu guda da yakeda mahimmanci wajena. If I take your proposal into consideration, it s because your Mom insisted.. Now get out..! Get out of my sight.! "

Haidar yaci gaba da girgiza kai yana duban mahaifin nasa disbelievingly. A haka ya juya ya nufi k ofa a fusace zuciyarsa na masa mugun d aci.

Mommy ganin damarta na k arshe zai kufce mata Ya sanyata bin bayan Haidar a d ari tana k ok arin dakatar dashi.

Anisa ta mik e tana lek en window jin irin kiran da Mommy ke ma Haidar. Nan ta hangesu sun fito daga side d in Daddy. Haidar na tafe kaman zai kifa yayinda Mommy ke take masa baya.

Mommy ta rik esa sosai  Haidar don t do this.. Just listen to me.. Bazai yuwu ka rasa project d in nan ba..

Yai murmushi mai ciwo  Oh Shiyasa kika tareni ranan a nan.. Kike cewa ni da Ke zamu had a kai.. Wann shine had in kan naki da d anki.. C mon Mommy.. I always knew baki tab a yin abinda bazakiyi benefiting a ciki ba.. What I don t understand here shine Auren kike so nayi ko kuma dai wann project d in ne a ranki..?

Mommy ta jinjina kai  Both Haidar.. But my top priority is the project.. Idan har baka amince da auren ba bazai tab a baka project d in ba. Think about it Haidar you are his only son. Tilon magajin shi. bazan tab a bari wani Ya d auki place d inka a wann Kampanin ba.

Ya murmusa yana dubanta  Na sani to him I m his failed investment. And to you& Your weapon.. Rayuwana baida

wani amfani a wajenku..

Zai shige Mommy ta dakatar dashi da fad in  Three month marriage.. AUREN WATA UKU Haidar.. Project d in zai fara nan da watanni uku. Idan ya riga Ya d auraka akai ka riga ka fara aikin he can t cancel the agreement. Zaka iya rabuwa da yarinyar.. Ni dai kawai damuwata shine ya baka wann project d in..!

Yai Shiru yana duban Mommy. Watau akan abinda take so zata iya zuwa ko wani mataki. Ya matso sosai yana dubanta  Har haka kike son project d in Mommy..? Shin yakai ki saka naki Auren cikin had ari ma AUREN WATA UKU. Kawai dan ya bani wann project d in.?

Ya kuma girgiza kai  But Mommy this doesn t make any sense. Ke kikayi kid anki kikayi rawarki. Da kunnuwanki Kinji ya fad a. Idan a nasa ra ayin ne bai damu nayi Aure ba ko kar nayi. Duk ba matsalarsa bace. Kece kike son Auren kaman yanda yace.. Toh meyasa Auren Ya zama hujja.?

Mommy ta jinjina masa kai  I couldn t just sit back and watch you lose your chance. Na kula abinda yake so kenan. Koda bai fad a ba deep inside yana so kayi auren ne.. Kaima kasan ba don yana so kayi Auren ba bazai tab a saka Kampaninsa on the line ba. Kayi tunani Haidar we are talking about your Dad here.. Mutumin da zai iya bada rayuwarsa ma wann Kampanin. Rana tsaka dan ina so kayi Aure sai ya amince cewa ka jagoranci aikin.. Aikin da future na Kampanin Ya ta allak a akansa. Think Haidar. Wllhi da ace mahaifinka baison kayi wann aure bazai tab a yarda da sharad in ba. Mahaifinka yana sonka Haidar kawai bazai iya nuna maka bane ko kuma lokacin nuna maka d in ne bai ba..

 Well I don t give a damn..!Ya soni ko kar Ya soni.. Ban damu ba kuma bana ma so naga ranar da zai so ni..

 In that case ka yarda ka amince kai AUREN WATA UKU. A lokacin da zaka fara project d in sai ka rabu da matar ba tareda mahaifinka ya fahimci komai ba. Tinda dama Auren yake so kayi d in. Toh kayi a wuce wajen. Dan ka rabu da matarka bazai ce meyasa ka saketa ba. Since we all believe ana aure ana rabuwa. Sann bazai tab a yuwa A amshe aikin daga hannunka ba tinda abu ne base on agreement Wanda Ya k unshi saka hannu daga duka b angarorin.

"Shiru Haidar yai yana dubanta. Yasan mahaifiyarsa akan abinda take so. Sann shid in tamkar makaminta ne da take amfani dashi wajen kare kanta. Idan Har ya amince da wann Auren za a basa project d in and everything he s long been planning for zai samu damar aiwatar dasu. He can finally have the chance to ruin his Dad and his so called company. After all, the marriage is just for three months. Sann idan komai Ya wargaje auren iyayensa ma zai wargaje kowa zai kama gabansa a wann ahali da babu komai cikinsa face k unci da k arya. Zai d auki matarsa Dareen suyi nesa da wann ahalin Wanda basuda hurumin saninta ko rashin saninta because bai d auki ahalin matsayin ahali ba. Kaman yanda suma baida mahimanci a wajensu. Haka zalika

17 / 103