AUREN WATA UKU by Sameena Aleeyou

Author :  Sameena Aleeyou Category :  KDP NOVELS

Chapter   72 / 103

213K to 216K   out of 306.8K words

dan ki raba namu Auren bazai dore ba bazai je ko ina ba domin kuwa an gina auren ne bisa zalunci.. Dan kawai a raba masoya guda biyu. Ina nufin ni da masoyi na Haidar.. Taci gaba da murmushi  And now more than ever Aurenmu da Haidar bazai tab a mutuwa ba Kinsan dalili Mommy.? "

Zukata sukaci gaba da bugawa. Mamaki da al ajabi yaci gaba da bayyana tsakanin fuskoki. Yayinda video d in Dareen yaci gaba  I am pregnant.! I am three months pregnant.. I am carrying your grandchild Hajiya Kwaise.. Your son s child. Ina d aukeda juna biyun Haidar har na tsawon Watanni uku.!

"Ba Haidar da yai mutuwar zaune yana duban Screen din ba, ba Ummul wacce ta koma tamkar mutum mutumi tana kallon abinda ke faruwa tamkar ba zahiri ba baga Mommy da ta koma tamkar hoto a wajen.. Baga su Tani da suka maida kawunansu k anun alhaki ba sakamakon ganin abinda ke wanzuwa kan idonsu. Kai duk wani mahaluk i dake wajen Daskarewa yai yana kallon ikon Allah.."

"Dareen taci gaba da murmushi cikin video d in  Haidar my love.. I am carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. You are going to be a father my love.. Zamu zama iyaye.. Ba haka naso na sanar dakai ba sai dan naga an shiga tsakaninmu da yawa.. Na sani this is going to affect your family business somehow.. But believe me, I didn t mean to jeopardize your business.. Please forgive me my love. D iff screen din ya d auke."

A daidai lokacin Anisa ta k araso ta tadda wann babban shiri da Hisham yai. Cak Anisa ta tsaya tana sakin murmushi tareda jinjina ma shed anancin Hisham.

Asshe ta mik e a firgice ta nufi yanda MC da sauran masu kula da event suke tana fad in  What s this.. What s the meaning of this.. Who s in charge of the event.. Wai meke faruwa ne.. Ya akai haka ta kasance..?

Kowa yace bai san Ya akai aka sabotaging event din ba. Baga securities ba baga MC s da sauransu ba.

"Anisa ta saki murmushi sanda ta hangi Azeema. Ta shiga shafa b arin fuskarta yanda shatin yatsun Azeema suka bayyana sakamakon marin da ta mata. A zuciyarta tace  Baki mari banza ba. Zan nuna miki barikin gaske.. Anisa nake, I always get what I want. Ta kuma murmusawa. Lallai dole tayi amfani da wann damar. Sai ta k araso tana kuka tana rik e Mommy tana fad in  Mommy ni ce wacce ta kamata tai coordinating komai a wajen nan kaman yanda kika amince mun, amma wancan munafukar ta kulleni a gida sai yanzu na samu na k araso.. Ma aikatan dake cen gida sune shaiduna.. Mommy I m sure bakinta d aya da duk Wanda sukai sabotaging event din nan.. Ita ta taimaka musu ta rufeni a d aki dan su samu saukin executing plan dinsu. Mommy ki yarda dani da shirinsu suka taho wajen nan. Tai maganar tana nuni da Azeema."

"Duk jijjiga Mommy da Anisa take Mommy bata iya cewa komai ta koma tamkar hoto, ko motsi k akk wara bata kuma yi ba tin bayan da Dareen ta bayyana cikin wann faifayin. Sai kawai AnisaTa tafi aguje zata shak o Azeema tana fad in she s working with the people that sabotage the event. Ta shiga kiran securities tana fad in su kama Azeema ita zata fad i wad anda take ma aiki wad anda suka sakata ta kulleta a d aki sabida kar ta samu damar halarta wajen event din."

"Haba nan fah Azeema ta shiga kururwa tana fad in ita wllhi bata san komai ba bata san kowa, sann bata aiki ma kowa. Mama Tani ganin securities sunyo kan  yarta ta nufesu cikin k ok arin k watan  yarta tana fad in su rufa mata asiri kar su kulle mata  ya ta d and ani zaman gidan yari bazata so wani nata ya kuma d and ana ba. Gaba d aya taro ya yamutse ya hargitse ya rikice."

