AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   85 / 103

252K to 255K   out of 306.8K words

Haidar.. Your Aunt is here.! Sai kawai yai bursting cikin kuka. Kuka sosai yake kaman k aramin yaro kukan da zata iya cewa bata tab a jin yai irinsa ba tun tasowarsa matsayinta na Uwar goyonsa.

Cikin rawar murya Asshe ke furta  Wann ba Zaki na bane.. Zakin da na raina baya kuka.. Na raini Jarumi.. Jarumin da ba a ganin rauninsa balle a gano lagnosa.! Tana maganar tana tuna yarintar sa sabida Sam baya kuka a yarinta sann ba wani abu da yake basa tsoro bayan wofantar dashi da iyayensa sukai a lokacin da Ya kamata su jasa jiki.

Saman wani kujera suka zauna ta dan waje. Haidar ya saka tafukan hannayensa ya share fuskarsa da ta rine ta koma jazir.

Cikin wane irin yanayi yake furta  When will all this end..? Yaushe ne komai zai wuce.? Meyasa rayuwa ta kasance haka..?!

Aunty Asshe ta jinjina masa kai  Wann sunnar rayuwa ce Haidar.. Jarabawa basu k arewa Har sai an bar gidan jarabawa wato duniya.!

Haidar yaci gaba da girgiza kai  Na kasa yarda.. Na kasa yarda da abinda ke faruwa.. Mutumin da nafi tsana a halin yanzu Ya zama D anuwana..! How is this possible Aunt.?! Ta ya zan kalli wann mutumin na kirashi da D anuwa..? Just how.?!

Cikin rashin fahimta Asshe ta girgiza kai  Wane D anuwa kake magana Haidar..? Meke faruwa.?

"Yaci gaba da jinjina Kai  Daddy yana can reuniting with his long lost son. Su d in Sun hadu da juna.. Daga k arshe dai, D a da mahaifin sunga juna.. I don t know how Mommy would take it.. Bansan ya iyaye na zasu d auka ba.. Amma abinda na sani shi ne wann mutumin bazai tab a zama D anuwana ba.! "

Muryar Mommy suka sinkayo tana fad in  D an uwa.. Wane D anuwa kake magana Haidar.?!

A tare Haidar da Aunty Asshe suka juyo suna duban Mommy.

SameenaAleeyou *AUREN WATA UKU..!*

*56*

*©þSameena Aleeyou& *

Haidar yai shiru yana duban Mommy. Ba huruminsa bane ya zamto mutum na farko da zai sanar da ita gameda al amarin. This is something for his Dad to decide. Kaman yayi shishigi ne idan Ya soma sanar da ita.

Mommy ta kuma jefo masa tambayar ganin yayi shiru ba amsa.

" Haidar, nace wane D anuwa kake magana.? "

Asshe ta dubi Mommy sai ta dubi Haidar. Sai ta d an murmusa kad an tace  D anuwansa Hilal dake makaranta yake

magana& 

Mommy dai kallonsu take bawai ta gamsu ba..

Wayar Haidar ce ta soma ruri. Daddy ne mai kira sai Ya mik e Ya dan matsa gefe yana amsa kiran Daddy yayinda Aunty Asshe ta k araso ga  yar Uwar nata jiki ba wani kwari dan har kawo lokacin ta kasa sakin jiki da Mommy kaman a baya.

Daga d aya b angaren Daddy yaci gaba  Kana jina Haidar.. Sadis yana hanya zai taho ya d aukeku kaida mahaifiyarka.. Ina so kuzo ku sameni a nan masauk i.

Haidar ya dan lumshe idonsa kadan Ya waresu yana duban Mommy dake zaune gefen Aunty Asshe tinda shidai yasan kwanan zancen. Bazai wuce kan Sabon D an Daddy bane da mahaifiyarsa. Sai Ya dan furzar da huci kad an yace  Ok Daddy.. Kaman yanda kace.

Yana ida wayan Ya dawo yanda ya baro su Mommy.

A tare suke dubansa itada Aunty Asshe. Sai gani sukai ya duk a gaban Mommy daga nan yanda take zaune saman kujera. Jikin Mommy ya kuma yin sanyi da al amarin Haidar. Hannayenta ya kamo cikin nasa yana dubata. Lokaci guda yake furta  You are the most precious to Me Mommy.. And.. Whatever happene know that I m here for you.. And I got your back. Ya jinjina Kansa kad an kafin ya k arada  I love you Mommy. So much.

Har lokacin jiki a sanyaye Mommy ke dubansa musamman da taji ya matse hannun nata sosai cikin nasa sanda yake maganan.