"Kasa komai Haidar yai har lokacin idonsa na kan screen d in dikda ya d auke. Har lokacin Dareen yake hangowa cikin screen d in. Wacce rabonsa da ita tin ranar da suka samu had arin mota shida Ummul, exactly two months back kenan.. Kalmarta na cewa tana d aukeda Juna biyu shine yaci gaba da duka dodon kunnensa."

Wajen taro ya yamutse ya watse. Masu tsegumi nayi masu nad an rahoto nayi domin kuwa abun nema ne ya samu.

Asshe ce ta janyo Mommy wacce har lokacin bata komo daidai ba duniyarta na nema juya mata sama ya koma k asa. A daidai lokacin Umma da Inna Dije suka take masu baya.

Can wani k aramin lambu na shak atawa dake daga cikin gidan ta baya kad an Asshe ta k arasa da  yaruwarta tana k ok arin zaunar da ita Umma ta k araso ta rik o hannun Asshe tana kuka  Ina zakuje.. Ina zaku gudu kuje ba tareda kun sanar dani makomar Auren D anku da  Yata ba.?!

Sai Mommy ta d ago tana duban Umma dukansu biyu hawaye ne saman fuskokin su.

Daga can nesa Anisa ke hango su kawai sai ta saki murmushi ta koma da baya.

A can wajen taro kuwa Mik ewa Ummul tai ba tareda tasan ina take jefa k afafunta ba. Caraf Anisa tasha gabanta. Ta dan girgiza Kai kad an tana duban Ummul d in  This is life of the rich.. Surrounded by scandals.! Ta d ago gajiyayyun idanunta tana duban Anisa. Sai Anisa daketa k ok arin k wak ulo hawaye ta isa ta rungume Ummul. Ta fashe da kuka tana fad in  I m here for you Ummul.. I m here for you. Ciwon  ya mace na d iya mace ne.

"Ummul bata motsa ba sann batace komai ba sann babu wani abu mai alamun kuka ko hawaye cikin idonta. Idanun ne kawai a bud e amma ita kanta bata san wace duniya take ciki ba. Anisa ta dubeta tace  Ummul mu bar maganan scandal din da matar Haidar tayi.. Na fad a Miki, rana irin wann nake tsoron zuwanta.. Su d in Sun jima suna b oye abubuwa.. Taho muje.. Muje.. Ki gani da idonki ki kuma ji da kunnuwanki.. B oye b oye ya k are. Ta k arashe tana janyo hannun Ummul wacce har lokacin bata um bata um um. Tafiya kurum take Anisa na janyota. Anisa ta kauda fuska gefe tana wata muguwar murmushi Wanda idan ba ita Anisar ba ko wanda suke shirya abubuwa tare ba lallai wani ya fahimta ba. Daga can gefe da yanda su Umma, Mommy, Asshe da kuma Inna Dije suke suka ja suka tsaya."

Umma taci gaba da girgiza Kai tana fad in  Ba haka mukayi dake ba Asshe.. K warai nasan yau ne wa adin Auren zai cika Shiyasa da kuka shirya biki jiki na ya bani bikin mutuwar Auren kuka shirya..! Wacece wancan matar kuma meyasa kukayi ma D anku AUREN WATA UKU da d iyata? shin kunyi masa Auren domin mahaifinsa ya basa wani kwangila wajen aiki ne. Ko kuma dai Kun masa AUREN WATA UKU da d iyata dan ku raba Aurensa da wancan matar tasa ce.?

Mommy taci gaba da girgiza Kai tana hawaye.

Yayinda Inna Dije ta k yalla ido ta hango su Ummul sai ta dubi Umma ta fara fad in  Kar kiyi wani dramarki na k arya a nan Suwaiba. Kowa ya kwana da sanin zakiyi fin haka idan Akan Auren da kika kudiri niyyan yima Ummul ne..! Taci gaba da huci  Kina so ki ce mun ba da hannuwanki kika saida musu Ummul ba.? Kina so kice kin mance tsananin son da kike Ummul tai aure ko ta halin k ak a zaki iya jefata cikin ko wani irin Masifa da sunan Aure.! Suwaiba harta  yarki Ummul tasan zaki iya mata ko wani irin Aure matuk a zatayi Aure ta bar gabanki..! Ta shiga nuna Asshe tana fad in  Wann matar ta sanar Dani komai Suwaiba.. Ta sanar Dani yanda kika wulak anta d iyar D anuwana kika saida musu ita dan a karya asirin da wancan shed aniyar matar D an nasu ta masa.! Ta sanar Dani yanda kika basu Auren Ummul domin ta zamto makarin asiri.! Ta sanar Dani cewa Boka shine ya basu lak anin cewa su nemo ma D ansu mace mai irin matsalar Ummulkhairi wacce maza ke guje ma Aurenta. Irin wann budurwar ita ce irin macen da za a karya asirin da akai ma D ansu da ita.. Ta sanar Dani yanda idonki ya rufe kikayi ma Ummul AUREN WATA UKU.. Auren mutuwa..!