Ta jinjina masa kai a hankali tana jin k walla na ciko idonta.  Nima Ina sonka D ana.. Ina matuk ar k aunarka.!

Ya murmusa kad an had ida mik ewa tsaye. Aunty Asshe ma murmushin tai cikeda farin ciki. Ta goge hawayen da suka gangaro mata ta mik e tana fad in zata shiga ciki taga jariri sabon angonsu.

Bayan ta shige Haidar Ya rik o hannun Mommy suna tafe sanda yaga isowar Sadis. Suka nufi motar hannunta na sakale cikin nasa. Ita dai Mommy bata san ina ake zuwa ba sai ji tai Haidar na fad in  Mommy akwai yanda zamuje

yanzu.. Daddy yana can yana jiranmu.. Ina so Ki kwantar da hankalinki.. Kuma ki sani ina tare dake. Ya k arashe yana bud e mata owners corner.

Duban Haidar kurum take ba tareda ta iya furta koda kalma ba sai k irjinta dake tsananta bugu ba tareda sanin dalili ba. Tana gani ya bud e front Seat Ya shige yace da Sadis suje.

Sadis yaja mota suka fara tafiya. Tinda suka soma tafiya saman kwalta Mommy bata iya cewa komai ba. Har kawo bud e musu wani tampatsetsen gate da akai. Suka shige cikin tsantsararren Villa Suite d in Sadis Ya nemi waje yai parking.

Haidar ne Ya bud e ma Mommy k ofan motar. Tai zaune daga cikin motar tana dubansa  Haidar.. What is this place..? Ina muka zo.. Wajen wa muka zo.?

Sai Ya murmusa  Mommy masauk inku da Daddy muka zo.. Daddy yana ciki yana jiranki.

 Amma.. Ummul da Jikana suna can asibiti.. Bai kamata mu taho mu barosu ba.

Ya jinjina Kansa a hankali yana kamo hannunta  Kar ki damu Mommy zamuje mu d auko su.. But for now.. Daddy needs to see you first. Let s go. Ya k arashe yana kamo hannunta suka nufi building d in.

Tamkar rak umi da akala haka Mommy ke biyeda Haidar Har suka isa k ofan parlorn.

Daddy ne zaune daga saman kujera dake daga centre& Hajja Fannah tana daga can gefe yayinda Hisham ke zaune

daga saman carpet gefen k afafun Daddy kansa kife kaman mutumin arziki.

Sosai Haidar Ya rik e hannun mahaifiyarsa cikin nasa idonsa kan Daddy Sam bai kula da Hisham dake zaune daga gefe ba.

Zuciyar Mommy yaci gaba da bugawa sanda suke shiga cikin parlorn musamman da ta hangi Hisham abokin Haidar wanda D anta Ya aminta dashi Ya kuma ci amanarsa.

Sai Mommy ta soma girgiza kai tana nuna Hisham  Haidar mai wann criminal d in yake a nan. He should be arrested. He supposed to be in jail.. Dashi da Anisa Sun had e kai sunyi yunk urin kasheku kaida Ummul.. Ta dubi Daddy  Engr mai wann azzalumin da Ya kusa halaka mana D anmu da iyalinsa yake a nan.?

Daddy ya mik e da sauri Ya nufota  Calm down Kwaise.. That s exactly why I asked Haidar to bring you here..

"Hannayen Mommy Daddy ya kamo yai k ok arin zaunarta saman kujerar dake fuskantar Wanda Hajja Fannah take. Idon Hajja Fannah akansu har Daddy yai masauk i ma matarsa saman kujera, sai Hajja Fannah ta sauk e idanunta k asa a hankali tana mai kifa kanta."

Sam Mommy bata kula da matar dake zaune daga kujera mai fuskantar nata ba idanunta naga Hisham tana fad in saidai a kira yansanda su tafi dashi. Daddy ya kamo hannayenta cikin k ok arin calming dinta  Kwaise ki natsu ki saurareni..!

Sai Mommy tai shiru tana dubansa.

Daddy yaci gaba  Akwai abubuwa da dama da Ya kamata ki sani harma da Haidar. Ya dan numfasa kafin yaci gaba

 Kin tuna Fannah..? Ina nufin tsohuwar Matata Fannah.?

Sai jikin Mommy ya kuma yin sanyi. Ta soma jinjina kai a hankali  Matarka Fannah da nai ajalin Aurenku a tsakanin watanni Uku tak.! Matarka da na koreta da jaririn cikin wata uku sabida son zuciya.! Muryarta yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata yayinda Hisham ke mata wani irin duba na tsana daga nan yanda yake zaune gumi na karyo masa kaman ba AC bane cikin parlorn. Yau dai da kumnuwarsa yake jin Kwaise Maitama tana amo laifukan da ta aikata masa shida mahaifiyarsa.

Mommy taci gaba sanda ta kamo hannayen Daddy sosai cikin nata  Engr da ita nake kwana da ita nake tashi.. Banida burin da ya wuce na ganta na kuma nemi yafiyarta.! Ta k arashe cikin kuka yayinda Hajja Fannah taci gaba da zubda hawaye daga can yanda take zaune saman kujera.

Daddy ma hawaye ne ya digo masa sanda yake jinjina kai yana duban Mommy  She s here Kwaise.. She s right here with us.. Fannah is here with us.. Ba ita kawai ba.. Harda wann jaririn cikin nata da ta fita dashi.!

Dumm! Haka k irjin Mommy ya buga. Ta d ago gajiyayyun idanunta tana duban Daddy dasu  Fannah..! Fannah da D anta suna nan a nan..?! Ta tambaya cikin rawar murya.

Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana karkatar da fuskarsa b angaren da Hajja take.

Cikin wane irin yanayi Mommy ke kaikaitowa tana duban yanda taga Daddy na duba. Cak ta mik e tsaye tana dubanta  Fann.. Fannah..! Ta furta a hankali still tana dubanta.

Sai Hajja ta d ago idonta mai zuban hawaye tana duban Mommy.

A hankali Mommy ta soma takawa har ta isa ga Fannah. Ta zuba mata ido tana kallonta. Sai ga Mommy na k ok arin duk awa gaban kujeran da Hajja Fannah take. Bata bari Mommy ta duk a ba itama ta sauk o daga saman kujeran.

Su duka biyu suna durkushe gaban juna. Mommy ta kai hannayenta masu shaking ta d aura saman na Hajja Fannah.

Daddy ya dubi Haidar da Hisham yace su taho tareda shi. Haidar yakai ma Hisham wani irin duba kaman bazai bi bayan Daddyn ba sai kuma yasa kai yabi bayan mahaifin nasa.

Parlorn Ya rage saura Hajja da Mommy. Sosai suke kuka su duka biyun an rasa mai bama wani baki.

Saida sukai ma isar su kafin Mommy ta iya bud e baki ta soma sanar da Hajja Fannah irin nemanta da tai sanda bata nan. Da irin nadaman da Tai bayan abinda ta mata sai kuma ta soma neman gafaran Fannah d in.

Hajja Fannah ta girgiza kai tana hawaye  Ta Ya zan iya yafe Miki bayan kin so ki maimaita tarihin abinda kika min akan Matar D anki Ummulkhair? Yarinyar da kika so hallak ata ta hanyar sihiri dan ki ceto naki D an.! Ta k arashe hawaye naci gaba da ganganci mata.

Saurin girgiza kai Mommy take tana hawaye  Kafin na gane kuskure na.. Kafin nayi tuba na gaskiya. Kuka ya hanata ci gaba da magana. Tai k ok arin nitsa kanta kafin ta dubi Hajja tace  Zan karanto Miki komai.. Irin zaman da na fuskanta nida D ana a gidan Engr Aliyu Maitama bayan tafiyarki da jaririn cikinki.. Shigowar Ummulkhair cikin rayuwarmu da yanda Allah Ya sauya al amarin ahalinmu bayan mun zab i mubi turba mik akk iya.. Nasan idan kikaji komai Watak ila ki Sami gurbi cikin zuciyarki ki yafe min Fannah.!

Taryan taryan Mommy ta soma karanto mata abubuwan da suka faru tin bayan barinta gidan.

**

A can d aya parlorn kuwa Daddy ne zaune daga saman kujera yaran nasa guda biyu suna daga saman carpet ko wanne yana daga nashi angle din. Kan Hisham a kife cikeda ladabi ya risina gaban Daddy ko iya d ago ido ya dubi Daddy cikin ido bayayi yayinda Haidar ke ci gaba da aika masa kallon k yama da tsana. Da kyar ma Haidar d in ya amince ya zauna a parlorn saida Daddy yai da gaske dan cewa yai bazai iya jure zama Inuwa guda da betrayer irin Hisham ba Wanda ko fuskarsa baya k aunar Ya sake gani balle Ya sauraresa.

Cikin dacin rai Haidar yaci gaba da nuna Hisham yana fad in  Everything make sense now Daddy. Wann azzalumin ya rab i ahalinmu ne domin Ya tarwatsa mu. Sai Ya fara da company kafin ya gangaro kan Matata Shiyasa yai amfani da shashancin Anisa ta zamto mataimakiyarsa. Everything is clear now.. There s nothing like coincidence.. Ya riga ya jima da shirya komai Daddy.!