Baki na rawa Umma ke girgiza Kai  Auren mutuwa kuma Dije.?

Inna Dije ta d aga mata hannu alamun dakatarwa  Har haka kika tsani Ummul Suwaiba..! D anuwana yana kwance yana jinya kika d auki Ummulkhairi kika saidata dan ta zamto makarin asiri kamar yanda Boka ya fad a ajalin Auren na tareda ajalin Ummul cikin watanni uku. Kaman yanda Auren D ansu da wancan shed aniyar zai Mutu haka Ummul zata Mutu tare da wancan Auren.!

Sai Umma ta d ago cikin tsananin daburcewa Jin Dije tana zayyano kalaman da batasan dasu ba dan a nata iya sanin Auren kwangila sukayi ma Ummul da D ansu wanda Auren zai faru ne kawai na tsawon watanni uku dan mahaifinsa ya basa kwangila. Umma taci gaba da girgiza Kai bakinta ya kasa furta koda kalma.

Mommy da hawaye suka wanke mata fuska sai ta soma girgiza kai. Murya na tsananin rawa take furta  Wann duk haka ne kafin mu gyara niyyarmu.. Bayan da muka fahimci Allah shi keyi ba Boka ba. Wllhi tuni mun mance wancan shirin namu kuma Aure na tsakani da Allah nake fata da burin Haidar yayi da Ummul. Ita d in Alkhairi ce ga ahalina.

Anisa ta juyo ta dubi Ummul wacce har lokacin ko motsi batayi sai kallon Ummanta da Mommy da take ga wasu hawaye suna sauk owa zuwa k uncinta ba tareda ta iya koda k ifta ido ba.

 Yau kin yarda dani Ummul.. Bayan tsawon lokacin da na d iba ina k ok arin fahimtar dake soyayyar bogi da Mommy ta jima tana nuna miki.? Matar nan  Yaruwar Mahaifiyata ce nasansu farin sani na kuma san zasu tafi da nisa koda zasu kashe rai ne dan su samu biyan buk atansu.. Na fad a miki idan ranan tazo zaki yarda ni kad ai ce na zauna dake bisa zallan gaskiya a cikin gidan.

Bata kuma tsayawa sauraron Anisa ba. A hankali ta soma takawa zuwa yanda suke duk sai suka juyo suna dubanta. Kai tsaye gaban mahaifiyarta ta tafi ta tsaya.

Umma ta d ago idonta mai zuban ruwa tana duban Ummul tana girgiza Kai.

Har lokacin idon Ummul Akan Umma  Wann shine dalilin ki Umma..? Wann shine dalilin da.. Yasa.. Kika hana na waiwayi gida sai bayan Watanni uku..? Haka ne Umma.? Muryarta yaci gaba da rawa . Yayinda Umma taci gaba da girgiza kai tana hawaye tamkar wacce aka d aure harshenta.

Duk sunyi shiru sai zuban hawaye. Mommy ma ta kasa tsaida nata hawayen.

Ummul taci gaba  Na kasance inada kurakurai na amma ba ni na zab i k addarata ba.. Muryarta yaci gaba da rawa  Umma nayi k ok arin na kasance  ya mai biyayya a gareki.. koda a wasu lokutan Babu Wanda zai fahimceki nakanyi k ok arin na fahimceki.. Sabida ke d in mahaifiyata ce.. Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye  Duka rayuwana k ok ari nake naga na faranta ma mutanen dake kewaye dani.. koda hakan na nufin na mance kaina.. Na kasance banida wani fata nawa.. Taci gaba da girgiza Kai  Auren karya sihiri..! Auren mutuwa..! Auren wata uku..! Sai ta soma girgiza kai sosai  Ki gafarceni Umma.. Ki gafarceni..!

Umma tai yunk urin bin bayanta amma inaa ta wuce cikin gidan a guje tana kuka sosai.

Mommy tai saurin rik o Umma tana fad in ta kyaleta abi komai a sannu.

Ummul shiga cikin gidan kawai take ba tareda sanin ina take zuwa ba har saida ta isa wani bedroom.. Tana shigewa ta maida k ofan ta rufe ta silale nan wajen tana mai fashewa da wani irin kuka. Sam bata kula da Haidar dake zaune shattered k asa a d akin ba. K afafuwansa mik e a k asa ga babbar rigarsa a gefe.