Cikin wane irin yanayi Hisham ke girgiza kai yana duban Haidar  I can t believe you Haidar.! Na kasa yarda zaka tafi da nisa Har haka. Throwing such acquisitions on me.. Haidar we ve been friends for quite some time now.. Ka sanni kasan abubuwan da zanyi da Wanda bazanyi ba.! Ta Ya zansan ku ahalina ne sann na zab i cutar daku.?

Ya waigo yana duban Daddy  Duk Wanda Ya sanni tareda Haidar yasan irin soyayyar da nake masa matsayin aboki Wanda Har ya zarce abota. mun koma tamkar yan uwa.!

 Shut up.! Kar ka sake kirana Danuwanka.. Kuma ka saka a ranka sai na sa ka biya duka abubuwan da ka aikata.! Haidar Ya dakatar dashi.

Daddy dake shafe goshinsa mik ewa yai tsakiyan su biyun  Enough.! Ya isheku haka.!

Ya dubi Haidar  Ka daina cewa D anuwanka yanada wani laifi a company dan Bakada wani proof akai.!

Cikin tsananin shock Haidar ke duban Daddy. Ya girgiza Kai kad an  Seriously Daddy.! Are you taking his side now.?

 Bana d aukan b angaren d aya cikin ku biyun.. K ok ari nake a samo maslaha. Daddy ya fad i haka a dan zafafe.

Haidar yaci gaba da girgiza kai cikin rashin yarda yana duban Daddy  The only solution here& Is for this snake to

pay for all he s done.!

"Hisham ya katsesa  I didn t commit any crime Haidar. On the contrary, ni taimakon ka kawai nake but you re blinded by your anger..! "

Cikin huci Haidar ke fad in  Ban buk aci taimako daga wajen wani ba.. And Much less from you..! Yaci gaba da jinjina Kai yana huci  Ka yarda dani zaka biya duk abubuwan da ka aikata.. You mark my words.

 Haidar.! Daddy ya daka masa tsawa kafin yaci gaba  Idan k ara akan Company na ne.. Na janye.. And I expect you to do the same.!

Cikin tsananin mamaki Haidar ke duban Daddy. Cikin rashin yarda yake girgiza kai  Seriously Daddy. Are you going to trust this traitor sama da D an daka rayu dashi tsawon rayuwarsa.? Daddy Anisa tana can a tsare kuma tayi confessing cewa tare suka aikata duka laifukan da ake tuhumar ta dasu& Daddy Anisa tayi rabin girmanta a gidanka koda ace baka shiga al amran gidan a baya amma kasan Anisa a matsayin  ya somehow.. Daddy Anisa might be stupid but I m very sure she couldn t have planned to kill someone ba tareda taimakon wani Wanda Ya fita wayo ba& Daddy this coward here amfani kawai yai da Anisa ya juya mata baya.!

 And this is where you are wrong.! Because you refuse to listen to him. You refuse to hear his side of the story.. Abinda Anisa Tai confessing kawai ka dauk a.. Mai Anisa da k awarta sukai confessing Haidar.? Cewa sukai su biyun Sun saka ma Ummulkhair guba cikin turare haka ne.? I don t remember her mentioning my Son s name cikin bayananta.!

Haidar yaci gaba da duban Daddy kurum yana girgiza kai cikin rashin yarda yayinda Hisham yaci gaba  Daddy zan fi so a tafi can. Gani gashi ga Anisa a warware komai..!

"Ya juyo yana duban Haidar cikin yanayi na ban tausayi  Haidar, I know we grow up quite a bit differently.. Ka girma with both your parents around you.. Ina nufin mahaifi da mahaifiya tareda kai. Ka girma cikin asali.. Amma ni kuma a nawa b angaren, is the other way around.. Na girma ban san mahaifina ba balle danginsa.. Fatherless Son..! Wasu suna kirana D an mace.. Wasu Har ce mun suke banida mahaifi banida asali.. I spent my entire life searching for people who would accept me. Yanda yake maganar dole ya raunana maka zuciya."

Tausayin Hisham Ya cika Zuciyar Daddy da jin irin kalubale na rayuwa da Ya fuskanta.. Sai yana jin duka laifinsa ne. Muryar Hisham Ya kuma sinkayowa sanda yaci gaba  Na fuskanci k iyayya.. Kyama daga wajen wasu mutanen na nemi aurarraki an hana ni duka sabida laifin da ban san dashi ba amma haka baisa na zab i zama mutumin banza ba..

85 / 103