Sosai take kuka tana girgiza Addu a take cikin zuciyarta Allah yasa mafarki take. Allah yasa zata farka daga wann mummunar mafarkin.. Mahaifyarta.. Ashe har mahaifya zata iya jefa  yarda ta haifa cikin irin auren da ta jefata.. Shin har haka Umma take so ta bar cikin rayuwarta.? Umma ta mik ata ayi tsafi da ita.! Sai ta rintse idonta sosai tana jin wani irin tashin hankalin da bata tab a tsintar kanta ciki ba. A haka Haidar Ya rarrafo gareta. Duk a tunaninsa maganganun da Dareen tayi ne Ya jefa Ummul cikin wann yanayi baisan idan maganganun Dareen Ya jefata cikin rud ani da firgici bai kama k afan abinda taji mahaifiyarta ta aikata mata ba.

Haidar ya shigar da ita cikin jikinsa tana kuka shid inma k ok ari ne kawai. Sosai Ya matseta cikin jikinsa yana fad in  Let it all out.. Na cancani duk hukuncin da kika mun amma kafin ki hukuntani.. Zan so ki saurareni.. Hear me out first please..!

Tana nan cikin jikinsa su duka biyun suna zaune k asa. Saida tayi mai isarta kafin ta soma furtawa a fili  Labarin duka k arya ne.. Babu wani gaskiya cikinsa...

Haidar Ya kuma matseta cikin jikinsa  Akwai abu d aya da yake gaskiya cikin labarin.. Shine soyayyarmu.. The love that I have for you Khairy.. I.. I love you.. I love you with everything I am..

Jin kalaman take har k wak walwarta. Ta cire jikinta daga nasa tana dubansa. Sai ta girgiza kai  Shin kana sane da cewa AUREN WATA UKU suka mana.?

Haidar da baisan da batun warware sihiri ba. Saidai yanada masaniyar AUREN WATA UKU na yarjejeniyar project da sukai da Mommy. Sai Ya soma k ok arin kauda fuskarsa kaman yana avoiding kallon idon Ummul d in.

Mamaki Ya cika Ummul. Ta dan girgiza kai kad an  Kasan da labarin AUREN WATA UKU.?

Sai Ya lumshe idonsa a hankali Ya shiga jinjina kansa alamun haka ne.

Kawai Ummul sai ta soma girgiza kai tana ja baya gareshi.. Tsoro ne firgici ne ta ma rasa mai takeji..

Haidar ya soma girgiza kai cikin kid emewa yana k ok arin nufota  But you need to listen to me first Khairy..

Dakatar dashi Tai ta hanyar d ago masa hannu. Muryarta na tsananin rawa  Kar ka masto yanda nake.. Kar ka k araso yanda nake.. Gaskiya ne.. Cikin labarin gaba d aya ni kad ai aka shashantar..!

Haidar bai fasa nufota ba yake fad in  Khairy please listen to me.. Please hear me out first.. Allah shine shaida na.. Nayi niyyar sanar dake komai yau d in nan.. Ciki harda Aurena da Dareen da kuma yanda namu Auren Ya kasance.. Dan Allah ki saurareni.. Na sani ni mai laifi ne.. But ki saurareni first.

Jikinta Har rawa yake bata daina k ok arin dakatar dashi da hannunta ba  Kar ka k araso yanda nake.. Bakada sauran abinda zaka sanar dani dan naji komai.. Auren.. Ya cika watanni uku a yau d in nan& Ya cika wa adinsa.. Ba abinda yai saura.. Lokaci yayi da zamu fice daga rayuwar juna. Ta k arashe tana k ok arin mik ewa ta isa k ofa.

Haidar ya tafi da sauri yai ma k ofar lock. Yaja Ya tsaya.

Huci take tana dubansa shima d in huci yake yana dubanta.

 Ka bud e min k ofa na fice ni ba matarka bace dan wa adin Auren Ya cika.. Ko baka gani bane.!

 Ank i a bud e d in baza a bud e ba.. Nace ki saurareni first kafin ki yanke duk wani hukunci.. And one more thing.! Kar ki sake cewa ke ba matata bace.!

Taci gaba da huci zuciyarta na mata rad ad i tasa hannu zata bud e k ofan Haidar Ya cire d an makullin Ya jefa bayan gado.

Ummul ta d ago tana dubansa cikin wane irin yanayi da bai tab a ganinta ciki ba  Ka bud e mun k ofa na fice..!

 Baza a bud e ba.! Ank i a bud e d in.. Na ce ki saurareni muyi

72 / 103